Follow us on social media

Showing 96001 words to 99000 words out of 140751 words

Chapter 33 - Alaƙar Zuci Complete Hausa Novel by Mai Dambu

29 May 2026

300

da Aunty Nuratu Kafaya ya dawo min daga lokacin da kike tsaya da kafarki a lokacin kowa zai soki."" Murmushi nayi haka suka ci abinci, sannan suka shiga ciki suka yi wanka da hutawa la'asar tana yi muka shirya bakiWaya zuwa Asibitin, tunda Rufa'i ya ganni ya rike baki. "" Adamu yarinyar nan sakata kuka yi a injin amma? Ke Lubnah gaya min wanke ki aka yi a injin ko?"" Dama can na san halins sai haka bai wani dame ni ba, haka muka yi ta hira na leka Abba yana barci. "" Shi barci kullum yake yi ne?"" Murmushi tayi tana faWin. "" Eh yana farkawa har ya ci abinci ma, tow jininsa da yake yawan sauka ake son a iya sarrafa shi."" ""Allah ya bashi lafiya!"" Kuka sai na fara kuka idan har wani abu ya sami Abba bai saka min albarka a rayuwata ba, ba zan yi kyakyawar karshe ba. Kukan da nake yi ne ya dami Mama ta ja hannuna muka fita. Kusan yadda abin ya tashi hankalina. ""Tow meye na kuka?"" ""Mama idan Abba bai yafe min ba, rayuwata zata lalace domin ina jin a raina ni ce sanadin wannan ciwon nashi."" Kura min idanun tayi tana jin wani irin abu a ranta. ""Wani ya zarge ki da cewa ke ce sillar ciwonsa ne?"" Cikin shashekar kuka na bude baki xan yi magana tura min kwakwa tayi a bakina. ""Ya isa haka, ba ke ce sanadin ciwonsa ba haka kuma ba zaki tab'a zama sanadin wani ba, ina da yakinin cewa Ubangiji ya amsa min addu'ata akanki, don haka ki daina kuka akan abinda baki da ikon sawa ko hanawa, kada ki manta Mamanki tana tare da ke a kodayaushe, kofata a bude take."" Haka tauna kwakwan da nake ya hana ni kuka, Mama tana sona sama da baya Mama tana kokarin bada har Rayuwarta domin ni.. ""shekaranjiya nayi mafarkin wani kyakkyawan bafulatani ya dauke min ke."" Ta fada tana murmushi, kallonta nayi sai kuma na tura baki nace mata.""Mama dauke ni fa!"" ""Eh amma na gaya mishi idan ya saka ki kuka ba xan yarda ba, idan ya saka ki damuwa ba xan yarda ba, idan ya sake wani abu ya same ki ba zan yarda ba, domin na hango shi cikin kuraye da macizai ne, sai dai ina ji a jikina shi jarumi ne domin shi Waya rike da sanda ya rike hannunki har wani kyakkyawar gida, kin ga kenan idan ba jarumi ba, babu wanda zai iya ratsa waWannan halittun ya wuce lafiya lau. Da haka nake jin a jikina Ubangiji ya amshi addu'ata ya kuma ajiye ta zuwa"

"lokacin da zai biya min ita."" Yake nayi mata domin naga Mama ita fa tayi nisa a kaina,Aqur'an bata jin"

"kira. A hankali ta riko hannuna ta zaunar da ni a kujeran da yake gaban wata office. ""Kin san yadda nake"

"son ki yi farin ciki kuwa? Kaf duniya babu wanda ya kai ni son ki yi farin ciki, sai dai abu daya zan gaya miki daga yau kada ki kara zama wani ya wulakanta ki, kada ki kuma cutar da kanki saboda zaa ce kina yawon aure kada ki damu ban kuma ce ki rena duk wanda zai zo rayuwarki da sunan aure ba, amma kuma kada ki rena kanki."" Kwantar da kaina anyi a kafadar Mama ina jin wani irin nutsuwa na shiga ita uwa duniya ce ga Yaranta, baya ga ita kanta tana bukatar kowa a tare da ita. Uwa ita take manta da kanta tayiwa danta addu'a. Mama she is amazing mother of me, ta gwammace ta rayu da ni akan aurenta. Mika min goran ruwa tayi wanda ta ciro a jakarta tana faWin. ""Gashi sha na san kina shan ruwa dama da kome!"" Amsa nayi na sha domin bakin a bude ya™e.. ""Mama kina ganin na karbi aikin da Ya Ado ya nima min ni nafi son aikin gwamnati ne!"" Zungure min goshi tayi tana faWin. ""Waye yasan gobe ban da Allah idan kika yi hakuri kafin ki dauki lokaci sai Allah ya sauya miki da abinda yafi alkhairi, ki cigaba da addu'a duk wata rayuwa tana bukatar addu'a, ita Addu'a mukulin dukkan wata Alkhairi ne da toshe duk"

"wata sharri."" ""Mamana, in sha Allah."""

"""Wai Mama nan kuka zo kuka zauna kun manta da da wasu a cikin."" Inji Aunty Raliyah, ta ce mata."

"""Raliyah bana son gulma taya zaki biyo Uwa da Autartar!"" ""Allah ya baku hakuri ya kuma bamu hakuri ."""

"Dariya na saka muka wuce cikin asibitin mika cigaba da hira, har na manta abinda ya faru. Kusan"

"mutane da suke zuwa ganin Abba abokan aikin ya Ado ne, kwanakin su Aunty Hindatu biyar suka juya zuwa gida, nayi kewarsu sosai. Itama Mama tana cika sati biyu ta koma Bauchi aka kawo Yadiko, zuwan Mama ban tab'a shiga wurin Abba ba, amma yadiko tana zuwa ta saka ni a gaba har inda yake zaune suna magana da Rufa'i, yana ganina ya dauke kai, haka na koma bayan Yadiko na tsaya ta ce min.. ""fito ke ai shi ya samar dake idan ya isa sai ya gayawa Allah baya kaunarki sai na san inda zan ajiye lamarin,."" Abinda na lura Abba ya Wan yi sanyi. Haka dai tayi ta surutu koda na gaishe bai amsa ba, ban kara ba. Ina zaune har Ya Ado ya zo yana zuwa na bishi muka bar asibitin. Ashe bayan fitata yake cewa Yadiko. ""Yaushe Yarinyar nan tayi kyan gani haka?"" ""Lokacin da kaso kashe ta Allah bai nufa ba, lokacin da ka ji gara ta mutu da ta cigaba da amsa sunarka. Lokacin da ka ji a ranka baka kaunar ganinta har kake mata fatar karuwa. Allah Alhaji ka ji tsoron Allah ka ji tsoron wanda ya mika lamarinsa ga Allah dubi Yarinyar"

"nan yadda ta koma kamar yar tsanar zinari."""

"Jin haka yasa yayi shiru, da Yadiko take gayawa Ya Ado ya sha mamaki, da ya sauko kamar bashi ba,"

"yana kuma iya gaya mishi yadda yake ji, babban matsalar da yake fama da shi shine rashin barci wanda shi yake haifar mishi da ciwon kai mai tsanani karshe jininsa yayi kasa. Haka yasa aka kara rike shi, basu san me yake damunsa ba, amma idan har akwai wani abu da yake damunsa bai wuce yadda Lubnah taki"

komawa gidan mijinta ba.

---

A Lagos din kuwa Baban Jama'are ne fa Baba Malam suke ta yawo a garin Lagos basu dan inda Ya Ado

"sun kashe kudin hannunsa, gashi an sace wayar Baban Jama'are, wanda da ita yake kiran Hafiz Baba"

Malam kuwa yaki bada wayarshi domin kanshi kamar zai juye da suka shigo lagos sun zata kamar Bauchi

"ne da bata da girma haka. Haka yasa suka yi ta yawo daga nan zuwa can daga can zuwa nan duk sun galabaita kusan sati biyu, haka yasa suka fara bara, suna samun abinci da zasu ci."

***

*Russia*

Moscow

Zaune yake gaban laptop hannunsa daya yana tallafe da fuskarshi. Idanunsa yana kan files da aka turo

"musu yana bin sunayen kowani mutum a hankali idanunsa ya sauka akan Lubabatu Usman Umar Jama'are, jikinshi ne yayi wani iri-iri amsawa yummmmmmm........."

"[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 40"

"A nutse yake kallon dan hoton passport da yake jikin CV din, a hankali yake bin information dinta, wani"

"irin abu ne ya ji ya tsaya mishi a rai, lokacin da yaga wurin marital status, sai ya tsinci kanshi da kashe laptop din, yana mai jin wani abu a ransa, amma a fusakarshi bai nuna yadda abin ya dake shi ba, wata zuciya ce ta ce mishi. ""Ba ita ba ce wata ce daban!"" Wani bangare na zuciyar ta sake ce mishi. ""Ina ga ita ce ba wata ba ce."" Zare medical glass din idanunsa yayi ya Wan saka yatsu biyu a tsakanin idanunsa yana dan taSa tare da musu massage, mikewa yayi tare da mika sai da kasusuwanshi suka amsa sannan ya kalli hadadden dakinsa, da yake can yamma da cikin gidan, bude kofar yayi yaji yanayin gidan ya sauya daga sanyin da ya koro shi dazun, yana da wani irin lalura da baya son sanyi sam, dumin da gidan ya dauka ya bashi damar fitowa, sanye yake da trouser brown na kamfanin Adidas, sai rigar shirt din jikinsa na kamfanin polo, kafarshi kuwa sanye yake da safa baki, a duniya abu daya yake gudu sanyi. Infact yana da allergy da sanyi idan ya cika yawa yana iya samun attack na mura mai tsanani, shi yasa a tsarin rayuwarsa tunda ya fahimci baya son sanyi ya haramtawa kanshi shan kankara ko wani abu me sanyi tun yana Yaro har zuwa yau da ya girma. Yadda gidan ya dauki dumi yasan mutane biyu ne zasu kula da yanayin domin har yau kallon Baby boy suke mishi. A hankali yake takawa duk da kasancewar shi"

"lafiyayye mai kuzari amma idan lokacin sanyi yazo haka komawa yake kamar kazar da ruwa ta mishi duka, a hankali ya dauko daga stair din da ya sada shi da parlourn, da aka wura wuta a irin gidajen turawa. ""Bilyl!"" Wata dattijuwar baturiya ta kira shi, ""Na'am Granny!"" ""Ka fito?"" Murmushi yayi mata sannan ya isa gaban dinner table ya dauki kofi ya zuba ruwa ya dauka ya sha. ""Na zata ka ayi barci ne?"" Wuce ta yayi ya zauna a daya daga cikin kujerun parlourn da alfarma. Juyawa fararen idanunsa yayi a kanta, ba zaka ce ya kai shekaru arba'in da wani abu ba, asalima yanzu yake jin kanshi. Dai irin yanayinsa na rashin son magana da hayaniya yasa tayi shiru. Yadda ya kalleta nan tasan ya gaji da magana ne. ""Kai dai baka da halin wannan idan shi mace zata gani ta soka tow ba zaka tab'a aure ba sai dai ka mutu a tuzuru."" Wata karamar murmushi yayi wanda ya fitar da asalin yanayinsa na shi ba Bature ba shi ba kuma bafulatani ba, ya mai da kansa ya daura a jikin kujeran. Turo kofar da yake cikin parlourn aka yi ya juya wata mata ce ba zata huce irin sittin da wani abu ba, amma saboda yadda jikinta ya samu kulawa zaka"

"Wauka irin yar talatin din nan ne. Sai ka nutsu zaka fahimci ai da wuce shekarunta. ""Turaki!"" Ita Waya ce"

take iya kiran sunan shi kai tsaye kamar yadda yan Nigeria suke kiran sunan. Shiru yayi bai amsa mata ba

"sai zuba mata idanu da yayi yana kallonta. ""Am sorry, amma ai na gaya maka ba yadda xan yi da Mandy!"" Tabe baki yayi yana cigaba da kallon tv yadda ake shirin bikin Christmas ya kalli kakar da kyau, itama kallon Yarta take tana mata magana da idanu. ""Amma kinsan ba zaki iya rike ta ba me yasa kika dawo da ita Herlim."" ""Amma Mama kin san dai ba zan barwa William Yata ba ko? Mutumin da bai da aiki sai safara da damfara!"" "" ""Ya isa haka Please!"" Ya fada yana dafe kanshi, ya fito waje ya sha iska na so yake a kara mishi wanda ya gani a laptop ba, turo kofar gidan aka yi wata matashiyar budurwa da ba zata wuce ashirin da uku ba, ta shigo tana marisa. Tashi yayi ya wuce kitchen daura tukunya yayi akan gas tare da zuba traditional Herb, ya juya ya kalli yarinyar tana ta marisa da surutu irin na wanda ya sha ya bugu. Shigowa wani matashi da kayanta yana zuwa ya gaishe su sannan ya ajiye ya gaida Turaki ya ajiye key. ""Mandy me yasa bakya jin magana ne?"" ""Mom taya zanji maganarshi bayan ya ce baya sona, cewa yayi baya sona zuciyarshi ya bawa wata can da bata san darajarshi ba, Mom ina son Bil!"" Ta kama shakuwa, rikota Uwar tayi zuwa dakinta ko kafin su isa ban daki ta kwara amai a dakin zuwa ban dakin ban da kirnin giya ba abinda yake tashi. Tana maganar uwar ya shiga wanke mata, sannan ta zube a"

"gadon barci ya dauke ta, a lokacin ya gama dafa kayan ya zuba a kofi sannan ya mikawa kakar ya ce mata. ""Granny!"" Yadda ya kira sunanta a kausashe kafin ya fadi abinda yake ranshi ta ce mishi. ""Ka kusan komawa gida ko?"" Yadda tayi magana sai ya kashe mishi jiki. Amma kuma yasan Datti yayi hakuri da rashinsa, Daddah tayi hakuri da rashinsa idan ya cigaba da zama baya jin yayiwa mutane biyun nan"

"adalci. ""Zasu so ka kamar ni kuwa? Ina sonka idan na kalle ka iyayenka nake tunawa da su."""

"Wato drama a cikin tsohuwar nan Allah kaWai ya san yawansa, tasan abinda zai iya hana shi komawa"

"shine ta fara kirkiro drama domin ita har yau bata yarda mutuwar Mahaifiyarshi ta Allah ce ta faru da ita tafi yarda da cewa kashe ta aka yi, kuma babban abin zarginta Hajiya Zeenatu.. A hankali ta fara girgiza kai ta sake kofin ruwan da yake hannunta ya fashe tare da watsuwa a jikinta. "" A'a Bilyl kashe zasu yi, ka zauna anan. "" Karar fashewar abin yasa Herlim ta fito tana kallonsu. "" Meye kuma? "" Da sauri ta zo ta rike hannunta. "" Herlim ki ji wai zai tafi Nigeria, bayan kashe shi zasu yi."" Murmushi tayi ta ce mata.."" Mama shima fa akwai wnada suke bu™atarshi! "" ""Ai dole ki fadi haka tunda bakya kaunar fadar da yake yiwa Mandy."" "" A'a Mama kada mu yi haka dake Turaki yana da tashi rayuwar kin turke shi wuri guda, akan me? Gaskiya ya kamata ya tafi idan ya samu sarari ya zo ya ganmu!"" Ai kuwa nan ta fashe da kuka ta wuce dakinta ta fara kiran number Sarah wacce take Germany tunda ya zauna a can."" Hello Sarah kin ji wai zasu tura Bilyl Nigeria yadda suka kashe Anna haka zasu kashe min shi."" Murmushi tayi ta ce mata. ""Mama aiki da ya bari ya zo nan da zama ki barshi ya tafi Please Mama shima can suna bu™atarshi Bulal ba yaro ba ne, da za a ce lallai sai ya zauna Bulal yana bukatar iyalin yana bukatar rayuwa akan me zaki rike shi? Wannan son Kai ne!"" Da yake tana son Yaranta Kuma tana jin maganarsu sai ta ce mata."" Shi"

"kenan amma sai after bikin Christmas zai tafi!"""

"""Tow duk yadda kika ce amma ki sani shi fa CEO ne guda fa."" Ta fada mata haka, sai kuma tayi shiru ta"

fara rarrashin mahaifiyar tasu.

"A can parlourn kuwa kallonshi Herlim tayi tana girgiza kai ta ce mishi. "" Ce mata kayi zaka tafi?"" Shiru"

"yayi kafin ya ce mata. "" Eh! "" Ya cika da cin apple din da yake kan table din. ""Kai baka iya lallabata ba ne sai ka na gaya mata magana gatsu?"" Kallonta yayi kafin yaa dauke kai idan ya ce zai yi magana maybe itama ya cabb'a mata mara daWi, kwanciya yayi abinsa bai kara ce mata cikanki ba, ita tayi ta masifa kafin"

"ta ce mishi. ""Nasan kana son ka kome amma maganar gaskiya Mama tana tsoron kada wani abu ya same"

"ka ne kamar Annah!"""

"""Sannan ka ga kai ko auren baka yi ba?"" ""Wannan ba reason ba ne!"" Ya furta a hankali, yana cigaba"

"da lumshe idanunshi. Shi fa bai ga dalilin da zai saka a cigaba da rike shi domin hatta kayansa yana dakin Granny amma ace bai da yancin motsi mai ™arfi, idan yana son ya fita sai ta tsare shi da tambayoyi kamar wata jami'ar tsaro. Yana daukar haka ne a matsayin soyayyar da take yiwa Mahaifiyarshi shine duk kome ya dawo kanshi. Tabe baki yayi yana jin kamar ya tattara ya bar kasar, amma yadda yaji tana kuka dazun sai yaji kome ya fita kanshi. ""Ok ki ce mata na fasa!"" Ajiyar zuciya Herlim ta sauke ta wuce dakin mahaifiyarsu ta sameta tana shafa hoton mahaifiyar Turaki da sauran kannensa da suka rasu, zama a gefenta Herlim tayi ya ce mata. ""Mama yace ya fasa tafiya!"" ""Zai tafi na ji haka a jikina zai tafi lokacin tafiyarshi ce tayi idan ba haka ba wata rana zai tafi ban sani ba!"" ""Amma dai shi yace ya fasa tafiya."" ""Shekarun baya da ya tafi kin sani ne? A yanzu ma da yace ya fasa zai tafi adalcin da zan mishi kenan ya tafi suma dangin mahaifinsa suna bu™atarshi. Idan nace yayi ta zama da ni yaushe zai tafi? Idan nace ya zauna nayi mishi adalci ne? Hmmm baki san wani abu ba, a ranshi yaji zai tafi gara na barshi ya tafi ba mamaki wata ™addaran ce ya kira shi, amma bana jin zan iya samun nutsuwa idan baya nan, amma haka zan sakawa raina hakuri da dangana, shi namiji ne yana bukatar rayuwa."" Yadda take magana a sanyayye zai tabbatar maka da ita kanta tana son yaki da kanta ne, turawa suna da mugun son Yara, don har sun fi Larabawa kaunar Yara, ita har yau ganin shi take kamar dan karamin Yaron nan, ganin dan karamin yaro tana tuna lokacin da ya rasa Mahaifiyarshi, yadda ya zauna silent na tsawon kwanaki uku baya ko magana da kowa, lokacin da yaji labarin tunda baya kasar a lokacin, ta girdWslmama shirunsa, take kuma girmama duk lokacin da zai yi magana to a wurinsa mai muhimmanci ne. Domin a lokacin da ya ji labarin mutuwar fushi yayi yaki zuwa ga babansa, duk da Baban yana zuwa amma shi ya yanke kafarshi da kasar, koda ya rasu lokacin ya gama karatunsa na farko, cewa yayi ai dama yasan main target Winsu kenan, domin da suka kashe Mamarshi sun san ba zasu samu kome ba, tun tun daga lokacin Granny ta rike a ranta kashe mata ya da suruki aka yi kuma idan har lissafinta daidai ne Turaki shine next target Winsu, Granny babu church din da bata je ba domin rokon abin bautarta ya amintar da soul din jikanta ya nisanta shi da duk wata masifa da fitina, sai gashi ya kara dawowa da wutar son da ya rasa, anan yan mata yadda suke mutuwar sonshi amma shi sam basa gabanshi, shekarun baya ita wannan kwailar dai ita ce yake mata kallon apple of him eyes, baya jin zai kuma kaunar wata mace bayan ita, Granny ta sani idan tana son su

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login