ENGLISH DESCRIPTION
If a single spoken word could shatter your father's trust, erase you from your family, and force you into a fateful marriage with a complete stranger... could you survive it?
Iftahal made a statement that unexpectedly sealed her fate. In an instant, she found herself married to Prince Maher Zaid—a breathtakingly handsome prince from Egypt, intensely reserved, yet burdened by dark secrets involving mysterious afflictions, secret societies, and sinister spells. As Shanwul warned her: living alongside Maher is a life-or-death gamble.
Every night, Maher's condition flares up, turning him unpredictable and dangerous. While a scheming physician plots behind closed doors and her father disowns her forever, Iftahal stands alone in a high-stakes battle for survival.
Will Iftahal become Maher's cure, or will he become her ultimate destruction?
HAUSA DESCRIPTION
Idan furuci guda daya kacal zai iya ruguza amincin mahaifinka, ya cire ka daga cikin danginka, ya kuma wurga ka cikin auren kaddara da mutumin da baka taba sani ba... zaka iya jurewa?
Iftahal tayi furucin da ya sauya mata kaddarar rayuwa gaba daya. Cikin sanyi da rashin sani, ta tsinci kanta a matsayin matar Prince Maher Zaid—kyakykyawan saurayi, dan gidan sarautar Misra (Egypt), mai mugun kwarjini da miskilanci, amma kuma mai dauke da wata sakaya ta sirrin aljanu, kungiyar asiri, da sihiri mai razana zuciya! Shanwul ya rigaya ya sanar da ita: zama da Maher tamkar kasada ce da rai.
A kowane dare, lalurar Maher tana tashi... wanda zai iya maida shi komai ko kuma ya aikata kisa batare da ya sani ba! Yayin da likitan gidan yake kulla makirci don shanye jininsu, shi kuma mahaifinta ya rantse ba zai taba yafe mata ba.
Shin Iftahal zata iya zama silar warakar Maher, ko kuwa shi zai zama silar komawarta makwancinta? Wanne irin rikici zai faru tsakanin zuciyarta da furucin baki?