Follow us on social media

Showing 18001 words to 21000 words out of 131683 words

Chapter 7 - NOOR IMAN Yar Baƙin Ciki BY Fatima Muhammad Gurin

min ba, yanzu da kullum zagin wanki nakeyi da ya zaki ji?" Zarah na dariya tace "Toh me zanji? Ni ba abinda zanji baiwar Allah" girgiza kai kawai noor iman tayi suka ci gaba da takawa har suka isa inda motar gidasu zarah take, nan fah zarah ta kafe akan se noor iman ta shiga sun sauketa gida ba yadda batayi ba amma zarah taki rabuwa da ita haka ta shiga suka tafi.

Da kwatance suka isa har kofar gidansu zarah tace "muje In gaida umma da kullum ake min maganarta amma anki had'ani da ita" a tare suka shiga gidan da sallama gabanta na fad'uwa tana tsoron kar umma ta wulakanta zarah me kirki da mutunci, zaune gaban murhu suka ga umman tana tankad'en garin masara da sauri zarah ta karasa kusa da ita ta duka tace "ummanmu sannu da aiki mun sameku lafiya?".

'Dago kai umma tayi ta kalli noor iman da ke tsaye tana ta adu'ar Allah yasa ta amsa mata, ta kuma kallon zarah se tayi murmushi tace "Lafiya kalau ya chan gidan naku?" Zarah tace "Lafiya Alhamdulillah" Tace "Toh masha Allah" kan ta maida kai taci gaba da abinda take cikin sanyin murya noor iman tace "sannu da gida umma" amma se bata amsa ba, da sauri ta maida dubanta kan zarah dake mata kallon mamaki tace.

"Zarah tashi mu karasa ki gaida mama" mikewa zarah tayi suspicious tabi bayan noor iman zuwa parlorn mama, nan suka sameta tana kallo da fara'a sossai suka gaisa da zarah da kanta ta kawo mata ruwa, zarah kuwa ta d'an sake sukayi fira ma kuwa kan ta tashi tana cewa "na bar driver a waje bari naje. Se anjima mama" mama ta amsa da "yawwa zara'u ki gaida su hajiyar taki" fita sukayi da noor a tsakar gidan de ta tsaya tayiwa umma sallama da "yauwa" kawai ta amsa ta juyawa aikinta jiki a sa'bule zarah ta tafi noor na d'aga mata hannu.

Tabbas tana zargin wani abu tsakanin noor da ummanta, amma bata san yadda zata sa abun ba, watakila kuma noor d'in ta mata laifi ne yasa take hakan, a haka ta ajiye maganar gefe ta ci gaba da chat a wayanta.

"Yauwa dare yayi kuma I'm very sure kina kwance kan gado ke ke kad'anki se ki cika alkawari" cewar Hammad, waro ido tayi tace "wani alkawari ni 'yasu?" Yace "Tab aiko baki isa ba se kin tuna" a shagwa'be tace "ni ba abinda zan tuna na sani tunda ba alkawarin da nayi" alamun yayi fushi yayi kan yace "ya miki kyau na gode da wulakanci" kittt ya kashe wayan.

Ajiyar zuciya ta sauke kan ta shiga message ta fara tunanin me zata tura mishi, da kyar de ta rubuta "kar ran miji na gari ya 'baci sbd wannan mata tashi a tausaya a yafe mata, ba don halinta ba" ta tura mishi kan ta kuma rubuta "sweet dreams Zaujii" ta tura tare da kashe wayanta tana murmushi, (hmmm Allah sarki baiwar Allah).

Cikin jin daad'i hammad ke kallon screen d'in wayanshi wani irin soyayyarta yake ji na kara ratsa shi, waro ido yayi ganin sunan mom na yawo 'baro 'baro a d'arare ya d'auka, ji yayi tace "Sameni d'akina" mikewa yayi jiki a sa'bule ya fice zuwa part d'inta.

Kan gado ya ganta zaune hakan yasa ya zauna daga kasa a gefenta kanshi kasa, cikin kaushin murya tace "Muhammad ka san abinda kake shirin jefa kanka kuwa? Ka san yarinyar da kake son aure kuwa? Toh bari In fad'amaka aurenta d'ai d'ai d'ai d'ai har 4 kaine zaka shiga layin na 5, dan Allah salun alun ka rabu da yarinyar nan tun kan maganar ya kai kunnen mahaifinka".

Zuciyarshi na bugawa yace "mom na sani, a haka nake sonta, mom aure rai ne dashi kuma tun kan Allah ya halicceta ya kiyasce mata auren da zatayi a duniya mom ita kanta na san ba yin kanta bane kaddararta kenan, a haka nake sonta kuma In shaa Allahu saina au......" tasss yaji saukan mari a razane ya d'aga yana kallon mom d'in tashi what!!! Did she just slapped him? Abinda be ta'ba shiga tsakaninsu  da ita ba kenan a zafafe tace.

"Baka isa ba wallahi Muhammad, wallahi Wallahi wallahi kaji rantsuwar musulmi ko to In har Ina raye baza ka ta'ba auren yarinyar nan ba, ko da na mutu ka aureta ban yafemaka ba Allah ya isa", a matukar razane yake kallon ta, har abin ya kai Haka? Me yayi zafi bud'e baki yayi da niyyar bata hakuri ta daga mishi tsawa "tashi ka fice min daga d'aki!!!" A hankali ya mike ya fice yana jin jiri na kwasarshi.





                      🖤Gureenjo🖤

🥀NOOR IMAN🥀

*Fatima Muhammad Gurin*
                 •Gureenjo6763 on Wattpad•

*'yar mutan Adamawa*

💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)

                         *012*

A razane ta d'aga tana kallon mahaifin nata a lokaci d'aya jikinta ya d'auki rawa, me baba ke nufi ne da rayuwarta? Wai se Baba Yaga tarwatsewar zuciyarta kan hankali shi ze kwanta ne? Me yasa ita ta fito duniya a haka ne? Hasbunallahu wani'imal wakeel ta dinga nanatawa a zuciyarta har ta d'an ji sauki, tsawarshi taji a kanta "ke wai ba da ke nake magana bane kin min zuru kina kallona da ido kaman na mayu, Toh kiji da kyau na baki sati biyu ki fitar da mijin aure In ba haka ba wallahi masallaci zan kai hotonki duk wadda yace kin mishi ko wanene kuwa aura mishi zanyi kinji nace wallahi".

Kukan ma yau ta kasa tsabar kad'uwa da maganan baban, me ta tare mishi ne ita a duniyar nan? Ita Ina zata samu miji cikin sati biyu, da jiri da komai ta karasa d'akin mama ta zube akan gado se lokacin kuka ya zo mata sossai ta fashe dashi kaman ba gobe kirjinta na mata wani irin zafi, da ma zata mutu da ta huta.

Shirin fita lectures tayi amma bazata iya fita a haka ba, don ta san ko taje ba abinda zata fahimta, tuna maganan me acha'ban da ya ta'ba kawota gida tayi, tabbas tana mantawa da kai kukanta wurin me duka, iyakarta sallaloli biyar nan da suka zama wajibi a kanta ko alqur'ani se ta manta yaushe ta bud'e shi bare kuma ayi maganar nafilfili da kai kuka wurin Allah.

Mikewa tayi ta fad'a toilet tayi alwala dama da hijabinta kanta, Alqurani ta Zara tare da zama kan dadduma ta bud'e ta fara karantawa cikin natsuwa, tafi awa zaune tana karatun dukda taji shigowar mama kuma ta san ita take jira suyi magana, amma ta kasa tsayar da kanta har maman ta fice, kiran da ya fara shigowa wayarta ba kakkautawa ne yasata tsayar da karatun ta duba wayan.

"Hammad" shine sunan da ya bayyana a saman fuskar, murmushi tayi don sossai karatun ya sauke mata duk wani nauyi na zuciyarta, ya gusar mata da damuwarta, ya bata wani kwarin guiwar da da bata dashi, ya goge duk wani hawaye dake fuskanta haka ya hana wasu zubowa tabbas alqur'ani rahama ne ga masu karantashi, kwanciyar hankali ne ga duk wani tashin hankalin bawa.

Ta yarda kuma ta tabbatar yau, da wani irin kwarin guiwa ta d'aga wayan kan yayi magana ma tace "ya hammad Ina kwana? Ya gd? Dan Allah da gaske kana so na tsakani da Allah?" Shiru yayi na mintuna kan yace "lafiya kalau iman, kwarai na soki tsakani da Allah kuma har yanzu Ina sonki sede...." kan ya karasa ta katse shi "Toh baba yace in gabatar mishi da wadda nake so nan da sati biyu, happy?" Cikin rawar murya yace "kenan ni kike so?" Dariya tayi kan tayi maza ta kashe wayan cikin yanayin jin kunya.

*******

"Innalillahi wainna ilaihi rajiun!" Ya dinga nanatawa tun da ta kashe wayan, kwata kwata daren jiya kasa bacci yayi yana tunanin ta yadda ze iya rabuwa da noor iman ba tare da tayi tunanin yaudararta yayi ba, be kuma son fad'a mata mahaifiyarshice ta sashi rabuwa da ita don kar ta tsani mahaifiyar tashi, da kyar ya samu ya harhad'a 'yan kalaman da yake son gayamata, amma ta fad'a mishi abunda baze iya tunkararta maganan rabuwarsu ba.

Mikewa yayi ya fad'a wanka sharp sharp ya shirya tare da d'aukan key d'in motanshi ya fice, kana ganinshi zaka san yana cikin damuwa ko be furta maka ba, direct gidan Uwais yayiwa tsinke ba tare da ya shiga ciki ba ya kirashi a waya "dan Allah in kana gida ka fito akwai maganan da nake so muyi" daga d'ayan 'bangaren Uwais yace mishi yana office ya sameshi chan.

Asibitin da Uwais ke aiki ya nufa minti minti yana dukan sitiyarin motar tare da taune lips, har Allah ya kaishi office d'in lafiya, zama yayi ya zubawa Uwais ido yana kallo har Uwais d'in ya sallami patient da yake dubawa yace "Lafiya kuwa abokina?"
Sighing yayi kan ya fara bawa Uwais labarin duk abinda ke faruwa.

Sossai Uwais yayi jimami kan ya bashi shawara "Hammad why not ka zauna da yarinyar kaji gabad'aya labarinta da dalilan mutuwan aurenta a ganina In har ba wani abu na tashin hankali bane ya rabo ta da gidajen aurenta se mu ma mom bayani mu kuma roke ta yadda zata gamsu da maganan auren naku." Gyad'a kai hammad yayi cike da gamsuwa yace "haka ma yayi zan kirata inji sadda zamu had'u se in tambayeta".

*******
Karkad'a kafa kawai yakeyi yana jiran fitowarta daga toilet, kallo d'aya zaka mishi ka san ranshi a matukar 'bace yake, lectures yayi shirin zuwa kasancewar ya bar karamar wayanshi a d'akinta jiya ya sa shi shigowa ya d'auka a shirye yake tsab cikin shirin fitanshi ya shiga d'akin.

To his biggest surprise ya ganta zaune a bakin gado tana ganinshi ta mike ta tsaya tare da fara wasa da fingers d'inta tace "dan Allah Hamma Abdul ka barni inje yola In ga umma bata da lafiya sossai, kayi hakuri nayi garaje nayi booking flight tun kan In sanar da kai tafiyartawa" kallonta yayi na mintuna kan ya ta'be baki a lokaci d'aya ya d'aga kafad'unshi.

Yayi hakan ne sbd ya kwana da sanin ko ya yarda ko be yarda ba se ta tafi tunda tayi niyya wuyan ta kira ummu ne kawai, cikin jin daad'i tazo ta rungumeshi tana godiya, bata jira cewarshi ba ta fad'a toilet don yin wanka, shi kuma ya nufi bedside d'inta don d'aukan wayanshi, sachets d'in magani da ya gani ne yasa shi kallon hanyar toilet ya kuma kalli maganin bata da lafiya ne kuma bata gayamishi ba?.

Me ke damunta haka? Maganin ya d'auka cikin kad'uwa yake kallon maganin what!!!! Maganin hana d'aukan ciki!! Hannunshi rawa ya dingayi tsabar irin shock d'in da ya shiga, Hamna! Hamna!! Hamna!!! Ya fad'a kasan numfashinshi tare da nausan gini har seda zafi ya ratsa har 'bargonshi.

Safa da marwa ya fara a tsakiyar d'akin yana tunanin me yarinyar take nema dashi a duniyar Allahn nan, me be yiwa Hamna ba da ta za'bi kin bari su haihu, yadda yake son haihuwan nan!! Me ze mata yaji saukin abinda.... jin kanshi na sarawa ne yasa shi neman wuri ya zauna tare da d'aura kafa d'aya kan d'aya yana karkad'awa.

Mintuna kad'an ta fito daga wankan da mamaki take kallon shi  kan tace "booo baka tafi ba har yanzu? Ko akwai abinda k..." makalewa maganan yayi, sbd idonta da ya sauka kan maganin dake hannunshi, kallon fuskanshi tayi kan ta fara taku baya baya, kaman kiftawar ido ta ganshi gabanta yayi grabbing dantsen hannunta da karfi.

"Me wannan??" Ya furta trying so hard to control his self in ina ta fara "ba.... a... fa.... abinda" "shut up you bastard!!" Ya daka mata tsawa, wani irin tsoro ne ya d'arsu a ranta ganin yanayin shi ta san yanzu ta sake ta harzuka shi ba abinda ze hana shi Lakad'amata na jaki, itafa bata ga wani laifin da tayi ba aaa jiki jikinta haka kuma ciki cikinta ne don bata ga damar d'aukan yaro ba se me, gaskiya ita bata shirya tsufa yanzu ba Haka kawai.

Magana ze yi amma sam maganan yaki fita don haka Allah ya halicceshi In har ranshi ya kai matukar 'baci ko magana baya iya wa, tureta yayi har seda ta fad'i kan ya sa kai ya fice, ya gama yanke shawara kuma duk duniya In ba mahaliccinshi ba ba wadda ya isa hanashi abinda yayi niyya, ze shayar dasu ruwan mamaki daga ita har iyayen nasu.

********

"Tabbas kinyi matukar kokari iman, na san abun ba me sauki bane haka na tabbatar dauriya ce kawai irin naki, da da yadda zanyi iman da babanku da nayi don hanashi abinda yayi niyya amma wannan karon karki tona kiga yadda muka kai ruwa rana dashi amma yaki lankwasuwa, na kira inna sbd na san In yayi irin wannan kafewar itace kawai me iya lankwasa shi amma ita ma ta watsamin kasa a ido tace ta bada goyon baya d'ari bisa d'ari nan da sati biyu wallahi In baki kawo wadda kike so ba da kanta zata bugo hotunanki dayawa ta tayashi rabarwa a massalatai.

Iman ki taimakeni ki fitar da wadda kike so kar a bada sadakarki, don hakan yafi komai bakanta rai, babban abinda ya kona min rai wai Ina waya da inna akan zancen nan ummanku ta kar'ba tace mata 'inna na san manyan yayyunshi zasuyi kokarin hanashi sbd suna son ita munafukar ga shawara duk yadda zasuyi kada ki yarda In sun matsa ki musu barazanar tsinuwa'" kuka mama ta fashe dashi tana share hawaye tace.

"Na rasa wace irin uwa ce ummanku, na rasa me ke damunta wallahi...." ta karasa da shesheka, d'ago idon da zatayi kawai taga noor kwance a kasa sumammiya ihu ta sanya tare da yin kanta da gudu tana kwala kiran sunanta, baba da shigowarshi kenan da sauri ya karasa ciki ya kuwa rud'e ganin ta kaman mattaciya da azama suka d'auketa zuwa karamar starlet d'in baban, mama ta shiga ya ja suka fice umma na zaune abinta tana gyaran farce ko a gyalenta.

General hospital ya nufa da ita, suna parking yana parking kifa kai yayi kan sitiyari yana tunanin hukuncin da ya gama yankewa nan d'in ma ya zo ne don neman shawaran dr sauban Amininshi, jin hayaniya a gefenshi yasashi juyawa yana kallon mirror waro ido yayi ganinta kwance akan gadon da ake tura marasa lafiya fuskanta ya fito tar se kan idonta da suka kumbura tsabar kukan da ta sha.

Doguwar rigar material ne jikinta gashinta baje akan gadon sbd ko hijab mama bata tsaya sakamata ba tsabar rud'ewa, da sauri ya fito daga motar yayi cikin asibitin a baya ya dinga binsu har aka shige da ita emergency ze juya kenan se suka ci Karo da dr sauban cikin sauri yace "Malabo jirani office na plz I've an emergency".

Be jira cewarshi ba ya wuce, shima jiki a sanyaye ya karasa office d'in sauban d'in amma se ya kasa zama safa da marwa ya dinga yi yana tunano moments d'in da ya ganta ba sau d'aya ba ba sau biyu ba, duk kuma cikin tashin hankali da kuka, me ke damun yarinyar nan ne? Ze so jin labarinta amma ko da ze iya taimaka mata amma ta yaya? Yana yawo yana duba agogo.

Kusan one hour yayi a tsaye yana yawo kan sauban ya shigo yana goge gumi, cikin takaici ya buga desk din gabanshi yana furta "what the fuckk!!!!" Ya kuma bugawa yace "shiiiiiitt" Abdulraheem yace "wani irin iskanci ne wannan sauban? Komai ya faru bazakayi salati ba se ka dinga ambatan  kalmomin da arna ne ya kamata su dinga amabata?" Cikin rawar murya yake maganan, girgiza kai sauban yayi tare da lumshe ido yace "I didn't make it" "whatttt!!".





                    🖤Gureenjoh🖤


🥀NOOR IMAN🥀

*Fatima Muhammad Gurin*
             •Gureenjo6763 on Wattpad•

*'yar mutan Adamawa*


💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)

                        *013*

Banko kofan da akayi ne yasa su duk maida hankali kai wata nurse ce ta shigo se faman haki take tace "Doctor!! Doctor!!! She's still breathing" da azama dr sauban ya fice har yana had'awa da gudu, wani irin wawan ajiyar zuciya ya sauke yana zama kan kujera a gabad'aya rayuwanshi ze iya cewa be ta'ba jin tsoro irin na yau ba, he was really scared, to amma sbd me? Amsan da be sani ba kenan.

Ya jima zaune a wurin har be san iya adadin lokutan da ya d'auka yana jiran sauban ba, finally se gashi ya turo kofa ya shigo a gajiye, zama yayi a normal cushion dake office d'in tare da furta "wash Allah" Abdul yace "sannu fah" sauban yace "yauwa, wallahi naji tausayin yarinyar nan, baka ganta ba 'yar karama da ita amma wai tana fama da matsanancin hawan jini ya hau fiye da tunanin me tunani, don In ta kara collapsing haka da kyar In bata samu matsala ba, ga ciwon zuciyar da ke barazanar kama ta".

Cikin damuwa Abdul yace "seriously?? Allah sarki Allah ubangiji ya bata lafiya" sauban yace "Ameen, se Allah ya San damuwanta" mikewa Abdulraheem yayi yana gyara riganshi yace "na tafi sauban" mikewa zaune sauban yayi yace "wani irin zaka tafi? I thought ka shigo muyi magana me muhimmanci ne as yhu said but you're leaving ba tare da munyi maganan ba".

Yana kallon wani wuri daban yace "as I can see ka gaji yanzu zan dawo ko after asr prayer ne se muyi maganan" sauban yace "ohkey then, Se ka juyo" ficewa Abdul yayi daga ka ganshi zaka san akwai abunda ke damunshi duk daga yadda yake ta kokarin 'boyewa, har ya nufi fita se kuma se ya fasa ya nufi emergency daga jikin kofa ya tsaya se kuma ya juya ya fice da sauri.

Motarshi ya shiga ya ja ya bar asibitin da mugun speed, tafiya kawai ya dingayi ba tare da ya san inda za shi ba tunani kala kala ke running a cikin mind d'inshi, me yayi ma yarinyar nan zafi a duniyan Allah nan da irin kananan shekarunnan take fuskantan wannan damuwa haka? Tausayinta yaji sossai ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login