Follow us on social media

Showing 3001 words to 6000 words out of 131683 words

Chapter 2 - NOOR IMAN Yar Baƙin Ciki BY Fatima Muhammad Gurin

takeyi In na matsa mata da magana In ka shigo gidanmu kaga yadda takemin zaka rantse 'yar kishiya nake a gareta, ban san daad'in uwa ba sam ban san d'uminta ba, ko d'akinta na shiga se ta korani waje.

Ko kitso takeyiwa kannena In naje bazata min ba dukda kwarewar ta a harkar, se de in zauna daga nesa Ina ganin yadda take wasa da dariya da kannena wani lokacin har 'buya nake a bakin kofan ta In ta kallonta Ina hawaye, bata ta'ba sakemin fuska ba wadda nake yawan mamakin 'Anya uwa ce'.

Ina girma suffan jikina na kara bayyana da kyaun da Allah ya bani wadda In ka ganni da ummana kaman photocopy banda kiba haka kuma banda rama jikina a murje yake da kalar fatata me d'aukar hankali sbd a chocolate dinma me tsada ne don haka yawan mutane suke fad'a Ina da dimple guda d'aya a 'bangaren kumatuna na dama.

Hakwarana farare sol kanana da su daga tsakiya kuma wushiryace me kyau, se madaidaicin hancina da kuma madaidaitan fararen idanuna na, Ina da cikar kirji da kuma hips yayinda gashin kaina ya kasance marar tsawo har chan amma baki sidik ga laushi.

Ina jss 2 maza suka fara layi a kofar gidanmu don Allah yayini da farin jinin samari hakan yasa baba ya sha alwashin aurar dani da na gama secondary dukda yadda yake so nayi karatu don nice ta gaban goshinshi yana son cika min burina na zama babbar lecturer a duniya amma yana shakka yadda ake zuwa mishi da magana na har tsoro yake bashi.

Kaman yadda na fad'a a baya tun jss 2 bello ya fara takuramin da nuna yadda yake sona ya kuma tabbatar min baze iya rayuwa ba ni ba, tun Ina shareshi har na fara sauraranshi, Ina cikin zana jarabawata ta kare secondary baba ya kirani ya tabbatar min ba zan ci gaba da karatu ba ze aurar dani In miji na ya yarda inci gaba so in turo da wadda nakeso.

Ba 'bata lokaci na gabatar da bello ya ko yi farin ciki sossai kaman ze had'iyeni da aka bashi ni a kuma lokaci kankani, Ina gama neco aka aura min shi, amma kayan takaici a daren ya sakeni ba tare da wani kwakwaran hujja ko dalili ba, wadda hakan yasa baba da sauran 'yan uwanshi kusa kasheni.

Basuyi la'akari da laifin nawa ne ko ba nawa ba, abunda ya fi yi min zafi kuma son da nakeyiwa bello amma aikin gama ya gama a shekaruna na sha takwas har na zama bazawara, tun baba na had'e min rai bayan dawowanmu gadon kaya, har ya daina ya fara min nasiha a kullum da yadda rayuwa yake da kuma fa'idan zaman aure duk laifina yake gani ba laifin bello ba.

Abun takaicin kuma yawancin nasihanshi na karkatuwa ne ga girman laifin zina wato shima ya yarda da rashin kai budurcina ya sa bello sakina hakan na sani kuka sossai da kunar rai, bayan mutuwar aurena da bello da watanni bakwai na had'u da Ahmad matashin saurayi me ji da kud'i a asibiti muka had'u bamu wani jima muna soyayya ba ya nemi turowa na fad'awa baba ya dinga ci min albarka.

Ba 'bata lokaci aka yi buki aka d'aura min aure da Ahmad, bayan d'aurin aure angwaye sun kasance suna turowa amarensu sakon jin daad'insu amma ni sakon bakin ciki da takaici Ahmad ya turo min, bayan an watse ya kirani a waya ya ci min mutunci akan ni bazawara ce bamu fad'a mishi ba muka cuce shi ashe ni 'yar iska ce, wai ashe yawon iskancin da nakeyi yasa mijinan chan ya sakeni.

Nayi kuka har na gaji da wannan sharrin haka aka kaini tunda aka kaini kullum wulakanci har dukana yana yi sede be ta'ba kusantata ba bare ya san gaskiyata na wahala sossai a gidan Ahmad na wata shidda kan ya sakeni na dawo gida, a lokacin hawan jini ya kama baba, kaman aurena na farko har gida su goggo kamila suka zo gabad'ayansu suka lakad'amin na jaki.

******

Ta'bani da mama keyi yasa ni dawowa daga duniyar tunanin da na fad'a "Iman tashi kinyi bacci bakiyi sallahn isha ba gashi har karfe goma, tashi maza kiyi sallah" salati nayi ina mikewa daga kwancen da nake na fad'a bayi, alwala nayi na fito na samu mama ta gama shiryawa zata tafi d'akin baba da yake itace dashi, sallama mukayi ta fita ni kuma nayi sallahna kan na koma gado na kwanta.

Ruri wayana ya fara yana neman agaji a kasalance na sa hannu na d'aga, Haka kawai wani lokacin se in manta Ina da waya sbd ba me kirana en uwana se na kirasu sbd duk haushina sukeji har gwara hafsy amma sauran kannena da sukayi aure ba me kirana haka goggonina ko na kirasu ba d'agawa sukeyi ba, na rasa kaddarannan kam ni na d'aurawa kaina ko ko Allah ne ya d'auramin.

Sake shigowar call wayana ya dawo dani daga tunanin da na fad'a da sauri na d'aga "salamu Alaikum" na furta cikin sanyin murya, murmushi na saki jin muryan zarah tana cewa "Amma baki da mutunci Noor Iman yanzu bakiyi saving number na ba? Don daga jin yadda kikayi sallaman nan baki san who's in the line ba" cikin murmushi nace "sorry zarah, wallahi shap na mance banyi saving ba amma karki damu yanzunnan zanyi".

"Ni de Allah nayi fushi tun fah d'azu nayi saving numbernki da my besty amma ke bakiyi ba" cikin mamakin halin sangarci irin na zarah nace "amma ke zarah 'yar autace ko?" Tace "yes Anty Rumah, ya Abdul, ya hafeez, Anty kalthum duk auta suke ce min har ummu da Abbu" na lura zarah yarinyace don na tabbatar zan bata akallah shakaru hud'u zuwa biyar amma zan d'auketa kawa don tana da daad'in zama kuma ma ni ta fini kiba da tsawo don duguwace sossai ba kaman ni da nake tsaka tsaki ba.

Itama na tabbatar da ta san asalin shekaruna sede ta fara kirana da Anty, ga aurarrakin da nayi, "Lallai auta nima haka zan dinga ce miki" I bet ta turo baki kan Tace "ni de bazan yarda ba sede my besty" nace "ohkey besty duk yadda kikeso haka za'ayi" "ke gobe fah muna da lectures d'in Dr. Abdulraheem kuma 8, dan Allah kizo da wuri karki yi letting ya koreki" cikin sanyin jiki nace "Ohk dear in shaa Allah se mun had'u, bari na zo na kwanta". Sallama mukayi na kwanta bacci.





                      🖤Gureenjo🖤

🥀NOOR IMAN🥀

*Fatima Muhammad Gurin*
             •Gureenjo6763 on wattpad•

  *'yar mutan Adamawa*

💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)

                        *04*

A Karo na biyu na kuma dunfaro class d'inshi 6mins past eight, dayake ban samu bacci cikin dare sossai ba sbd period pain da nayi fama da shi ban samu salama ba seda jinin yazo gabannin asuba kan nayi bacci.

Bani na farka ba se karfe bakwai, kan nayi wanka na shirya na taho takwas da mintuna shidda, zuciyata na dukan tara tara sede banjin zan iya komawa da baya sbd bana son samun matsala da course d'inshi sam gashi yanzu attendance na biyu ke shirin wuceni.

Nannauyar ajiyar zuciya na sauke kan na tura kofan a hankali na sa kai, muryanshi dake tashi a hankali cikin sanyin da yake naturally ne ya doki dodon kunnena wadda har seda naji faduwar gaba da na rasa dalili, ba tare da na kalli inda yake ba na nufi karasawa cikin ajin sede ko taku biyu ban yi ba na ji shi yana cewa.

"Hey yhu!!!! Get out of my class" 'Dago eyeballs dina nayi da niyyar bashi hakuri amma me? Bakina kwata kwata yaki bani had'in kai wurin motsashi har muryan ya fito, sbd hardewa da idanunmu yayi cikin na juna.

Wani irin disgusting look yake jifana dashi da ya sa ba shiri na juya na fice jikina na tsananta rawa, Ina jin tsakinshi cikin microphone kan ya ci gaba da bayanin cikin natsatsiyar muryarshi me tafiyar da hankalin me saurare.

Wuri na samu na buga tagumi cike da jimamin sake makara a class d'in bawan Allahn nan Dr. Abdulraheem kaman yadda zarah ta ambaci sunanshi, ina nan zaune har ya gama lecturing ya fito kaman jiya yau ma bakaken kananan kaya ne a jikinshi ko don ya san suna mishi kyau ne yasa yake sakawa? Oho, idona na kanshi har ya bud'e wata Mercedes benz ya shige itama baka yaja da gudu kaman de jiya ya fice.

Ajiyar zuciya na sauke tare da kauda kaina daga hanyar da motar ta bi jin hannu a kafad'ana, kallon me hannun nayi murmushi na saki ganin zarah, fuskantan nan a turbune kaman zatayi kuka cikin dariya nace "lafiya autan ummu?" Kara turo baki tayi tace "yhu know what yhu did is not fair right? Me yasa kika zo late plz, wallahi dr. Abdul cewa yayi In baka da 75 percent attendance d'inshi you will not sit for his exams"

Matsa mata nayi ta zauna Ina me sauke ajiyar zuciya nace "In shaa Allahu bazan kara ba, yau ma da dalilin hakan" girgiza kai tayi tare da cewa "and in kin san kinyi late karki dinga shiga wallahi it hurts to see him humiliating yhu In public ba mutunci ne dashi ba" girgiza kai kawai nayi shiru ya d'an ratsa kan nace "tashi muje mosque mu d'an yi karatu tunda se 2 muke da wani lectures din".

Mikewa tayi muka fara tafiya muna 'yar hira har muka isa masallaci daga chan baya muka zauna muka baje handouts na chemistry ta fara koyamin duk abinda ban gane ba, ba mu muka motsa daga nan ba se karfe d'aya muka yi sallah muka fito zuwa cafeteria abinci muka ci wadda zarah ce ta biya kud'in duk da yadda nayi kokarin hanata.

Multipurpose muka nufa mukayi education 2-4 wadda sossai na fahimta kuma lectures din ya min daad'i har nake jin nan gaba karatun ze iya d'aukemin duk wata damuwana, "muje muyi sallah kan azo d'aukanki ko?" Na fad'a Ina kallon zarah dake chatting a wayanta kirar iphone 11pro ba tare da ta kalleni ba tace "yes sure, kin san kanon nan in yamma tayi holdup d'in bala'i ne da ita kan ka isa gida past five".

Murmushi kawai nayi ina mamakin surutun zarah Abu d'aya zaka tambayeta amma ta baka amsa sama da ashirin, a natse muke takawa musamman zarah 'yar gayu da tafiyarta ma kad'ai abun kallo ne, ga shiganta ba wai me nuna tsiraici ba a'a kawai de da ka kalleta zaka san daga gidan arziki ta fito hutu ne ko ta Ina a jikinta.

Kallon jikina nayi ba laifi sanye nake da material doguwar riga da bakin hijab da bakin takalmi se bakin agogo da d'an side bag d'ina, daidai gwargwadon talaka me madaidaicin karfi, na san mutane zasuyi ta zagina da zund'en na makalewa 'yar masu kud'i wasu dayawa suna son kawance da zarah amma na kula ko ta kansu bata bi.

Bayan munyi sallah mun fito muka nufi hanyar barin school din tun kan mu shiga ta kira driver d'inta akan yazo ya d'auketa hakan yasa bamuyi wani nisa ba muka hangi motar wadda ni ban ma gane ba dayake ba da shi aka zo d'aukanta jiya ba, yau ma tayi tayi dani In shiga su saukeni naki har fushi tayi ta tafi.

Hmm zarah kenan da kin san irin maganan da shiga motar gidanku ze jamin da baki fara min tayi ba, na raya a raina Ina tarar machine da yazo wucewa ciniki mukayi dashi kan na d'ane yaja muka tafi.

*****

"Amincin Allah da yardarshi su tabbata akanki yake ma'abociyar kyau da kwarjini" dakatawa daga saurin da nake nayi ba tare da na juyo ba har seda me maganan ya sha gabana ya tsaya ajiyar zuciya na sauke ina me d'auke idanuna daga kan kamilalliyar fuskan shi, "Baki amsa ba ranki shi dad'e" a hankali na ce "Wa'alaikassalam warahmatullah".

"Yauwa ranki shi dade...." "Noor Iman" wara ido yayi kan yace "masha Allah suna me daad'i, kar na 'bata miki lokaci gashi na tsaidake a titi na san ba mutuncinki bane amma ba yadda na iya ne" ajiyar zuciya ya sauke yana tuna irin maganganun da aka gayamishi akanta tunda ya fara zuwar ma abokinshi da zancen yana son yarinyar.

"Sunana Hamza Noor Ina sonki, so na tsakani da Allah kuma aurenki nake son inyi" hawaye ne ya ciko idona tun bayan barina gidan Ahmad ba wani namijin da ya ta'ba tarana da sunan so se hamza sbd wani irin bakin fenti da jama'a suka shafamin ba tare da sun san kaddara bane kuma yana kan kowa, "aurena biyu, ni bazawara ce" ga mamakina murmushi naga yayi yace "ko menene kike ni Ina sonki kuma zan aureki ba wadda ze iya hanani se Allah se kuma idan baki sona sarauniya".

Murmushi nayi kan na ce "ni ban ce ba, Allah ya za'ba mana abinda yafi alkhairi" cikin jin daad'i Hamza yayimin godiya yayinda ya rakoni har gida don dama na shigo layinmu, soyayya me tsafta ce ta shiga tsakaninmu da hamza dukda irin maganganun da ake gayamishi a kaina ya toshe kunnuwanshi iyayenshi kuma masu fahimta sam basu nuna kina ba se adu'ar Allah ya tabbatar da alkhairi.

Matarshi da kannenshi ne suka so tada fitina amma dashike ya isa da gidanshi da kuma kannenshi abin beyi nisa ba, iyayenmu sun gana inda baba ya kuma tabbatar musu aurena biyu sun nuna sun sani aka sanya mana rana, kullu yaumin baba ze ajiyeni yamin fad'a sossai akan wannan aure da yake ta gabatawa In har na kashe to wallahi sede In nemi wani uban ba shi ba.

Har na gaji da jin wannan kalaman nashi, na san kaddara ni ko shi ba wanda ya isa hana Allah abinda yaso In har rubuttacce ne a cikin shafin kaddarana, wasa wasa lokaci ya matso inda walima kawai nayi shima don tirsasawar hamza, rana bata karya a ranar 17 ga watan d'aya 2019 aka d'aura aurena da hamza da karfe goma na safe, a kuma lokacin Allah ya kar'bi ran Hamza bayan an gama shafa fatiha.

Mutuwar da yamin ciwo fiye da komai a duniya nayi kuka har kaman raina ze fita sede ba yadda na iya ba iya dawo dashi zanyi ba, har abada bana jin zan manta wannan rana zan kuma manta wannan rashi na mijina me kaunata tsakani da Allah, se namijin kwarai ne irin Hamza ze iya jurar irin maganganun dake yawo a kaina ya toshe kunne yace duk duniya se ni.

Nan kam ba yadda baba da 'yan uwanshi suka iya tunda mutuwane amma fah maganganun mutane na watakila Ina da miji cikin jinsin aljannu ya fara tasiri akansu sbd abun akwai d'aure kai, nide nawa adu'a na tabbatar ba wani aljannin da ya aureni kawai de haka Allah ya tsara mini, bayan wata da mutuwan Hamza su goggo hindatu suka fara kawo min magani da wasu jike jike wai na kariya duk suka nan ba sha nakeyi ba sede In ajiye mama ma sam bata goyi bayan In sha ba suna tafiya zata tayani zubarwa.

Ummana!!! Hmmm umma bata ta'ba nuna ko digon damuwanta akan lamarina ba hakan yasa na lalace na kara fad'awa, Ina rayuwane cikin duhun kai dukda na san mama na sona amma akwai abubuwan da se uwa ce kad'ai zata iya ma d'anta zan iya cewa ko azkar wannan banayi iyakacina lokacin da nake zuwa islamiyya In naje nayi karatun qur'ani achan ban sake bud'ewa se kuma In na sake zuwa yanzu da na bar islamiyyar ma se ayi sati biyu ban bud'e alqur'ani da sunan karantawa ba.

********

"Malama!!! Baiwar Allah!! Baiwar Allah!" Firgigit nayi na dawo daga duniyar tunanin da na fad'a ashe ma mun iso tuntuni yayi magana har ya gaji hankalina be kanshi se hawaye wasu samari ne suka tayashi dawo dani cikin tunani na, sauka nayi nace "kayi hakuri baba" don babba ne me acha'ban murmushi yayi yace "ba komai d'iyata ki dinga kokarin boye damuwarki duk wani tsanani yana tare da sauki komai maganinshi Allah, ki dinga kaiwa Allah kukanki kinji?".

Gyad'a kai nayi Ina mika mishi kud'in shi "In shaa Allahu na gode" da sauri ya girgiza kai "barshi 'yar nan je ki Allah ya kawo miki mafita" nace "Ameen Ameen na gode Allah ya saka maka da alkhairi" jan machine d'inshi yayi ni kuma na tsallaka kan na juya kuma ban hangeshi ba ko da gilmawanshi, ban damu ba na nausa cikin layinmu.




                      🖤Gureenjo🖤


🥀NOOR IMAN🥀

*Fatima Muhammad Gurin*
          •Gureenjoh6763 on Wattpad•

*'yar Mutan Adamawa*

💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)

                            *05*

Tsaye yake hannu a kwankwaso yana karewa room d'in kallo cikin takaici da  bakin ciki, tied vest ce baka sanye a jikinshi da black three quarter me zips dayawa a jiki, wadda hakan ya bayyana murd'ewar jikinshi da de gani ma'abocin gym ne damar bayyana.

Jikinshi gargasa ne bakake sidik a kwance gwanin sha'awa, hannunshi dake waist d'inshi d'aya ya d'aga ya shafa kwancaccen gashin kanshi da ya ji gyara tare da jan tsaki a lokaci d'aya, ya zaiyi ne wai wani irin mata Allah ya bashi? Me ta nema ta rasa da bazata iya natsuwa ta nemi lahirar ta ba se aukin yawace yawace da sunan business.

Tsaleliyar wayarshi ya zara ya danna kira, cikin yanga da wani irin iyayi da zaka iya rantsewa ko mace bazata iya irin yanganshi ba, yace "Ki zo Lil, am in my home" be jira amsanta ba ya sauke wayan tare da kwad'ata kan gadon kaman itace ta 'bata mishi rai, zarya ya ci gaba da yi cikin tafiyanshi da izza da jin kai, Allah ya gani be san ya ze yi da Hamna ba duk yadda ya d'auki lamarinta a da ya wuce nan.

Duk wani nasiha da wa'azi da yake 'bata nyaun bakinshi yake mata a banza shiga ta nan yake yi ya fita ta chan, ummu ma da yake iya gayamata matsalarshi ya fad'a mata amma wai yarantace zata dena, Ina yaranta a jikin me shekaru 25 ko Lil d'inshi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login