Follow us on social media
Showing 75001 words to 78000 words out of 131683 words
Chapter 26 - NOOR IMAN Yar Baƙin Ciki BY Fatima Muhammad Gurin
ya isa ya hanaki har shi wadda ya gina gidan, In ko ya hanaki kaman nima ya shata min layi da rayuwarshi ne" kai jawahir ta gyad'a suka juya suka shige d'akin hamna gabad'ayansu har ummu kan su shige ta nunawa zarah waje tace "wuce kiyi gida shashasha marar kishin er uwarta".
Fita zarah ta nufi yi tana kuka sossai cikin damuwan da bata san ya zatayi da shi ba, bayanta ya bi a parlorn kasa ya rike hannunta kawai se ta fad'a jikinshi tare da kara volume d'in kukanta "Hamma wallahi Allah ummu bata cikin hankalinta, hamma Noor fa tace kar na karayiwa magana Hamma taya zan iya Noor abin tausayice duk duniya bata da kawa da ta wuce ni duk waenda suke zagaye da ita Ina zargin ba da zuciya d'aya suke zaune da ita ba I badly want to help her ko wurin iya zama da Anty hamna, amma ummu...... sannan mari????" Idanunshi da suka kad'a sossai suka rine ya bud'e yace "kiyi Shiru ki dena kukan nan watakila mu kuma hakan ne kaddaranmu, but with time everything will be fine again in Shaa Allah, ohk??" Kai ta gyad'a mishi yace "me kika zo yi?".
Ta fad'a mishi yace "Ohk ki je gida and karki kara kukan nan zan kai mata kayan" Kai ta gyad'a ya goge mata fuska tare da kissing forehead d'inta ta juya ta fice shi kuma ya koma sama se ya rasa me ma ze d'auko shi ba mace ba, shawara kawai ya yanke ya tafi asibitin ya ba kalthum kud'i taje supermarket ta sayo mata duk abinda zata bukatan hakan yasa shi juyawa ya fito zuwa hospital d'in, se kuma ya samu suna fama da ita taci abinci taki.
Gadon kawai ya nufa ya zauna daidai inda kafafunta suke ya rankwafo sossai tare da d'aukan plate d'in abincin ya sa kan kafanshi ya d'ibo a spoon ya kai mata baki, ganin fuskanshi ba alamun wargi yasa ta bud'e ya saka mata hawayen idanunta na gangara, ci gaba da bata yayi hawayenta kuwa kaman an bud'e fanfo, daka mata tsawa yayi "wani irin iskanci ne wannan? Me aka miki zaki zauna kinawa mutane kuka?" Anty rahama ce tayi saurin cewa "Abdul kai wai kullum me ke kara hawa kanka ne? Ka shigo ba sallama sannan ka zauna kana turawa er mutane abinci dole harda tsawa baka ganin bata da lafiya ne meke damunka ne?" Runtse ido yayi tare da bud'esu cikin nata da hawayen suka kafe tsoronshi na taso mata sede a take tsoron yayi hanyarshi ganin shima hawaye ne kwance a kasan idanunshi wadda se ka mishi kallon cikin ido zaka iya ganewa juna suka kurawa ido.
Hmmmmmm bani da Abinda zan ce muku Annur hausa Novel.
🖤Gureenjo🖤
🥀NOOR IMAN🥀
*Fatima Muhammad Gurin*
*Gureejo6763 on Wattpad*
*'Yar Mutan Adamawa*
💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)
*036*
Cikin tausayawa ta d'aga hannunta da ba Karin ruwa a jiki ta d'aurashi kan kwantaccen sajenshi ta kuma narkar da idanunta cikin nashi cikin kasa da murya tace "hamma!!!" Lumshe idanunshi yayi wani tausayinta da wani abu da har yanzu be tabbatar menene ba na taso mishi, tattausan hannunshi ya d'aura kan nata shima cikin sanyi yace "ki ci abinci pls kinga baki da lafiya" yana kai nan ya zame hannunta tare da maida hannunshi kan spoon ya kuma d'ibowa ya kai mata baki, ba musu ta fara ci.
Anty rahama da Anty kalthum dake gefe suka had'a idanu suna dariya, waya Anty rahama ta d'auko tana cewa "Ina zarah ta tsaya ne daga d'auko kaya har yanzu bata dawo ba, bari In kirata inji" kallon Anty rahama yayi yace "Anty karki kirata zaki sa ta kuka, kalthum zo ki kar'ba ki sayo mata duk abinda kika san zata bukata a supermarket" ya karasa yana karkatawa tare da zaro dubu dubu da d'an yawa yana mikawa Anty kalthum, kar'ba tayi, Anty rahama tace "me ze sata kuka kuma Abdul? Sannan ga sabbin kaya a akwatunanta me yasa za'a sayo wasu kuma?".
Lumshe idanunshi yayi tare da waresu kan Iman dake kallonshi baya so ya sata kuka da damuwa haka kuma bayaso a kira zarah don ya Santa sarai ko zuwa yanzu tayi shiru aka kirata aka tambayeta In har zata bada labari se ta kuma yin kuka, gwara de ita Iman d'in tana gabanshi ne ze san yadda ze yi ya hanata yin kukan sossai, labarin Abinda ya faru ya basu dukda ba in details ba don main point d'in kawai ya fad'a.
Salati suka d'auka a tare Anty rahama tace "Allah ya isa fa? Ka gayawa Abba?" Anty kalthum tace "Toh kwata kwata ma me auta ta sani ina ita ina Allah ya isa?" Idanunshi na kan Iman da tayi kaman bataji abinda yace ba da mamaki yake kallonta ganin bata nuna damuwanta ba dukda kuwa shi yana iya ganin tashin hankalinta a cikin kwayar idanunta, ita kuwa tayi Alkawari bazata kara nuna mishi damuwanta akan fuskanta ta kara mishi damuwa bayan wadda ya sa kanshi a ciki Don ita ba.
Cewa yayi "Ba zan iya ci gaba da fad'awa Abba komai ba, shi karan kanshi yana cikin damuwa ummu ta chanza gabad'aya har a yadda take kula da shi da yanzu kwata kwata batayi, menene kuke ganin ze sauko da ummu ta koma kaman da?" Anty kalthum tace "Hamma ni kam wallahi ban yarda Haka kawai ummu take ba why not mu nema mata magani?" Anty rahama Tace "sannan ni inaga fad'an da Abba da kuma su baba galadima ke mata yake kara tunzurata kan Iman kuma tabbas akwai alamun asiri ko shafan aljannu jikinta, ummu yanzu ko ni da bama kwana bamuyi waya da juna ba tunda na kawo kayan auren nan ko na kirata bata d'auka bare har muyi shawarwarin da muka Saba".
Hafeez ne ya katse maganan da Abdul ke niyyan yi, ba tare da yayi magana ba ya ci gaba da bata abinci yana kallonta, ganinsu jugum jugum yasa ya tambayi me ya faru? Anty rahama ce ta bashi labari, Shiru shima yayi cikin nazari da tunani da gaske kaman yadda sukayi hasashe ne shima yana Zargin In ba asiri ba to fa akwai aljannu jikinta.
"Ga shawara" duk kallonshi sukayi har malabo, "ina da numbern Baba fufore why not mu kirashi mu mishi bayanin duk yadda takeyi ko akwai taimakon da ze iya bamu?" Anty rahama tace "yes hakan yayi ba se mun fad'awa su baba galadima ba kar hankalinsu ya fi na yanzu tashi" abinci ya kai mata baki se ta shagwa'be fuska da gira ya mata tambayar ya? A hankali kasa kasa tace "na koshi Allah in na kara amai zanyi" shi karan kanshi ba don yana kallon bakinta ba da baze ji me ta fad'a ba murmushi yayi yana ajiye bowl d'in, se suka had'a ido da en uwanshi harara ya dankara musu kan yace "ban son gulma da sa ido Allah".
Dariya suka saka har Iman seda ta murmusa yadda yayi maganan kaman irin dama wani gulman suke har had'e rai ya kara yi, kallon Hafeez yayi yace "kirashi mana y ko credit ne baka da?" Anty kalthum tace "haba ya isa manager guda?" Murmushi hafeez yayi Yana dialing numbern baban, bappansu ne wato yayan sarki na yanzu, yaki gidan sarauta Don ko lokacin babansu be rike mukami ba, sede yayi karatun Addini sossai da sossai, jama'a moddibo suke kiranshi wato malami a hausance amma su Hafeez baba fufore suke ce mishi Don duk rayuwarshi a fufore yayi wurin en uwan Mamansu da bata kasance er sarauta ba.
"Assalamu alaikum babban Aboki an tuna da ni kenan?" Murmushi Hafeez yayi yana amsa sallaman shin kan ya d'aura da "dama chan ana tunawa da kai sati biyu ne fah kawai nayi ban Kira ba ko ka manta duk juma'a se na kira d'an tsohon?" Dariya yayi yana cewa "Da gaskiyanka ka fi sauran en uwanka mussamman wannan nasaren" dariya suka saka Abdul ma seda yayi murmushi ya san da shi yake hakan yasa yace "Allah ya taimaki moddibo" yana murmushi yace "laaaa ashe Hafeez a handsfree ka sani? Yanzu yaji na ce mishi nasare baze kaini makka ba bana wayyo ni" duk dariya sukayi.
Su rahma suka gaidashi duk ya amsa yana jansu da wasa kan Hafeez yace "wani muhimmin magana ke tafe damu baba" yace "to to Allah ya sa lafiya?" Anty rahama tace "da sauki dae baba, gashi gashi gashi" ta bashi labarin abinda ke faruwa tas, bayan ta gama ya jima zaune shiru kan yace "Toh Alhamdulillah, tabbas Haka kawai ni karan kaina na san Rashida bazatayi haka ba sbd sanin halinta tun yaranta amma ance zato zunubi zan so na ganta Don in tabbatar se a nemi waraka wurin sarki me duka".
Abdul ya sauke ajiyar zuciya yace "moddibo kana ganin zata yarda tahowa ba dalili?" Yace "zan kirata da kaina in Shaa Allahu sannan kan nan zan sa d'alibaina su fara yi mata sauka da adu'o'i" godiya suka fara mishi yace "khayya ku nayiwa ko 'yata nayiwa ban son azar'ba'bi" dariya sukayi duk maganan da sukeyin nan da fulatanci sukayi sallama ya musu ya kashe wayan.
Duk ajiyar zuciya suka sauke dukda Iman bata ji ko da kalma d'aya da sukayi ba ta de san in Shaa Allahu anyi nasara daga yanayin fuskansu, hira suka ci gaba dayi su uku Anty kalthum ta fice sayo mata abubuwan anfanin kaman yadda ya bukata, Amma har ranta ta rike In ta had'u da Hamna se ta dankara mata zagi ko mari yadda zata huce takaicin marar musu auta da ta sa akayi.
Hafeez ne ya mishi bayanin ya kar'bi result na test d'in ya kai office d'in Doctor Ameerah, da kai kawai ya amsa sun d'an jima kan kalthum ta dawo da kayyayaki a hannunta kar'ba yayi duk suka fice zuwa haraban asibitin Hafeez kam office ya wuce, murmushi yayi yana tauna lips very naughty yace "tashi muje In miki wankan tunda baza ki iya ba" waro ido tayi a kanshi.
Kau da fuskanshi yayi yana zare mata ruwan hannun hannunshi ta rike idanunta na cika da hawaye, "menene?" "Kayi hakuri dan Allah" yace "ikon Allah me kikayi?" Shagwa'bewa tayi tace "wallahi zan iya da kaina" girgiza kai yayi se hawaye sharrr, murmushi ya saki yana goge mata da d'an yatsanshi yace "to sarauniyar kuka na duniya, up we go in rakaki toilet d'in but ni zan shiryaki In kin fito" shirin sauka ta fara ganin tana d'an layi Don jikin ba wai Karfi yayi ba, hakan ya sa ya d'auketa chak a hannunshi sukayi toilet se da ya ajiyeta ya had'a mata ruwan wanka ya tabbatar zafin yayi daidai tukun ya juyo kanta se yaga tana kallonshi ido ya kashe mata da kai ya nuna mata ruwan.
Pouting tayi ta kalli kofa ta kalleshi, juya idanunshi yayi yace "kika sake turomin bakin nan ko!!!" Gyara bakin tayi tace "kayi hakuri" girgiza kai yayi yace "no ki sake plz" kanta ta dukar murmushi yayi yana cewa "bazan fad'i me zan miki ba amma plz ki sake I love it, na san me hali be fasa halinshi, kiyi wanka In kin gama ki kirani" ya juya ya fice yana murmushi, murmushin itama tayi ta fara wankan a hankali cikin taka tsantsan Don ji take kaman zata fad'i.
Seda ta gama wankan tukun taga tsiyan da ya mata towel babba da karami Anty ta sayo tabbas ta gani se ya ajiye mata karamin kawai ya fice abinshi gashi kayan da ta cire ta zubasu cikin brockets d'in ruwan da ta gama wanka tayi niyyan wankesu ne ma se taga bazata iya ba, dafe kai tayi tana furta Innalillahi, a razane ta kalli bakin kofa jin an kwankwasa muryanshi taji yana cewa "are you done?" Shiru tayi tana hararan kofan kaman shine a jiki kawai se taga ya bud'e da sauri ta juya mishi baya tana rintse ido.
Bayanta ya kurawa narkakkun idanunshi yana kallo daga kafanta har zuwa saman cinyoyinta kad'an da suka bayyana zuwa bayanta wuyanta da gashin kanta ke d'igar da ruwa kad'an kad'an na wanka, da kyar yayi jarumtar fusgo numfashinshi har jikinshi seda ya d'auki rawa tsabar yadda take half naked ya d'auke mishi hankali.
Ajiyar zuciya ya sauke tare da shigowa ciki yana nad'e hannun riga ya d'auketa chak zuwa kan gadon asibitin
Mai da dama ya fitar ya bud'e ya sa a hannunshi cikin wani salo ya fara shafa mata idanunta ta kara runtsewa tsikan jikinta na tashi malami na ba anji jiki me taushi ba daga shafa mai se aka nemi zarmewa amma sak abinda ya faru ranan shi ya kuma faruwa yau.
Da sauri ya sa mata doguwar riga me kauri da pant dukda yadda take sumewan tana farfad'owa tare da jan numfashi kaman asthmatic, da sauri ya fita har yana had'awa da gudu zuwa office d'in Doctor Ameera yana kwala mata kira su Anty rahama da suka biyoshi suna tambayarshi menene yayi banza dasu da gudu suka fad'a d'akin ganin yadda takeyi yasa suma suka rud'e.
Ko knocking be yi ba ya riko hannunta be ma san yayi ba ya fara janta duk ya bi ya d'aga hankalinshi da gudu itama take binshi dukda shi sauri yake yau ma irin allurar da aka mata jiya aka mata se da yayi hawaye, me ke damunta ne haka? Seda ta samu bacci kan Doctor Ameeran ta fito, tana sauke ajiyar zuciya "menene ke damunta ne dr.?" Ya jefowa Doctor Ameera tambayar.
Kwantar da kai tayi tace "wallahi Dakta ban sani ba duk wani irin ciwo da nake tunani an mata tests d'insu babu su a jikinta ciwonta da dama na ga record d'in a file d'inta high bp and heart attack amma shima taji sauki sossai da sossai, to wannan kam ban san dalili ba" dafe kai yayi yana cewa "ko waje za'a fita da ita?" Sauban da tun d'azu ya zo wurin yace "Da waje da nan duk d'aya malabo tests da muka mata shi zasu mata mu kara hakuri dae muga ko zata sake samun attack d'inshi, se kuma a kara mata wasu tests d'in da suke da shige da irin ciwon."
Ba don ya so ba ya aminta sbd dama sauban d'inne abokin shawara, su Anty rahama ma sunyi na'am da zancen sauban d'in, d'akin suka koma suka zauna shi kuma ya zauna bakin gado tare da kura mata idanu, Abba ne ya shigo da sallama duk mikewa sukayi "Abba Sannu da zuwa" yace "yauwa ashe duk kuna nan kun barni hangame da baki ban san daughter na ba lafiya ba" Shafa kai Abdul yayi yace "Abba kayi hakuri na manta ne wallahi gashi abubuwa sun min yawa".
Abba yace "ba komai Hafeez ya min bayani har abinda ya faru jiya, kunyi kokari Allah ya ganar da mahaifiyarku" duk suka amsa da Amin ganin yanayin malabon yasashi tambayar ko ya jikin? Bayani ya mishi akan sake tashin ciwon, shima kwarai yayi mamaki to wani irin ciwo ne wannan, ya d'an jima dasu kan ya musu sallama ya tafi.
Yini chur Abdul yayi a asibitin duk hankalinshi ba a kwance ba ganin bata farka ba har yanzu Anty rahama taje gida tayo musu abincin rana yayinda ta taho da mai aikinta wata tsohuwa akan ta kwana da iman yau kam kar ya kwana asibiti bayan ya yini zaune, nunawa yayi baze iya ba hankalinshi baze kwanta ba In baya tare da ita, Shiru kawai Anty rahama ta mishi Anty kalthum tayi musu sallama akan se gobe da safe ta fice.
Biyar daidai wayanshi ya fara kara dubawa yayi se yaga hamna ajiyewa yayi ba tare da ya d'auka ba nan ita kuma Tace se ya d'auka a jere a jere ta mishi miscall kusan goma kan ya d'auka yana tsaki, "kace kai me adalci ne kuma kana adalci amma banga alamu ba kwanana ya shiga amma har yanzu baka dawo ba" cikin kasan makokoro yace "kiyi hakuri mana ki bar mata kwanan bata da lafiya she can't sleep all alone" Tace "wallahi ban bayar ba In baka dawo ba Allah ya isana ban yafe ba Haka kawai In d'auki kwana In bata, bata isa ba kuwa In taga dama ba rashin lafiya ba ta mu...." kit ya kashe wayanshi yana d'agowa suka had'a ido da ita.
Murmushi ya sakar mata ita kuma ta mishi yake ita kad'ai ta san abinda take ji banda ciwon dake damunta, "sannu Bari In kira Doctor" Kai ta gyad'a mishi ya mike ya fice ba jimawa ya dawo da dr. Ameera ta duddubata komai lafiya se ciwon kan de da zafin jikin, "dakta a jika towel a ruwa a dinga share mata jiki sbd idan zafin jikin nan ya fi haka it might be possible ta sake samun wani attack d'in".
Anty rahama ya kalla yace "Anty ki zo ki mata" Tace "aaa ba za ka mata ba?" Ya girgiza kai "zan tafi gida ne zan dinga kiranta a waya after every 30mins inji jikin kan inyi bacci hope baaaba zata iya?" Ya karasa yana kallon baaban tace "In Shaa Allahu Alaji za'a kula" gyad'a kai yayi ya mike se yaji ta rike hannunshi juyowa yayi dama abinda take so kenan ya kalleta taga yaki kallonta.
"Tafiya zakayi?" Ta furta cikin murayar marasa lafiya, zame hannunshi yayi tare da maidashi goshinta ya d'an rankwafo kad'an kan yace shima cikin kasa da murya "In Shaa Allahu gobe da safe zan zo Ina fitowa sallahn asuba, ki kula plz" Kai ta gyad'a idanunta na cika da hawaye d'an kallon kwayar idanun yayi yace "baki so in tafi ne?" Girgiza kai tayi, uwargida tayi kira Ai dole ya tafi.
"Allah tashemu lafiya, ka san halin rayuwa ka yafemin In na mu.." "menene haka??? Wa ya gayamiki zaki mutu?" Sassauta murya yayi yace "dan Allah ki dena ambaton mutuwan nan bana son jinta In de a kanki ne ke se kin haifamin yara dayawa masu kama dake se kin zagaya duniya har ki ce kin gaji da hawa jirgi, se kinyi rayuwar farin cikin da ba wacce ta ta'ba samun irinta a fad'in duniyan