Follow us on social media
Showing 63001 words to 66000 words out of 131683 words
Chapter 22 - NOOR IMAN Yar Baƙin Ciki BY Fatima Muhammad Gurin
fice ta juya da nufin komawa kenan taji an bud'e kofan dake tsakiya dakatawa tayi se taga shine, juyawa tayi da nufin komawa taji yace "Ina kuma zaki?" Tsayawa tayi be kara kula ta ba ya nufi dinning.
Abinci ya d'iba da d'an yawa Don ko breakfast be yi ba, ba tare da wani damuwa ba ya hau cin kayanshi, gajiya tayi da tsayuwar hakan ya sa ta nufi dinning d'in har ta ja kujera zata zauna yace "koma ki sa d'ankwali" baki ta tura ya d'an kalli lips d'in kan ya kalleta ya kau da kai, d'aki ta koma ta sanyo d'ankwalin ta zauna ta d'ibi abincin kad'an ta fara ci tana dafe kai.
Ya jima da gamawa yana zaune ne kawai yana aikin kallon abinda take yi cin abincin take kaman me cin magani tana 'bata fuska hannunta dafe da kai, mikewa yayi ya shiga d'akinshi chan ya fito da paracetamol ya ajiye mata a gefenta a hankali tace "thanks" kan ya juya yayi komawanshi, bayan ta gama cin abincin kuwa ta sha, a wurin ta bar komai to ko ta tattare bata san inda zata kai sauran abincin ba.
Kwanciya taje tayi bacci ya kuma surarta ba ita ta farka ba se la'asar wasai taji ta ba ciwon kan kuma, sallah tayi ta zauna danna waya, Instagram ta shiga tana ta kallon hutunan bukin mutane, wani wadda ta gani nasu da wasu account suka sa ne ya mata kyau sossai, wadda ya duka a gabanta hannunshi na kan takalminta yana cirewa ita kuma tana d'an lekan abinda yakeyi hoton yayi kyau sossai dukda sides d'in su ne ba full ba.
Saving tayi a wayanta ta koma settings ta d'aura shi a wallpaper d'inta yayi kyau sossai kuwa tunawa tayi da bata mishi godiyan wayan ba, to yanzu ita ta Ina zata mishi godiyan? Ta'be baki tayi ta ci gaba da danne dannenta gabad'aya ranar zarah bata shigo mata ba har dare, ba tare da tayi wanka ba ta chanza zuwa kayan bacci, tayi kwanciyarta bayan ta kira Mama taji jikin da sauki, maman ke fad'a mata gobe zasu wuce.
Da tunanuka fal ranta tayi bacci, wuraren 10 ya shigo duba ta ya samu kuwa ta jima da yin bacci, ya jima tsaye yana kallonta kan ya ja mata blanket ya kashe mata wuta ya fice, kiran sallahn farko ya farka kaman yadda ya saba yayi wanka yayi nafilfilinshi adu'anshi guda kar fushin Ummu yayi tasiri a kanshi yana rokon Allah ya sassauta mata jin haushin matarshi, adu'o'i sossai ya musu kan a kira sallah.
Mikewa yayi ya fito d'akinta ya fara lekawa ya ganta tsaye tana mika dayake tana farkawa ta kunna wuta, da sauri ya kawar da kai yana tsaki ya fice, toilet ta fad'a tayi alwala tazo tayi raka'atanil fajr tayi sallahn asuba kan ta d'auko wayanta qur'an app da tayi downloading jiya ta bud'e ta fara karantawa, seda gari yayi haske kan ta mike ta shiga wanka bayan ta fito ta shafa mai ta d'auko wata atampha A shape gown anyi ado da pattern d'in rigan red ta sanya.
Katon gyale ta d'auko ta ajiye bakin gado bayan ta kafa d'aurinta, akwatinta take gyarawa ta fara jin kamshinshi lumshe ido tayi kamshin na shiga har ranta, bata gama dawowa daga duniyarshi ba taji sallamanshi, amsawa tayi kan ta zame kasa ta gaidashi, sanye yake cikin kananun kaya bakake as usual kanshi se shekin mai irin na gyara yakeyi haka sajenshi zuwa gemunshi.
Amsawa yayi yana cewa "ya headache d'in?" Tace "Alhamdulillah yayi sauki" ba karamin kyau ta mishi a haka ba hakan ya sa ya d'an tsaya yana kallonta, ganin ta d'ago sun had'a ido yasashi cewa "breakfast" Kai ta gyad'a ya fita tabi bayanshi, kaman jiya yau ma Shiru Shiru sukayi breakfast d'in bayan sun gama ya dubeta yana cewa "karfe 9 jirginmu ze d'aga so make sure kin gama duk abinda zakiyi before 8:00" hankalinta na kanshi tace "In shaa Allahu, Dan Allah in su mama basu wuce ba inje In duba jikinta?" 'Dan Shiru yayi kan yace "saura sun wuce mama kuma da ita zamu tafi don i don't think zata iya tafiyar mota".
Mikewa yayi ya fice, zama tayi tana aikin sake sake da tunane tunanen yadda ya damu da en uwanta musamman mama ya d'auketa kamar mahifiyarshi yana darajata fiye da tunani, har time ya qure se ganin Zarah tayi a kanta duk murmushi suka sakarwa juna kan Iman tace "nayi missing d'inki wallahi, kika kama kika tafi kika barni ni ka.." se kuma tayi shiru, hararanta zarah tayi kan tace "karasa mana....." murmushi kawai Iman tayi kan ta mike suka karasa d'aki suka fiddo akwatin Iman d'in yafa gyalenta tayi saman ka, ta riko wayanta a hannu suka fito.
Mota suka shiga direct zuwa part d'in nenne, nasiha sossai tsohuwar ta mata kan ta bata wani leda tana fad'amata duk bayanin yadda za'ayi anfani dasu yana ciki, sossai tayi mata godiya har da hawaye, zarah ma ta taya ta kan suka fito zuwa sashen me martaba nan suka samu duka family d'in har da su hamna nasiha sossai shima ya kuma yi musu yaja hankalinsu akan su zauna lafiya.
Sallama sukayi mishi suka fito, ganin duk su Nabeeha kowacce da akwatinta yasa Iman jin daad'i, jiransu sukayi har suka karaso kan suka jera, Iman tana murmushi Tace "masha Allah, baba ya yarda kenan Amma tare zamu zauna ko?" Teema tace "ke rufa mana asiri, ki bari mu tafasa kan mu kone" kallon mamaki Iman ta musu Ameerah tace "A to Haka kawai kisa yaya Abdul suburbud'anmu muna zaman zamanmu" Nabeeha tace "In banda abunki ma Ina mu Ina tarewa gidan Amaryar shekaranjiya" zee zatayi magana Iman tayi gaba alamun tayi fushi tana cewa "ba se kun min terere ba malamai, In kun ga dama kar ku zo har ku dawo" dariya suka saka gabad'aya, wadda hakan ya maida hankalin Hamna kansu, haushi ne ya kamata har wuya.
Tirrr wallahi da rayuwar family d'insu ace tana er uwarsu amma suka wani je suka makalewa kishiyarta bare a cikinsu, motoci suka shiga tuni akayi dasu Airport, bayan sun sassauka ne Iman taga Mama wurinta ta karasa tana rike hannunta take cewa "mama ya jiki?" Tana murmushi tace "naji sauki Ai Iman Alhamdulillah" tura baki tayi gaba tana Shagwa'ba dama mamance take sakankancewa tayiwa shagwa'ba son ranta, tace "tun fah Jiya nake ta so in ganki" murmushi Mama tayi kan tace "to ba ga ni ba" tana kallon fuskan Mama Tace "yanzu In kinje gida mama wa ze kula dake? Pls pls mama ki rokeshi muje gida tare In kin warke se na bishi".
Mama na hararanta tace "ke rabani wani irin rashin hankali ne wannan? Ke kam se yaushe ne zakiyi hankali ne wai? Yanzu aka ce ki bi ni se kije?" Rau rau tayi da ido zatayi kuka se suka had'a ido murmushi ya saki yana girgiza kai tun d'azu yake kallonta dukda ba jin me suke fad'a yake ba amma yana kallon yadda take zuba ma mama shagwa'ba se yaji ina ma shi takeyiwa, Allah yayi shi da son mace me shagwa'ba amma hamna sam bata iya ba itakam wai komai a yi shi classy shagwa'ba kaman zubda kima ne.
Kau da idanunta tayi zatayi magana se ga Zarah da Hafeez sun iso wurinta tana nuna ta tace "ka ganta nan Hamma Hafeez itace amaryar yayan" murmushi Hafeez yayi yana kallonta yace "Anty na barka da safiya" waro ido tayi tana cewa "innalillahi Mama kiji Hamma Hafeez ni yake gaisarwa harda kirana Anty" tayi maganar kaman zatayi kuka (karku manta dama chan na gayamuku Iman macece me faran faran da surutu rayuwa ne ya maidata haka, gashi yanzu ta fara sakewa sbd irin mutanen da take had'uwa dasu masu sonta tsakani da Allah).
Hafeez na murmushi yace "Mama Ai Anty na ce tunda matar yayana ne" Mama tace "da hakan ma amma Ai ko matar yayanka ne ka girmeta Don haka be kamata ka kirata Anty ba, sede ita ta kiraka baba ma" waro gabad'aya idanunshi yayi zarah ta kwashe da dariya Iman na tayata, "baba kuma" ya fad'a kaman ze yi kuka, Iman na murmushi Tace "eh mana sunan babana gareka" yace "ahhh nide gaskiya banson wani baba Ina laifin hamma Hafeez d'in?" Iman tace "a'a da kunya mana gwara de in dinga cewa baban" zarah na dariya har yanzu Tace "baba hafeez, Tab" d'aga hannu yayi da nufin maketa da sauri tayi bayan Mama tana dariya.
Isowarshi wurin ne yasata had'iye dariyarta amma har yanzu fuskanta washe, cewa yayi "Kai wai se yaushe zaka girma ne hafeez? Kana ga mama bata da lafiya amma ka biyewa yaran nan kuna sakata surutu tuntuni, to ku wuce mu tafi" sum sum suka nufi shiga cikin Airport d'in har zuwa gaban jirgi Anan ne ma Mama suka had'u da ummu, gaisheta mama tayi amma ko kallon arziki bata samu ba, sema shigeta da tayi zuwa cikin jirgi.
Da mamaki mama tabita da kallo, Iman dake bayanta ne tace "mu je Mama" ajiyar zuciya ta sauke kan ta fara taka matattakalar zuwa ciki Iman ce ta kama hannunta zuwa sit d'inta se sukayi sa'ar samun sit d'aya da maman, kallon gefe da gefe zuwa baya tayi a fili Tace "Tab yau en gidan lamid'o sunyiwa masu jirgin nan ciniki" murmushi Mama tayi gaskiya suna dayawa gayya guda.
Daga inda take zaune tana hango Abdul da suka samu kujera d'aya da Hamna wani iri takeji a zuciyarta da ta rasa menene ji take kaman ta tashi taje ta finciko hamnan ta zauna wurin maganan mama ne ya dawo da ita hankalinta "Iman kaman mahaifiyar Abdul bata sonki?" Ajiyar zuciya ta sauke ba tare da tayi magana ba, "Ina so muyi magnan anan ne sbd In mun je kano ba lalle mu samu ke'bewa ba" A hankali iman ta bata labarin abinda ya faru tana hawaye.
Karan text taji a wayanta wadda hakan yasa ta d'ago wayan tana kallon fuskan, number ne special one, an rubuto "you promised but you failed" ta karanta yafi sau abinda yafi bata gane ma'anan hakan ba se ta maida hankalinta kan Mama dake cewa "na sani Iman zama da uwar mijin da bata sonka babban kalubale ne dukda kuwa ba gida d'aya zaku zauna ba, Ki kiyaye plz na san tarbiyarki amma ki kara ki zama me hakuri akan duk abinda zata miki, karki kuskura kice zaki bud'i baki ki amsa mata sbd komin son da mijinki ke miki da zaran kin fara raina mahaifiyarshi darajarki zubewa ze yi a idanunshi, sannan karki gaji da yi musu alkhairi abinci kowanne juma'a haka da kyauta, dukda basu rasa ba amma kyauta be kad'an ko da bata kar'ba ki ci gaba.
Ki zama me mata biyayya fiye da yadda 'ya'yanta suke mata in shaa Allahu zata so ki watarana" kuka Iman ke yi abinta in fa ta tuna ko gaisuwar mijinta bata amsawa se taji hankalinta ya tashi tana tsoron kar ta koma mishi irin ummanta, nasiha da ban baki Mama ta dinga mata akan yadda zata zauna da uwar miji, sossai hankalinshi ya d'aga ganin irin kukan da takeyi gashi ba halin yi mata text sbd sun tashi, me yasa ta mishi alkawari ta karya shi da yayi alkawarin baze kara barin hawayenta zuba ba se gashi tana chan tan kuka shi yana nan yana zaune.
Zafin kukanta yake ji har cikin ranshi, jinginar da kanshi jikin kujera yayi tare da lumshe ido ko uhm be had'asu da er mulkin nashi ba ita a dole tana fushi dashi yayinda shi ko iskar da ya kwasota ma be kalla ba, a haka suka sauka Kanon dabo, drivers kusan biyar da motoci daban daban ne suka zo d'aukansu, Anty rahma da Anty kalthum kuma mazajensu.
Dayake da 'ya'yan Anty rahma da ta bari gidan Ummu kan ta wuce aka tafi adamawa da gudu sukayi wurin babansu, sallama tayiwa Abba da ummu akan se anjima da yamma zata kawo boxes d'in akai gidansu Iman su kalla se a kai mata kayanta daga chan, Anty kalthum ma sallama ta musu tabi mijinta, Abba ummu da Hafeez suka shiga mota d'aya, zarah, Nabeeha, Ameera, zee da teema suka shiga d'ayar Picnic d'in, se Mama ta shiga d'aya da kayanta Abdul yayi ma drivern bayanin unguwarsu Iman d'in ya tabbatar mishi In sun isa unguwan mama zata mishi kwatance da kyau.
Seda yaga fitansu kan ya shiga gaban d'ayar motanshin, Umma, hamna da Iman suka shiga baya suka fice, dukda yana mamakin me ze sa umma ta bi su gidansu ba gidan Ummu ba amma ya kasa magana, ya san biyosu da tayi da biyu akan Iman da har yanzu take hawaye musamman da mama zata tafi kukanta har da shesheka takeyi ita har ga Allah tsoron su hamna ne ma ya shigeta.
In shaa Allahu baze bari su kuntata mata ba daga ita har uwarta dalilin da ya hana manya su haneta tarewa gidanshi shi ko baze ki mata rashin M ba In tace zata hana Iman zaman lafiya BS BS ne ze zama tsakaninsu, da wannan tunanin suka karasa gidanshi, fita yayi Iman ma tayi saurin fita tana share Hawaye shi mamakin hawayenta ma yakeyi ace mutum kullum se yayi kuka?.
Ciki ya nufa tabi bayanshi har sama nan ma kaman Gidan lamid'o d'akuna uku ne a jere a parlorn saman se babban kitchen d'insu daga gefe, ta lura d'akunan kasa sunfi na saman yawa sede bata san girmansu ba, Dayake Abba ya fad'amishi anyi mata furnishing room d'inta da ya kasance daga hagunshi komai na bukata an saka mata, kitchen kam Dayake guda d'aya su biyu Komai na ciki aka chanza.
Har cikin d'akin ya mata jagora shi karan kanshi d'akin ya burgeshi gashi colors d'in da yake so, royal sets ne had'add'u black and Ash, dayake duk d'akunan saman masu Part biyu ne bedroom and parlor amma irin waenda suke a had'en nan kaman yadda nayi bayanin d'akinshi daga farko, kujerun ma kad'ai abin kallo ne in taga dama zata iya kwanaki a d'akin nan bata fita ba In har ta sa fruits da drinks a fridge d'inta na ciki, Ac har biyu ne a d'akin ga katon plasma da decoder d'inshi gaban had'ad'un kujerun da tsakiyarsu ya kasance da had'ad'iyar center table me wani shape na ban mamaki.
Ko tana kwance kan gadonta zata iya kallonta ba tare da wani hijabi ba, wall to wall wardrobe d'inta ma kad'ai aka bar wani bakyauyen dashi se ya d'auka wata kasa yake, anyi laying bed nan abin sha'awa, ga dressing mirror d'inta d'an d'as dashi me full image, kuka ta kuma rushewa dashi wadda ya sa shi dafe kai, daga cewa "ga d'akinki" se ta sa mishi kuka, Lord have mercy ya furta beneath his breath.
Juyowa yayi ya kalleta yace "Wai ni kam baki tsoron hawayenki su kare ne da kukan nan? Ayi mutum shi kullum kuka? Saudah bazan iya ba Alkawarin kulawa dake da hanaki sake kuka na d'auka amma banga kina shirin tayani cika wannan alkawarin ba sema karyashi da kike ta aikin yi, to bazan iya ba In ke bakya jin zafin kukanki to ni yana damuna" hawayen ta share cikin rawar voice tace "kayi hakuri, nima ba cikin son raina nake kukan ba, yanzu kam ma kukan farin ciki ne wai wannan shine d'akina? Irin d'akin da sede mu kalla a waya ko a tv wadda ko gidajen masu kud'in ma da wuya ka samu irin wannan wai nice a ciki kuma komai na d'akin mallakina ne? Na gode da karamcinku gareni, na gode, na gode, bani da abin cewa Abba se Allah ya biyashi da gidan Aljannah, yaji kanshi kaman yadda yaji kaina, ya saka mishi da d'inbin alkhairi duniya da lahira, Allah ya biyamishi bukatunshi na alkhairi yaci gaba da bashi dukiya ta hanyar halal ya kareshi daga sharrin dukkan abin ki ko mutum ko aljan......"
Kuka ne ya sarke ta hakan yasashi karasawa ya sanyata jikinshi yana shafa bayanta a hankali yana d'an jujjuya jikinshi alamun rarrashi ko ince irin jijjigan da akeyiwa yara In sun fara bacci ba'a so su tashi, lub tayi tana sauke numfashi sun jima a haka kan suka ji an banko kofa🤦♀️
🖤Gureenjo🖤
🥀NOOR IMAN🥀
*Fatima Muhammad Gurin*
•Gureenjo6763 on Wattpad•
*'Yar Mutan Adamawa*
💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)
*I am really really sorry wallahi Ina busy ne kwana biyun nan kuka ji ni Shiru and har yanzu ban gama abubuwan dake gabana ba In kun samu gobe to In kuwa baku samu ba kuyi hakuri zuwa jibi, and please ina barar adu'o'inku gobe in Allah ya kaimu zan d'au hanya tafiyar 12hours A yafi juna*
*032*
Hamna ce tsaye rike da kwankwaso tana watso musu kallon rashin mutunci, cikin masifa tace "ka kyauta kenan yaya Abdul? Tunda haka ka za'ba shikenan gobe de kwananta ya kare tunda de bazawara ce" sake Iman yayi yana kallon fuskanta yace "kiyi wanka ki huta zan fita In na dawo zan ganku" tsintar kanta tayi da cewa "Toh Allah ya tsare ya kiyaye se ka dawo" wani kallo ya mata yana sake murmushi kan ya d'an kalli hamna da ta choje bakin kofa kaman d'akinta girgiza kai yayi kan yace "Ameen thanks dear" ya zagayeta ya wuce.
A kafatanin rayuwanshi be ta'ba wai don ze fita ko ze yi tafiya hamna ta mishi adu'a ba, gwara ma farkon Aurensu tana cewa take care amma banda yanzu, hannun hamna ya kama suka fice d'akinshi ya shiga da ita Don ya san d'akinta uwarta na ciki, suna shiga ya saketa ya juyo yana kallonta yace "Kubra! Kubra!! Kubra!! Sau nawa na kiraki?" Tace "uku" tana wani 'bata fuska yace "kin san Allah in baki shiga hankalinki dani ba, ba abinda ze hana In had'a dake da wacce ta kawoki duniya In koraku waje, karki natsu In kin ga dama" ya juya ya fice, what wai ita da uwarta ze had'a ya Kora akan wanchan shashashan yarinyar? A fili tace "duk abinda