Follow us on social media

Showing 114001 words to 117000 words out of 131683 words

Chapter 39 - NOOR IMAN Yar Baƙin Ciki BY Fatima Muhammad Gurin

nan ya juya motar sukayi gida a hankali yake jan motan yana kara jan lokaci basa magana sede ya lalu'bo hannunta ya sanya cikin nashi a lokaci d'aya kuma yana bin wakanshi wadda na larabci ne kad'an kad'an kawai takeji amma ta fahimci na soyayyane.

Se past ten suka shiga gidan sun samu motar hamna da alamu ta shigo a tare suka sauka suka jera zuwa sama shi ke rike da ledojin a kofan hamna ya tsaya yayi knocking tana bud'ewa ya mika mata kallonshi tayi ranta na kuna bata so suka shigo yanzu ba shirin fita d'akin Iman take tayi wankan maganin nan amma sun kwafsa mata suka dawo da wuri, kar'ba kawai tayi ta juya ciki, d'akinshi ya shiga da d'ayar itama Iman d'akinta ta shiga ta tu'be kaya ta watsa ruwa tana fitowa ta shirya cikin kayan baccinta purple masu taushi riga da wando ta saka hula a kanta tare da sanya hijab.

Fita tayi zuwa kitchen ta san dole ne kawai taci shiyasa gwara ta kawo plates da cups tun be sata ba, a d'an karamin tray ta shiryasu ta fito zuwa d'akinshi har ta kai kofa se kuma ta dakata ajiyewa tayi ta nufi d'akinta ta tuna turaren da Nenne ta bata tace ta tabbatar se zata ke'be dashi zata shafa karkuma ta yarda wani namiji yaji kamshin a jikinta In ba shi ba Don wani sirri ne ciki.

Direct karamin kit d'inta ta nufa ta d'auko ta bud'e ta d'auko turaren garin bud'ewa abu kam ya zube kusan kwatanshi a kayanta bayan ance d'an kad'an kawai zata shafa bayan wuyanta haka ta fasa shafawa ta mike ta fito duk kamshin ya dameta.

Trayn ta d'auka ta shiga d'akin da sallama tsaye yake yana fesa body's pray da alamu shima wankan ya fito Don sanye yake da bathrobe fara me bud'ad'en kirji igiyar kawai ya d'aura kuma iyakarshi kasan guiwanshi kafanshi sanye da farar silifas d'inshi me gashi da a d'akin kawai yake yawo dashi, yana ganinta ya sakar mata murmushi ta cikin madubin itama ta mayar mishi tana ajiye abubuwan hannunta kasa gefen dardumanshi inda taga ledojin, zama yayi ya juyawa madubin baya yana kallonta.

Tana ajiyewa yayi mata hannu akan tazo isa gabanshi tayi a hankali cikin wani irin tafiya ta Jan hankali wadda bama ta san tanayi ba, tana sa hannunta cikin nashi ya fisgota kan kafanshi ta zauna lumshe idanunshi yayi na seconds ya bud'e take idanun suka rine kamshin turarenta yake ji har cikin kwakwalwanshi wani irin kamshi me fisgar hankali, hijabin jikinta ya cire tare da hulan gashinta ya baje don garin cire hulan ya zare da band d'inta.

Rud'ewa ta fara jin fuskanshi cikin wuyanta yana shunshunata yana wani lumshe ido cikin kasa sossai da murya yace "wani irin turare ne wannan hayatee?" Tace cikin rawar murya "nenne ce ta bani" yace "uhmmm akwai daad'i ki samin kullum kinji?" Tace "uhm" tana zillewa sede kam ya riketa da kyar ya iya controlling kanshi ya d'auketa chak zuwa kan darduma shima ya zauna ya sanyata jikinshi da hannu d'aya ya bud'e kazan ya fara bata da kyar take tauna jikinta na tsananta rawa haka gabanta na fad'uwa kad'an kawai taci shikam ko loma d'aya be iya yi ba ya tsiyaya mata fresh milk d'in.

Garin bata ya zube a jikinta sbd yadda jikinshi ke rawa kokarin gogewa take ya rike hannunta ya kara tsiyayar mata da sauran a fatan jikinta ya d'auketa chak zuwa kan gado, inda ya zuba ya fara bi yana lashewa yana isa daidai inda turaren nan ya zuba ai se ya rud'e mata, ya fice hayyacinshi gabad'aya duk yadda take son mai magana ya hanata se hannunshi da ya mika ya kashe wuta.

****

Salap salap take takawa zuwa tsakiyar d'akin Iman d'in tana ta'ba kofar tajishi a bud'e murmushi tayi tana tuna yadda umma tace tayi ai wankan magani base ka jika kanka ba ko shafawa kayi is Ohk, daga ita se towel tana isa tsakiyar d'akin ta yasar ta fara shafa maganin tana cikin jujjuyawa tanayi kenan tsantsin tiles ya kwasheta ihu tayi tana ambatan "Umma!! Wayyo Umma na" bata kai kasa ba ta samu ta rike kujera ajiyar zuciya ta sauke tana karasa shafawa da sauri ta gama ta kira sunan Iman sau uku ta d'aura towel d'inta ta fito.

A 'bangaren umma kuwa itama seda ta tabbatar kowa yayi bacci kan ta bud'e jakanta ta d'auko layun ta fito, da sauri zahra dake safa da marwa ta 'buya bayan labule sadap sadap ta wuce zuwa waje zahra na binta a baya har bayan windown Abba inda wasu en flowers suke an zagaye da interlocks tonewa tayi sossai ta yi duk wani abinda boka ya sata tana mikewa kenan taji wani abu ya tsikareta daga kanta zuwa kafafunta kanta ta Sosa ta juya ta koma d'aki zahra dake la'be ta fiddo wayanta ta kira Hafeez yana d'agawa tace "sameni bayan windown Abba" a hankali fitowa yayi ta nuna mishi wurin tare da fad'amishi abinda umma tayi, kallon time yayi wuraren biyu ya tabbatar baba fufore ya tashi sallah dukda yana jin ba daad'i kira a lokacin kar ya d'aga mishi hankali amma ba yadda ze yi basu san wani irin mugun illah abinda ta binnen nan ze musu ba.

Kiranshi yayi a ringing na biyu ya d'aga da sallama kan yace "hafeezu lafiya dae ko?" Hafeez ya amsa sallaman kan ya mishi bayani abinda ke faruwa sede be fad'amishi umma bace, salati baba yayi ya sallamar kan ya fad'a mishi wasu adu'o'i yace ya dinga nanatawa har ya tone layan yana gama tunewa yayi fitsari kai kan ya kone, nan take sukayi sallama Ai ko ya fiddo zahra ta koma ciki kawo ashana da kerosine kan ta fito yayi fitsarin suka kone layun tas suka koma d'akunansu.

******

Asubar farko ta farfad'o daga wahalalliyar baccin da ya kwasheta tun cikin daren ba karamar baqar wuya da azaba tasha hannun mutumin nata ba wadda shi ya tunkaretane da duk wani karfinshi sbd sanin ita d'in ta sha aure ba ta'bawa ba yaci ace ta san duk kalan mazan wadda alamarin da ya farun ya zo masa a asalin bazata sbd be zata ba sam be ta'ba kawo haka a zuciyarshi game da ita ba.

Tunda ya samu kanshi yake aikin gadinta idanunshi a kanta yayin da hannayenshi suke cikin nata, cike yake da sabuwar soyayya, tausayi, farin ciki da murnan babu wadda ya ta'ba sanin masa mata, se yanzu ya tabbatar da Don shi kad'ai akayi NOOR IMAN haka itama Don ita kad'ai aka halliceshi sbd zuciya da gangar jikinshi ita kad'ai sukewa mahaukaci da fitananniyar soyayya.









                    🖤Gureenjo🖤


                🥀NOOR IMAN🥀

*Fatima Muhammad Gurin*
          *Gureenjo6763 on wattpad*

*'Yar Mutan Adamawa*

💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)

*ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH NA GAMA JARABAWATA LAFIYA NA DAWO MUKU DA CI GABAN NOOR IMAN DAGA INDA MUKA TSAYA, NA GODE KWARAI DA ADU'O'INKU GARENI, SON SO🥰🥰🥰🥰

SADAUKARWA GA DUK WANI MASOYIN LITTAFIN NAN.


                         *051*

Ganin ta bud'e ido ne yasashi matsawa ganganta sossai yasa hannunshi a kan fuskanta ya shafa cikin tausayawa yace "I'm so sorry hayatee, ki yafemin kinji?" Shiru ta mishi se sabon hawaye, lumshe idanunshi yayi yanzu In akwai abinda yake tunanin yafi komai yi mishi zafi a duniya shine hawayenta, musamman ma In shine sila, cikin kasa da murya yace "nace I'm sorry kukan har yanzu be isa haka ba? Ko nayi miki rauni ne?" Nan ma Shiru tayi se mikewan da tayi zaune tare da zame d'ayan hannunta dake cikin nashi ta zura kafafunta kasa tare da mikewa tana d'aga kafa da sunan takawa ta sake kara tana dukawa se ta rushe da kuka.

"Ya salaaam" ya furta a hankali kan ya mike ya d'auketa chak yayi toilet da ita yana ajiyeta ta tubure mishi se ya fita zatayi abinda zatayi ba don ya so ba ya fito ya kyaleta sede fa a bakin toilet d'in ya tsaya yana safa da marwa, ruwan me d'an zafi sossai ta had'a ta shiga ciki da kyar da ihu da komai ba yadda ta iya ne kawai ta san in batayiwa kanta hakan ba ba gata tayiwa kanta ba.

Sau kusan uku tanayi bayan wadda ya mata cikin dare da ko natsuwan sanin ya ruwan yake batayi ba, bayan ta gama ta d'aura farin towel karami tasa wadda be kaishi ba a kanta ta d'aure sbd gashinta dake a jike alwala tayi kan ta fara takowa cikin taka tsantsan dukda yadda zafi ke ratsata har cikin kanta amma aikin d'auke d'auke ba da ita ba idan bata warke ba har ya koma d'akin Hamna fah.

Tuna hamnan ma se taji wani azababben kishin da bata ta'ba ji ba a ranta se yanzu da ta gama jin sirrin zuciyarshi da gangan jikinshi ta san menene akeyiwa kishi, tana bud'e kofan ya dakata chak yana kallonta kauda kai tayi ta nufi kofa hannunta ya rike yana cewa "Ina zakije?" Kallonshi tayi se ya bata tausayi gabad'aya yadda take acting bayan tashinta ya sashi shiga wani yanayi da ya kasa 'boyuwa a fuskanshi.

Cikin kasa da murya tace "room d'ina" ze yi magana ta zame hannunta taci gaba da tafiyanta a hankali, ajiyar zuciya ya sauke bayan rufo kofanta ya shige toilet yayi alwala ya fito ya fice masallaci, tana shiga d'akinta ta nemi riga dogo me hannun vest ta saka dayake straight gown ne kuma bata saka komai jikinta ba yasa ya fiddo da siffanta sossai hijab ta sanya har kasa ta tada raka'atainil fajr, seda taji an tada sallah massallaci kan ta mike ta mika nata, tana idarwa ta zare hijab d'in kwanciya take son yi sede kuma bazata iya wani bacci da jikakken kan nan nata ba kujeran dressing mirror taja ta zauna ta bud'e a kasalance ta d'auko hand dryer ta jona tare da kunnawa ta fara busar da kanta.

Tana farawa taji an turo kofa kallon hanyar kofan ta juya tayi don bazata iya gani ta madubi ba In ba kusanta ya matso ba, had'a idanu sukayi ta kawar tana ci gaba da abinda take, wurinta ya nufo ya sa hannu a kan nata yana kallon fuskanta ta madubi sakin dryer d'in tayi ya amsa ya cigaba da mata dukda be ta'ba gwadawa ba sede yana kallon yadda zahra ke yi wani sa'in In yana gida ta fito parlorn kasa yi sbd kawai suyi hira.

Tsab ya busar mata dashi ya shafa mata mai se aukin kallo da yake binta dashi wadda yake sata jin wani uncomfortable feelings, "ashe nayi babban laifi haka da ko gaisuwa baza'a iya yi min ba? To gimbiya tuba wannan bawan Allahn yake Abdulraheem be da masaniyar Saudah tashi ce shi kad'ai don shi kawai aka hallici budurcinta".

Ta tsinci magananshi kaman daga sama, da d'an hanzari ta zame ta duka kasa tana taune baki tace "sorry Ina kwana?" Murmushi yayi duk ta koma wani iri d'agota yayi ya sanyata jikinshi yace "Lafiya kalau ya jikin?" Tace "Alhamdulillah" kara shiga jikinta yayi yace "I love yhu more than everything I can love In earth and I don wanna spend a single day without yhu, ever I will protect you, respect yhu and cherish you no matter what the situation is, you know I can't dare hurt you knowingly, I'm sorry once again".

Hannunta ta sa ta zagayeshi ita batayi fushi dashi ba ita a wa ko da tayi ma wannan hakuri da yake bata ita a wa da zataki hakura? Ko ba komai daren Jiya was her one and only night da bazata iya mantawa dashi ba har abada, ko ba komai taji sirrukan zuciyarshi da ta san komin son da yake mata baze iya fad'a a fili ba, cikin sanyin murya tace "Ka dena bani hakuri zaujii ban yi fushi dakai ba, taya zanyi fushi da zaujiii? Kenan ma Ina wasa da aljannata" wani murmushi ya sake yana shafa bayanta yace "thank yhu hayatee, thank yhu so very much" hamma tayi kan ta ajiye taji an d'agata se kan gado kwantar da ita yayi shima ya kwanta da kanta ta matso jikinshi ta shige yayi pecking d'inta a gashin kanta, ba jimawa bacci ya d'aukesu a tare.

Wuraren karfe tara da rabi yaji ana buga kofa ba Don baccin ya isheshi ba se Don kawai be son ta tashi baccin be isheta ba yasa ya mike da sauri, ya isa kofan ba tare da ya sa jallabiyarshi ba, daga shi se three quarter sbd ya san be wuce hamna ba, aiko ita d'in ce tsaye da waya a hannu kallo d'aya ta mishi ta kau da kai tana ta'be baki tace "ummu ke son magana da kai" kar'ba yayi ya kara a kunne tare da sallama tana amsawa bata jira cewarshi ba tace "yi maza kazo babana" Kit ta kashe kallon wayan yayi ya kalli hamna hannunta ta mika mishi ya d'aura mata wayanta ba tare da wani magana ya had'asu na gaisuwa a matsayinshi na mijin ta ba ta juya ta tafi.

'Dakinshi ya shiga sharp sharp ya watsa ruwa ya shirya cikin kananan bakaken kaya as usual ya zari car key ya fito rike da wayoyinshi da kuma agogonshi a hannu, seda ya leka d'akin yaga har yanzu bacci take kan ya fito ya fice.

Da hanzari yayi parking yana fitowa sbd horn da ya dingayi ba'a bud'e ba kuma daga inda yake yana jiyo hayaniya cikin gidan da sauri ya bud'e gidan ya shiga a tsakiyar compound d'in yaga su mudi driver dasu baba me gadi da duka drivers d'in gidan suna kokawa da wata ummu na tsaye gefe tana kuka Abba, Hafeez da zahra duk sunyi cirko cirko, muguwar ajiyar zuciya ya sauke ganin ba ummu bace kuma ba zahra bace yana d'aga kafa da niyyar karasawa ana bud'e get kusan a tare Kalthum da rahama suka shigo kana ganinsu zaka san hankalinsu a tashe yake a tare suka karasa dashi se lokacin ma ya gane umma ce ke ta fisge fisge daga ita se wata doguwar rigan bacci, gira ya d'age a zuciyarshi yana cewa "ita kuma wannan lafiya?" Be san a fili yayi maganan ba seda yaga ummu ta mishi dakuwa tana cewa "kanwar tawa ce wannan d'in? Sannan Lafiya ce ze sa ka ganta haka a....." maganan ummu ne ya makale ganin umma ta fisge tayi kanshi tana kurma ihun "kaine shege duk kai ne se na kashe ka yau, me rabani da kai se mutuwa!!!!!! Ihhhhhhuuuu" da hanzari ummu ta riketa aiko ta bankad'e ta saura kad'an ta kai kasa ba don Abdul yayi hanzarin tare ta ba da tayi mummunan fad'uwa bayanshi ya bata aiko ta fara yakucinshi tana jan riganshi Hafeez da su mudi ne suka kuma yin kanta suka kama ta, shikam hankalinshi na kan mahaifiyarshi.

Maganan Abba ne ya katse tambayar da yake wa ummu "ummu bakiji ciwo ba?" Inda Abba yace su shigar da ita d'akin da aka sauketa su d'aureta da gado, aiko suka shige da ita da fad'a da komai hauka fah tuburun gashi bakinta se ashar yake kundumawa, ajiyar zuciya duk suka sauke bayan an 'bace da ita, Abdul ne yace "wai me ya sameta ne ummu?" Ummu cikin kuka tace "wallahi ban sani ba Abdulraheem kawai na shiga room d'inta ganin bata fito ba tunda gari ya waye se gani nayi tana ta soshe soshe tana ashariya tana ganina kaman an tsikareta ta kurma ihu tayo kaina da sauri na fito ganin ba hankali ne kaman da ita ba, nan naga su Abbanku da Hafeez suka tareta amma suma se ta fara ikirarin kashesu, zahra da ta fito ne ta fice ta nemo taimakon su mudi, me ya sameta haka ni nyasu? Me zan cewa nenne" kawai ta rushe da wani kukan.

Abba yace "kukan nan ya tsaya haka zata samu lafiya in Shaa Allahu, muje ciki muji shawaran da zamu tsayar" duk parlorn suka shige a lokacin har sun d'aureta sun fito bayan sun sawa kofan key kururuwanta har inda suke tana furta se ta kashesu dukkansu wallahi basu isa ba, duk Shiru sukayi shi Abdulraheem kam Allah ya gani tunaninshi da hankalin shi gabad'aya yana kan matarshi.

Hafeez ne ya katse shirun da gyaran murya tiryan tiryan ya basu labarin abinda ya faru jiya be gama saukewa ba ummu ta katseshi da "baka da hankali hafeez er uwar tawa guda?? Yanzu a duniya ka rasa wacce zakayiwa sharri se pendonka? Kar ka manta mu biyu fa kawai iyayenmu suka haifa?..." duk ta rud'e, kallon zahra tayi tace "zahra ki fad'i tsakaninki da Allah zaki mutu ki kwanta kabarinki ke kad'ai da halinki da gaske ne abinda hafeez yake cewa ko karya ne?" Duk ido suka zuba mata cikin rawar murya da tausayin mahaifiyarsu tace "ummu kiyi hakuri gaskiyace ya fad'a" kuka ta saka Abdul ya tashi ya koma gefenta aiko ta d'aura kanta kan kafad'anshi, shi har ga Allah dama ya san zata rina ta riga ta sane mishi tun randa ta fara taransshi da sukar Iman, duk Shiru sukayi se kukan ummu dake tashi Abba ne yace "ba fa kukane solution to this problem ba Rashida, bari In kira baba fufore muji abinda ze ce".

Kiranshi yayi suka gaisa kan ya tamabayeshi abinda hafeez ya fad'a ya kuwa tabbatar gaskiyace anan ya fad'amishi wacce ta binne asirin gashi yau ta tashi da hauka, salati yayi ya sallamar ya kara wani cikin alhini yace "kash kash me ya kaita? Me ta nema ta rasa a duniyan nan me ya kaita kai kanta wuta tun a duniya? Hasbunallahu wani'imal wakeel, Ahmad ku kawota yola mu had'u fada kuzo dukkanku sbd muji dalilin asirin In ze yiwu ku taho yau" Abdulraheem be san sadda yayi magana ba yace "nide bazan samu zuwa ba hayatee ba lafiya bazata iya yin tafiya ba" Dakuwa ummu ta mishi tace "baba zamu taho In Shaa Allahu".

Sallama sukayi yana me ci gaba da alhinin wannan hali na umma, suna kashewa ummu ta kalleshi tace "me ke damun daughter?" Kame kame ya fara yana Sosa keya karya ba d'abiarshi ba ya ma rasa me ze ce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login