Follow us on social media

Showing 72001 words to 75000 words out of 131683 words

Chapter 25 - NOOR IMAN Yar Baƙin Ciki BY Fatima Muhammad Gurin

light da ya d'an haska daidai gadon, bata san ko yana kai ba Don ba sossai take gani ba sbd daga haske ta fito.

Kujera ta samu ta kwanta Bayan ta cire hijabin jikinta kara ta saki jin an d'aga ta chak tun kan ta gama ajiye hakarkarinta kasa, "hey matsoraciya nine" har ga Allah ta tsorata ko da yace shinen ma ta kasa natsuwa a gado ya sauketa yana sanyata jikinshi yace "taya mata zata zo turakar miji ta kwanta kan kujera?" Baki ta turo kaman ya sani kuwa yace "ci gaba da turo min baki na fara musu hukunci kar a ga laifina" maida bakin tayi da sauri murmushi ya saki yana hayewa gadon tare da sanyata jikinshi.

Jikinta yaji da zafi hannunshi yasa a wuyanta zabura tayi sbd sanyin hannun nashi ga taushi kaman jikin kule, yace "baki da lafiya ne temperature d'inki is not normal" girgiza kai tayi hannun dake wuyantan ya fara yawo dashi a jikinta a take jikinta ya hau rawa zuciyarta ya fara bugawa zafin jikinta kuma na karuwa, ci gaba yayi da binta hankali cikin natsuwa lips d'inta da suke kan rawa ta bud'e da niyyan mishi magana amma se yayi saurin had'e bakin da nashi, numfashinta yaji ya fara d'aukewa tana wani irin ja da karfi, da sauri ya d'ago yana kunna hasken d'akin gabad'aya haske ya gauraye d'akin.

"Subhanallah" ya furta ganin tana convulsion, da sauri ya lalu'bo wayanshi ya shiga lalu'ben numbern sauban har hannunshi na rawa, sauban na d'auka ko sallamanshi be amsa ba yace "sauban sauban Saudah tana convulsion plz arrange something we on our way to ur hospital pls I need a female doctor" d'aukanta yayi ya nufi waje, hamna dake niyyan shigowa ta koma baya da sauri zuwa d'akinta tana daka tsalle.

Da mugun sauri har yana had'a steps ya gangara har yanzu tana jan, me gadi da ya hango fitowarsu da gudu yaje ya bud'e mishi motanshi gidan baya ya kwantar da ita tana sauka ta sake ajiyar zuciya se suma, da gudu ya zagaya ya shiga driver sit ya danna button d'in motar ta tashi yaja da mugun gudu ya fice, ko Allah ya kara sauki da me gadi ke mishi be iya amsawa ba.

A tsiyace ya shiga asibitin, a tsaye yaga wasu nurses da gadon marasa lafiya sauban na tsaye gefensu, da sauri ya fita ya bud'e ya d'aukota ta farka daga suman da convulsion d'in again, nurses d'in ne suka matso da niyyar kar'banta ya daka musu tsawa, "just show me where to take her!!!!!" Gabad'aya ya rikice ya rikita nurses d'in,Da sauri sauban ya shiga gaba yana nuna mishi hanya da sauri sauri gudu gudu suka karasa A&E d'in anan suka samu doctor d'in hannunta rike da allura yana kwantar da ita taja wandon jikinta sama zuwa cinya ta tsikara mata allurar hannunta.

Wani kara ta sake na azaba da sauri ya  kau da kanshi yana ficewa daga d'akin hankalinshi In yayi dubu to a tashe yake, me ya ja mata convulsion da daren Allahn nan? Safa da marwa ya dinga yi a kofan d'akin sauban de na tsaye yana kallonshi mamakin abokin nashi yake shi gabad'aya rayuwansu ze iya cewa be ta'ba gani ya tashi hankalinshi irin haka ba kuma sunfi shekara goma sha biyar tare, sam shi ba mutum bane me nuna damuwanshi ta sauki amma yanzu gabad'aya ya rud'e har tsoron magana sauban d'in ke mishi.

Sunfi 30mins tsaye kan doctor Ameera ta fito tana kallon Malabo da yayi saurin nufanta yana cewa "ya jikin?" Tace "da sauki ta dena yanzu bacci takeyi, amma kafin convulsion d'in ba wani rashin lafiya da takeyi? Kaman zazza'bi me zafi?" Girgiza kai yayi yana cewa "lafiyanta kalau, temperature d'in jikinta ne kawai ya d'an hau" girgiza kai tayi kan ta nufi office d'inta tana cewa "muje inyi maka prescribing drugs and injections da zaku kar'bo mata" kai ya gyad'a shi da sauban suka rufa mata baya se a lokacin sauban ya Samu mishi magana shima cewa kawai yayi "she will be fine in shaa Allah" Kai kawai Malabo ya d'aga.

A gida kuwa umma na ganin Hamna na tsalle tace "ke plan d'in yaje" cikin farin ciki hamna tace "umma mike kawai plan nan ya watse yanzu ya fita da ita da gudu rai a hannun Allah" washes baki umma tayi kan tace "shegiya da ma ta mutu kowa ma ya huta" murna suka dingayi kaman ance musu zasu shiga Aljanna(Allah ya tsare mana zukatanmu)

*****

A zaune ya kwana gefenta hannunshi sanye cikin nata yana aikin gadinta har garin Allah ya waye be rintsa ba, nurses d'in dake shigowa suna dubata mamakin irin son da yake mata suke har kuskus sukeyi tsakaninsu, da wani namijin ne tun yaushe ya shantake a gida yana baccinshi cikin kwanciyar hankali, amma wannan ko ruwa suka zo Chanza mata se ya ce "kuyi a hankali pls" ya dinga 'bata fuska kenan kaman shi ake cakawa Allura a jiki.

Kiran sallahn asuba da aka kira ne yasashi mikewa ya fid'a toilet d'in d'akin dayake Sun dawo da ita Amenity, kanshi na tsananin sara mishi alwala yayi ya fito ya nufi massallaci bayan an idar da sallah ya jima zaune seda rana ya fara fitowa kan ya mike ya fito, a kasalance ya d'aga waya ya kira Anty Rahama, ta d'aga da tsokana "shalelen ummu yau kuma da ni aka tashi kenan?" Siririn tsaki ya sake kan yace "Anty muna hospital Saudah ba lafiya tun jiya".

Cikin mamaki tace "wace kuma saudah??..." da sauri kuma tace "oh oh subhanallah me ya faru da Iman d'in?" Wani tsakin ya kuma ja kan yace "Asibitin su sauban" ya kashe wayanshi, d'akin ya koma yana zama sauban na shigowa bargon ya kara ja mata sama sossai da sauri, murmushi sauban yayi a 'boye kan yace "sannu malabo" yace "ban son iskanci Sannu se kace wani me ciwon kafa" dariya sauban yayi yayinda malabo ya banka mishi harara.

"Ya jikintan?" 'Dan fuskan damuwa malabo yayi yace "gashinan dae sauban har yanzu ko motsi batayi ba" sauban ya d'an duddubata kan yace "everything is normal bacci takeyi sbd allurar da aka mata karka damu" Kai ya gyad'a yana kamo hannunta, fita sauban yayi ba jimawa sossai Anty rahama ta iso bata kira malabon ba sauban ta kira ya kawo ta d'akin yana fad'amata abinda ya faru Don ta san ko zata mutu bazata ji a bakin malabo ba.

Bayan ta gama ji tayi mata adu'ar samun lafiya, da sallama ta tura d'akin yana nan zaune ta ganshi gaisawa sukayi sama sama sbd magana ba wahala yake mishi yadda yaken nan, tace "kaje gida ka huta Abdul zan kula da ita kaji? Na kira kalthum zata dafo mata abu mai ruwa ruwa ta taho mata dashi kan ta tashi" girgiza kai yayi da kyar suka lalla'bashi ya yarda ya wuce gida gani yake yana tafiya komai ze iya faruwa da ita.







                      🖤Gureenjo🖤


                🥀NOOR IMAN🥀

*Fatima Muhammad Gurin*
           *Gureenjo6763 on Wattpad*

*'Yar Mutan Adamawa*

💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)

*this page is dedicated to yhu Maman Ameer (Amina Ibrahim) ina me tayaki murnan gama littafinki na zaytoonah wadda be karanta ba yaje ya nema ya karanta kar a barshi baya, In Ana sallah toh fa ba'a magana littafin zaytoonah me kankat ne ya ta'bo abubuwa dayawa marar lissafuwa manya manyan kuwa sune Fad'akarwa, nishad'antarwa, soyayya, ladabi, iya magana da gujewa 'bata daga tafarkin ubangijinmu, Masha Allah, Masha Allah, mun karu da abubuwa dayawa cikinshi, Allah ya baki lada. Sannan Ina me tayaki farin cikin fara sabon littafinki "A barwa rai" Allah ya shigemiki gaba Ina yinki irin over d'innan mutuniyata🥰😘

                         *035*

Zaune suke a parlorn sama sun kunna waka sun kure kaman gidan rawa, jawahir da Hamna ke takawa yayinda umma ke zaune tana karasa taune sauran kazan Amarcin Iman da kukun Hamna ya d'umama musu suka gama breakfast dashi, (ummu Ameer da ummu haneef😝😝😝😝😜 gashi mutanenku sun cinye basu ragemuku ba🤣🤣🤣) tun shidda jawahir tazo gidan Don lokacin da akayi bukinsu Iman bata kasar amma tana samun Information daga wurin ita hamnan.

Tun daga kasa yakejin kid'in ranshi ne yaji ya 'baci ainun ga kanshi dake sarawa ga damuwan ciwon Iman a hankali ya dinga haurawa har ya isa tsakiyar parlorn ba tare da ko ya kallesu ba yaje ya kashe kid'an ya nufi hanyar d'akinshi, umma ce ta dakatar dashi da kiran sunanshi tsayawa yayi ba tare da ya juya ba tace "ya zaka kashe muna chacewar tayaka murnar Karin aure?" Kuji iskanci🙄 taune lip d'inshi na kasa yayi na seconds kan ya sake wani munafukin murmushi yace.

"Ai zakuyi hakuri in angwance tukuna, yanzu Ina ango ne, In na angwance I will let you guys know se kuyi rawar da tushe" Hamna tace "yanzu hamna umma kake gayawa magana irin wannan? Ko ba kanwar mahaifiyarka bace ba ai ta girme maka har haifanka zata iya yi, sannan Ina ruwan mu da wani angwancewanka da b.........." hannu ya d'aga mata "duk babban da be ji kunyar yarda girmanshi ba yaro bazeyi shayin hawa ya taka ba" yana kaiwa nan ya shige d'akinshi.

Jagwab hamna ta zube kan kujera yanzu take jin tana son mijinta se yanzu takejin bazata iya rayuwa ba shi ba, ji take ko me yace ta dena baza ta sakeyi ba har abada, amma yanzu taya zata juyo hankalinshi kanta? Jawahir ce ta dafa ta tace "ke ki dena d'aga hankalinki plz akan wannan gayen na sha fad'a miki In kina so ki mallakeshi se kin bi ta masu duniyar wato bokaye(waiyazubillah) sannan ki sake nairori amma kinki yarda dani" umma tace "Ai yanzu ta yarda tunda munje har sau biyu, ke wani babban boka kika sani me kankat wadda daga munyi shikenan?" Jawahir tace "yanzu mu shiga daga ciki muyi magana kar ya ji mu, huuuuuu kawata kice kin shigo gari wallahi kukanki ya yanke inde wannan mijin naki ne kad'ai matsalarki" murmushi tayi suka shige ciki suna ta hure mata kunne akan boka shine maganin komai. (Allah ya shiryemu ya tsare mana imaninmu).

********

A hankali ta fara bud'e idanunta kanta na tsananin sara mata da fankan d'akin dake juyawa a hankali ta fara cin karo, "Sannu Iman kin tashi?" Taji An fad'a daga gefenta juyawa tayi a hankali tana d'aga hannunta da taji alamun ba komai a jiki tana dafe goshinta, Anty rahama ta gani gefenta Anty kalthum da zarah se Hamma hafeez, murmushi tayi musu tana amsawa da "yauwa" zarah tace "bari In kira ya sauban.

Fita tayi chan anjima suka dawo da sauban da kuma dr Amira, yana dariya yace "Anty kuka tura zarah kirana kuna so mutumin yayi kuli kulin kubura da ni ne yau?" Anty kalthum tace "me yasa ze yi kuli kulin kubura da kai?" Tayi maganan tana dariya tun kan taji me dalilin. Labarin abinda ya faru jiya ya basu dariya duk suka dingayi suna mamaki har Doctor Ameera dariya take yayinda kunya ya rufe Iman, Anty rahama tace "eyeeee malabon ne ya rud'e kan mace aaa Lallai Iman kin taki sa'a".

Anty kalthum tace "sossai ma se ki rikemana d'an uwa da amana Don ko ni yanzu na tabbatar ba karamin so yake miki ba ko da kuwa be furta ba" Hafeez yace "ke se yanzu kika gane? Lallai an barki baya ni wallahi tun kan ayi auren na gane yana mugun sonta, da fa nace ya barni In aureta In yana tsoron fushin ummu bakuga mugun kallon da ya watsamin ba seda hanjin cikina suka kad'a".

Dariya suka saka har Iman seda tayi murmushi dukda jikintan ba wai sakewa yayi ba zazza'bin be sauka ba ga ciwon kai da take fama da, dr Ameera ce ta rubuta mata wasu tests nurse ta d'ibi jininta Hafeez da har lokacin suke hira yana ta aikin basu dariya ya kar'ba yayi lab Don a gwada a bashi result ya taho dashi, zahra ce ta taimakawa Iman da silver, brush and macline da ta taho dasu sabbi tayi brush.

Kasa kasa tace mata "kaya fah zahra baza ki iya kije ki kawo min ba?" Cikin jin jiki tayi maganan, zarah tace "Ohk bari In kar'bi keyn Anty kalthum ko na Anty rahama inje In d'auko miki" kai Iman ta gyad'a zahra ta tashi tana cewa "A ara min key in d'aukowa matar yaya kaya a gida" Anty rahamace ta mika mata ta fice, "A sa miki abinci kici ko kan ta dawo se kiyi wankan" cewar Anty rahama, girgiza kai tayi tana cewa "A'a Anty in nayi wankan zanfi jin karfin jikina watakila har da apatite Don yanzu bandashi sam"

Kai Anty kalthum ta gyad'a tace "Anty mu bari zarahn ta dawo" ba Haka Anty rahama ta so ba Don ba daadi zama da yunwa musamman ita da bata jin daad'i gashi 12 zata fara shan wasu drugs dole kuma se ta ci abinci, hira suka ci gaba dayi tsakaninsu suna sanyata ciki amma sede tayi murmushi kawai, da Anty rahama taga har after 1hour da fitar zarah bata dawo ba yasa ta bawa Anty kalthum Umarnin sa mata abinci.

Ba tare da ta Musa ba ta tashi ta sa mata Irish pottage da ta kawo mata ta yanka dafaffun kwai manya manya a ciki ta had'a mata tea.

Taimaka mata tayi ta gyara zamanta tare da d'aura mata abincin gabanta 'bata fuska tayi tana kallon Abincin sam bata da apatite se tsabar headache dake nukurkusarta, kallon abincin take ta aikinyi sam taki ko gwada kaiwa bakinta gashi de a ido kaman ka lashe amma sam bata jin ci.

Anty rahama ce ta kula bata ci tace "a'a Iman ya baki fara cin abincin ba? Ko be miki ba a sake girka miki wani?"  Girgiza kai tayi a hankali Tace "zanci Anty" hira suka ci gaba da yi da Anty kalthum after like 2mins Anty kalthum ta juyo taga har yanzu bata fara ci ba "ikon Allah Noor Iman kici mana samu kisha drugs da suke jiranki" hawaye ne ya ciko mata ido ta karkata kai tace "Anty na koshi" Anty rahama tace "kin me?? Oya gy............" bud'e kofan da akayi da kamshin turaren da ya bule su ne ya katseta daga maganan da takeyi.

Dukda ta san ba me irin wannan kamshi kaman Abdulraheem aiko shine ya bayyana sanye da yadin kashmiyya baka d'inkin half jumpha irin na yayi da ya matukar kar'barshi ba hula a kanshi hakan ya sa gashin da yake matukar ji dashi da asalin gyarashi bayyana se sheki yake, kallonsu yayi fuskan nan ba fara'a sam Don Allah ya gani ya tsorata da jikin Iman d'in gashi be samu wani baccin kirki ba, ga asalin damuwan ummu bayan ya koma ya kwanta ya samu yayi bacci kad'an tashinshi ya gwada kiran layin ummu, ya Saba kullum safe in be samu ya shiga sun gaisa ba ze kirata a waya.

Sam ya manta da wani bata shirya dashi ba muryarta kawai yake son ji hakan ya sa ya kirata ya mata miss call yafi biyar amma bata d'aga ba hakan ya kara sanyaya mishi jiki tabbas ta gani ba wai bata gani ba don da wuya ka ganta ba rike da wayanta ba, wanka kawai yayi ya fito, daga d'akinshi yake jin dariyar Jawahir da Hamna da tun dama su suka hana shi bacci musamman wannan figeggiyar yarinyar yanzu be da lokacinsu ne yasa be bi ta kansu ba bari ya sukliti tukuna.

Basu san fitowanshi ba sbd sun ba kofan shi baya suna facing zarah Hamna tace "Baiwar Allah kanwar baabarki da kikazo wurinta bata nan" dukda zarah ta kalleshi hakan be hanata bata amsa ba da "Eyyah ai bata bani labarin ta bar karnuka gida ba" wucewa tazo yi Hamna ta mike ta tare gabanta "kutt mune karnuka zarah?" Zarah tace "wadda ya tsargu" jawahir ta d'aga hannu ta kifa mata mari batayi wata wata ba ta rama kuwa hamna ta d'aga hannu da niyar marin zarahn taji an rike.

Juyawa tayi ta ganshi zatayi magana ya nuna mata d'aki fuskanshi ba ko d'igon fara'a shakkan magana taji hakan yasa ta kama hannun jawahir zasu wuce yayi saurin rike hannun hamnan kallonshi tayi idanunshi na kan jawahir yace "would you pls kindly leave my house and don't you dare step your foots into it again? ever!!!" Ya maimaita ba wani hayaniya a muryanshi.

A zuciye jawahir ta nufi room d'in Hamna Don d'aukan kayanta se hamna ta rike hannunta tare da fashewa da kuka daidai lokacin ummu ta shigo gidan umma ma ta fito tana murmushin mugunta su fah tunda sun san lagwanshi se abinda sukayi tunda baze Kamu ba Ai me fad'amishi taji ta kamu duk d'aya, "me ya faru?" cewar ummu, Abdul yace "ummu lafiya kika taho da kanki, ai da kin kirani ni se in zo In sameki" hararanshi tayi tana cewa "Toh nazo ko korata zakayi ne in sani?" Girgiza kai yayi yace "kiyi hakuri" tsaki taja tana kallon zarah tace "nace me ya faru? Me ma ya kawoki gidan nan ke da kikace makaranta zaki?".

Labarin abinda ya faru zarah ta bata tana saukewa taji saukan mari, a razane ta kalli ummu hannunta dafe da kunci bata ta'ba dukanta ba kafatanin rayuwarta se yau shi karan kanshi malabo ya kad'u, cikin fad'a ummu tace "idan wanchan uwartaki zata miki karya nima kenan zan iya miki, sannan yaushe kika fara karya ban sani ba? Wato kawance da fitsararriyar matar wannan asararren ya fara koyamiki fitsaranci tayi karyar rashin lafiya ya d'auketa sun tafi hotel ke kuma kika zo har gidan nan da sunan kin tafi makaranta kike ciwa er uwarki mutunci har da mari wai kina tayata kishi, to bari In miki me kankat tunda na hana kinki ji, wallahi wallahi Fatima daga yau kika kara yiwa wanchan munafukar magana Allah ya isa ban yafe ba".

Sossai zarah ke kuka abin tausayi furucin karshen yafi marin d'aga mata hankali, Abdul ze yi magana ta d'aga mishi hannu tana kallon jawahir tace "kiyi hakuri d'iyar Albarka ki zo sadda kika ga dama ki fita sadda kika dama inga uban da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login