Follow us on social media
Showing 93001 words to 96000 words out of 131683 words
Chapter 32 - NOOR IMAN Yar Baƙin Ciki BY Fatima Muhammad Gurin
yace "uhm uhm naki hakurin se an biyani" dariya ne ya kamata ganin da gaske shagwa'ban da takeyi yake kwaikwaya tace "to da me zan biyaka d'in?" Yana sake wani munafukin murmushi yace "just a kiss" da sauri ta rufe fuskanta tana dariya sossai tare da yarfe hannu.
Murmushi yakeyi yana kallonta tana matukar burgeshi, tana mishi kyau har na wuce misali yana sonta fiye da tunanin me tunani, banko kofan da akayi ne ya katse su daga yanayin da suka fad'a, kallon kofan sukayi ummu ce tsaye tana leke leke dayake ta sauke labulen da ya raba tsakanin parlor da d'aki hakan ya sa ita bazata iya kallonsu ba.
Fitowa sukayi suka zura mata ido tace "to romeo and Juliet se a fito haka ko uban wanke wanke dasu ke tare kitchen d'innan waye bawanki da ze miki? Wato da hajja umma ta gayamin kuna bar mata duk aikin gidanku ban yarda ba se yanzu, kai kuma ashe da gaske kai ba ruwanka da er uwarka kuma uwargidanka na lura ko kallonta bakayi ba d'azu se kuma kazo ka kule wurin wannan munafukan, to ba ita ta haifarmin kai ba ehe don haka ki raba kanki kan In waiwayo gabad'ayata zuwa kanki na gayamiki daga ni har d'ana kurwan mu kurrr mayun banza mayun wofi".
Ta fice fuuu da alamu dae su suka zugo ta ta taho ta sauke, a sanyaye ya kalleta ze yi magana ta sake murmushi tace "bari inyi inzo ina da magana please" Kai kawai ya iya gyad'a mata ta fice shi kuma ya samu wuri ya zauna, se kuma ya kara mikewa ya fito ummu ya gani da jakanta alamun tafiya zatayi ya mata sallama tana fita ya shige kitchen d'in.
Tsaye ya ganta tana wanke wanke, hannu ya sa ya fara d'auraye mata kwanukan ido ta waro "subhanallah dan Allah ka rufamin asiri ka bari kaji" ba wai ya iya bane Don abinda ya iya kawai had'a tea, coffee shikenan ko gwada wanke wanke be ta'ba ba amma baze barta ita kad'ai tayi wahalan ba, yace "asirinki a rufe yake kuma In Shaa Allahu baze ta'ba bud'uwa ba, so ba ruwanki dani" zatayi magana yace "musu zamu fara kuma?" Se tayi shiru ta ci gaba da wankewa yana d'aurayewa har suka gama kowanne da irin tunanin da yake a ranshi.
A tare suka goge kwanukan suka mayar wuraren zamansu, suka fito ko kallon hamna dake tsaye bakin kitchen d'in tuntuni ba wadda yayi a cikinsu kowa ya shige d'akinshi a gajiye ta tu'be kayan jikinta ta fad'a wanka, bayan ta fito ta shirya cikin cotton kayan baccinta masu kauri riga da wando ash ta d'aura hijabinta kai ta kashe electronics d'in room d'inta gabad'aya kan ta fice tana shiga room d'inshi yana fitowa wanka daga shi se towel iya kwankwaso duk wani hallita nashi na murd'add'un maza a bayyane karami a kanshi yana share ruwa, da mugun hanzari ta juya bayanta.
Murmushi ya saki da d'an d'aga murya sbd tazarar dake tsakaninsu daga arean room zuwa arean parlorn yace "Allah ya nuna min ranar hayatee" bata amsa ba sbd ta tabbatar In ta tamabaya amsar ita ze kunyata zama ta yi nan parlorn ta kira Baba suka gaisa ta tambayi jikin mama ya bata tabbacin da sauki, bayan sun kashe ta kirasu teema duk su hud'un ta had'asu conference Don ta san d'aya se tayi complain me yasa aka fara kiran d'aya ba ita ba, bayan sun gaisa sun gama tsokananta tana musu dariya take tambayarsu ya akayi bata gansu bane a asibiti Abba ba lafiya.
Duk salati sukayi suna tambayar me ya sameshi ta basu amsa anan suka sanar mata Ai tun ranar da hamna ta had'asu da baba yarima suka tarkata suka koma gidan pendon zahida wacce suke uwa d'aya da mamanta basu da wani Matsala a gidan kaman nan da ummu ta fara chanza musu, inda tace ya kamata su zo su dubashi itama gobe zata je amsawa sukayi kan suka bud'e wani chaptern hiran duk tsokanarta sukeyi itakam ba amsa se murmushi bata ankara ba taji an fisge wayan ya kashe yana kallonta yace "yanzu lokacina ne fah hayatee" murmushi tayi kamshinshi na kashe nata duk wani laka na jikinta yana sa mata kasala.
Sanye yake cikin bakaken pjms masu tsansti rigan upon chest wandon kuma dogo har kasa farin fatanshi se yalki yake a cikin kayan yana d'aukan ido mikewa tayi suka karasa bakin gado duk suka zauna shikam aikin kallonta yake yayinda ita kuma idanunta suke kasa muryanshi ta tsinta yana cewa "Anya bazakiyi deferring semester d'innan ba hayatee?" Ta d'ago ta kalleshi yace "yes jibi zamuje yola sbd matsalanki, mun dawo zamuje Miami daga nan New York then London ina so kuma mu kara wasu kasashen bayan nan ciki harda Saudi Arabia, babban matsalan ma shine gobe zanyi covering syllables d'ina hayatee be wuce sau uku kika je class d'ina ba, ba yadda za'ayi kiyi exams ba tare da 75% attendance ba I mean it, kina so kiyi carrying azo ana cewa matar lecturer da kanshi tayi carrying?"
Kai ta girgiza yace "to please kiyi deferring kar kiyi zaton zan hanaki karatu ne sam ba haka bane you can read as much as you can ina so inga matata ta tara degrees dayawa" Tace "to Allah ya sa hakan shi yafi alkhairi" yace "In Shaa Allahu hakan ya fi, Ina so in bar lecturing ta karfin tuwo sbd stress na min yawa more again bana so mu dinga samun matsala dake sbd attendance as i know yhu kan kije class se na shiga and ba ta yadda za'ayi In kasa koranki sbd zanyi sonkai so gwara In dena kan a fara sa bulala ana Zane ni" bata san sadda tayi dariya ba Tace "ahh na isa?" Yace "har Kin wuce, d'azu kikace kina so muyi magana uhmmm?" Tace "dama akan school d'inne...." ringing na wayanta ne ya katseta duk wayan suka kalla "Hamma Muhammad" kallon sunan yayi se ya kalleta suka had'a ido ya d'an ta'be baki tare da kawar da nashi a sanyaye ta amsa tare da sawa a speaker.
"Amarya" ya ambata ta d'anyi yake kan tace "Ina yini hamma muhammad?" Yace "kalau ya gd? Ashe kuma wani yayi sa'ar samunki, bazance kinyi sa'a ba Don shine yayi dace, Allah ya sanya alkhairi" tace "Ameen" tana kallon Abdul da ya had'e fuskanshi kaman ba shine ya gama dariya yanzu ba ya koma mata sak kaman randa ta fara ganinshi.
Har rawa muryanta yake wurin cewa "lafiya kuwa Hamma muhammad?" Yace "kalau kawarkice ke wainani yasa nace bari In kira inyi kamun kafa dake" ajiyar zuciya ta sauke tace "ba halin in mata magana Hamma Muhammad" kallonta Abdul yayi se ta kawar da kai tana ji Muhammad yace "sbd mene?" Abdul na jira yaji tace ummu ta hana se ji yayi tace "Ai zarah taurin kai ne da ita yanzu na takura mata nima se ta dena min magana ka san halin ai" sukayi dan dariya a tare, haushin dariyar da Abdul yaji ne ya sa ya d'aga wayan yace "amm da ni ya kamata ka fara kama kafa ba matata ba so In kana son zarah da gaske ne ni zaka sama, and please kayi hakuri karka kara kiramin mata ina da kishi wadda har tsoron kaina nake da kaina sbd abinda zan iyayi akan iyalina se anjima" ya kashe wayan ya kalleta "ko da kina friendship ko irin wanna shirmen Besty besty da maza ki dena I hate it zamu iya samun damuwa sbd hakan" yana kai nan ya kashe wutan d'akin ya hau gadon ya kwanta.
Gadon ta haura itama ta kwanta jikinta a sanyaye sede wani shashin na bata gaskiyace abinda ya fad'a ba ta yadda za'ayi ta zauna tana hira da wasu mazan bayan tana da aure sede komai kamawa take, cikin sanyi da shagwa'be murya kaman zatayi kuka tace "bazan kara ba kayi hakuri" Shiru ya mata se ta sa mishi kukan da ya d'auka da gaske ne take ya juyo ya janyota kirjinshi ya rungume "is Ohk, sleep baby, am damn tired and sleepy" Kai ta gyad'a tare da gyara kwanciya bacci me daad'i da ni'ima ya kwashesu.
*shawara nake nema readers wannan semester d'inmun wuta ne tsakani da Allah ina wahala sossai daga dawowata zuwa yanzu ban samu hutun da ya kamata bawa ya samu ba, kullum In na fita school daga 8 se 6, inyi rushing d'in book d'innan a kammalashi kowa ya hutane ko ko In ci gaba da yadda na tsara a zuciyana sannan In ci gaba da kokarin ganin na muku kowanni bayan kwana d'aya ne? Me kuke gani??*
🖤Gureenjo🖤
🥀NOOR IMAN🥀
*Fatima Muhammad Gurin*
*Gureenjo6763 on Wattpad*
*'Yar Mutan Adamawa*
💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)
*wannan page d'in is a dedication to duk wani masoyin littafin nan duk naga comments d'inku kuma naji daad'i sossai na gode da kulawarku, kaman yadda na fad'a a shafin da ya wuce shawara nake nema kuma Alhamdulillah kun bani had'in kai wurin fahimtar junanmu dama ba ta yadda za'ayi ayi tafiya tare ba'a fahimci juna ba, Toh masu cewa a bi littafi a tsanake kar ayi rushing su sukafi yawa Don hakan shawaran za'a d'auka zan dingayi ko wani bayan kwana d'aya Allah ya bani iko, Ameen na gode kwarai love you guys🥰🥰🥰*
*043*
Ita ta fara motsawa da asuba da niyyar tashi wadda hakan yayi sanadiyar tashinsa bud'e idanunshi yayi yana kallon ta dukda duhun dake d'akin yasa baya iya kallon fuskanta, a hankali ta zame wai Don kar ya tashi ta sauka bata shiga toilet d'inshi ba kawai ta nufi room d'inta, seda ta fita tukun shima ya mike ya fad'a toilet d'inshi wanka yayi kan yayi alwala ya fito bayan ya zura jallabiyarsa milk color daga cikin bayin.
Massallaci kawai ya fice, bayan ya dawo be duba d'akinta ba kawai ya shige room d'inshi kwana biyu be yi exercise d'inshi ba har ji yayi ya fara gaining weight hakan yasashi shiryawa cikin Armani sport wear d'inshi bakake ya d'aura karamin farin towel a bayan wuyanshi, ya duka ya saka wata adidas black and white canvas d'inshi kan ya mike ya fito be nufi gym room d'inshi dake kasa ba kawai se ya fice seda ya hau kan titin unguwan kan ya fara jogging a hankali kaman baya so.
Ta 'bangarenta kuwa Bayan ta idar da sallah tayi azkar d'inta ta mike direct ta nufi kitchen tunanin me zata girka kawai ta hau yi ita ba wani girkin zamani ta iya sossai ba zata iya kirga waenda ta iya su ma albarkacin waya, karshe de doya ta fere tayi musu shi da egg sauce ta had'a musu tea me cike da kayan kamshi ta juye a flask bata kai ba seda ta fito ta share parlorn duk girman shi tayi mopping ta samu karamin towel ta goge kan dining da wuraren electronics d'insu, kan ta koma ta d'auko abincin ta shiryasu kan dining.
'Dakinshi ta nufa ta gyare tas daga ciki har parlorn ta share tayi mopping duk ta gaji a haka dae ta kunna burner ta sa turarukan wuta daga parlorn har d'akinshi, Allah ya taimaketa nata d'akin ba dattin da yayi hakan ya sa bata share ba Don ta gaji wanka kawai ta fad'a tana fitowa ta shirya cikin wata atampha orange color me ratsin baki da fari d'inkin bubu mai aljihu kad'an ya kamata daga kirjinta amma duk sauran a sake yake atamphar ta amsheta ba kad'an ba powder ta shafa da lip balm, d'ankwalin ta d'auko da niyyan d'aurawa d'aga idon da zatayi se suka had'a ido da mutum.
Da farko razana tayi, da ta tabbatar shine se ta sauke ajiyar zuciya tana dafe kirji dariya yayi kad'an bottle water dake hannunshi ya karasa shanyewa tare da jefar da bottle d'in cikin dustbin dake gefen bayin, wurinta ya nufa yana murmushin shi me kashe zuciyar 'yan mata yace "matsoraciya" shagwa'be fuska tayi tace "to banji shigowarka ba fa Ai dole In tsorata" murmushi ya kuma yi yana tsayawa dab bayanta ta cikin madubin ya zura mata ido yana kallo itama shi take kallo da mamakin yadda akayi yayi zufa haka bayan sanyi akeyi seda ta kalli kayan jikinshi da kyau tunanin watakila gym ya fito ya fad'o mata.
Ajiye d'an kwalin tayi tana mikewa ta juyo suka had'a ido kawar da nata tayi kan ta zame kasa tace "mun tashi lafiya?" Yace "lafiya kalau Alhamdulillah hayatee, ya gajiyan aiki? Naga kin shaa Aiki dayawa haka sannu, Allah yayi miki albarka" murmushi ta sake tana jin daad'i har kasan ranta mikewa tayi ta kar'bi towel d'in hannunshi ta matsoshi sossai ta sanya ta fara goge mishi zufan fuskanshi tana cewa "Ameen hamma, Ai aikin ba wani me yawa bane abinda ya kasance dole ne ga kowacce matar gida" har lokacin murmushi ne kwance saman fuskanshi yace "hmmm banda kazamai da malalata" dariya tayi dukda ita har ga Allah bata san da wadda yake ba shi kuwa da Hamna yake nufi kuma ya fad'i hakan ne sbd ganinta da yayi bayansu ta jikin madubi tana tsaye parlorn tana watso musu mugun kallo, dayake labulen da ya raba d'aki da parlorn a d'age yake.
Seda ta share mishi fuska zuwa wuyanshi kan ta sauke hannunta tace "muje Hamma In had'a ma ruwan wanka kayi samun kayi breakfast na san kila ka fita aiki" cikin jin shi fa wani ne yanzu me martaba da daraja a gidanshi yace "uhm uhm hayateee sede In ke zaki min" waro idanunta tayi tana dafa kirji tace "ni??" Dariya hakan ya bashi sossai be rike ba kuwa ya fara darawa se kuma taji kunya ta juya mishi baya.
Kafad'unta ya kamo ya juyo da ita har lokacin yana dariya yace "yes ke, me sabon abu a gareki, menene baki gani ba😉" ya karasa da wink, juyawa tayi zata gudu yayi saurin chabke hannunta yana dariya, wani wawan bugu da akayiwa kofar d'akintan ne yasa su duk maida hankali kan kofan, murmushi yayi yana kau da kai yace "muje to a had'amin hakan ma na gode" murmushi tayi ta d'auki d'an kwalin ta yafashi kawai kanta suka fice zuwa d'akinshi, direct toilet d'inshi tayi ta had'a mishi ruwan tare da zuba mishi turarukan wanka masu kamshi ta ajiye mishi towel babba da karami daga gefe kad'an, ta juyo kara ta saki tana rufe idanunta da mamaki yake kallonta shi kam yana rasa gane kan yarinyar wani lokaci ace aurenta hud'u amma ganin shi da boxers ze razanata haka?.
Matsawa yayi ya koma bayanta yace "to sarauniyar kunya zaki iya wucewa" da sassarfa ta wuce tana kau da kai, cikin bakaken kayanshi ta za'bamishi sweatpants da V shaped shirt me karamin hannu, ta ajiye mishi kan ta fice d'ankwalinta ta d'aura ta fiddo gyalenta orange da zata yafa, jakanta ta d'auka ta ajiye gefen gyalen, ta fito ta zauna kujerun main parlor.
"Wallahi umma Hamma Abdul ze kashemiki ni zuciyata ze buga, umma zafi yake min kaman dutse aka d'aura ya zanyi ne" tayi maganan cikin kuka umma ta rungume d'iyar tata tace "komai ze yi daidai hamna nan ba da jimawa ba, ki bar maganan se ya amincen nan kan ki wuce, jibi ko ta yaya ne zamu bar Nigeria bade Nijar bane ko ta mota se muje" cikin aminta da maganar mahaifiyarnata ta gyad'a kai tare da share hawaye yayinda uwar ta ci gaba da banbami da fad'an munanan kalamai dake nuna tsantsar hassada da kyashi ga er uwarta da suka fito ciki guda.
A shirye tsab ya fito se tashin fitinanen kamshinshi me sanyi da ratsa zuciya dake tashi, kallonshi tayi suka sakarwa juna murmushi ta mike tana cewa "mu karasa dining d'in ko" bayanta ya bi zuwa dining area da kanta tayi serving d'inshi kan ta sawa kanta tura mishi tayi seda ya d'auki fork kan ta juya ta nufi d'akin hamna da kallo ya bi ta be hanata ba har ta shige da sallama, ita hamna na kwance bakin gado tana danna waya yayinda uwar ke zaune gefenta tana shirya musu kaya a akwati, duk d'agowa sukayi suka zuba mata mugun kallo, kau da kanta tayi tana ta'be baki kad'an tace "umma, Anty hamna Breakfast is ready" harara hamna ta zabga mata tace "ummau nace ummau In uwarkice ita se ki gayamin In banda gulma da kinibibi da son a sani, wani Umma... Anty Antau" kallon lafiya daga magana? Iman ta mata bata tankata ba sbd tana son mijinta yaci abinci cikin kwanciyar hankali juyawa tayi zata fice taji hamna tace "yarinya karama da ita ta iya kinibibi da sa miji a gaba shima In banda kare ya lashe mishi zuciya me a jikin wannan? Me akayi akayi wannan da yake ta wani rawar kafa a kanta har da bud'e baki yana mata dariya" cikin takaici ta karasa maganan.
Murmushi Iman tayi tare da fara waka "Ahayye yaro Ahayee yaro, Ahayye ba yaro ba iye nanaye....." a hankali take tafiya tana d'an jujjuyawa "a kyau wata tafi wata, a kyau ko ni nafi...... A kugu wata tafi wata a kugu ko ni nafi...." ta d'an karkad'a kugun, wani tsalle da Hamna tayi zata chabke ta ne ya sata kwasa da gudu zuwa waje tana fashewa da dariya sossai, kallonta yayi dama tun d'azu yake kallon kofan dariyarta sossai ya mishi kyau har be san sadda murmushi ya su'buce mishi ba dukda ya san wani abin tayo.
Dining d'in ta nufa tana ta dariyarta Don sossai hamnan ta bata dariya se kace wata er dambe, zama tayi ta fara cin abincinta ba tare da tace mishi komai ba shima be nemi ba'asi ba ya ci gaba da cin abincin yana kallonta minti minti se tayi murmushi ta kalli kofan d'akin ta san watakila umma ce ta hana ta fitowa, har suka gama basu fito ba, plates d'in da suka ci ta had'a ta kai kitchen, se sannan su hamna suka fito tana lekowa ta gansu tsaye dashi yana gaida umma a d'agen dai yadda ta Saba ta