Follow us on social media
Showing 78001 words to 81000 words out of 131683 words
Chapter 27 - NOOR IMAN Yar Baƙin Ciki BY Fatima Muhammad Gurin
nan, ki kular min da kanki wannan alqawari na ne" ya duka yayi mata peck a goshi kan ya juya ya fice.
Su Anty rahama da tun da ta rike mishi hannu suka fice, suka shigo bayan sun mishi seda safe nan suka dinga hira suna sata nishad'i bayan tayi sallolinta da ake binta a zaune nan kan gado, dukda tana murmushin hirar tasu amma zuciyarta na wani wuri, yanzu making love ze je yayi da matarshi ko gashi ita rashin lafiya ya hanata bashi komai, wasu irin zafafan hawayen kishi ne suka cika idanunta tana da kishi na bala'i haka Allah ya halicce ta, ya kirata kusan sau uku wani abu a zuciyar na hanata d'auka dayake wayan a silent yake se ta kifeta kasan pillow tayi kwanciyarta, se bayan isha Anty rahama ta fara shirin tafiya kaman daga sama suka ji an banko kofa.
*Assalamu Alaikum ya kuke ya family? Kuyi hakuri da ni ku kara na chanza tsarin littafina na Noor Iman sbd abubuwa da suke min yawa har ga Allah Ina takura, muna da marasa lafiya har biyu a asibiti ga harkokin gida sam banda time Allah, so na yanke shawarar ringa typing NOOR IMAN sau hud'u a sati kan abubuwa su koma min Normal In ci gaba da yadda nakeyi tun farko, hope ban 'bata muku ba Na gode.
🖤Gureenjo🖤
🥀NOOR IMAN🥀
*Fatima Muhammad Gurin*
*Gureenjo6763 on wattpad*
*'Yar Mutan Adamawa*
💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)
*037*
Wani wawan ajiyar zuciya ya sauke ganin duk sun zuba mishi ido suna kallonshi yasa ya juya kawai ya fice a jikin gini ya jingina yana sauke ajiyar zuciya wallahi yayi mugun tsorata anya hankalinshi ze kwanta har ya samu yin bacci cikin nitsuwa kuwa? ya yi ta kiranta bata d'aga ba haka ya kira Anty rahama ma bata d'aga ba ya gama zata ciwonta ne ya sake tashi se kuma ya zo ya gansu suna hira abinsu.
Ita kuma a ciki se bata ji daad'in abinda tayi ba kar ta zama me son kanta dayawa mana matarshi ce Hamna da ita ta sameshi ba laifi bane don tayi kishin shi amma babban laifi ne da zata iya ignoring calls d'inshi sbd wani kishi bayan tana gadon asibiti, Anty rahama ce tace "lafiyan Abdul kuwa? Ina zuwa" ta mike ta fito a nan ta ganshi tsaye jingine da gini ya d'an Lumshe idanunshi "Abdul" a hankali ya bud'e idanunshi ya zuba mata.
Tace "menene?" Wani Ajiyar zuciyar ya sauke kan yace "Ina son yarinyar dayawa" murmushi Anty tayi tare da dafa kafad'arshi "ba wadda ya hanaka sonta ai Abdul ta chanchanci a so ta" cikin wani irin yanayi yace "ban san sadda sonta ya min Illa ba Anty yayi yawa sossai a zuciyata wallahi" fad'ad'a murmushi Anty tayi kan tace "Abinda ya fito dakai kenan?" Murmushi shima yayi yana shafa kanshi yace "I was calling your phones bakwa picking I thought wani abin ne ya faru" dariya Anty rahama tayi kan tace "sorry majnun wayata na cikin jaka kuma a silent yake Ina tunanin wayan Iman d'inma a silent yake Don bamu ji ringing ba".
Hararanta yayi yace "Toh kuma mutum be iya fad'a miki damuwanshi ba me kuma wani majnun? Mtseww" ya wuce ta zuwa d'akin cikin d'aga murya tace "eh d'in Romeo kawai" murmushi yayi ya tura d'akin ya shiga dama baza su had'u su wanye Lafiya ba abinka da sako da sako, kan gadon ya nufa ba tare da ya kalleta ba yace "where is your phone?" 'Daga pillow tayi ta d'auko ta mika mishi.
Kar'ba yayi ya cire a silent kan ya mika mata, ba tare da ya kalleta ba ya juya ya fice, yana cewa baaba "se da safe" ta Amsa da Allah ya tashemu, Anty rahama ma ta d'auki jakanta tayi musu sai da safe ta Bishi da sauri akwai abinda take so suyi magana akai, babban yatsanta ta sa akan numbern wayanshi tana shafawa batayi saving ba kuma ta rasa da me zatayi saving sede ta haddace numbern tas a kanta.
Daga karshe kawai tayi saving da "Hamma" kawai ta ajiye wayan tare da kwanciya cikin tunani har bacci yayi awon gaba da ita.
Washegari
Tayi ta zuba ido a kofa ko ze shigo amma be shigo ba kuma be sake kiranta ba taji rashin daad'in hakan sossai, har Anty kalthum ta zo mata da breakfast suka sata ta d'anci baaba ta taimaka mata zuwa toilet tayi wanka tazo ta shirya ta sake kwanciya be shigo ba, Hafeez ma ya shigo ya d'inga tsokananta tana mishi dariyar yake kawai, ya d'an jima kan ya musu sallama akan office zashi ya biyo duba jikintan, bayan fitanshi Anty rahama ta shigo.
Nan de suka baje akan taburaman da suka taho dashi suka shimfid'a daga gefen d'akin, turo kofa akayi da sauri ta d'ago se taga dr Ameera kanta ta sauke a hankali wai ita yaushe ta fara mishi irin wannan son ne? Ji take kaman zatayi yaya ba abinda take so illa ta d'aura idanunta kan kamilalliyar fuskanshi, a zuciyarta kuwa tunani take watakila matarshi ta d'auke mishi hankali har hakan ya sa ya manta da ita, abinka da mace se taji kaman tayi ta kuka ko zuciyarta ze yi sanyi fata kawai take Allah ya sanya mishi sonta kwatankwacin wadda take mishi Don tana da tabbacin ba sonta yake ba ya aureta ne kawai out of pity.
"My patient magana fa nake" firgigit tayi tana kakalo murmushi tace "Ina kwana dr?" Dr Ameera tace "lafiya kalau tunanin me kike ne haka? Kin san be kamata ki dinga tunani har kina fita cikin jama'a ba sbd high Bp d'inki tunda an samu heart attack d'in ya watse" Kai ta gyad'a tare da furta "In Shaa Allahu zan kiyaye, dr yaushe za'a sallameni? bana jin daad'in zaman asibitin nan gashi lectures na ta wuceni".
Murmushi dr tayi kan tace "za'a sallameki sede ba fa nan kusa ba sbd har yanzu bamu gane wani irin ciwo ne dake ba" Anty rahama Tace "amma zuwa yanzu ya kamata a gane tests kusan nawa aka mata" dr Ameera Tace "nima abin na d'auremin kai wallahi duk irin illness dake kawo convulsion mun mata gwajinsu babu, amma gaskiya In sauran results d'in da suke lab sun fito bata da d'aya daga cikinsu I will definitely discharge her ku gwada na gargajiya".
Cikin amincewa da hakan Suka gyad'a kai ta d'an dudduba jikin kan ta fice, wayanta ta d'auko ta kunna data ajiyewa tayi gefe seda sakon nin gabad'aya suka gama shigowa kan ta d'auko ta shiga group d'insu na school, waro ido tayi ganin yayi lectures yau karkata kanta tayi cike da damuwa tana kurawa wayan idanu a yadda take tunani baze ta'ba raga mata ba kaman yadda taga yakeyi da zarah.
Sunan zarah da ta tuna yasa ta kuma dulmiyawa tunanin zahran Allah sarki aminiyar kwarai har zuciyarta take kewar zaran, Anty kalthum tace "haba Noor ba yanzu aka hanaki wannan tunanin ba?" Murmushi tayi kan tace "Anty na daina" Anty rahama tace "Allah ya sa" dayake tunda ta shigo tayiwa baaba umarnin tafiya se dare kuma Bayan ta bata kud'in napep.
Mazajen Anty rahama da Anty kalthum duk sun zo sun dubata yayinda Abba ya kira aka had'asu yayi mata ya jiki, wani irin daad'i take ji idan taga yadda suke nuna damuwansu a kanta, ba'a ta'ba nuna mata kulawa dayawa haka ba dama mama ce kawai, murmushi tayi tuna mamanta bata fad'a mata bata da lafiya ba sbd kar hankalinta ya tashi, amma bari ta kirata yanzu.
Kiranta tayi kusan ringing na karshe tukun taji an d'auka se taji muryan baba murmushi tayi kan tace "baba mun tashi lafiya?" Ya amsa mata da "Lafiya kalau Alhamdulillah ya gidan naki?" Tace "mun gode Allah, Mama bata kusa kenan?" Yace "mamanki Ai ba lafiya ko magana ma bata iyawa yanzu" a rud'e ta furta "innalillahi wainna ilaihi rajiun jikin ne har yanzu? Me suka ce yana damunta baba? Kuna wani asibiti ne?".
"Kwantar da hankalinki muna nan FMC female ward jikin ma ai da sauki ba kaman jiya ba" hawayen da ya gangaro mata ta goge tace "to bari yazo zan shigo In Shaa Allahu nima Ina asibitin" yace "subhanallah me ke damunki haka?" Tace "zazza'bi ne kawai baba na warke ma" yace "to Allah ya baki lafiya" ta amsa da "Ameen se na shigo" sukayi sallama tana share hawaye tana murmushi a lokaci d'aya hawayen rashin lafiyan mamanta da kuma murmushin sakewar Babanta gareta, ta manta when last baba ya sake mata sukayi magana haka ba komai a muryanshi na tsana ko ki.
"Me ke faruwa ne Noor?" Anty rahama tayi tambayan tana dafa kafad'anta fad'amusu tayi mama ce ba Lafiya Adu'ar samun lafiya suka mata suna jajantawa, ita kam hankalinta na kan waya se kokarin kiranshi take.
********
Kwance yake kan kujeran office d'inshi idanunshi a lumshe kaman me bacci bayan ba baccin yake ba, hankalinshi da tunanin shi gabad'aya yana kan maganan da sukayi da Anty rahama, duk da har zuciyarshi kaman be yarda ba amma yanzu da ya zauna ya nitsar da kwakwalwanshi se kuma ya fara shakar kamshin gaskiya a maganan, amma ze gwada ya gani tabbas In gaskiya ne ba abinda ze sa shi yin delay akan hakan.
Dukda tana makale a zuciyarshi amma ya kasa tashi zuwa asibitin ya tara abubuwa dayawa kanshi duk ya tara aiki da kwana biyu baya shiga offices d'inshi, karan wayanshi ne ya dawo da shi daga tunanin shi, kaman baze d'auka ba se kuma ya sa hannu a table d'in gefen kujeran ya d'auko "Hayateee💝🔐" ya gani ke yawo jikin screen d'in, receive ya danna tare da karawa a kunnenshi itace ta fara yin sallama ya amsa mata tare da d'aurawa da "ya jikin?" Tace "Alhamdulillah" se tayi shiru.
Kallon su Anty tayi ganin suna ta hiransu hankalinsu kwace yasa ta sassauta murya kasa kasa tace "Hamma shine baka zo ba kuma baka kira ba ko bayan fa ka san bani lafiya" Tayi maganan har zuciyarta abinda ke ranta kenan, murmushi yayi kan shima murya kasa yace "sorry dear na d'auka ai ba'a bukatata ne shiyasa" tura baki tayi tace "ni kam bance ba" murmushi yayi yace "na san baki ce ba ai, office na shigo abubuwa na min yawa" Tace "Ohk ba matsala ai, plz mama ba lafiya tana nan FMC Ina so in shiga in ganta" cikin muryan damuwa yace "jikin har yanzu? Subhanallah Allah ya bata lafiya, ki jirani in zo se mu je tare ohk? And ki kwantar da hankalinki she will be fine
In shaa Allah".
Kai ta gyad'a hawaye na gangaro mata lumshe ido yayi ko be kalleta ba wallahi jikinshi ya bashi hawaye takeyi cikin kasa da murya yace "In ba kina son hanani zaman lafiya ba ki taimaka ki dena hawayen nan yanzu zan taho se muje, kinji?" Tace "uhmm na dena Allah ya kawoka lafiya" yace "that's my girl thanks" ya kashe yana mikewa briefcase d'inshi kawai ya d'auka yayi waje dole wanka ze je ya farayi sbd ya gaji class biyu yayi da safen ya san in yaje asibitin nan se ya jima kuma baze iya yini da kayan nan ba.
Direct gida yayi yayi wanka tare da shiryawa cikin fararen kananan kaya da sukayi matukar kar'barshi dukda har ga Allah ba wai so yake ba Don jinshi yake wani iri, ko ta kan dinning da Peter ya shirya mishi be bi ba ya nufi sauka se ganinta yayi gabanshi, "Hamna Ina zaka?" Harara ya buga mata kan yace "inda kika aikeni" Sosa kai tayi kan tace "amm hamma nace ba wata sister d'in babanmuce dake Nijar Allah ya mata rasuwa Ina so zan bi umma gaisuwa in ba damuwa".
Wani munafukin murmushi ya saki yana mata kallon wonders shall never end kan yace "Ahhh tooo sabon salo......" abinda ya fad'i kenan kan ya zagayeta ya wuce da sassarfa ya san iman ta gaji da jiranshi, cikin lokaci kankani ya isa sbd be had'u da holdup ba seda yayi sallah a masallacin asibitin kan ya karasa amenity, tsaye ya ganta jikin gadon tana d'aura gyale a kanta yayinda Anty kalthum ke sallah a kan taburma, Anty rahama na zaune gefenta tana cin abinci.
Cikin fara'a yace "masha Allah jiki yayi kyau kenan?" Juyowa tayi gareshi tana murmushin ganin fara'a sossai a fuskanshi tace "Ai yanzu ko 'yar tsere aka sanya min da kai zan wuceka" murmushi yayi yana mamakin ta yaushe ta fara bud'e baki haka a gabanshi? Dama shi haka yake so ai ya tsani yadda take kin yin magana In ta ganshin nan, "haka ake so ai Alhamdulillah, kinyi sallah?" Tace "eh kai kawai nake jira Don Allah muje In ga mamana" hijabinta ta d'auka ta sanya yana kallon Anty rahama yace "to acici a ci abinci lafiya tunda abinci ya hana a gaidani sbd kar ince nima zanci" hararanshi tayi tace "ka ji min yaro ni ya kamata In gaisheka ko kai ya kamata ka gaisheni?" 'Bata fuska yayi yace "nine yaron?" dariya ta fara mishi ta san abinda ya tsani ace mishi kenan yasa ta fad'i hakan, yana hararanta yace "kema kin san wuce nan wallahi, yanzu Abba ya kwanta dama nine nan babban yayan familyn nan har ke" be jira cewarta ba ya ja hannun iman suka fice.
Se mamakin wasanshi take ashe yana sakewa haka sossai ta d'auka ko da en Uwanshin ma kullum rai a had'e har gwara da zarah ma, ashe ba haka bane, tafiya suke cikin natsuwa dukda ba wani kayan kirki me tsada ne jikinta ba amma tayi kyau sossai tayi fayau da ita yadda ya rike hannuntan ko ajikinshi yasa sukayi attracting hankalin mutanenmu na Nja duk wadda ze wucesu se ya waiwayo ya sake kallonsu gashi sunyi wani irin dacewa da juna they are just so perfect couples.
Ba wadda yayiwa wani magana har suka karasa female ward kiran baba tayi ta tambayeshi gadon da suke ya fad'a mata kan suka shiga, gadaje ne a d'akin sunfi ashirin mutane ko ta Ina ga hayaniya kaman kasuwa dukda wasu securities da nurses na zuwa akai akai suyi magana akan hakan amma abinka da mata se a hankali, gadon suka karasa tana kwance oxygen na makale a hancinta ba abinda ke tashi jikin gadon se saukan numfashinta a hankali.
Baba ne gefenta akan kujera yayinda yayarta matar bappa yushe'u zaune bakin gadon da alamu ita ke zama da ita, har kasa ya duka ya gaishesu se kallonshi Anty raliya ke yi tana mamakin wai wannan ne mijin Noor Iman, iman ma gaishesu tayi Bayan ta duka a hankali garin mikewa jiri ya kwasheta da hanzari ya tareta tare da manna ta jikinshi bata da option se na tsayawa haka Don In beyi supporting d'inta ba zata iya fad'uwa any moment.
Baba da ba shine da aikata hakan ba amma shine da kunya mikewa yayi daga kan sit d'in da yake zaune yace "sannu mamana zo zauna mana ga wuri In ba rashin ji irin naki ba Ina ke Ina zuwa dubiya bayan ke ya kamata aje dubawa" murmushi Abdul yayi yana taimaka mata da zaman yana tunanin yaushe kuma bawan Allahn nan ya fara son ershi?.
Bayan ta zauna yayi excusing kanshi ya fita chan anjima ya dawo da wasu nurses babbar ciki ce ta dubi baba tace "baba d'anku ya chanza muku d'aki ku tattara kayanku mu kaiku chan" baba yana kallon Abdul ze yi magana kenan malabo yace "baba muje zata kuma ganin likita yanzu" Kai baba ya gyad'a speechless ya fara shirin taya Anty Aliya da sauran flakes d'in.
Iman yazo ya kama abin mamaki nurses d'in na ta'ba gadon da niyyan ja Mama ta birkice ta fara fisge fisge da sauri suka ja gadon zuwa Emergency d'aya tayi gaba da gudu zuwa office d'in doctorn da mama ke hannunshi cikin tashin hankali suka bi bayansu se kuma aka hanasu shiga da sauri doctorn ya zo ya shige yana kokuwan saka lab coat. Kuka Iman ta fara lumshe ido Abdul yayi ya bud'e kan ya fara shafa bayanta a hankali basuyi mintuna goma ba doctorn ya fito jiki a sanyaye ya kallesu yace "sede fah hakuri Allahn da ya bamu ita ya d'auke kayanshi" da karfi Iman tace "innalillahi wainna ilaihi rajiun" kan ta sulale zata fad'i kuma riketa yayi yana kwala kiran sunanta, basu ankara ba suka ji fad'uwar baba ma a take nurses maza sukayi kanshi yayinda Abdul ya sungumi matarshi da sauri ya nufi d'akinta da ita dayake suna kusa da amenity ba 'bata lokaci suka karasa yana shiga d'akin Anty kalthum ta fita da gudu zuwa office din dr Ameera se gasu tare a hanzarce umarnin fita ta basu yayinda ta fara aikinta cikin kwarewa.
"Tooooh Mama fah an tafi, masu zarginta se su dena Allah sa mu cika da imani"
🖤Gureenjo🖤
🥀NOOR IMAN🥀
*Fatima Muhammad Gurin*
*Gureenjo6763 on Wattpad*
*'Yar Mutan Adamawa*
💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)
*038*
"Ba yanzu ba Mama bazaki tafi ki barni ba Mama kece gatana plz karki tafi" abinda take ta furtawa kenan tun farkawanta daga suman shock d'in abinda doctor ya fad'a, d'agota yayi ya rungume yana shafa bayanta a kunnenta ya dinga rad'a mata adu'o'in da zatayi Don samun saukin tashin hankalin da take ciki sbd mutuwar Mama, ta kuwa kar'ba tayi ta maimaitawa har seda taji ta samu natsuwa kan ta d'ago da sauri "karfe nawa hamma?" Yace "hud'u saura" Da sauri ta nufi sauka ya riketa "Ina zaki?" Tace "Hamma baza'a kai Mama bamuyi sallama ba dan Allah ka kaini In ganta" tayi maganan hawaye na ci gaba da gangara daga idanunta.
Taimaka mata yayi ta sauka sossai tausayinta da sonta suka kara narkewa cikin zuciyarshi ita kam haka Allah ya so ya ganta, Allah ya bata daman haye waennan kaddarorin rayuwar, jikinshi ya manna ta har suka isa motanshi ya