Follow us on social media
Showing 84001 words to 87000 words out of 131683 words
Chapter 29 - NOOR IMAN Yar Baƙin Ciki BY Fatima Muhammad Gurin
zama cikakkiyar mutum fiye da tunanin me tunani" hawayen ne ya gangaro mata ta sa hannu ta zagaye bayanshi da kyau yau kam ta tabbatar ta yi dacen miji, ta samu shouldern da duk wani abinda ze Faru da ita zata iya kwanciya akai tayi kukanta son ranta, tayi dacen da ba wata mace a duniyar nan da zata iya katarin samun mijin da zai zauna da ita ko da bazata anfaneshi da komai ba, tabbas Abdulraheem d'an halak ne wadda ya san hallaci ya kuma gada, ko ba komai tana sonshi fiye da tunanin me tunani rabuwa dashi shi ze yi ajalinta ta tabbatar, bata san yaushe ba, bata san ta yaya ba, bata san sa'arda sonshi ya shige zuciyarta yayi kane kane ba, halaccinshi gareta kuma ya kara fad'ad'a son har ya rufe duk wani gur'bi lungu da sako na zuciyarta.
Kalaman kwantar da hankali da nasihohi har da kissoshin sahabban da kar'ban kaddara da kuma hakurinsu ya shigar dasu aljannah, ya dinga bata se 12 saura suka samu mikewa zuciyyoyinsu wasai damuwar duk ta gushe musu dukda yana kasan zukatansu amma a fuskokinsu ko alamar hakan babu duk sbd su kwantarwa da junansu hankali kar d'aya yasa d'aya damuwa, (so kenan).
Wayanshi dake silent ya fiddo bayan ya bud'e mata Sit ta zauna, wasu nurses en mata ne suka biyosu da tarkacensu wadda duk daga na Anty rahama se na kalthum se kuma kayan da aka sayo mata a supermarket, da kanshi ya bud'e musu boot suka saka, cikin karairaya d'ayar ta ce "kana da kyau, handsome kaji daad'i kai kam" murmushi yayi sbd kawai kar ya dizga ta taji ba daad'i bayan sun mishi aiki, ba tare da yace komai ba ya wucesu ya bud'e murfin da niyyan shiga d'ayar tace "pls handsome in ba damuwa ka bamu number d'inka ma dinga zumunci" had'e gabas da yamma yayi kaman ze yi magana se kuma yace "excuse me" ya shige motan tare da tayarwa kaman ze buge d'ayar yayi ficewanshi.
Kaman ance ya kalli Iman tab ta had'e gabas da yamma tare da cunno baki, murmushi ya saki ya san be wuce kishi ba tunda Lafiya lau suka fito daga cikin asibitin zuwa mota, yaji daad'in hakan sossai sbd hakan ya sa ya gane tana sonshi ko da kankani ne tunda ta iya yin kishin shi, tuna daren jiya yayi yadda suka rabu kan tafiyan shi, bari de ya gwadata ya gani "Hayatee me yasa kika ki d'aga wayana jiya da dare bayan na san kin gani?" Kallonshi tayi tare da yin raurau da ido tace "kayi hakuri wallahi sharrin zuciyane nima na san ban kyauta ba" murmushi kawai yayi wani nishad'i da farin ciki na mamayeshi ya tabbata itama tana sonshi, ganin yayi Shiru tace "I'm so sorry In Shaa Allahu hakan baze sake faruwa ba" Kai ya gyad'a mata, hasken wayanshi yasa ya maida hankali kai picking yayi ganin Anty rahama.
"Ayi ta kiranka baza ka d'auka ba kai kam" yace "wayan na silent" tace "wai nace nazo na samu baaba ma na d'an ciwon ciki da amai shine nayi ta kiranka In fad'a maka baza ta samu zuwa ba ya za'ayi da kwanan se kuma bakayi picking ba" yace "mind not an ma yi discharging d'inmu" Tace "what???? Ba de abinda muke zargi ne ya tabbata ba?" Ajiyar zuciya me nauyi ya sauke kan yace "muyi waya gobe plz" ya kashe wayanshi.
Ba wadda ya kara magana cikinsu har suka isa gida, zagayawa yayi ze taimaka mata tace "zan iya fah" yace "na sani madam" a tare suka shiga gidan yana tallafe da ita har sama, zaune kuwa suka tarar da Hamna a parlorn saman cikin wata arniyar kayan bacci da ko kunyar idon mahaifiyarta be hana ta sawa ba, tana ganinsu ta mike tsaye tana rike kwankwaso, ko kallonta duk cikinsu ba wadda yayi ita iman yanzu yadda take tana jin duk wadda yayi kuskuren shiga gonanta zata koya mishi hankali, yayinda hamna ke kiyasta yadda zatayi da Iman sbd lokutan da Abdul ya 'bata tare da ita a ranan girkinta.
"Me kake nufi da ni ne hamma" tayi maganan cikin sanyi wadda hakan ya sa shi jin ba daad'i, tare da dakatawa fisgewa Iman tayi daga jikinshi ta fad'a d'akinta dama sun isa kofan, ta rufe kayanta daga ciki, da kallo ya bi kofan kan ya kalli hamna yace "kaman me fah?" Tace "amma ka san yau kwana na ne ko? Amma se yanzu kake dawowa kalli time, sannan na tambayeka zuwa nijar kaki bani gamsasshen amsa wai me kake so in maka ne plz da ze sa ka gane Ina so rayuwanmu ta ingata mu wanxar da farin ciki tsakaninmu" kuka ta saka tana cewa "ka yarda dani nayi nadamar rayuwar auren da nayi da kai a baya, zan gyara In Shaa Allahu baza ka sake jin wata matsala daga gareni ba".
Tausayi ta bashi hakan ya sashi karasawa gareta ya rungumeta "is Ohk, komai ya wuce muje mu kwanta dare na kara yi" wani shegiyar murmushi ta sake a 'boye plan d'insu ya tafi yadda suka tsara, hararan kofan Iman tayi tana cewa a kasan makoshinta 'Sannu Sannu dae bata hana zuwa sede a Jima ba'a je ba, muje zuwa wai mahaukaci ya hau kura, yanzu wasan ya fara' d'aki suka nufa tana manne jikinshi tana mishi wani salo irin na yaudara da kirsa irin ta mata, nan take ya rufta.
Wanka kawai tayi bayan shiganta d'akin ko kaya bata saka ba tabi lafiyan gado daga ita se towel, bata iya farkawa ba har se da taji bugun kofa juyi tayi tana mutsike idanunta a hankali ta sanya kafafunta kasa ganin me knocking baze dena ba, kofa ta nufa ta ma manta me jikinta kawai ta bud'e kofan, kallonta yayi yadda tayi mishi wani irin kyau a haka daga ita se towel, fuskanta ya d'an kumbura kad'an idanunta suna lumshewa da bud'ewa da kansu tsabar baccin be isheta ba aka tashe ta.
Ganin kallon yayi yawa yasa ta shagwa'be fuskanta tare da d'an bubbuga kafanta kasa tace "dan Allah hamma bacci" yayi murmushi yana me enjoying kallon nata a haka tare da shagwa'barta yace "kiyi sallah tukuna se ki koma baccin" da mamaki tace "wai har asuba tayi?" Yace "zauna nan" tare da juyawa ya wuce zuwa room d'inshi, itama d'akinta ta koma tana shiga bayi ta kalli kanta mirror se ta sake kara tana sake kallon jikinta, wai haka ta fita ya ganta kaman wata mahaukaciya ga karamin towel iya cinya, ita kam ta shiga uku gata da Kishiya a haka ne zata karkata hankalin mijinta kanta.
Dafa goshi tayi cikin kasala tace "ummu plz.... Ina da bukatar zahra ki tausaya" yanzu ta dawo ta Ina zata fara Don fa bazata zauna hamna da ummanta su mayar da ita wata bi ta chan ba, hawaye ne ya gangaro mata tuna bata da wani anfani yanzu ga mijin ma da take Shiri akanshi, sharewa tayi tana nufan basin da wannan tunanin tayi alwala, ta fito ta sanya doguwar riga tayi sallah da raka'atanil fajir ta fara kan ta gabatar da na farilla, bayan ta gama bata kwanta ba seda tayi karatun qur'ani har seda gari ya fara haske kan ta kwanta bacci abinta.
Yana komawa d'akin ya samu wayanshi na neman agaji tunani ya fara waye da asuban nan haka gabanshi ne ya fad'i ganin Zahra, d'agawa yayi tare da sallama, ta amsa tana d'aurawa da "hamma Abba ba lafiya ka taimaka ka zo kar ya mutu ya barmu..." yanke wayan yayi yana zaran keyn da ya ajiye jiya kan dressing mirror, da gudu ya fita zuwa kasa yana shiga motan ya sakarwa me gadi horn da sauri ya bud'e mishi get ya fita a guje.
Dayake ba kowa kan titi nan da nan ya isa gidan nasu ko parking me kyau be yi ba ya fice da gudu Hafeez da yanzu shigowanshi daga masallaci sbd d'an makara da yayi yana tafiya ne yana mamakin rashin ganin Abba masallaci, dama ya tafi da mamakin abinda ya hana Abba zuwa buga mishi kaman ko yaushe, ganin Abdul haka ya sa shima ya rufa mishi baya a tare suka isa part d'in Abban parlor suka sameshi kwance kan doguwar kujera yana numfashi da kyar yayinda zahra ke zaune kasan kujeran tana aikin kuka.
A rud'e sukayi kanshi suna kiran sunanshi ganin halin da yake ciki yasa sukayi saurin sa'barshi zuwa mota zahra tabi bayansu, da mahaukacin gudu Abdul ya ja motan, wani private hospital dake nan kusa ya kai shi nan take suka amsheshi zuwa emergency, tunda dr ya shiga ba shi ya fito ba se wuraren 8, kallonsu yayi yadda duk suka tashi hankalinsu ba me iya magana cikinsu, d'an murmushi yayi kan yace "ku kwantar da hankalinku mun shawo kan komai Alhamdulillah, jininshi ne yayi mugun hawa kuma ya jima cikin wannan yanayin ba'a bashi taimakon da ya dace ba hakan ya sa jikin tsananta amma yanzu komai ya koma normal se kuyi kokarin kwantar mishi da hankali har jininshi ya sauka gabad'aya yadda ya dace".
Hafeez ne yace "In Shaa Allahu mun gode dr. Zamu iya shiga mu ganshi?" Yace "yes sure amma plz banda hayaniya" Kai ya gyad'a likitan ya bi gefensu ya wuce, wani wawan ajiyan zuciya duk suka sauke, cikin karfin Hali Yacewa zahra "me ya sameshi?" Yana tsoron jin amsanta har ga Allah, kar tace ummu ce sila kuma ta sanadiyarshi da Iman.
Abinda be so jin bane kuwa yaji "rikici sukayi da ummu akan hanani magana da Iman da tayi.... Hamma dan Allah kuyi wani Abu maganganun ummu na jiya ga Abba wallahi sun mugun d'aga min hankali..." ta karasa da kuka sossai, Hafeez ne ya karasa yana bubbuga mata baya yayinda Abdul ya buga bayanshi da gini yana dafe kanshi ya tabbata a tsakanin nan aka dubashi shima ba abinda ze hana a ga jininshi yayi matukar hawa, wani irin Abu ne wai haka? Me mutanen nan suke so yayi ne kam, wani zuciyar yace Sakin Iman shine solution to all this problems don lokacin da ya auri hamna ba haka ba, da sauri ya gyad'a kai yana mikewa daga jinginan da yayi ba tare da ko ya kallesu ba ya nufi hanyar waje.
🖤Gureenjo🖤
🥀NOOR IMAN🥀
*Fatima Muhammad Gurin*
*Gureenjo6763 on Wattpad*
*'Yar Mutan Adamawa*
💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)
*this page is a dedication ga duk wata Nurse me karanta littafina I'm so sorry if yhu guys feel disappointed, or some kind of disrespect a page d'ina na jiya, ban sa don cin mutunci ko wani abu ba if yhu noticed and baka ji daad'i ba sorry!!!!!.
*040*
Banko kofan da akayi ne ya sanyata d'ago kai daga kallon jibgin akwatunan dake gabanta da take shirin fara jerasu cikin wardrobe, kallon Hamna takeyi cikin mamakin wannan isa haka, ta tashi da wuri sbd bata wani iya baccin safe ba amma taji daad'in d'an baccin sossai fiye da yadda zatayi na awanni jinta take garau kaman ba jiya aka sallamota ba hakan yasa ta watsa ruwa kawai ta zura wata cotton doguwar riga ba tare da ta nemi d'ankwali ba ta janyo akwatunanta da shirin shiryasu cikin wardrobes d'in.
Cikin ta'be baki take karewa d'akin kallo up and down side by side, daga karshe ta ja tsaki tana cewa "Eyyah abin kunya da Allah wade na gode Allah da nawa iyayen ne suka min komai na d'akina basu jira gidan miji ba" ta'be baki tayi tace "Au ashe fa talakawa ne likis ba sisi bare kobo na taburman kaba" Zatayi wani maganan Iman tayi saurin cewa "toooh Allah sa de lafiya baiwar Allah se kace ba musulma ba? Ki shigowa mutum wuri ba sallama sannan ki tsaya kina haushi kaman......" bata karasa ba ta wani kwa'ba fuska ta maidashi kan kayan.
Cikin 'bacin rai hamna tace "kutumarr ni kike kira karya??" Ko kallonta Iman batayi ba ta bud'e wardrobe ta fara shirya atamphopin da ta fidda daman, "ke da ke fa nake magana, don uwa....." "kulll" cewar Iman tana karawa da "Uhmmm uhmm uwata fah ba sa'an wasan wata uwar bane bare wata yarinya ta samu daman zaginta a kiyaye" cikin 'bacin rai Hamna tayi kanta tare da d'aga hannu da niyyar marinta, hannunta taji an rike a zuciye ta juya se suka had'a ido yanayin da taga fuskanshi kad'ai yasata sanyaya nata zuciyar kofa ya nuna mata juyowa tayi ga iman tayi mata wani kallo kan ta juya ta fice fuuu.
Kallo d'aya ta mishi ta dukar da kanta hankalinta na tashi me ya sameshi Ko kuma tace me ke damunshi, kallonta kawai yakeyi zuciyarshi na tsananta bugawa ga sake sake da waswasi da suka taru suna mishi zirga zirga a kahon zuciya, batayi aune ba kawai se ji tayi ya mata wani wawan runguma har seda ta d'an yi kara sassauta riqon da ya mata yayi yana me lumshe idanunshi, a sanyaye ta d'aga hannunta zuwa bayanshi tana shafawa ta lura yana cikin damuwa ba kad'an ba.
Ajiyar zuciya ya dinga saukewa a jere a jere cikin sanyin murya yace "hayateee bazan iya rayuwa ba tare da ke ba wallahi Ina sonki sossai, kallonki kawai da nayi naji rabin damuwana sun yaye" d'agowa tayi ta kalleshi kad'an wani irin sonshi na kara mamaye mata jiki da jini, hannunshi ta kama be musa ba ya bita har bakin gado suka zauna kwanciya yayi tare da d'aura kanshi kan cinyarta ita kuma ta sa hannu cikin sumar kanshi tana wasa da shi.
Cikin taushin murya tace "menene ya faru? Akan matsalata ne ko?" Hannunta d'ayan ya kama ya d'aura kan kirjinshi tare da d'aura nashi kai idanunshi lumshe yace "Abba ba lafiya" a rud'e tace "innalillahi wainna ilaihi rajiun me ke damunshi haka?? Yana Ina asibiti ko gida?" Bud'e lumsassun idanunshi yayi ya zuba mata yadda ta rud'e kawai yasa yaji jikinshi yayi sanyi har hawaye ta fara ko su iya rud'ewar da zasuyi kenan.
Me laifinta? Bata da ko d'aya abinda ya kamata ya tambaya shine me ke damun ummu ne a duniyar Allahn nan? 'Digar hawayenta kan fuskanshi ne yasashi sauke ajiyar zuciya yace "da sauki fah yana hospital" share mata fuska yyi da tafin hannunshi cikin damuwa tace "Eyyah Allah ya bashi lafiya bari In tashi in shirya ka kaini pls in dubashi". 'Daga kanshi yayi ta mike shi kuma ya janyo pillow ya kwanta da kyau, a maimakon tayi toilet se ta fita zuwa kitchen, da tunanin abinda zata girka musu har mijin nata da ta tabbatar be karya ba ta shiga.
Fridge ta bud'e ganin kaza ya sa ta fiddo shi ta sa mishi ruwan zafi nan da nan ya narke kan ya narke ta had'a abubuwan da zata bukata ba 'bata lokaci ta had'a pepper soup na kazan da vegitables ta barshi on low heat, tana aikin ne tana sake murmushi time to time sbd tuno yadda ya furta yana sonta, bata ta'ba zato ba kuma har yanzu bata yarda ba taya za'ayi ya so ta cikin lokaci kankani haka, watakila ya fad'a ne kawai Don yana cikin damuwa amma ko ma menene ta ji daad'i har kasan ranta daad'in da ta jima bata ji ba a rayuwanta wannan ranar yana d'aya daga cikin waenda bazata manta ba har Abada.
Irish da plantain ta soya a d'ayar cooker d'in kuma ta dafa white basmati rice, cikin sabbin coolers d'in kitchen d'in ta shirya komai ta sa a basket tare da d'aura tumakasa ta rufe saman, a plates ta d'iba musu ita da shi ta zuba p soup d'in a bowl me d'an girma ta kara zuba plantain and chips d'in wani plate ta d'aurasu kan tray bata san ko ze sha tea ba, amma de ta dafa ruwan zafi ta juye a karamin flask ta d'aura gefen tray d'in da cup da kuma spoons, teaspoon and forks, ta d'auka ta nufi room d'inta da shi a kan center table d'in parlor ta ajiye, wayanta da ta tuna ta manta shi kitchen ya sa ta koma d'aukowa, daga bakin kitchen d'in taga umma da plate da serving spoon ta nufi basket d'in da ta shirya don Abba, da azama ta karasa ta d'auke shi dayake ta fi kusa da basket d'in.
Wani wawan kallo umma ta mata kan tace "ke yaushe na fara wasan haka dake? Kin ajiye min abinci na d'iba ko se na kutuma miki na maguzawa?" Cikin ladabi tace "umma Abincin na Abba ne asibiti za'a kai mai" wata uwar harara ta buga mata kan tace "aaa Baba ne ba Abba ba kin ajiye ko se na sa'bamiki?" Juya kai tayi kan tace "gaskiya umma kiyi hakuri ba zan iya d'ibar miki ba, In akwai gaskiya ma Ai Anty hamna ce da girki har mu ya kamata ta bawa amma ana neman 10 ko kitchen d'in bata shigo ba bare ta d'aura wani abin".
Tana kai nan ta juya ta fice waro ido umma tayi tace "kuttt kan kaza fah ya fara wayewa ya kamata mu d'auki mataki cikin gaggawa dama ance talaka be iya samun wuri ba" Shiru tayi cikin nazari in ta barta zata ga kaman bata isa da gidan bane gabad'aya In ko ta bita zata kawo mata raini tunda taga ta fara gashi abincin ya shiga ranta. Da karfi ta fara kwala kiran sunanta tana cewa "ke saudatu ne ko wace uwar tsaya wallahi ko kiyi nadama yanzu In kira wacce ta kawo mijin naki duniya ta nuna miki Ina da muhimacci sossai a rayuwanku in kuma nuna miki isata".
Da waennan surutan ta karasa ta banke kofar d'akin Iman d'in wadda hakan yayi sanadiyar tashin Malabo hayaniyarta ta ci gaba dayi har cikin d'akin yayinda iman ko ta kalleta taje ta ajiye basket d'in gefen gado, kallonshi be sa ta dena masifanta ba yayinda Iman tayi kaman bada ita take ba shine yayi karfin halin cewa "umma lafiya?" Tace "Ina fah Lafiya ka kawo fitsararriya marar tarbiyya me ji......" hannu ya d'aga mata yace "no please go straight to the point" waro ido