Follow us on social media

Showing 69001 words to 72000 words out of 131683 words

Chapter 24 - NOOR IMAN Yar Baƙin Ciki BY Fatima Muhammad Gurin

bayan sun gama fad'ar Abinda zasu fad'a ummu ta kalli Anty rahama tace "ke rahama raba akwatunan biyu, hamna za'bi wadda ya miki" daga bakin kofa sukaji ance "excuse me!!!" Duk juyawa sukayi se suka ga Abba.

Se a lokacin Abdulraheem ya fito ashe tun fara abin yana jinsu yayi niyyar ya fita ya sassa'ba ma hamnan se kuma ya fasa jin sun kira ummu kar ta zo taga abinda yayi niyya laifinshi ya karu a wurinta shi wallahi yanzu har ga Allah tsoron Ummu yake, mamakin halinta na yanzu kuwa yana ga har kwanan gobe baze dena mamaki ba, the silent, loving and caring ummunshi ta dawo wuta yanzu, "Am rahama da kud'in wa kikayo sayayyan nan?" Inji fad'ar Abba, Anty rahama tace "Abba kud'inka" yace "good, d'auki kayan ku shigar mata" jiki a sanyaye su Anty rahama suka fara shigarwa.

Juyawa tayi kan Abdulraheem tace "Don ubanka In ni na tsuguna na haifeka kuma Nono na ka sha kayiwa hamna irin kayannan inga uban da ya isa ya hanaka" kanshi ya dukar kasa idanunshi na kad'awa a lokaci d'aya cikin sanyin murya yace "In Shaa Allahu" ya juya kawai ya shige d'akinshi, Abba karan kanshi se da yaji hawaye ya cika idanunshi me Rashida ta zama ne? Zarah kam kuka ta saka musu, juyawa Abba yayi ya tafi, ummu ta rufa mishi baya bata so hakan ba ta so Abdul ya ja da ita ta kikkifa mishi mari ko zata rage abinda ke cinta a rai, su hamnan ma basu so hakan ba haka dai suka juya suka shige suna kwafa, bayan sun gama shigar da kayan duk suka fice kowa rai ba daad'i suna kuma jima Iman tausayi Don kiyayyar uwar miji ba karamin abu bane.

Su zarah ne suka shiga karshe sukayi mata sallama ta kasa kallon zarah kaman yadda zarah ta kasa kallonta, ita zarah na ganin tsantsar rashin dacewar Iman d'in da uwar miji, gashi kuma wai mahaifiyarta kunya ya hanata kallon Iman d'in, yayinda Iman kuma ke jin kaman itace sanadin komai, duk abinda ya faru da family d'insu itace sila, da kaddararta be bi ta gidansu ba da ummu bata tsani Abdulraheem ba, da ummu da Abba basu samu matsala for the first time a zamansu ba.

Bayan tafiyan su zarah kukanta ta ci gaba da yi seda taji an kira magariba kan ta mike ta shige toilet ta wanke fuskanta tazo tayi alwala, daga ka ga fuskanta zaka san ta sha kuka, ko kayan da suka jere bata kalla ba, ji tayi ta tsani kayan ma da ya bi ta tata da ya d'iba duka ya bawa Anty hamnan ita kam basu dameta ba sam wallahi, d'an waenda ya saya mata wurin malabis ma sun isheta rayuwa.

Bayan ta idar da sallah ta d'auki alqur'ani ta fara karantawa, cikin daddad'ar qira'arta, tana cikin karatun taji an turo kofa dayake labulen da ya raba parlor da d'aki na sauke yasa bata ga me shigowa ba dukda kuwa kofan take facing daga inda take zaune, lumshe ido yayi wani sanyi na ratsa shi sanyin kamshin turarukan wutan dake tashi cikin d'akin, ya had'u da sanyin Ac da suka kure duk na ciki da parlorn, da kuma sanyin daad'in karatunta.

Kasa karasawa yayi ya zauna nan parlorn ya kishingid'a tare da lumshe ido, ita kuma a 'bangarenta ganin ba wadda ya shigo ya sa ta ci gaba da karatunta hankali kwance seda aka kira isha ta dakata ta d'aga hannu sama ta dinga kwararo adu'o'i a fili dukda ciwon da kanta ke tsananin yi hakan be hanata yin adu'anta cikin hawaye da kaskantar da kai ga mahallicinmu ba.

Duk adu'an da tayi akan Allah ya sasanta tsakanin family d'in mijinta ya kawo musu karshen wannan tashin hankalin In itace sila Allah ya kawo sanadiyar da zasu rabu kar wani ciwon ya kamashi sanadin tashin hankalin mahaifiyarshi, rokon Allah tayi Allah ya hana ta tankawa Hamna da mahaifiyarta ko da kuwa hannu ta d'aga ta mareta, ta roke Allah ya tsareshi ya kareshi da sharrin masharranci sbd ta san ita kam guba ke yawo jikinta duk inda ta ratsa se an samu matsala.

Shigowarshi ya sa ta shafa adu'an tana hawaye, a gaban sallayan ya zauna bayan ya d'age qur'anin lumsassun idanunshi da suka kara komawa ciki tsabar damuwa ya zuba mata yana girgiza kai cikin sanyin murya yace "karki kuma irin wannan adu'an plz saudah!!!" Kanta ta dukar hawaye na kara gudu kan kuncinta  ya ci gaba "idan kika ci gaba komai ze iya faruwa kiyi adu'ar zamanmu lafiya amma plz karkiyi adu'ar fita a d'akin aurenki, In Shaa Allahu kin shigo kenan mutuwa ce kawai zata raba".

Kai ta gyad'a mishi yasa hannu ya share mata Hawayen fuskanta ya ce "ke watarana se kin nemi hawaye kin rasa a idanun nan naki" ya karasa yana lakace mata hanci murmushi ta sake tana kau da kanta, shima murmushi yayi yace "ki dena damun kanki idan kika ci gaba bazamu shirya ba Don ban shirya yin jinya ba, and kiyi hakuri da ummu ba haka take ba, ban san sadda ta zama haka ba nima..... I'm really confused and afraid.....".

Ya karasa muryanshi na chanzawa Allah sarki bata san sadda tayi hugging d'inshi ba tana kuma sa mishi kuka, tausayi yake bata a labarin da zarah ta bata sunfi kowa kusanci haka tafi sonshi duk cikin 'ya'yanta to me yasa take mishi haka? Bayanta ya dinga shafawa a hankali yana hura iska daga bakinshi da ze iya da kukan yayi ko ze ji damuwar dake dankare a zuciyarshi sbd fushin mahaifiyarshi ya sauka.

A hankali yace "me na gama cewa yanzu?" Shiru tayi tana goge hawayenta tare da mikewa daga jikinshi tace "na dena" yace "good, tashi kiyi sallah In kin idar ki fito parlor zanyi magana daku" tace "to se ka dawo" ya mike ya fita ta tashi ta tada sallah, bayan ta idar ta zubawa kayan ido yanzu waennan kayan Allah kad'ai ya san irin kud'in da suka kashe wurin yinshi gashi ze sake yin wani.

Ajiyar zuciya ta sauke kan ta mike ta fito ba tare da ta Cire hijabin kanta ba, bata samu kowa a parlorn ba hakan ya sa ta samu kujera ta zauna idanunta suna kan tv, wani wa'azi ake da ya sata maida hankali kai Shiek Tijjani Ahmad guruntum ke wa'azin rayuwar aure da yadda mace zata kula da kanta, hankalinta ya tafi gabad'aya wurin wa'azin se gani tayi tashan ya chanzu ya koma wurin rawa wato boom tv, kallo d'aya ta mata ta kau da kanta.

Tare da mayar dashi kan yatsun hannunta, ita bata da lokacin tashin hankali wallahi baza ta iya ba, ita kuwa hamna ta so ta tanka ta yadda zata samu ta ci mata mutunci son ranta amma se taga bata ce komai ba, kwafa tayi. Da sallama ya hawo saman idanunshi na sauka kanta sam zuciyarshi baya jin daad'in yadda yake ganinta, yau gabad'aya yini kuka tayi shi da yayi alqawarin baze kara bari hawayenta ya zuba ba.

Tsakin hamna yasa ya kau da idanunshi ya mayar kanta yana zama, kusa dashi tazo ta zauna ajiyar zuciya ya sauke ya fara da sallama kan ya musu nasihar zama lafiya, ya jima yana musu nasiha har seda ya ga Mutuniyarshi ta fara hawaye kan ya dakata, kallon hamna yayi da hankalinta gabad'aya ke kan tv ko jin abinda yake fad'a be yi tunanin tanayi ba.

"Hope zaku had'e kanku ku zauna lafiya?" Yayi maganar yana kallonta kallonshi tayi kan tace "eh in bata shiga harkata ba kenan" kallon Iman yayi ta d'anyi murmushi kan tace "In Shaa Allahu, Allah ya bamu hakurin zama da juna" yace "Ameen, and maganan kwana biyu biyu yayi, and batun abinci kowacce ranar girkinta zatayi girki gida gabad'aya Safe da rana kowa ze iya cin abinshi shi kad'ai amma dole abincin dare mu ci gabad'ayanmu tare kullum" 'bata rai hamna tayi taya za'ayi ace zata yi girki da wannan matartashi dukda ba ita zata girka ba amma Ai ita ke biyan kukun.

Zatayi magana ya tari numfashinta da cewa "it's constant ba chanji abinda nayi niyya kenan, and batun kwana bazan iya dinga bin kowacce d'akinta ba duk wacce ke da girki dole ta dinga kwana d'akina" hamna tace "Amma Hamma kaima ka san ban iya kwana d'aki d'aya da kai taya zamu fara Don zuwan wata?" Yace "dole ne shima ba shawara ba" had'e rai tayi cikin gatse tace "kenan daren yau kwananta ze kare tunda de BZ ce" d'an kallon Iman yayi se yaga tayi murmushi girgiza kai yayi yace "yes gobe da yamma zaki kar'ba" wani irin murmushi ta saki kan tace "shikenan ko? Ko akwai wani abin?" Girgiza mata kai yayi, ta mike ta shige d'akinta se lokacin Iman tayi mata kallon tsab ashe wata shegiyar night gown ce jikinta dake bayyana komai na jikinta ko kunyan uwarta bata ji ba yanzu ta fito a haka?.

Allah ya kyauta ta furta tana kawar da kai se suka had'a ido dukar da kai tayi ya mike ya nufi room d'inshi ba tare da yace komai ba, cikin sanyin murya tace "Abinci....." tsayawa yayi kan ya juyo ta mayar da kanta kan yatsun hannunta tace "munyi girki da su Zarah yana kan dining nace ko zaka karasa In zuba maka?" Murmushi yayi kan yace "kira Hamna and meet me in the dining room" Kai ta gyad'a ya nufi dining ita kuma ta nufi d'akin zuciyarta na bugawa.

Bata san me kuma ze faru ba ita kam yau ta ga ta kanta da su hamna daga safe zuwa yanzu sun mata abubuwa kala kala, tana tsoro kar hakurinta ya kare, sallama tayi yafi sau hud'u basu amsa ba kuma tana jin surutunsu shiga tayi daga bakin kofa ta tsaya tace "Anty hamna, umma ku fito muyi dinner" hiransu suka ci gaba da yi kuma zaginta suke fah amma ko a jikinsu murmushi tayi ta juya ta fice.

Yana zaune yana danne danne a wayanshi kallon Ina suke ya mata tace "suna zuwa" zuba mishi tayi ta tura mishi har zobon, itama ta zuba ma kanta tare da zama suka fara ci, har suka gama ci ba su hamna ba labarinsu girgiza kai yayi hamna baza ta ta'ba jin magana ba, be san ya ze yi da ita ba, d'akinshi ya shige ba tare da ya bi ta kan hamnan ba, bayan ta gama ci ta tattara wurin  gabad'aya abinda ta san ze 'baci ta sa duk a fridge.

'Daki ta koma ta tu'be ta sa cotton kayan bacci me kauri riga da wando ta saka hula tare da kara fesa turare, ta d'auki khimar ta saka tare da jan tunga ta tsaya, se kuma ta fara safa da marwa ya zatayi taje d'akinshi itakam taga ta kanta, gashi baza ta iya fara karya mishi doka ba, shahada tayi ta fito tare da jan kofanta ta rufe ta nufi nashi da wayanta a hannu, ta jima tsaye bakin kofan tana sake sake kan tayi shahada ta tura kofan da sallama.










                     🖤Gureenjo🖤



                  🥀NOOR IMAN🥀

*Fatima Muhammad Gurin*
         *Gureenjo6763 On Wattpad*

*'Yar Mutan Adamawa*

💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)

*this page is dedicated to my two beautiful, amazing, caring, loving, and troubles🙄😏 sisters and friends Haneefa Muhammad Gurin(Oda half) and Hauwa Ibrahim yahaya(Dbestest) kuyi yadda kuke so dashi and plz a sarara min da masifan yin typing da wuri, Shaa I love you guys so very much🥰🥰 Happy sisters day*

                         *034*

Tsaye ta hangeshi kan sallaya sanye da Ash jallabiya sallah yake shirin tayarwa da alamu shafa'i da wutiri, amsa sallamar yayi yana kallonta kanta kasa kaman wata 'barauniya ta lalla'ba ta zauna, se yanzu ya tuna da ashe ana sayawa Amarya kaza, murmushi yayi tare da nufo parlorn be ce mata komai ba ya wuce ya fita.

Kallon d'akin ta hau yi tana mamakin irin kud'in da aka zuba don komai na d'akin kana kallo zaka san ba karamin kud'i ke gareshi ba, ta kai 1hour zaune a wurin kan taji bud'e kofa kallon kofar tayi se suka had'a ido da sauri ta dukar da kanta, lumshe ido yayi ya bud'e kan ya nufi cikin room d'in ba tare da ya kalleta ba yace "ki yi Alwala".

"Ina dashi" ta furta yana ajiye ledojin hannunshi daga gefen sallayan da ya shimfid'a yace "bismillah" mikewa tayi ta karasa ta tsaya daga bayanshi wani sallayan ya d'auko ya shimfid'a mata tare da juyawa ya tada sallah, har lumshe ido takeyi tsabar yadda qira'arshi ke shiganta bata so sam suka gama sallahnan ba raka'a biyu sau biyu sukayi kan yayi sallama ya fara kwarara musu adu'o'i tana amsawa.

Bayan ya shafa ya juyo ya dafe kanta yayi mata adu'ar da Allah ya tanadarwa Amarya ko sabon Abu, ido ya zuba mata bayan sauke hannunshi daga goshinta tunda ya d'aura hannunshi wurin ta lumshe ido, idanunta da lips d'inta sun d'an kumbura sunyi ja dukda ba fara bace yana iya ganewa, rawa ta farayi da lashes d'inta hakan yasashi sa yatsanshi d'aya a hankali ya shafa saman idon, wara idon tayi a kanshi kokari yayi ya rike idanunta cikin nashi.

Sun jima suna kallon juna kan tayi saurin kau da idanunta lumshe nashi yayi yana cewa "samo mana plate da cups" har ta mike yace "tsaya, zo ki zauna" komawa tayi ta zauna shi kuma ya mike ya nufi kofa, yana so ta samu duk wani gata da mace ke samu a rayuwarta be so tayi missing komai, kowanni miji da ze auri matar da yake matukar so a daren da zasuyi na farko baze iya bari tayi wani aiki ba gashi be bata gatan ba tunda yau ma yini aiki tayi.

Kitchen ya shiga ya d'auko plate da cups biyu da spoon and fork ya d'aurasu kan tray ya fito, karo suka kusa ci da Hamna da matukar mamaki take kallonshi a zuciyarta tunani take me bawan Allahn nan ze yi da abubuwan nan, ba tare da ya tanka ta ba ya wuce yayi d'akinshi, inda ya barta nan ya dawo ya sameta a kasan shima ya zauna ya bud'e ledojin ba tare da ya juye kajin ba ya d'aura haka kan plate ya san sunci abinci ba lalle taci na kirki ba.

Fresh milk ya bud'e ya zuba musu a cups kan ya sa hannu ya d'auki fork ya yanko kazar ya kai bakinta kallonshi tayi da ido ya nuna mata bakinta alamun ta bud'e shagwa'be fuska tayi shima ya shagwa'be nashi murmushi ta saki shima kuwa ya saki ba tare da ya san ma yayi ba, kad'an ta bud'e ya sanya mata ta fara taunawa a hankali kallonta ya dingayi yana murmushi har ta gama na bakintan shi kad'ai ya san manufar kallon da yake mata mussamman lips d'inta dake tauna abinci kaman basa so.

Ya bata kusan sau biyar kan ta kau da kai a na shiddan gira ya d'aga mata alamun ya? Tace "na koshi" fresh milk d'in ya d'auka ya sa mata a baki da gayya yaki cirewa seda ta sha rabin cup ya d'an d'aga zatayi magana a shgwa'be ya mayar da cup d'in be cire ba seda ta shanye ya ajiye yana murmushi fakon idonshi tayi ta zuba mishi harara kasa kasa tana cewa "wannan gayen ya kware a mugunta wallahi Haka kawai a saka shan abun dole gashi yanzu cikina kaman ze fashe tsabar koshi shi yana nan yana dariya" ta karasa tana tura baki.

Be ko kalleta ba seda ya shanye fresh milk d'inshi ba tare da yayi loma ko d'aya na Kazan ba, yace "me ma kika gama cewa?" Waro ido tayi kan tace "ni?" Ya d'age mata gira d'aya ta kad'a idanunta kan tace "ba abinda nace" cikin kunkuni shima ya maida mata abinda ta gama fad'a d'azu, a d'ari ta mike ta sa'bi tray d'in tayi kofa a kunyace ita kam ta shigesu duk sadda zata yi magananshi se ya ji ta kaman wani maye.

Tana bud'e kofa suka had'a ido da Hamna da alamun ta jima jikin kofan don ba daga 'bangaren d'akinta take ba ta wurin d'akin Iman take, harara ta sakarwa iman yayinda ita kuma tayi mata murmushi haushi ne ya zo wa Hamna wuya a take, wato hamma yarinyar nan ya d'aukowa kwanukan cin abinci Don bala'i shi da ko cup be ta'ba tace ya mika mata ya mika mata ba sede ya sakar mata harara amma yarinyar nan har plate da cup fork and spoon ya d'auko mata the biggest issue d'in kuma kaza da yayi son kai ya sayo musu su kad'ai banda ita da ummanta.

Iman na shiga kitchen ta fara hawaye sossai yanzu kukan takeyi har zuciyarta abin ya mata zafi ba kad'an ba, jikin umma ta kwanta tana kukan umma dake aikin waya da en duniyan kawayenta suna fad'a mata wani sabon malamin da suka samo a nijar, da sauri tayi musu sallama tana kama Hamna tace "lafiya hamna me ya faru?" Cikin kuka tayiwa umma bayanin abinda ya faru yanzu fitanta d'ibo musu abinci da makalewa da tayi tana leken abinda sukeyi.

Shiru umma tayi ita karan kanta ta san hamna bata da wuri a zuciyar Abdulraheem dukda bata tabbatar da ko yana son Iman ko baya sonta ba, har gwara da yana d'an damuwa da damuwar iman amma tunda ya gane da gangan tsawon shekarun da yayi yana neman d'a take shan magani ya tattara lamarinta ya watsar, tunanin mafitan 'bata musu wannan daren ta fara cikin mintunan kad'an ta samo d'aya a zuciyarta tace bari mu gwada.

A kunne ta rad'awa iman abinda zata je ta fad'o mishi ita kuma ta kwanta tare da jan blanket ta rufe jikinta Bayan ta cire kowanni abun kwalliya dake jikinta, da sauri Iman ta tashi ta nufi d'akinshi.

A 'bangaren Iman kuwa Bayan ta ajiye tray d'in d'akinta ta nufa tayo brush tana tunanin halin hamna how on earth someone could stood so low like that? La'be fah take musu, Ajiyar zuciya ta sauke tana furta "Allah ya kyauta" Bayan ta gama ta koma room d'inshi duhu ta gani se blue dim

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login