Follow us on social media
Showing 87001 words to 90000 words out of 131683 words
Chapter 30 - NOOR IMAN Yar Baƙin Ciki BY Fatima Muhammad Gurin
tayi tace "aaa ashe ga inda ta gani kaima raina ni kenan zakayi toh shikenan d'an halak kafasa mu zuba ni da ku" ta fice fuuuu.
Dafe kai yayi kan ya d'aga ya kalleta fuska ta shagwa'be tare da cewa "Allah ni ba ruwana" girgiza kai yayi yana shirin mikewa fakonta yayi ya fisgo hannunta zuwa jikinshi yace "bakya ji ko?" Da farko ta tsorata kan ta shagwa'be tace "Da gaske ni ba ruwana" serious ya ci yace "ki dena neman maganansu pls kinga bana so a ta'bamin lafiyanki d'azu da ban zo ba fah?" Shiru tayi a zuciyarta tace 'tabbb sun isa ma? Ni kuma Ina me?' A fili tace "ba abinda ze faru in shaa Allahu, abinci na sanyi zaka ci ko zaka fara yin wanka?" Murmushi yayi cikin wani yanayi na jin daad'i abinda ba'a ta'ba yi mishi ba kenan a gidanshi ace wai abinci ne yau ake mishi iso ya ci kar yayi sanyi ko wanka tukuna, abinda da yayi da ko kar yayi duk d'aya wurin matarshi.
"Bari In ci kan wankan rabona da sa abu a cikina tun lunch na jiya shima snacks" d'agowa tayi tace "Eyyah muje to ka ci" gaba tayi yabi bayanta zuwa parlorn kasa ya zauna ta sauko musu abincin suka fara ci, se santi yake mata tana dariya wallahi kaman ba shi ba, bata ta'ba ko da hasashen haka yake ba a da yadda ko fara'a bashi da shi a gaban mutane, shi ya fara ajiye cokalin yace "Alhamdulillah thanks for this wonderful meal hayatee" murmushi kawai tayi, bayan ta gama ta mike kenan da nufin zuwa d'akinshi had'a mishi ruwan wanka se kuma ta tuna ashe ba itace da girki ba, tray d'in ta d'auka ta fito da shi, wani kara ta saki wadda ya sa malabo dake shirin shiga room d'inshi shigowa kitchen d'in da sauri, da gudu ta 'buya bayanshi "lafiya me ya sameki?" Ya fad'a yana shirin juyo ta amma sam taki sakinshi ta makale a bayanshi ga plates d'in duk zube kasa Allah ya sa unbreakable d'in nan ne.
"Innalillahi wainna ilaihi rajiun baka ganshi ba?" Yace "wa?" Tace "wani kato tsaye yana anfani da kitchen utensils?" Ajiyar zuciya ya sauke yana dafe kai lokaci d'aya murmushi na su'buce mishi a lokaci d'aya kuma ya had'e rai yace "Peter will yhu please excuse us?" Peter da ya hangame baki yana kallonsu yace "yes sir" kan ya bi ta d'ayar kofan ya fita stairs ya gangara kasa ta inda yake bi.
"Cook d'in mu ne fa" ta d'ago da sauri tana cewa "yanzu wannan gardin ke yawo muku a cikin gida a matsayin kuku? Tabb" ta juya ta fice shima fita yayi zuwa d'akinshi duk wanka sukayi suka fito kusan a tare a shirye shi sanye da normal kananan kayanshi bakake ita kuma ta sa wata atampha doguwar riga hijab ta sanya sbd kamata da kayan sukayi ba komai a fuskanta hannunta rike da wayanta da kuma basket d'in abincin Abba, sossai ta mishi kyau ba tare da sun nemi mutanen gidan ba suka fice, Allah kad'ai ya san me suke kullawa sun kule a kuryar d'aki.
Wata BMW d'inshi ya d'auka suka fice zuwa asibitin hira suka dingayi a hankali akan rayuwanta wadda shi yake d'an tambayanta abinda ya d'aure mishi kai tana bashi amsa for the first time a rayuwanta da ta ta'ba ba da kad'an daga cikin labarinta batayi kuka ba, gani take yanzu fah komai ya wuce In Shaa Allahu damuwowinta sun kare bayan na ummu shi kuma tana sa rai wata rana komai ze wuce.
A jere suka shiga asibitin wani irin kima yake gani yayi da ita sanye da hijab be ta'ba sanin darajar hijabi ba se yau da ta sa yadda ake kallonsu ma kawai daban ne, tunawa yayi hamna bata ta'ba sa khimar wai zata fita ba, shi hijabinta ma d'aya ya sani na sallah wadda bata ma cika anfani da shi ba, da sallama ya tura kofan d'akin hafeez dake zaune kan plastic chair ya amsa yana d'ago kai murmushi ya saki ganinsu yace "Masha Allah Amarya anji sauki kenan" murmushi tayi tace "Alhamdulillah babana, ya jikin Abba?" Yace "ni de ban son wannan babanan, jikin Abba kuma da sauki bacci yake yi ma d'azu ya farka har magana yayi" murmushi itama tayi tace "masha Allah" Mikewa Hafeez d'in yayi ya ba matar yayan nashi kujera godiya tayi kan ta zauna shi kuma ya zauna empty bed d'in d'akin yayinda malabo ya zauna gefen Abba yana tambayar shi Doctor be kara zuwa ba, yace ya shigo sau d'aya ya kara dubashi, ze yi magana kenan aka bud'e kofan toilet aka fito duk wurin suka mai da ido zarah ce, murmushi tayi kan tace "yaya ka dawo?" Yace "eh" Iman tace "Zahra in......" dakatawa tayi ganin ko kallonta zarah batayi ba hakan ya sa ta tuna abinda ummu tace cikin sanyin jiki da karayan zuciya ta dukar da kanta tana shafa fuskan wayanta, zarahn ma jiki a sanyaye ta gyara yafin d'an kwalinta tana kallon yaya hafeez tace "hamma muje tunda babban yaya ya zo samu inyi wanka se In dawo" Kai ya gyad'a shima cikin rashin jin daad'i ya mike, malabo ya d'auke idanunshi daga kan matar tashi yace "kun fad'awa su Anty?" Hafeez yace "a'a ban fad'a musu ba" Abdul yace "Ohk zan kirasu, sannan ku tabbatar kun fad'awa ummu kuna isa gida" Kai suka gyad'a suka mishi sallama suka fita.
"Hello baba Ina kwana?" Be ji me aka ce daga d'aya bangaren ba yaji ta kara da "ya jikin mama?..... Ohk har yanzu ba'a barku kun shiga ba?" Ta kuma yin Shiru kan ta kara da "amma sun ce da sauki?....... toh Allah ya kara sauki ya bata lafiya ka gaida su umma" suka kashe wayan kallonshi tayi se ta sakar mishi murmushi shima murmushin ya mayar mata ganin bata sa abin sossai a ranta ba, wayan shi ya fidda ya kira Anty rahama da Anty kalthum ya fad'a musu a rud'e duk suka ce gasunan zuwa dukda ya fad'a musu da sauki.
Yana kashewa aka kirashi d'agawa yayi na mintuna kan ya mike yana ci gaba da amsa call d'in yace "ganinan zuwa yanzu Ohk Ohk" yana kashewa yace mata "hayatee ana nemana a office bari inje bani one hour" Tace "Toh Allah ya kiyaye ya tsare" ya amsa da Amin yana ficewa, da wayanta ta ci gaba da wasa Haka kawai taji tana son kiran inna ta kuwa kirata suka gaisa cikin mutunci kaman ba inna ba wadda hakan yayi matukar bata mamaki, har de sukayi sallama bata bar mamaki ba, su Goggo ne ma suka dinga amsa mata wani iri amma se da ta kirasu tas, tana kashe wayan ta d'ago se suka had'a ido da Abba.
Murmushi ta saki kan tace "sannu Abba ka farka?" Kai ya gyad'a ta dan zame daga kan kujeran tace "Ya karfin jikin?" Yace "Alhamdulillah" a hankali ya fara kokarin mikewa ta karasa ta d'ago mishi pillow ya jingina tana mishi Sannu, toilet ta shiga ta samo silver ta zo table water ta d'auka ta d'auki sabon brush da ta gani da alama su hafeez ne suka tanadar mishi ta sa mishi macline ta kawo mishi.
Brush yayi ta tattare kayan ta mayar toilet ta fito ta saka mishi abinci tare da jan irin abin cin abinci da ake ajiyewa a amenity d'in ta d'aura akai ta ja dayake me taya ne zuwa gaban gadon kara gyara zaman shi yayi yayi bismillah ya fara ci a hankali, yana cikin ci Doctor ya shigo da murmushi yace "masha Allah patient d'ina ya farka" Tace "eh doctor be jima da farkawa ba" yace "haka ake so yanzu zan rubuta wasu magunguna se a sayo mishi yana gama cin abinci ze sha in an sayo ki sameni office d'ina In miki prescribing yadda ze na sha Har Allah ya kawo sauki".
Amsa mishi tayi ya karasa ya duba Abban suka gaisa kan ya ja farin plain sheet ya rubuta magungunan ya bata kar'ba tayi ta mike ta fita Bayan ta cewa Abba bari taje ta zo, kai kawai ya iya gyad'a mata, seda ta fito har wajen asibitin kan ta samu POS tayi musu transfer duk kud'in account d'inta dubu goma suka bata cash, asibitin ta dawo pharmacy d'insu ta sayi maganin kan ta koma cikin asibitin ta nemi office d'in doctorn yayi mata prescribing kan ta koma d'akin.
Anty rahama da Anty kalthum ta samu har Abba ya gama cin abincin sun tattare Kwanukan Anty rahama tace "Ina kika shige ne Abba yace kin je Sayan magani tuntuni" tace "eh wallahi se da na fita POS and kuma pharmacy d'in akwai layi, ga nan magungunan Doctor yace ya sha yanzu" kar'ba sukayi Abba na yabawa karamci irin nata abinda 'ya'yan cikinshi zasu mishi ya tabbatar itama abinda zata iyayi kenan watakila ma har ta fi su, dubi yadda tayi wahalanshi daga zuwa dubiya, ita kuma a 'bangarenta gani take ko me zatayiwa Abba bata fad'i ba tunda har ya fi uban da ya haifeta ya tsaya mata akan komai har ta samu his handsome, gentle and super loving son, kofan da aka bud'e ne yasa duk suka maida hankalinsu kan kofan Ummu ce ta shigo cikin shiganta na yau da kullum wadda basu wuce na alfarma ba.
Cikin isa ta karaso tana kallon Iman ta had'e gabas da yamma "Ina kwana ummu?" bazata iya shiru ba hakan yasa ko gaida Abban batayi ba tace "tooo su gayyan sod'i wa ya gayyatoki? Ina ji da cikin ki wallahi ki jira randa zan haifeki kar ki d'auka duk abinda kike ban sani ba Ina sane d'ana kuma tunda ba ke kika haifarmin shi ba se kin rabu dashi alakakai wacce tunda ta shigo zuri'ata zuri'ata ya wargaje, malama kin fita ko se na ci mutuncin waenda suka kawoki duniya?" Mikewa Iman tayi da sauri kanta kasa ta fice su Anty zasu yi magana tace "duk wacce ta yarda ta min magana kan wannan watsatsiyar In ranta yayi dubu to se ya 'baci" tana fita hawayen idanunta suka fara gangara me tayiwa ummu ne da ta tsane ta haka? Wata zuciyar tace uwar da ta haifeki ma ta tsaneki to waye baze tsaneki ba? Tana tafiya tana share Hawaye har ta fita get ta tare napep da sauran chanjin hannunta ya kawota gida, shiga tayi bayan sun gaisa da me gadi bata ko kula su hamna ba da ganinta cikin kuka yasa suka kwashe da dariya harda tafawa ta fad'a d'aki zuwa gadonta ta fashe da kuka me sauti.
🖤Gureenjo🖤
🥀NOOR IMAN🥀
*Fatima Muhammad Gurin*
*Gureenjo6763 on Wattpad*
*'Yar Mutan Adamawa*
💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)
*041*
Murmushi yake sakewa akai akai yana sauraran sauban dake zuba mishi surutu akan Iman, tsaye yake ya d'an jingina bayanshi da gini tare da hard'e kafanshi "khaih Abokina ka rufta dayawa wallahi wai kaga yadda ka rud'e kuwa akan yarinyar nan? Allah ban ta'ba zaton zaka so wata mace haka ba duba da yanayinka akan mata" wani murmushin ya saki yace "Ni Allah ka rabu da ni In ba kana so ka neme ni ka rasa bane sbd In kana hiranta ji nake kaman inyi tsuntsu In sauka gareta".
Wani irin dariya Sauban ya saki yana cewa "sannu Romeo ko ince majnun kai yanzu ka zama fah mijin tace" harara ya sakar mishi yana kauda kai yace "Kai ta shafa d'an sa ido" dariya ya ci gaba dayi har seda Abdul ya buga desk d'in gabanshi yana cewa "Allah ko ka gayamin abinda ya sa ka juyo dani daga asibiti zuwa office d'inka ko In maka rashin M" tsagaita dariyar muguntan shin yayi yace "akan maganan mama ne matar fa tana wahala sossai gashi alamu sun nuna tana kumbura da kad'an da kad'an why not in da hali ka kaita wani kasan sbd su duba ta da kyau mu iya dubawanmu bamu gano komai ba dukda sauran results d'in se nan da sati biyu, amma ni a ganina wajen zasu fi mu kayan gwaje gwaje ingantattu" gyad'a kai yayi kan ya gyara tsayuwarshi yace "kana ganin wani kasa ya kamata a kai ta?" Sauban yace "I think Miami ko de Cairo" dafe kai yayi abubuwa na cha'be mishi gabad'aya.
Ga ciwon Abba ga shi an turashi wani aiki New York, ga shi yana so cikin santin nan su tafi Adamawa wurin baba fufore sbd matsalan hayateenshi da ummunshi, yana so yaga komai ya tafi smoothly amma be san...... katseshi sauban yayi da cewa "ya y lafiya kuwa mutumi na?" Ajiyar zuciya ya sauke kan ya fad'a mishi damuwanshi amma ya 'boye akan me Iman zataje ganin baba fufore, murmushi Sauban yayi yana cewa "Abu mai sauki ka bar mana Mama a nan zuwa sati biyu in de har zuwa wurin baba fuforen baze fi haka ba, and Ina ce office se next two weeks suka ce tafiyan? Fine se ka d'auke matarka ku tafi daga chan ku tafi yawon honeymoon" murmushi Abdul ya sake yana girgiza kai dama chan yana son zuwa london don duba Company d'inshi.
Ya rasa ya akayi be yi tunanin haka ba seda sauban ya fitar dashi ko Don abubuwan gabanshin na dayawa, "Allah gayen nan sa idonka yayi yawa se kace haka na sa maka ido da naka iyalan, mtseww by the way thank yhu" be jira amsan sauban ba ya fice abinshi yana ji sauban d'in na wasu maganganu cikin dariya girgiza kai kawai yayi ya karasa motan shi ya tayar ya nufi asibitin da Abba yake, cike ya samu d'akin da en gidansu gabad'aya kowa da kowa na nan wurin ummu ya nufa ya duka har kasa ya gaidata a d'age ta amsa.
Ya dawo kusa da Abba ya gaidashi cikin fara'a sossai ya amsa shi, Anty rahama ya gaisar daga nan itama ta amsa duk yanayinta ba daad'i sbd har lokacin abinda ummu tayiwa iman na ranta, Anty kalthum, Hafeez da zarah suka gaida shi, amsawa yayi yana d'an murmushi, sede tunaninshi na Ina Iman tayi be ganta a d'akin ba bayan yace ta jira shi a nan, be de yi magana ba se mikewa da yayi ya fita yana danna waya layinta ya ta kira bata d'aga ba.
Dawowa yayi ciki a lokacin umma da Hamna suka shigo cikin fara'a sossai ummu ta tarbesu yayinda sauran da kyar suka gaisheta duk harara ta zuba musu a fakaice ta gaida Abba ya amsa ba yabo ba fallasa, Abdul kam ma ko ta inda suke be kalla ba bare har ya wani gaisheta, Don rashin ta ido a tsayenta yadda take ta gaida Abban gaisuwan ma ba ladabi bare taushi a harshenta.
Dr. Ne ya shigo da murmushi ya bawa mazan hannu suka gaisa, yace "amm please kuyi hakuri ku je waje bari In duba shi" duk fita sukayi yayinda Abdul ya mike don fita kenan Abba ya kira sunanshi, dakatawa yayi, Dr yacewa Abba "hope ka sha magungunan da 'yar ka ta kawo?" Murmushi Abba yayi yace "na sha tuntuni, yanzu ni Ina ganin za'a iya sallama na Don bana jin komai jirin ya daina" Doctor yace "ciwon kan fah?" Abba yace "shima kad'an kawai nakeji" dr yace "masha Allah bari In duba jinin In har ya sauka sossai za'a iya baka sallama" aikinshi ya fara, Abba na kallon Abdul yace "mahaifiyarka ta koreta ta tafi" Da sauri ya d'ago zuciyarshi na bashi yanzu kuka take kenan.
Abba ya d'aura da "Hafeez ya min bayanin komai game da yadda kuka yi da baba fufore Ina tunanin lokaci yayi da zata wuce yolan nan haka" Abdul yace "Amma Abba jikin ka fa? Se nake ganin kaman In ba um...." katseshi Abba yayi yace "In ta zauna tana kara dulmiyar da kanta da jawa kanta raini da tozartani lafiya zata bani? Se de akasin hakan ni nayi sauki ka kira baba fuforen kuyi magana" Kai ya gyad'a kan yace "to Abba" daidai lokacin dr ya gama dubashi yana murmushi yace "ka ci gaba da kwantar da hankalinka Alhaji jinin ya sauka sossai In aka ci sa'a zuwa dare ya koma normal za'a baka sallama" godiya Abba ya mishi ya juya ya fice su Anty rahama suka shishigo yayinda umma da ummu suka tsaya daga waje suna magana.
Fita yayi ya nufi hanyar waje yana kallon mahaifiyarshi kewanta na shiganshi wani iri yake ji har kahon zuciyarshi In yaga irin kallon da take mishi ba so a cikinshi bare kulawa da damuwa, kau da kanshi yayi be mata magana ba tunda ya san abinda bata so kenan ya tanka ta, direct gidansu Iman yayi yana ci gaba da gwada number d'inta amma bata d'aga ba, daga kofa yayi parking tare da bud'ewa ya fito, da gudu yaga ikhlas zata shiga gida da sauri ya tareta yana cewa "hey kiddo" kallonshi tayi se ta wangala mishi baki tace "laaaa bature" dariya yayi yace "ke ni ba bature bane ni mijin Anty Iman ne" Ihu ta saki da karfi tana tsalle kan ta shagwa'be "dan Allah zaka kaini wurinta? Ai a chan kam Umma baza ta hanamu zuwa wurinta ba ko?" Kai ya gyad'a yace "zan zo In da'aukeku musamman In kai ku kuyi mata sati biyu" tsalle tayi cikin jin daad'i, se yaji wani iri da bai sayo musu komai ba.
Yana kallonta yace "ban riko muku komai ba muje se In sayo miki alawa kina so?" Baya tayi tana kad'a kai tace "Mama ta hanamu shiga motan kowa se na gida" mamakin wayon yarinyar yake sossai, yace "ni d'an gida ne mana tunda nima mijin Anty Iman ne" kallonshi takeyi yace "In bazaki ba shikenan shiga kice Ina sallama da baba" juyawa tayi ta fara tafiya se kuma ta kwasa da gudu daga inda take take ihun "Umma, baba ga mijin Adda Iman, ikhram zo kiga baturen mijin Adda Iman" murmushi yayi yana dafe kai ko a wani gari aka ce mata shi bature ne? Kallon fatan jikinshi yayi ya saki murmushi hmm.
Yana