Follow us on social media
Showing 39001 words to 42000 words out of 131683 words
Chapter 14 - NOOR IMAN Yar Baƙin Ciki BY Fatima Muhammad Gurin
sadda mijinki ya kawo min karan ki se na mugun 'bata miki rai shi ba sa'anki bane ba kuma ba wadda zaki yiwa rashin kunya bane ba, kar kiji nace kar ya kara dukanki kice zaki bud'e mishi babin rashin kunya kar ki kuskura a fara jin kanki dani".
Be kara kallon ummu ba ya wuce part d'inshi, Malabo ma juyawa yayi ya fice daga gidan cikin damuwa, wai me ke shirin faruwa tsakanin iyayenshi? Baze ta'ba zama silar samun matsalan gidansu ba In har be zama me gyarawa ba, ya fara kokonton auren Saudah sede In ya tuna halin da take ciki da wadda zata shiga gaba se yaji baze iya ba, dafashi da yaji anyi ne yasa shi juyawa se yaga hafeez.
Fuskanshi na bayyana damuwar da yake ciki shima cikin tashin hankali yace "Hamma me ke faruwa?" Ajiyar zuciya Abdul ya sauke kan yace "kira zarah kace ta samemu part d'inka" juyawa yayi ya wuce part d'inshin shi kuma ya kira zarah a waya seda ta fito ta iso inda yake kan suka nufi part d'inshi tare, a kishingid'e suka sameshi kan kujera zama duk sukayi.
Da kyar yace "zarah bashi labarinta" ba 'bata lokaci ta bashi labarin iman kab, seda yayi hawaye tsabar tausayawa, kallon Abdulraheem yayi yace "Hamma wallahi jihadi zaka yi In ka auri yarinyar nan, In kuwa kana ganin sbd hamna da ummu ne ka bari ni zan aureta ko don kwad'ayin ladar ubangiji, zan iya aurenta In ajiyeta a gidana ita kad'ai har Abada ba tare da na kuntata mata ba, zan zama mata uwa da uba da ta rasa a baya In har ba son...." "enough" Abdulraheem ya furta cikin sanyinshi kan ya mike ba tare da ya kara cewa Uffan ba ya fice.
Motanshi ya shige ya fice daga gidan a guje ya jima yana yawo a gari kan ya koma gida wanka yayi ya shirya cikin kayan baccinshi ya fad'a gado amma bacci yaki zuwa juyi ya dingayi tunanuka fal dayawa cikin ranshi ya tabbatar zuwa yanzu ummu bazata ce baze auri iman ba sbd rantsuwar da Abba yayi, ya tabbatar tafi kowa sanin Abba akan kalmominshi sede ya san shi bata barshi haka ba, kuma bazata ta'ba barinshi haka ba.
Da kyar ya samu bacci ya d'aukeshi ba tare da yaji dawowan Hamna ba ya tabbatar ummu ce ta hana ta dawowa, da safe bayan yayi sallah yayi wanka ya shirya ya fito direct gidansu ya nufa a parlor ya samu ummu da daga ganinta ka san bata samu bacci sossai ba tsabar damuwan da ta d'aurawa kanta, har kasa ya duka yace "Ina kwana ummu?" In dutse ya tanka to fah ummu ta tanka kallonshi kawai ta dingayi ba tare da ta iya cewa komai ba. A sanyaye ya mike ya shiga part d'in Abba suka gaisa Abba seda ya sashi zama suka karya tare kan ya mike ya fito zuwa school, da ya ganta kuma se yaji ko duniya zata had'e baze ta'ba fasa aurenta ba In shaa Allahu.
Knocking da akayi kofan office d'inshi ne ya sashi dawowa cikin tunanin shi da muryarshi dake a sanyaye yace "yes come in" tura kofar tayi ta shigo tare da sallama kanta kasa nannauyar Ajiyar zuciya ya sauke tare da kafeta da shanyayyun idanunshi, a take jikinta ya d'auki rawa cikin rawar murya tace "Ina kwana malam?" Wani kasalalliyar murmushi ya saki da shi kad'ai ya san ma'anarshi yace "Eyyah sede ba malam a office d'innan" sam ta kasa d'ago kai tace "am uhmm Ina nufin Dr. Ina kwana?" Yace "Lafiya me ke tafe dake?" Tace "malam amm Dr. na zo ne akan test d'in da kayi bani da lafiya ne yasa banyi attending ba i even wrote a letter a gave it to class rep ban san ko ya baka ba".
Tunda ta fara magana idonshi ke lumshe wani irin murya Allah ya ba baiwar nan? Ya subhanallah, ganin yayi Shiru yasa ta zata ko baze saurareta bane hakan yasata fara hawaye shikenan course d'inshi ya dawo mata ya gama, duk laifin zarah ne da ta yarda sun shigo tare da watakila ya yarda ko don sbd ita amma gashinan bata ma san sheshekarta ya fito ba, da sauri ya bud'e ido tare da kafeta dasu in disbelief ooh Allah na shiga uku daga magana se kuka? Ya Ayyana a ranshi a fili kuma yace "hey" ta d'ago ta kalleshi.
Da sauri ya kawar da kai zuciyarshi na bugawa what the hell did just happened, wani irin abu yaji da be ta'ba ji ba daga kallon crying eyes d'inta, be kara kallonta ba yace "ki je I will decide when to give a makeup test, but mark you bance zanyin ba I will decide what will please me" tana share fuska tace "thank yhu sir" ko ba komai tana saka ran ze yi d'in.
Fita tayi a office d'in ta nufi inda ta bar zarah anan d'in ta tadda ta tana danna waya duka ta d'aka mata a baya wadda ya sata mikewa tana sosa bayan "me nayi miki" hararanta tayi tace "Da be yarda ze yi maka up test ba da nayi ta dukanki har gobe da safe, Haka kawai kika ki rakani seda nayi ta mishi kuka kan ya amince ze yi" dariya zarah ta fashe dashi har tana dukawa cikin dariya tace "kuka? Akan test? Hahaha" zuciya iman tayi ta juya ta fara tafiya da sauri zarah ta bita tana "besty! Besty!! Besty!!!".
*sorry for yesterday but here is a long chappy you should plz manage with it, lectures ne ya sha min kai dayawa*
🖤Gureenjo🖤
🥀NOOR IMAN🥀
*Fatima Muhammad Gurin*
•Gureenjo6763 on Wattpad•
*'Yar Mutan Adamawa*
💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)
*022*
Tsaye Abba yake yana magana da mijin Anty rahma tambayar izininshi yayi ko ze iya aikan rahama wani kasa yau? Cikin ladabi mijin ya tabbatar mishi da ko Ina yake so taje ze turota, godiya Abba ya mishi yana kashe waya yayi kira Airport nan da nan yasa aka mata arranging tafiya dubai.
Mijinta na kashe waya ya dubeta yace "Rahma Abba yace ki shirya ze aikeki wata kasa" waro ido tayi tana cewa "wata kasa kuma? Tooh bari In tashi In shirya" yace "ki shirya su kabeer ma ki kaisu gidan Abban se ki bar su chan" amsawa tayi kan ta mike ta shige d'aki cike da mamaki Ina Abba kuma ze aiketa? Trolley karama ta d'auka ta shirya kayanta 'yan daidai a ciki, har ta d'auko wadda zata saka kayan su halima kuma se ta tuna akwai kayayyakinsu gidan Abban ma.
Gyalenta ta d'auka tare da janyo trolleyn parlor ta barshi nan ta shige d'akin yaranta kabeer ta gani zaune gaban tv yana playing game halima kuma kwance kan gado yayinda nanny ke sawa fuad kaya wadda shine bata jima da yayewa ba, tafa hannu tayi tace "oya a tashi zamu je gidan granny" da ihu suka tashi suna tsalle dama a shirye suke se ficewa sukayi bayan sunyiwa babansu sallama.
Driver ne ya ja ta zuwa gidan tare da juyowa da motan, da sallama suka shiga parlorn daga yadda ummu ta amsa ma ta San ba Lafiya yaran ma suna mata oyoyo da kyar ta sake musu fuska, suma kuma dayake yara ne se basu damu ba suka haura sama abinsu, zama Anty rahma tayi tana kallon ummu tace "ummu lafiya kuwa?" Ummu tace "ba lafiya ba rahama burinku ya cika shikenan ubanku ya sa Abdulraheem kara aure" wani irin murmushi Anty rahma tayi kan tace "dan Allah ummu yanzu don Abdulraheem ze yi aure se ki d'aga hankalinki haka? Haba ummu se kace Abba ne ze yi aur..." katse ta ummu tayi "ya isa haka dama na san bayan ubanku zaku bi dukkanku ba wadda ze iya tausayawa hamna tana 'yar uwarku".
Mikewa rahma tayi ita wallahi tayi murna sossai finally d'an uwanta ze samu kulawa ya san yayi aure, part d'in Abba tayi tana mamakin me yasa take kiran ubanku ubanku haka ba abin fad'an ummu bane, watakila Abba ya goyama Abdul baya shiyasa take jin haushinsu duka, Da wannan tunanin ta karasa parlorn a kasa ta zauna tana gaida Abba amsawa yayi "jam koid'um ni, na tashe ki kina zaune ko? Amm nayi miki booking flight zaki je dubai ki had'owa Babana kayan aure and Ina so kiyishi a gobe gabad'aya ki dawo jibi plz" kanta kasa tace "Toh Abba yaushene zamu wuce d'in?" Yace "karfe hud'u na yamma".
Tace "Toh Abba" har ta mike yace "ga wannan check d'in In be yi ba se ki min magana" Tace "Toh Abba" tare da ficewa direct d'akin zarah ta nufa, a corridor ta gamu da hamna tsaye tana waya da alamu kuma da uwarta take magana ko kallonta batayi ba haka itama bata kalleta ba bare kuma ta nemi gaisuwa suka gogi juna suka wuce, girgiza kai tayi tana furta "Alhamdulillah Allah ya nuna mana gobe da rai da lafiya, Ayyirrirriiii" ta sake gud'a.
Wani irin malolon bakin ciki ne ya tasowa hamna se ta fashe da kuka tana cewa "umma ba kinji ba gobe ne fah auren ni dan Allah ki zo, gashi 'yan uwanshi se wulakantani suke" murmushi rahma tayi kan ta fad'a d'akin zarah zaune ta sameta bakin gado tana chatting da gudu ta taso ta rungumeta "oyoyo Anty rahma yanzu na kori three musketeers d'inki suka zo suka addabeni, na sauka miki oyoyo ummu ta koroni" murmushi rahma tayi tace "ke bar surutun nan ki shafamin yanzu In kira kalthum In shafa mata" zarah ta zauna yayinda Anty rahma ta zauna gefenta.
"Dan Allah Anty rahma karku tsani iman sbd labarinta na tabbatar ba laifinta bane tana da saukin kai sossai ga sanyin hali, sam bata da hayaniya bare wani hali na ki, amma kaddararta be zo mata da daad'i ba" Anty rahma tace "ke ni ba surutu na tambayeki ba" nan Zarah ta bawa Anty rahma labarin iman daga farko har karshe se ga Anty rahma da kuka wadda hakan yasa zarah ma hawaye sun jima zaune shiru tukun Anty rahma tace "Allah sarki baiwar Allah, Allah ya kara mata hakuri da juriyar kaddara irin nata" zarah tace "Ameen" Anty rahma tace "Ai ko zan had'a mata lefen da zai bawa su ummanta da Babanta da kuma wannan innan mamaki, se na za'ba na darje zan d'auka mata Abba sede yayi hakuri aljihunshi ba karamin kuka ze yi ba" dariya zarah tayi kan tace "wai ke zaki had'a lefe?" Tace "kwarai ma kuwa yanzu haka da shirina na zo karfe hud'u zan d'aga dubai" ihu zarah ta yi cikin murna tace "ni wallahi Buki ma na so a mata a turawa su Goggo saratun nan haushi, da wannan hamnan" dariya Anty rahma tayi kan tace "ke kin san abinda za'ayi?" Girgiza kai zarah tayi.
Rahma tace "mu kira nenne mu fad'amata Abdulraheem ze kara aure amma shi da Abba sunki a mata event sbd hamna, ta sa azo yola ayi" zarah tace "good idea, kan nan mu bata labarin iman d'in se inga kaman ba haka aka barta ba ko da adu'o'i zata taimaka mata na san nenne sarai" Anty rahma ce ta fiddo wayanta ta danna mata kira ringing biyu ta d'auka "Assalamu Alaikum Rahama hande 'be numti be am kenan"(yau an tuna da ni kenan) dariya Anty rahma tayi kan tace "wa'alaikissalam pul debbo dama chan kina ranmu ba'a mantawa dake, noi shomri noi saare"('yar tsohuwa, ya gajiya ya gida?)
Ta amsa da "Lafiya klau Alhamdulillah, toh dum'e habaru?"(me labari?) zarah ce ta sa baki ta gaida ta tana tsokananta amsawa tayi amma bata wani sake sunyi wasan ba sbd magana ma wahala yake mata, zarah ne ta bata labarin Iman gabad'aya da irin taimakon da Abdul yayi niyyan mata na aurenta da kuma abinda ummu tace da Abinda Abba yayi a kai, tas harda hana hamna komawa gidan Abdul da ummu tayi.
Duk shiru sukayi kowa da abinda yake sakawa, chan nenne tace "tooh Allah ya mana mai kyau, Zan yi magana da mai martaba da shi Ahmad d'in, ba ta yadda za'ayi ayi bukin nan haka, a d'aura auren ku tattaro duka ku taho zamu shiryamata buki na ji da fad'a, sannan zan yiwa baba na fufore magana banyi tunanin Haka kawai aka bar yarinyar nan ba, da izinin me duka kuma wannan shine Aurenta na dindindin karku damu kunji?" Zarah harda tsalle daad'i tayi tana fata iman ta shirya da ummanta koman daren dad'ewa kuma ta san yadda baba na fufore ya shahara da malamta da kuma iya bada ayoyin karya sihiri se inda karfinshi ya kare.
Godiya sossai suka dinga mata kaman sune iman d'in kan sukayi sallama, Anty rahma ta kira Anty kalthum ta fesa mata aiko itama taji daad'i sede bata ji daad'in yadda ummu ta d'auki maganan har take jin haushin family d'inta ba, ta kuwa ce yau zata nemi izini gobe a gidan zata yini a tare ma za'a wuce yola da ita don ba za'a barta a baya ba.
Da wuraren d'aya Abdul ya shigo gidan, yaran rahma da ita kanta da zarah ke zaune a parlorn yaran suna wasa yayin da iyayen ke ta aikin hirar yadda auren ze kasance Anty rahma na ganinshi ta saki gud'a hannu a kan hanci, murmushi yayi yana girgiza kai yaran sukayi kanshi da gudu d'aya bayan d'aya ya dinga d'agasu yana saukewa fu'ad da ya d'aga karshe ne ya rike shi da kyau yana zama gefen Anty rahma.
"Ango Ango ka sha kamshi na Iman bada kanka a sare kaje gida kace ya fad'i, hoo...." hararinta yayi tare da saurin cewa "dan Allah ki rufamin asiri kar ki kara min laifi wurin ummu" zarah tace "hamma wai iman Tace zakayi makeup test?" Hararanta itama yayi kan yace "wai yarinyar nan don kin raina ni shine kika kama kika kira wachan tsohuwar matar sarkin nan kika fad'amata zanyi aure ko?" Waro ido tayi tare da d'aga hannu sama tana girgiza kai, se kuma tayi saurin nuna Anty rahma tana cewa "ba ruwana wallahi Hamma itace" Anty rahma tace "laaaa zarah ni zakiyiwa sharri? Yaushe mukayi haka dake?".
Zarah zata Musa Anty rahma ta kai mata duka da gudu ta mike tana dariya, murmushi kawai yayi Anty rahma tace "yauwa Abdul ina kud'in lefe? Yanzu haka shirin tafiya airport nake zanje dubai had'o maka lefe da izinin Abba kuma ya bani kud'i amma gaskiya lefen kece raini nake so in had'o sbd 'yan bakin ciki su gani haushi ya kashesu".
Girgiza kai kawai yayi yana mikewa "Abdul da kai fah nake magana" ko kallonta be kara yi ba ya haura saman ummu a zaune ya ganta da hamna, hamnan ta d'aura kanta kan kafan ummun se aikin kuka take, shi fa mamakin kishin hamna yake ita da bata sauke mishi wani hakki na aure yadda ya kamata don ze kara aure ne ze d'aga mata hankali? Sannan ga ummu da daga ganinta zaka san tana cikin tsananin damuwa sbd kawai za'a yiwa hamna kishiya, Abun na bashi mamaki se kace Abba ne ze yi auren? Sallama ya kuma yi, kan ummun ta d'ago ta kalleshi.
"Me ya kawoka wurina ni da bani da amfani a gareka ban kuma isa In fad'a ka ji ba?" Zama yayi a kasan kafanta kanshi kasa yace "ummu dan Allah ki dena damun kanki akan maganan auren nan haka, kin san wannan halin da kike ciki ze iya tada miki hawan jininki? Ummu ke ma fa kin san karin auren nan be haramta a gareni ba tunda ba wani abun sa'bawa Allah bane ba, na san kin san yadda rabo yake In ya rantse beside me hamna take mini a duniya da zan kalla inji daad'i In san nayi aure? Babu kullum ni kenan banda kwanciyan hankali da natsuwa kaman na kowani mijin aure, ban isa ince tayi tayi ba, haka ba isa cewa kar tayi ta kiyi ba, bata ta'ba shiga kitchen don yi min girki ba kullum In ba Ina gidan nan ba Ina restaurant, zan iya sati biyu ban sa hamna a idona ba tayi tafiyarta wani kasa ba tare da izini na ba, don zanyiwa irin wannan matar Kishiya shine abin damuwa? Na rantse da Allah yanzu hamna bata raina ince ma bata ta'ba shiga ba ko da iman bata shigo rayuwata ba Ina da niyyar karin aure se kuma Allah ya kawota a lokacin da ya dace, duk abinda hamna take so ummu kina sani dole ko bana so se na mata wannan karon plz and plz ki barni inyi abinda raina ke so for once a rayuwana, na barki lafiya".
Ya mike ya fice abinshi jikin ummu ba karamin sanyi yayi ba amma wani abu daya tokare mata kirji ya ki bari tayi la'akari da lamarin Abdul har ta juya magananshi, hamna da ranta ke 'bace ta d'aga waya ta danna kiran wata kawarta da ta sata tayi bincike akan iman kuma tayi ta kirata ta fad'a mata d'azun, bayan ta d'aga tace "ke zuby ga ummu nan Ina so ki mata irin bayanin da kika min, ta san fah irin 'bara gur'bin da za'a kawo mata cikin zuri'arta".
Nan fah zuby ta yi gyaran murya tare da fara bada labarin iman na karya da gaskiya wani abin ma ko huka aka d'aurawa iman baza ta iya aikatawa ba, Ai ko ummu ta d'auka d'an magangnun Abdul da suka fara tasiri tuni sun watse wani irin haushin Abba da duk yaranta take ji akan wannan irin bakar munafukar da suke shirin kawo mata cikin zuri'ah tsanan yarinyar take ji tun kan ta ganta.
A zuciye ta mike tayi part d'in Abba dawowanshi daga sallar azahar kenan suna zaune da Abdul suna tattauna kiran da nenne tayiwa Abban akan zuwa yola ayi buki kuma ya yarda d'ari bisa d'ari tsarawa sukayi ayi d'aurin auren kawai karfe takwas se su wuce yolan da wuri, se ganin mutum sukayi bata zauna ba tace "wai ka san irin yarinyar da ka yarjewa Abdulraheem aurenta? Bazawara ce fah aurenta biyar shine na shidda kuma.....".
Hannu ya d'aga mata "ba abinda ban sani kanta