Follow us on social media
Showing 45001 words to 48000 words out of 131683 words
Chapter 16 - NOOR IMAN Yar Baƙin Ciki BY Fatima Muhammad Gurin
zuwa yanzu ne gidan nan ya cika haka? Har fa da 'yan wudil duk sun zozzo, Ana ganinta aka fara shewar ga Amarya ga Amarya, ko murmushi ta kasayi haka ta bisu ta dinga gaishesu d'aya bayan d'aya wasu na amsawa tsakani da Allah wasu kuma suna yi suna ya'ba mata bakar magana.
Zarah de sama sama ta gaida su tana kallon 'yan matan dangin yadda suke hararan Iman kaman ta ci musu wani abu, itama hararsu tayi sunje wucewa kusa dasu taji wata Tace "watakila ma wani me ruwa d'an cin rani baba hafeezu ya had'ata da shi" d'ayar tace "ke me ruwa Ai kin kai da nisa kila de me kwasan kashi" suka kwashe da dariya d'ayar tace "ke salma baki da kyau ko kinyi wanka wallahi" d'ayar Tace "Ai gaskiya ta fad'a In ba hakan ba wa ze kwasa irin ta" har Zarah ta taka zuwa gabansu da niyyan gaya musu magana Iman tayi saurin rike hannunta ta ja ta gaba, haushi seda ya kawo zarah wuya a gidan nan sbd maganganun 'batanci da akeyi kan Iman.
Daga karshe ma sallama ta mata tace zata dawo gobe da sassafe ana idar da sallar asuba, da haka sukayi sallama Iman na mata godiya tayi saurin cewa "No thank yhu In friendship so bana so in sake ji, bye bye take care" har ta kai kofa ta juyo tace "besty" iman ta d'ago, tace "wallahi kina da hakuri inaga kan a gama bukin nan se na gurje bakin wata" ta juya ta fice murmushi iman tayi tana girgiza kai.
Seda ta kai hakarkarinta gado kan ta fara tunanin Abdulraheem, wallahi mamakin da tayi baze iya fad'uwa ba wani irin ikon Allah ne wannan? Anya bata kai kanta da nisa ba? Ina ita Ina Abdulraheem ga mata kyawawa masu class a duniya? Gaskiya tana bukatar karin bayani ta ya akayi abu ya kasance a haka? Kanta gabad'aya ya d'aure ba irin tunanin da batayi ba, ta tuna ko kallonta me kyau bayayi tana ga ko kammanninta be sani ba, watakila baba ne yaje ya dinga rokonshi ya aureta, kai baze yiwu ba, watakila kuma Zarah ce ta rokeshi don ta tausaya mata.
Da sauri ta mike zaune har ta d'auko wayanta don kiran zarah taji don In har hakane baza ta iya aurenshi ba da alfarmar kanwarshi kaman ta shiga hakkinshi ne ta d'aurawa zarah damuwar da ba nata ba, In ta tuna daidai kuma a labarin da Zarah ta bata Ummu na matukar son hamna bata son abinda ze 'bata mata rai kenan ummu is against auren su, kenan Abdulraheem ze aureta ba da yardar mahaifiyarshi ba? Baza ta samu soyayyar uwar miji ba, bazata samu soyayyar miji ba abin ya mata yawa ita kenan haka rayuwanta ze kare? Duk auren da zatayi ba jin daad'i, kuka ta fashe dashi tana kifa wayanta kan katifar da take, cikin sanyi take kukan yadda ba wadda ze iya jinta, sossai tayi kuka kaman ranta ze fita kan ta mike ta fad'a toilet tayo alwala tazo ta fara nafilfili tana rokon Allah alkhairin auren, In ba alkhairi bane Allah ya wargaza maganan tun kan a d'aura.
*******
RANA BATA KARYA
Tun bayan sallahn Asuba ba wadda ya koma bacci gidan se wanka ake yi wasu kam ma tun kan asuban yayi sun yi wanka, dayake abin aure kan kace kobo an had'u an had'a breakfast na kunun gyad'a da kosai wadda duk cikin aljihun Abba, tun kan su gama motocin sun zo, baba da kanshi yake za'ban waenda zasu tafi yake kuma shirya arrangement d'in zaman, Inna de ta riga kowa shiga se su goggo saratu da sauran 'yan uwa, lokaci kad'an suka cike people choice biyun nan pim ba 'bata lokaci suka tashi.
Se a lokacin zarah ta iso sanye da normal riga ready made da gyalenshi kanta, hannunta rike da karamin jaka wadda komai na amarya da Zata saka yau yana ciki don seda ta biya gidan maymz ta kar'bo, Mutane kad'an ta samu a gidan daga umma se wasu 'yan uwan da basu tafi ba, da suma yau zasu watse, d'akin Mama ta shige nan ta samu Iman zaune bakin gado tana kallon wuri d'aya alamun tunani takeyi.
Har yanzu jikinta be dawo ba wallahi sam kana ganinta ka san damuwa dayawa na tattare da ita, dafa kafad'anta zarah tayi tace "wai tunanin me kike ne besty bayan kin san mijin da zaki aura se me kuma?" Iman tace "me yasa bazanyi tunani ba zarah duk aurarrakina daga wahala se wadda ya sakeni a daren farko na se kuma wadda ya mutu a wurin d'aurin aure, zarah bakya tsoron wani abu ya sameshi daga taimako?" Hawaye ne ya fara zuba a idonta, Cikin kuka tace "zarah dr Abdulraheem yana da kirki rasa shi na tabbatar ba karamin razanarwa ne ba ga family d'inku, bana so wallahi na fasa auren In har shi zan aura, I can't bazan iya ba, za.....rah bana son komai ya sa...me..shi ta sanadina" ta karashe cikin kuka.
Zarah tace "wa ya gayamiki shi Abdulraheem kaman sauran mazajen da kika aura ne? In shaa Allahu yayi musu fintinkau ba abinda ze sameshi se Alkhairi" girgiza kai tayi cikin rashin yarda da maganan zarah ba wai tana ja da ikon Allah ba a'a sam ko d'aya kawai tana tsoron abinda ze je ya zo ne, waya zarah ta d'auka ta danna mishi kira yana cikin shiryawa yaga call d'in zarah.
'Dagawa yayi tare da sallama, amsawa tayi kan ta d'aura da "Hamma ga Iman tun d'azu take ta kuka wai a ce maka ta fasa bazata iya auranka ba sbd tana tsoron kar ka mutu kaman yadda hamza yazo da niyyan taimakonta ya mutu" d'an Shiru yayi kan ya zauna yana furta "bata wayan" mika mata tayi se ta ki kar'ba, zama tayi a gefenta tare da sa mata wayan a kunnenta, sheshekar kukanta ne ya sashi gane tana kan layin.
Lumshe ido yayi ya kuma bud'e a lokaci d'aya cikin husky voice d'inshi yace "Saudah!!" Kuka ta fashe dashi sossai kukan da ya bayyana damuwa da tashin hankalin da take ciki, ga fargaba da ya kara mata daga jin muryanshi "God" ya furta a kasan makokoronshi, se kuma ya bud'e murya yace "Ki dena kukan nan haka ki tashi ki shirya, kuma ki kwantar da hankali nothing will happen to me there are many differences tsananina da sauran waenda suka aureki so plz relax, Ohk?" Kai ta gyad'a tana share hawayenta, cikin sanyi murya tace "promise me yhu will not die, please..." yace "you have my words, I repeat nothing will happen to me, and yhu should also promise me you will never shed tears again" tace "bazan yi ba" se ya d'an yi Shiru kan kuma ya tsinke wayan.
Mukawa zarah wayan tayi kan ta mike ta fad'a wanka cikin kankanin lokaci tayi ta fito zarah ta shiryata tsab Allah ya sa ta iya make up sossai da d'auri ta chanchara mata make up bayan ta d'auko kit d'inta daga mota, ta kafa mata d'auri me d'aukan hankali se ga Iman ta chanza kammanni.
*****
A harabar gidansu ya Parker motar tare da bud'ewa ya fito Hafeez da Abba ya gani tsaye alamun suma shirin tafiya auren suke, Abba na ganinshi yace "dama na sani ai, Hafeez ka ga?" Hafeez yayi murmushi dama seda Abba yace yauma bakaken kayan ze saka kaman shed'an Ai ko su d'inne jikinshi getzner baka me kyalli, bakar hula da bakar cover shoe gaban babban rigan ya sha zubi da zare baki me d'aukar hankali.
Hannunshi Abba ya kama zuwa parlornshi wani farin kashmiya me layi layi tsirara baki da ya sha guga akan kujeranshi riga 'yar ciki da babbar riga ya d'auka ya mika mishi, kallon kayan Yayi kaman ze Musa se kuma ya sa hannu ya kar'ba zubin da baki da farin zare akayi har ya fi na asalin kayan da ya saka kyau, da mamaki Abba ke kallonshi yadda ya kar'ba ba musu a aurenshi da hamna ba yadda ba'a yi da shi ba yasa wasu color d'in kayan yaki fir haka aka kyaleshi, se gashi yau ya kar'ba.
'Dakin Abba ya shiga ya chanza se ya bar bakar agogon fatan dake hannunshi wadda na company d'inshi ne, haka takalmi cover d'inshi ya bari shima na company d'inshi ne da akayi da zallar bakar fata, se hulan zanna da ke kanshi shima fari ne yaji guga ya zauna d'as ya fito a asalin angonshi yayi kyau har ya gaji farinshi se sheki yake, turarukan Abba ya feffeshe kan ya fito hannunshi Abba ya kama sukayi waje.
Mota d'aya suka shiga su uku motar Abdul d'in bakar benz d'inshi latest one d'in, ba 'bata lokaci suka isa Al-Furqan mosque dayake anan za'a d'aura auren sun kuwa samu an cika pim mutane ko ta Ina dayake Abba ba karamin gayyata yayi ba tun daga randa yaje wurin baba, baba yace ya bashi ya buga kati a washegarin ya aikawa duk wani wadda suke huld'a a kanon nan manyan mutane har sarki se gashi ya zo, har governor ya gayyata but be samu zuwa ba se ya tura deputy d'inshi.
Baba da su Bappanun iman are very very speechless sun rasa ya abun yake gashi baba ya ce musu yayi bincike yaron de bashi da karfi sossai amma se gasu ga sarki ga kuma mataimakin gomna baba har hawaye yayi, be ta'ba mafarkin ze yi Musabaha da sarki ba se gashi ta dalilin Iman yayi, ba 'bata lokaci aka d'aura auren Dr. Abdulraheem Ahmad Malabo da Amaryarshi Saudatu hafeez Muhammad akan sadaki naira dubu d'ari biyar.
Kusan suma baba yayi, duk cikin zuri'arsu babu wacce ta kar'bi sadaki kwatan wannan se Iman, kallo kawai yake bin mutane dashi kaman mutum mutumi, be zaci haka ba sam, hafeez ne ya fiddo wayanshi ya turawa zarah sakon an d'aura.
*****
Wani irin gud'a ta sake wadda yayi sanadiyar zuban hawayen iman shikenan rayuwanta kuma se abinda Allah yayi, Mikar da ita zarah tayi suka fito daga d'akin Mama tana kallon wata 'yar uwar babansu da tazo daga wudil, ta bud'e baki galala tana kallon Iman dukda kwalliyanta ya ragu sbd rashin lalle amma tayi kyau har ta gaji komai na jikinta fari ne In ka cire head, pose, jewelries da shoe da suka kasance silver.
Yaddiko cikin rawar murya tace "Aishatu! Aishatu!! Kuzo kigani" fitowa sukayi gabad'aya se sukayi turus suna kallon Iman, d'ayar tace "oh duniya yanzu Iman Don kinyi kawa me kud'i se ki roketa ta yi miki d'inkin da zaki sa a aurenki? Wani irin ta'bewa ne wannan?" Zarah tayi charab tace "Ina wadda kuka mata? Kunyi ne kunga bata sa ba? Toh ma bari kuji ba ni na mata ba mijinta da yake 'wa' na uwarmu d'aya ubanmu d'aya shi ya sayamata da kud'in guminshi" duk waro ido sukayi suna kallon kud'in da aka kashe a jikinta.
Hotuna Zarah ta fara mata se ga baba ya shigo babbar riga a hannu yana zare idanu ya kalli Iman yace "ke wa kika kawomin ya aureki?" Da mamaki tace "baba ba kai ka za'bamin shi ba nima ban sanshi ba" innalillahi wainna ilaihi rajiun ya furta "karde d'an yankan kaine ya yanke min kan 'yan uwa gabad'aya, harda innata" umma tace "me ya faru ne?" Yace "dubu d'ari biyar fah ya biya sadaki" duk salati suka sake.
Zasuyi magana suka ji sallama Anty kalthum ce ta shigo ta kalli zarah ta kalli mutanen da sukayi cirko cirko se ta d'an duk'a tace "am Abba yace kuyi hakuri en uwanmu duk suna nesa ba wadda ya samu zuwa d'aurin aure sbd abun yazo a kurarren lokaci, ni sunana kalthum kanwar ango nazo d'aukan amarya ne sbd jirgin goma zamu bi zuwa yola" "jirgi fah, jirgi kika ce d'iyarnan?" Wata cikin tsoffin ta fad'a zarah tace "kwarai kuwa" tare da janyo hannun Iman zuwa gaban umma da baba ta saka musu hannayenta ciki nasu kan tace.
*in kun jini gobe toh, In baki jini ba kuyi hakuri ga long page*
🖤Gureenjo🖤
🥀NOOR IMAN🥀
*Fatima Muhammad Gurin*
•Gureenjo6763 on Wattpad•
*`Yar Mutan Adamawa*
💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)
*025*
“Umma, baba kun san ko Iman na da laifi a mutuwar aurarrakinta kun fita laifi da zunubi? Umma aure fah aka ce ba wai zaman kwana biyu ba, baba ko min ‘batawar Noor gareku be kamata ku ki ta haka ba, umma, baba idan har kuna son wannan auren na Noor ya zama na karshe kuma ya zamana gidanta na har Abada ku taimaka ku dubi girman Allah kusa mata albarka ko da sau d’aya ne, rashin sa albarkanku kaman shine yake zama jagoran ‘bata mata sauran aurarrakinta.
Umma ko da Iman ba ‘yar ki bace ‘yar kishiyarki ce zaki iya bud’e baki kice Allah ya sanya alheri bare kuma noor dake ‘yar cikinki” kasa ta duka Noor ma tayi yadda tayi hawaye na aikin kwaranya daga cikin idanunta, baba da jikinshi yayi sanyi ya kurawa Zarah ido yana kallo, umma kam baza ka gane yanayin da take ciki ba, cikin damuwa zarah tace “Don darajar manzon Allah umma da baba ko da wannan shi ze zama magananku na karshe da Noor ku sanya mata albarka kuyi mata fatan Alkhairi a zaman gidan Aurenta” baba ne ya fara bud’e baki yace “Allah ya sanya alkhairi ya bada zaman lafiya” se ya juya ya fice, umma zarah ta kurawa pleasing eyes d’inta tana kallo, kaman bazatayi magana ba har ta juya zata shige d’aki se sukaji tace “Allah yayi albarka” tayi shigewarta ba tare da ta juyo ba, rungume zarah iman tayi tana kuka sossai.
Da wani irin baki zatayiwa Zarah godiya? Yau zarah tayi sanadiyar samun albarkar ummanta a gabad’aya rayuwanta abinda ta jima sossai tana murd’in samu, ‘yan sauran en uwan da suka saura ne d’aya daga ciki ta duka ta d’agota sukayi waje sauran suka rufa mata baya, zarah ma ta mike Anty kalthum ta rike mata hannu tare da bubbuga kafad’anta da d’ayan hannun cikin kasa da murya tace “proud of you lil” murmushi kawai zarah tayi suka fito.
A motar Abba da Anty kalthum ta taho a ciki aka sakata a baya dayake driver ne ya kawo ta yana zaune a mazauninshi, zagayawa Anty kalthum tayi ta shiga, zarah taje ta shiga nata motar suka ja suka fice, direct GRA sukayi a harabar gidan driver yayi parking Anty kalthum ta taimaka mata ta fito kanta kasa suka shige ciki, a parlorn ummu suka dakata.
Zarah ta kalli kalthum, kalthum ta kalleta basu san ya zasuyi ba, sam be dace ta shigo gidan bata je ta gaida ummu ba sede kawai su had’u a jirgi gashi suna tsoron su kaita ummu tayi mata wulakanci, kalthum ce ta yanke shurun da “Iman muje ki gaida Ummu ko” Kai ta gyad’a kan ta d’aga kafa ta fara tafiya gabanta na tsananta fad’uwa, da sallama suka haura parlorn saman, zaune suka hangi ummu ta ci ado na fitar hankali ba wai kwalliya a fuska ba a’a wata arniyar milk da pink less ta saka ta kafa d’auri da d’ankwalin daga abinda yayi wuyanta, kunnenta da hannunta duk gwala gwalai ne In ka ganta zaka d’auka wata matar shugaban kasa ce, farin babban gyalenta na ajiye gefenta da farin handbag se farin flat shoe d’inta.
Trolley d’inta na zaune gefe, idanunta sanye da medicated glass hannunta waya ne tana dannawa, a kasa Iman ta zube ba tare da ta d’ago kai ba tace “Ina kwana ummu?” Shiru ummu tayi kaman bata ji ba, ta sake nanatawa nan ma Shiru, Zarah tace “ummu ana gaisheki” wani banzan harara ta sakarwa zarah kan ta ja tsuki ta mike ta shige d’akinta.
Ajiyar zuciya kalthum ta sauke kan tace “zauna da kyau Iman kiyi hakuri kuma da abinda ummu ta miki sam ba haka halinta yake ba” zarah ma ajiyar zuciya ta sauke kan ta mike “Anty kalthum zanje nayi wanka na fiddo akwatina kan su Abba su shigo, Besty Bari inje In zo ko muje tare kiga room d’ina?” Kai Iman ta girgiza murmushi Zarah tayi kan ta fara tafiya tana cewa “zaki shiga ne ma wata rana”.
Shiru Anty kalthum tayi tana tunanin sabon halin da ummu ta fara wadda basu ta’ba gani tanayi ba ko su Mama da yaranta batayiwa wannan hali su da suka nuna basa sonsu karara, Iman ma tunanin Abinda ummun ta mata take Allah sarki mata me mutumci zata ‘bata mata rayuwa da tsanarta Ai da ba haka take ba, sau nawa suna gaisawa ta wayar zarah amma yanzu gashi ta shiga tsakanin d’a da uwa.
Wani irin fisgan gyalen saman kanta da akayi wadda ba shiri ya sata yin baya tana d’ago kai, wata farar kyakyawar buduruwa da zatayi tsara da Anty kalthum ta gani sanye cikin wata arniyar bakar lace riga da skirt sun kama ta tsam kaman zasu yage fuskan nan ya sha wata irin makeup da zan iya cewa In ba don iman amaryace kuma bata saba makeup ba akayi mata yanzu, da se ince Tafi ta had’uwa.
A take Iman tayi guessing wacece cikin kasan makoshi tace ‘Hamna’ don sossai kamansu ya fito da Abdul kuma farinta irin nashi, se iman ta ganta mummuna a gabanta gata baka, yana da irin wannan matar me ze yi da ita? Zuciyarta ya tsinke ita kam Ai maid zata zama a gidan waennan, lumshe ido tayi tana ji Anty kalthum tace “me haka hamna?” Hararanta hamna tayi tace “madam ba ke nayiwa ba so ba ruwanki”.
Kallon fuskan Iman tayi kan ta kwashe da dariya tana kallon Anty kalthum tace “yanzu dama akan wannan Useless human being ko ince Animal kuke Min wulakanci” hahahaha ta kuma kwashewa da dariya ta juya ta kuma juyawa tace “ke bakar munafuka, magajiyar karuwai Ina so ki kalleni sama da kasa ki kalleni da kyau nayi tsarar zaman kishiyoyi da ke?” Shiru Iman tayi, hamna tace “ke ‘yar kauye bana magana amin banza se in kifa miki mari wallahi kuma In kwana lafiya, wallahi na fi