Follow us on social media

Showing 111001 words to 114000 words out of 131683 words

Chapter 38 - NOOR IMAN Yar Baƙin Ciki BY Fatima Muhammad Gurin

jela ta saka, ta saka black hula a kanta se after magrib taji shigowar mutumin da uwargidan nashi a lokacin ko ba abinda taji.

Mikewa ma tayi ta fito tayi mishi Sannu da dawowa ba ruwanshi gaban hamnan yace "hayatee sannu kema da gida mun barki ke kad'ai" murmushi tayi tace "ya jikin umman? Hope taji sauki?" Yace "yes da sauki sossai watakila ma a sallameta gobe in Allah ya kaimu" tace "to Alhamdulillah, Sannu Anty" ko kallonta hamna batayi ba se d'akinta da ta fad'a.

Kai iman ta girgiza tana murmushi bata da lokacin wannan shiriritar, kallonshi tayi shima ita yake jifa da wani irin kallo yana sake murmushi a kunyace ta dukar da kanta dukda bata saba sa kananan kaya ba amma fah ita yanzu ta shirya zaman aure daram so ba abunda bazatayi ba don kwato martabarta da dawo da hankalin mijinta kanta ba, tace "hafsy ta kira Allah ya saka da mafificin alkhairi ya kara bud'i" ya amsa da "Ameen ya rabbi don adu'ace kawai yasa na amsa" murmushi ta mishi.

Ta juya d'akinta shima room d'inshi ya fad'a se bayan isha suka had'u a dining sukayi dinner tare godiya ya mata har taji kunya ya kamata, gashi ya dinga santin abincin ko a jikinshi, hamna kuwa haushi har makokoro gashi bata iya girki ba bare tace itama zatayi don ta burgeshi be ta'ba mata santi kan abinci ba se yau, dama ina zai yi tunda abincin gardi ya saba ci.

Washegari da kanshi ya sa ta shirya ya d'auketa suka tafi aka mata passport ya fara musu chukuchukun tafiya, driver ya kira ya maidata gida shi kuma ya tafi harkokinshi ta so ta biya asibiti ta kalli Mama sede ya tabbatar mata ko taje baza'a barta ta ganta ba so haka ta hakura suka koma gida tana shiga ta samu zahra nan ta sa ihun jin daad'in ganinta a take suka kule d'akinta aka hau hira, chan yamma se ga kiran muhammad abin mamaki taga zahra ta d'auka harda kashe murya tare da cewa "boo ya kk?" Duka ta d'aka mata tana dariya tace "lallai zahra yaushe kika zama munafuka ban sani ba?" Yayinda zahra ta wani shagwa'bewa tana kai karanta wurin muhammad d'in.

Sossai yinin ya musu daad'i da yamma suka shiga kitchen sukayi girki tare dukda zahra ta so hanawa tunda ba girkinta bane, seda Iman ta nuna mata be dace ba ai ko yaya ne mahaifiyarta ce kwance asibiti ba lafiya so Don tayi girki ba matsala, jollof rice sukayi da salat se zobo suka shirya komai dining kan suka koma d'aki nan zahra ta fara haramar tafiya Don magrib da ya kawo kai iman bata so ba Don ji take kaman kar su rabu gashi ita kad'aice gidan kaman rai.

Ba yadda ta iya haka ta rakata har mota ta tafi, itakuma ta dawo sama ta gyara d'akinta ta share ta kunna turaren wuta kan ta shiga tayi wanka yauma same thing kananan kaya ta saka bayan ta cire atamphar da suka fita dashi kaman jiya yauma kan magrib suka shigo gidan tare da matarshi akwai abu d'aya da ta lura dashi daga gareshi ko yaya idan ba wani abu bane yake dashi me muhimmanci baya wuce magrib be shigo gidanshi ba.

Haka ta fito ta tarbesu da fara'anta shima a sake ya amsata yana cewa ya gaji sannu ta mishi ya shige d'akinshi hamna ma tayi nata bayan ta gama watsa mata harara, murmushi tayi kawai ta koma d'akinta bayan isha suka fito suka ci abinci, nan yake fad'amata ai gobe za'a iya zuwa duba Mama so ta shirya ze d'auketa ya biya ya d'auki umma se suje baba yace daga wurin aiki ze wuce, murnanta ya kasa 'boyuwa sossai ta nuna jin daad'inta.

Washegari kuwa ta shirya cikin wata arniyar orange lace ta tufke kanta yayi kaman acuci ta kafa d'aurinta da ya rufe mata gabad'aya kan ta saka brown gyale, takalmi da jaka ta fito d'as da ita gashi fatanta yayi wani fresh da kyau sbd mayukan da take anfani dasu yanzu na oriflame har wani kumatu tayi na kwanciyar hankali kunneta da wuyanta siraran d'an kunne da sarka ne na zinari haka zoben hannunta, shi karan kanshi seda ya 'bata wasu lokauta yana kallonta har seda hamna taja wani muguwar tsaki kan ya kau da kai daga kallonta ya mayar kan hamnan ta riga ta bud'e gaba ta shiga tare da buga kofa.

Shiga mazaunin driver yayi yace "wai da wa kike wannan tsakin?" Tace "da kaina Hamma mantuwa nayi kuma na san bazaka yarda na koma na d'auko ba" sarai ya san karya take sede a barshi a haka, daidai lokacin Iman ta bud'e baya ta shiga ta madubi ya kalleta yana sauke ajiyar zuciya yacewa hamna "kije kiyi sauri" ta kuwa fita kaman gaske ta koma cikin gidan, se lokacin Iman ta kalleshi se suka had'a ido murmushi tayi yace "kina da kyau hayatee" Tace "waii hamma wannan kam zagi ne ko? Baka kallon kanka a madubi ne?" Dariya yayi yana d'aga mata gira yace "me kike tunani ne? Kina zaton na fiki kyau?".

Tace "sossai ma Ina da gami" murmushinshi me narkar mata da zuciya ya saki yace "ni kam ban gani ba a duniya banga me kyaunki ba hayatee, kin kuwa san kin fi d'awisu?" Dariya ta saki tana kama baki yace "dariya na miki kyau kiyi tayi please kinji?" Murmushi tayi tana gyad'a kai daidai lokacin hamna ta shigo motan be kara magana ba se murmushin da yake sakewa akai akai har suka fice asibitin da umma take ya fara sauke hamna har ya tada motan iman tace "Hamna please in shiga in gaidata?" Yace "Ohk bari In gyara parking se mu shiga".

Gyarawa yayi suka sauko suka jera a tare gwanin sha'awa se d'auke idanun Jama'a suke, bacci ma suka samu takeyi ummu na zaune kan plastic chair da fara'a sossai ta tarbi Iman har tana cewa tayi fushi shine ko a waya bata nemeta ba tun dawowansu shine ya bada hakuri ya kuma tabbatar mata yau a gidanta zasuyi dinner don haka ta tanadarwa daughter d'intan better, cikin jin daad'i tace "aiko ba se ka fad'a ba daughter yau se abinda kika za'ba" murmushi Kawai iman ke sakewa yayinda hamna tazo wuya.

Kenan asirin da sukayiwa ummu ya karye garin yaya? Tab dole ko ta wani hali ne yau a sallami umma su samu su aikata aikin nan in ba haka ba suna gani komai zai ida chabewa gashi yanzu duk wani so da kulawa da ummu ke bata ya koma kan wannan bakar munafukar se kwafa take saki minti minti, sallama sukayiwa ummu suka fice dayake umman na bacci tun shigowansu, suna fita ya rike hannunta lumshe idanu tayi ta bud'e akanshi suka sakarwa juna murmushi gaskiya he can't wait..... he just can't wait dare yayi ya nunawa wannan baiwar irin son da Allah ya d'aura mishi nata.

Da wannan tunani suka karasa mota seda ya zagaya ya bud'e mata ta shiga kan ya dawo ya shiga mazauninshi se gidansu da ihun umma umma ta shiga gidan umman dake zaune kasan bishiya tana tsince shinkafa tace "ikon Allah menene kuma haka maama?" Dayake haka take ce mata tun daga fufore, jikinta ta fad'a tana cewa "nayi kewarki ummana" tureta umma tayi tace "bani son shiririta Ina shi mijin naki kika baroshi?" Tace "yana waje" karar fad'uwar tray sukaji da sauri suka kallo wurin.

Hafsyce tsaye ga trayn silvern da ta d'auko a kasa, mutsuke idanunta tayi ta kara bud'ewa umma da ta gane abinda takewa haka ta mike tana cewa "toh maaama ga wata mashirmaciyar 'yar uwarki" tayi d'aki don nemo hijab, dariya iman tayi tana cewa "ke ba gizo idanunki ke gane miki ba labarine me tsawo na san kuka dawo umma zata baki" Da gudu hafsy tazo ta rungumeta tana tayata murna nan umma ta fito da hijab a hannu tana mitan sun bar mutum a waje.

Hafsy ta mike ta janyo gyalenta daga kan igiya iman ma ta mike suka fito seda umma ta rufe gidan kan ta karaso Abdul ya duka har kasa ya gaidata ta amsa da fara'a tana tambayarshi ummunshi baya suka shiga ita da hafsy yayinda iman ta shiga gaba suna ta aukin surutu ita da hafsyn har asibiti ba abinda ke had'asu da malabo se kallo don kunyar Umma da yakeji.

Har d'akin da mama take suka shiga wasa wasa kumburintan yayi yawa wadda hakan ya bawa iman tsoro da tausayi nan fa ta fara aikin kuka, da kyar umma ta sata tayi shiru yayinda malabo ya zuba mata idanu yana kallo adu'a sossai baba ya mata inda anan malabo ke fad'amu In one week zasu wuce dukda be so su kai haka ba sede ba yadda ya iya dole ya jira visa d'insu.

Sun jima sossai nan kan sauban yazo ya fad'a musu time ya kare yanzu sa iya tafiya, ba don sun gaji ba suka fito baba ya d'auki su umma da hafsy yayinda Abdul ya d'auki matarshi sukayi gidan ummu Don su rahama da kalthum sun dameshi da kira akan suna son ganinta, se a mota hafsat ke bawa su umma labarin irin taimakon da Abdul ya musu yanzu ya chanzawa mijintan ma wurin aiki zuwa company d'inshi albarka sukayi ta sa mishi nan umma tayi briefing d'inta kan tafiyansu fufore da nema musu magani da kakanshi yayi, har suka isa gida labarin kirki, alkhairi, sanin ya kamata da son mutane irin na Abdul suke.








                      🖤Gureenjo🖤



                  🥀NOOR IMAN🥀

*Fatima Muhammad Gurin*
           *Gureenjo6763 on wattpad*

*'Yar Mutan Adamawa*

💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)


*hakika bani da abinda zan ce muku sisters se Allah ya saka da mafificin alkahiri ya bar kauna, duk naga adu'o'inku gareni na gode kwarai Allah ya amsa ya biya mana dukkanin bukatunmu na alkhairi ba shaaka wannan page d'in naku ne sadaukarwa ne ga dukkan waenda suka iya 'bata lokacinsu da data d'insu wajen min adu'a na gode kwarai na muku wannan page d'inne sbd jin daad'in adu'arku, ranan litini In Allah ya kaimu zan fara jarabawar na gama tests. Allah ya bamu sa'a gabad'aya a duk abinda muke.


                           *050*

Cikin farin ciki da jin daad'in ganinta Anty rahama, Anty kalthum, zahra suka rungumeta murmushi kawai take musu tana jin daad'in yadda suke kaunarta har kasa ta duka ta gaida ummu dake "ga daughter, ga daughter" a kunyace ta gaidata ta amsa da fara'a ta gaida Anty rahama da Anty kalthum duk suka amsa suna mata barka nan fa hira ya 'barke akan ire iren abubuwa haka da suke faruwa.

Sun jima zaune parlorn ana hira kan Abba, Hafeez da Abdul suka shigo a tare kasa ta zame ta gaida Abba ya amsa fuska a sake cike da farin cikin ganinta barka ya mata na shiryawa da ummanta ya sa musu albarka gabad'aya ya wuce parlorn shi, nan Hafeez ya fara tsokanarta su Anty rahama suna rama mata gogan nata kam zama yayi ya zaro waya ya fara aikin call idanunshi a kanta wadda hakan ya sa gabad'aya ta takure ta kasa sakewa kunyan su Anty kalthum na kamata musamman da taga Antyn da zarah na kuskus.

Dayake tun shigowar Abba ummu ta bi bayanshi, yana gama wayan ya taso yazo inda take a kasa ya zauna gefenta har cinyansu na gogan juna wayanshi ya dadanna ya fito da wasu hotuna ya d'an duko gefen kafad'anta yace "duba kiga wanne ne yafi kyau anan?" Kar'ba tayi ta fara kallo wasu motoci ne masu asalin kyau colors daban daban daga gani kuma zasuyi tsada akan wata BMW ta tsaya sede colourn Dark blue ne ta san shi kuma baya son colored car kallonshi tayi shima wayan yake kallo yace "ita tafi kyau?" Kai ta gyad'a yayi murmushi tare da kar'ban wayan.

Kashe wayan yayi da sauri ganin Anty rahama na leko kai, hararinsu yayi yana mikewa yace "gulma dae ajali" suka kwashe da dariya gad'aya iman na sakan murmushi, kiran sallah ne ya katse musu hiran da suka d'auko ana gama kiran Abba na fitowa suka had'u da mazan sukayi masallaci basu dawo ba seda sukayi Isha, bama su zauna ba ummu ta nuna hanyar dining tana cewa "bismillahnku dinner is ready" duk dining sukayi ta d'aga wayanta ta kira zarah tana d'agawa tace "me kukeyi ne har yanzu baku sauko ba? Kunga In ku bakwa jin yunwa ku turomin 'yata taci abinci" tana kai nan ta kashe waya.

Zarah ta sauke wayan tana kallonsu Anty cikin muryan shagwa'bewa tace "mu kuma da bola aka tsinto mu se muyi ta zama da yunwa" dariya suka saka Iman na murmushi ta mike sbd su Anty ne kawai bata make zarah ba, dama tunda suka shigo take ta kwaikwayan yadda ummu ke masifa akan Iman se dariya suke, da dariya suka sauko suna hiransu duk suka zauna se suka bar mata seat d'in dake facing d'inshi.

Zarah ce tayi serving kowa tana bawa Abba labarin itama fah ta kusa zama graduate, Hafeez yace "a ina d'in ke da yanzu kike level one" Anty rahama tace "kyaleta shekaru kusan hud'u ke gabanki Don bakiyi komai ba madam" Anty kalthum tace "kila ma harda spill se ki kara mata shekaru biyu kin san itace Anty olodon gidan nan" bubbuga kafa ta fara kasa tana cewa a shagwa'be "Abba ka gansu ko?" Yace "Kunga rahama banaso ku kyale min auta ta sarara, In Shaa Allahu ba spill da zakiyi kinji?" Kai ta gyad'a tana murmushi a lokaci d'aya tana musu gwalo.

Shifa duk abinda sukeyin nan ba sauraransu yake ba tunaninshi da hankalinshi duk ya d'auke akan matarshi murmushin da takeyi ji yake kaman fuskanta ya dawwama a haka har abada, wushiryan tan nan me kyau da one side dimples d'inta da yafi komai d'auke mishi hankali, dayake saitinshi ta zauna ta d'an mike kafa kanta kasa tana juya chokali a lokaci d'aya tana murmushin dramar zahra don har time d'in bata gama ba.

Ita harga Allah matsanancin kunyan cin abinci a haka take surukanta ne fah, wasu surukan ko kujera ka zauna gabansu ba kasa ba se sunyi mita akan  hakan amma su waennan ba ruwansu en boko ne na gaske yadda suka d'auki su zahra haka suka d'auke ta, wani irin zabura tayi tana zaro ido da sauri suka maida hankali kanta har suna had'a baki suka ce "Lafiya??" Cikin In Ina tace "ba komai" satan kallonshi tayi ya sake wata munafukar murmushi bata san sadda ta harareshi ba ido ya zaro da idanun ya mata alamun ni?? Bakinta ta d'an turo, kanshi ya gyad'a ya sake kai kafanshi kaman farko ze mata tafiyar tsutsa a tafin kafa da babbar yatsarshi da sauri ta mayar da kafan kasan kujera, Abba da ummu da suka fahimci abinda yake faruwa kallon juna kawai sukayi suna sakan murmushi.

Da kyar taci abinci kad'an shima da takurawar ummu seda duk suka bar dining d'in kan ta mike ta fara tattare kwanukan ummu daga parlor tace "maza daughter ajiye kizo akwai waenda zasu tattare ba se kin yi ba" ajiyewa tayi ta je parlorn nan ummu ta kara basu hakurin abinda tayi musu duka, duk suka ce ba komai wallahi ai sun san ba yin kanta bane.

Sun mike da niyyar tafiya gida kenan Hamna da umma suka shigo, gaban Iman ne ya fad'i haka kawai ta rasa dalili wadda hakan ya sata fara ambaton Allah, ummu ta mike da sauri tana cewa "an sallamekune hamna?" Hamna tace "eh wallahi ummu an bamu sallama kuma umma tace nan take son sauka In ta kara jin sauki se ta wuce yola" Kai ummu ta gyad'a tana cewa "to mu karasanku part d'ina, Sannu hajja" Kai kawai umma ta gyad'a tana hararanta kasa kasa wadda a idanun zahra da hafeez kallon juna sukayi.

Hamna ta kalli Abdul tace "Hamma gida kukayi In zo muje?" Yace "I thought da car d'inki kika zo? Besides ba gida mukayi ba, ummu, Abba Allah ya bamu alkhairi" Abba yace "Ameen ya rabbi Allah tashemu lafiya" ummu da hankalinta ke kan kanwarta tace "A huta gajiya, se da safenku" suka fice ba jimawa Hamna ma ta fice Anty kalthum da Anty rahama ma suka tafi, Abba ma yayi part d'inshi, zahra ta kalli Hafeez shima ya kalleta tace "kana tunanin abinda nake tunani hamma?" Yace "ba alkhairi ya kawota ba" tace "exactly amma zan sa mata ido baza ta zo ta dinga ruining life d'inmu a banza da wofi ba".

Suna fita daga gidan ya kama hannunta ya matse cikin nashi yace "ni kike harara d'azu ko?" Tana karkad'a idanu tace "wayyyo Hamma Allah ba da kai nake ba fa" yace "to da wa?" Yana kallonta tace "Da kujera fah nake" murmushi yayi yana cewa "amma kujeran da nake ko?" Tace "dan Allah kayi hakuri hannuna" ta karasa a shagwa'be murmushi yayi don ya san ba wani rikon arziki ya mata ba shagwa'bace kawai a lokacin suka isa mota seda ya bud'e mata ta shiga kan ya zagaya ya shiga me makon ya tayar se ya rankwafa kanta yace "wato don kin rainani har turomin wannan bakin naki kike ko? To bari su kar'bi hukunci" Kan tayi magana ya had'e bakinsu.

Seda yayi kissing d'inta son ranshi kan ya saketa yace "gobe ki kara turomin wannan bakin kiga hukunci Ina da hukuncinshi kala kala" Kai ta dukar tana taune lips d'inta murmushi ya sake yana tada motar cikin nishad'i ganin duk kunya ya hanata d'ago kai yasa shi sa hannu ya kunna waka abinshi, Yana bi a hankali chan yace "Hayatee!!" Kallonshi tayi tana amsawa a saman lips d'inta yace "kaman bakici wani abin kirki ba muje mu samu abinda zakici?".

Tace "a'a na koshi fa" yace "no baki koshi ba oya fad'amin me kike son ci" Tace "da gaske na koshi" be kara magana ba ya juya kan motar yayi cikin gari chan wurin gasa nama ya tsaya ya saya gasashen kaza irin me ruwa ruwan nan ya had'a da zallan gizzard, gaba kad'an ya kara ya kuma tsayawa ya saya fresh milk masu sanyi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login