Follow us on social media
Showing 54001 words to 57000 words out of 131683 words
Chapter 19 - NOOR IMAN Yar Baƙin Ciki BY Fatima Muhammad Gurin
d’inkin zamani aka mishi da ake kira half jumpha me wani style me d’aukar hankali rigan me dogon hannune hakan yasa be d’aura agogo ba se links d’in da ya saka golden color, hulan kanshi milk ce da d’an adon golden se takalmin kafanshi half cover milk yayi kyau har ya gaji, kamshinshi da nata suka had’u suka bada wani kamshi me kashe jiki da wuyar fassarawa.
Duk cikin seconds da basu fi talatin ba ta gama kare mishi kallo, ko d’agowa be yi ba, kaman be san da zaman mutum gefenshi ba, fuskanshin nan ba’a had’e ba ba kuma a sake ba yana nan dae yadda ta saba ganinshi, ajiyar zuciya ta sauke kan ta maida kanta kasa tana wasa da zoben hannunta, cikin sanyin muryarta Tace “Ina yini?” Kallonta yayi se kuma ya d’auke kanshi be zaci zata gaisheshi ba, hakan yasa seda yaja lokaci kan yace “fatan kina lafiya” Tace “Alhamdulillah”.
Shiru sukayi basu kara magana ba har aka isa wurin dinner d’in, basu fito ba seda aka bud’e musu kofa fita yayi, itama ta fito seda ta zagayo inda yake kan suka jera su Ameera ma sun jera biyu biyu, yayinda abokanshi sun riga da sun shige ciki, wasu kuyangi ne suke zuba flowers a gabansu masu kamshi suna takawa suna wucewa, yayinda masu busa da kid’i irin na masarauta suka fara aikinsu, nan fah jin kai ya tashi wani irin tafiya su zarah sukeyi irin na asalin sarauta se na Abdul ya dame nasu ya shanye.
Kun gane Ai irin kana jin algaitar nan tana ratsa jikinka, wayyo seda suka burge kowa har Iman dukda ba irin tafiyar ta iya ba sede itama a hankali take tafiya daidai shi, tattausan hannunshi ya saka ya kama nata a tare suka kalli juna se ya sakar mata murmushin gefen baki yana d’auke idonshi, seda suka zauna tukun masu busa suka fice dj ya saki kid’a.
Taro fa yayi taro su Inna de an zama se kallo baki ya mutu murus sun tabbatar na gaba yayi gaba na baya se labari, Ahhh daga bayansu Iman Hamna ta shigo itama da gayyar kawayenta da suka ci anko, ita kuma tana sanye da red swiss lace taci kwalliya seka rantse itace amaryar kawayenta ankon blue suma sukayi sede ba mix bane irin na su zarah, haushi har wuya zarah taji sede bata ce komai ba, Iman kam ko a jikinta sema kyaun da suka mata yayinda uban gayyan ko kallon inda suke be yi ba bare ya tanka.
Mc ya fara gabatar da taro, bayan en gaishe gaishe da jawabai aka kira babbar kawar Amarya ta bada labarin Amarya fita zarah tayi ta kar’bi mic ta bada biographyn Amarya sede bata fad’a duka ba iya makaruntun da tayi se halayenta ta fad’i cikin harshen turanci, aka kira babban abokin ango ma Sauban ne ya fito ya bayar, nan fah aka fara shagali, buki fah yayi buki ba abinda kake gani se ruwan liki.
Kannen ango aka kira don taka rawa se kawayen amaryar gabad’aya suka fito, suka cashe gashi basu da kunyar rawa, bayan sun zauna aka sake kiran kawayen amarya su fito da abokan ango fitowa sukayi aka basu gasar da zasuyi wato na rawa aga waenda suka fi iyawa kowa kuma shi ze za’bi wakar da za’a sanya mishi, nan fah aka fara ba laifi abun yayi kyau sossai dayake abokan Abdul shakiyai ne haka kawayen amaryar ma rawa sukayi kaman ba gobe, kan aka sallamesu bayan kawayen Amarya sunci gasar.
En uwan Amarya aka kira wasu daga ciki suka fito suka d’an tattaka har da su Inna a filin rawa, bayan sun tafi se Mc ya kira en Annur Hausa Novels wayyo zo kuga rawa, kowacce rawa tayi na kece raini abin se wadda ya gani😎, bayan sun tafi en wattpad ma suka fito sukayi nasu daga su fah se na hango en Mukaru da Juna sun fito waai ashe haka mutanen nan suka iya rawa ban sani ba🤥 Ni sun barni a baya ko hannu ban iya juyawa da kyau ba bare rawa☹️.
En uwan Abdul fah sun zuba liki ba kad’an ba haka abokanshi, Iman de na zaune tana kallon kowa waenda suka bata dariya tayi ta murmushi musamman waennan kungiya masu sonta tsakani da Allah, rawar da har Abdul ma seda yayi murmushi suka sha, bayan kowa ya gwangwaje aka kira Ango da Amarya su d’an taka se su yanka cake, Abdul ya fara mikewa tare da mikowa Iman hannu, kallonshi tayi ya lumshe mata ido alamun ta saka, sanya hannu tayi ya taimaka mata ta mike suka fito, shifa ba wai bai iya rawa ba sarai ya iya sossai Don duk cikin abokanshi ya fi su iya rawa amma anan be yi ba se d’an jujjuyawa da yake da ita bayan ya mannota da jikinshi, waiii had’uwa, kawayenta suka fara fitowa suna mata liki kan abokan ango se en uwa amma banda en uwanta kayan takaici, bayan sun gama suka karasa inda cake d’insu me hawa kusan shidda yake,da milk shima akayi Icing d’inshi, bayan an kirga Harrufan sunanta suka yanka, ita ta fara yanka d’an kad’an ta kai bakinshi da umarnin Mc budewa yayi yana dafa hannunta ta saka mishi, shima ya yanko ya kai bakinta kad’an ta bud’e ya sakamata hakan yasa gefen lips d’inta ‘baci, hannu ta sa da niyyar sharewa se yayi saurin rike hannun ya kura mata ido kur yana kallo itama shi take kallo da tilastawarshi don ya rike mata ido cikin nashi ya hanata kata’bus, babbar yatsarshi ya d’aura akan lips d’inta a hankali ya tafi dashi yadda janbakinta baze goge ba ya cire mata icing d’in shagala sukayi da kallon juna, dj kuwa ya sake musu sautin wakar soyayya ta turanci me ta’ba zuciya, be san sadda ya fara matsowa gareta ba har ya had’e fuskansu yana shirin d’aura bakinshi kan nata Hamna ta saki karar da ya sashi saurin janyewa ya wani basar kaman ba shi ba🤣.
*Wayyo sorry baku jini jiya ba lectures ne ya hanani yi wallahi na dawo na gaji, amma ga wanna 3288 words hope zakuyi hakuri dani*
🖤Gureenjo🖤
🥀NOOR IMAN🥀
*Fatima Muhammad Gurin*
•Gureenjo6763 on Wattpad•
*'Yar Mutan Adamawa*
💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)
*this page is dedicated to yhu Aisha Gazara Mrs. Bello, Allah ya kara dankon love yasa bad'i war haka mu gwangwaje, Allah ya barku tare har Aljannah, much love dear*
*028*
Kowa ido ya zuba mata yana kallo har shi uban gayyan kawai se ta mike ta fice da sauri, tsaki yaja kan ya kama hannun matarshi suka koma mazauninsu, nan aka fara niyyar cin Abinci serve ur self ne, kowa mikewa yakeyi ya d'ibi abinda ya san ze iya ci ga abincika kam kala kala, kai na dafe hango Rukayyah farouk, bushira, herpcert sabee'u, Maman two girls da cool ramcy tsaye kowacce rike da plates d'inta tana jiran layi ya zo kanta, ban hankara ba fa naji an bankad'e ni har takadda da birona yayi kasa, a zuciye na d'ago se naga Adama Aliyu, maman khalil, khadija Queen da Kawata Aisha ne tuni sunyi gaba bama su san sun bangaje ni ba, dariya na fara ganin suna kokarin yi ma maijidda da Zuwaira Musa satan layi.
Girgiza kai kawai nayi na juya kenan na hango maman habeebty, rabiya basiru, Aysha Adam, hussaina A sidi da khadeeja hussaini sun shige chan lungu suna dambe akan cinyar kaza🤣🤣🤣, juyawa nayi na fara neman Namesy na zahra iliyasu, faizadikko, ummu Ameer, ummu haneef da ummu Aslam Don su zo su raba su amma duk ☹️ ba wadda ya kulani se ma nunawa da sukayi basu sanni ba don kowacce ta ciko plate da kaji😋.
Ban hankara ba na juya naga abinci ya kare kap neman wadda ze tsammin nashi na fara, Hanifatulkhair(didi) na fara nufa ta juya kaman bata sanni ba tayi gaba abinta🥺 Mmn habeebty, mommy Anwar, Mrs Abmin, hajara Aminullah, hadixa da shafa'atu duk kowa ya hanani ya juyan keya😭.
High table na nufa da sauri kawai naga Smeenarl, meenerl, hasfatsafyan da sameera Ahmad sun kwashe na gaban Ango kam sun fece ganin yana ta yanga ko kallon inda abincin yake be yi ba, se bowl d'in fruit salad da ya d'auko tare da sa spoon ya d'ibo kaman ze sha kuma se ya juya ya kai bakinta, d'ago ido tayi ta kalleshi da ido ya nuna mata spoon d'in alamun ta sha, a hankali ta bud'e bakinta ya saka mata, su zarah ne suka takalo camera man suna nuna mishi high table, mastowa yayi ya fara haskasu ko a jikinshi se ci gaba da bata da yayi itace ma kunya duk ya hanata sakat dukda ma hankalin kowa be kansu se su inna suna yagan kaza suna kallon kwakwap.
A hankali tace "na koshi hamma" kasa kasa ya kalleta yace "are yhu sure?" Tace "Eh" kafanta ta ke ta lankwasawa tun kan ya fara bata fruits salad d'in ya lura, cikin kasa da murya yace "are yhu okey? Your legs me ya samesu?" Cikin daburcewa kaman wata marar gaskiya Tace "ba komai" Kau da kai yayi ba don ya yarda ba, ana gama asalin dinner aka fara shirin tashi yanzu ma tare zasu tafi, duk tayi ta duba su zarah bata gansu ba bata ma san sadda suka fice ba.
Ganin ya mike yana ta sallaman manyan bakin da suka zo yasa itama ta mike ta tsaya gefenshi iyakaci tayi murmushi shi ke aikin godiya da sallama, kan kace kobo hall kam ya watse kaman ba yanzu aka gama fad'an kaza ba😜 Su Mmn Nurr da kawata jamila idris (ummu Afreen) har guzuri seda sukayi, se tsiraran abokanshi da baza'a rasa ba, tsayuwan da tayi se ya kara karawa kafan gajiya, har wani jiri take ji yana kwasarta, juyowa yayi ya kalleta ya kuma kallon kafan kan ya kamata ya zaunar da ita.
Da tsananin mamaki take kallonshi don ganin ya durkusa kan gwiwanshi, zarazaran yatsunshi ya sanya a hankali a kan fatar kafanta wadda sanyin hannun ya sa ta d'an razana tsikar jikinta suka tashi, takalmin ya cire mata ya fara mammatsa mata kafan zuwa kan yatsunta lumshe ido tayi yayinda sauran abokanshi suka saki ihu, ko kula su be yi ba seda ya gama ya koma d'ayar kafan ya d'an mamatsa mata kan ya kawar da takalmin.
Ya mike bata hankara ba se jin kanta tayi a sama ya d'auketa chak kaman wata 'yar tsana, hoto sauban ya matso ya d'aukesu sauran de se dariya sukeyi kunya ya sata shigar da kanta kirginshi ta sa hannayenta biyu ta zagaye wuyanshi, har mota ya kaita driver yayi saurin bud'e musu ya sanyata, ya juyo ya d'agawa abokanshi dake bin bayanshi yatsarshi na tsakiya tare da sakar musu wani munafukin murmushi yana d'age gira, zaginshi suka fara da sauri ya zagaya ya shiga yayiwa driver hannu suka fice, dariya me sauti ya d'anyi sanin ya kular da su kuma kaman bashi ne ya d'auka en Iskan se sun rama.
Itakam kunya yasa ko d'ago kanta ta kasa se mamakin dariyarshi take dama gayen na dariya? Tsintar magananshi tayi yana cewa "karki sake sa irin takalminchan, ko daad'in ciwon da yake ji miki kike ji?" Kai ta girgiza, Shiru yayi kaman baze kara magana ba se kuma yace "wai ke kurma ce?" Da sauri tace "A'a, naji in shaa Allahu bazan kara sakawa ba" yace "better" suna parking ya sauka har ta bud'e kofa da niyyar sa kafanta kasa yayi saurin dakatar da ita da cewa.
"kina da hankali kuwa? zaki taka bare foot d'inki kasa bayan kin san ba kyau ga mace?" Shiru tayi ya d'anyi tsaki kan ya duka ya d'auketa kuyangi da dogaran da suke arean se kuskus suke ko kallonsu be yi ba ya shiga da ita har parlorn tukun ya sauketa, a hankali tace "na gode" juyowa yayi ya kalleta se ta dukar da kai, ta sake cewa "Ina so inyi magana da mama tunda tazo ban ganta ba" da mamaki yake kallonta Don zatayi waya da mama se ta nemi izininshi?.
Ganin be fa fahimta ba yasa tace "wayana" yace "oopss sorry zan aiko miki later, shikenan?" Kai ta gyad'a mishi, ya juya ya fice yana cewa "seda safe" ajiyar zuciya ta sauke kan ta nufi cikin d'aki nan ma bataga zarah ba tooh Ina kuma tayi? Cire kayan jikinta tayi tare da sanya rigar da ta saka d'azu ba tare da ta saka d'ankwali ba ta zauna bakin gado tana tunanin en uwanta gaskiya ya kamata taje ta gansu ace suna gida d'aya amma basu had'uwa!!.
Bud'e kofan bedroom d'in taji anyi dayake ta ba kofan baya so ta d'auka zarah ce Don ta san kuyangin basa shiga basu nemi izini ba, surutu kawai ta fara tana cewa "Allah harinyar nan baki had'u ba sam ko kinyi wanka, wa ya gayamiki kawaye na tafiya gabad'aya su bar amarya?" Bata juya ba bata kuma jira amsan zarah ba ta d'aura da "ke dama haka yayankin nan yake? Shi be jin kunyan mutane? Da yayi kissing d'ina yau a wurin nan da inaga kasa ne kawai zata bud'e In shige bazan kara kallon kowa ba har Abada!!! Waii".
Jin ba'a amsata ba yasa ta juyowa da sauri tana cewa "wai kin san d'a...." makalewa maganan yayi sbd idonta da ya fad'a cikin nashi yana tsaye jingine da kofa ya hard'e hannunshi da kirji tare da zuba mata idonshin nan, rasa abinyi tayi natsuwarta duk ya bar jikinta a lokaci d'aya jikinta ya d'auki rawa, da sauri tayi kasa da kanta, murmushi ya saki ganin yadda ta rud'e ya kula tana da saurin rud'ewa musamman In yana wuri, takawa ya farayi a hankali zuwa gabanta yana kare mata kallo.
Ba laifi yarinyar tana da kyaun jiki ba kad'an ba be ta'ba mata kallo irin haka ba sbd ta kasa d'ago kanta bare shi ya kauda idonshi gashinta ya mishi kyau sossai dukda na Hamna yafi nata yawa sede kuma nata yafi mishi kyau da tsari sbd baki ne sid'ik yayinda na hamna ya kasance ja, nata Virgin ne yayinda hamna ke saka relaxer, gaskiya baze yarda ta 'bata mishi gashin nan ba.
Don ya ga yadda zatayi yace "yarinyar nan kin raina ni fa, first of all kince farina irin na zarah da me ma..." ya sa hannu a ha'banshi alamun yana tunani se ya ce "na ma manta yanzu kuma kince banda kunya, nine marar kunya?" Waro fararen idanunta tayi a kanshi cikin In ina tace "wallahi ba haka nake..." bakinshi ya ciza yana kau da ido kanta yayinda ita kuma maganan ya makale ta rasa ma me zata ce mishi.
Gabanta ya matso sossai ya kama hannunta ya d'aura mata waya, tare da dukowa kanta yace "kin kyauta tunda zagina abu ne da yake miki daad'i ki ci gaba" ya juya ze tafi tayi saurin riko hannunshi ba tare da ta sani ba da karfi ya janyo hannunta yana juyowa ta fad'o jikinshi hannu ya sa ya zagaye kwankwasonta hawayen da suka cika mata ido ne suka gangaro ta bud'e baki ta ce "dan Allah Kayi hakuri ba zaa.." bakinshi ya rufe da nata hakan ya sata waro ido shima ita yake kallo da sauri kuma ta lumshe nata, yayi kissing d'inta son ranshi kan ya saketa yana cewa "first punishment na zagin farko, night" ba tare da ya jira amsanta ba ya juya ya fice yana murmushi.
Ta kai mintuna biyar tsaye wurin kaman an dasata hannunta na d'aure bisa saman lips d'inta ji take kaman har yanzu bakinshi na kan nata, shigowar zarah ne ya dawo da ita hayyacinta ta sauke hannunta tana kakalo murmushi tace "Ina kika biya ne? Kika tafi kika barni" zarah tace "wallahi Ummu ce tayi kirana" tayi maganan kaman ba zarah ba da alamu wani abin na damunta, cikin sanyin murya Iman tace "Lafiya kuwa me ya faru?" Murmushi zarah ta kakalo tace "kalau" wayan da malabo ya d'aura mata a hannu ta d'ago Don kallo se taga wata wayar ba nata ba, kaman ma irin na zarah, sede wannan pink ne yayinda na zarah ya kasance red, matsowa zarah tayi tace "wayan waye?" Iman tace "yanzu hamma Abdul ya bani" murmushi zarah tayi tace "congrats" iman tace "thanks" kunna wayar tayi wadda ya kasance iphone X max, dayake tana kar'ban na zarah ta d'an iya kallon time tayi taga ashe dare yayi sossai bari ta bari se safe tayi kiran en gidansun.
Don taga sim d'inta ne a kai, zarah de bata kara magana ba ta tu'be kayan jikinta ta shige toilet da kallo Iman ta bita tabbas akwai abinda ke damunta sede ta kasa fad'amata ne, Adu'a tayi Allah sa de lafiya ummun take kan ta kwanta tana janyo blanket ta rufe jikinta tare da lumshe ido tunaninshi gabad'aya ya cika mata kwakwalwa, wannan wani irin mutum ne shi? Ta rasa gane kanshi, ta rasa dalilinshi na aurenta sede ta tabbatar duk duniya bata da kamarshi yayi abinda duk mazajenta basu mata ba, ya taimaketa be mutu kaman yadda hamza ya mutu ba, kuma be mata wulakanci kaman sadda sauran mazajenta a daren aurenta suke mata ba.
Tana ji zarah ta fito ta shirya cikin kayan bacci tazo ta hau gado ta kwanta ba tare da ta ko d'auki wayanta ba Zarah da komai gajiyanta se ta danna waya kan take bacci adu'a tayi mata na Allah ya yayemata damuwarta In bazata iya fad'awa kowa ba, tana nan tana tunaninshi itama bacci ya tafi da ita ba tare da ta sani ba wani irin gajiya take ji dama har 'bargonta.
*******
"Wallahi umma bazan iya jira a gama auren nan ba, In ban yi da gaske ba kan a watse taron nan ze kusanceta In shiga uku, umma bazan iya ganin wata macen kwance kan kirjin Abdul ba In ba ni ba, tayi kad'an ta dasa min bakin ciki." Ta karasa da kukanta, umma tace "hamna me yasa kike son tada zaune tsaye bayan na ce miki zamuje Ai zam....." cikin tsawa tace "umma kissing