Follow us on social media

Showing 126001 words to 129000 words out of 131683 words

Chapter 43 - NOOR IMAN Yar Baƙin Ciki BY Fatima Muhammad Gurin

taga sun shiga kings collage inda anan ya kuma neman aiki dayake da yayi musu visiting lecturing yadda taga en mata turawa suke harinshi se abin ya firgitata gasu zafafa masu class, a zuciyarta take raya yadda zata ci uban duk wacce ta shigar mata hanci akan mijinta dukda admission ya nemar mata dayake ana ji dashi kuma sananne ne nan da nan suka tabbatar mishi da ta fara shiri kawai kuma exact course da ta bari shi zatayi Wato BSC Ed Biology, amma rannan a had’e ta cika tayi tab saura kad’an ta fashe.

Yana driving yana satan kallonta hannunshi da ya sa cikin nata yana murzawa ta cire ta juya ta cigaba da kallon window, cikin sanyin murya yace “sarauniyata laifin me na aikata a gareki? Tuba nake tun banji laifi na ba, a fad’amin samun In hukunta kaina tun kan fushinki ya gama illatani” tura baki gaba tayi cikin kunkuni tace “haka zaka ce Ai bayan ka gama zagayawa kaga en matanka ka nuna musu ka dawo” yana shiga manyan offices da anan ne ze kar’ba mata licenses na zama a kasar har iya yadda ta so yace “en matana kuma hayatee?” Shiru tayi ajiyar zuciya ya sauke bayan yayi parking ya janyota jikinshi cikin raunin murya yace “ashe zuciyarki bata gama tabbatar miki da cewa ke kad’aice a cikin birnin Abdulraheem ba? Ashe Abdulraheem yayi gazawar da har Saudah take ganin kaman ze iya kula wasu en matan bayan ita? Me zanyi Saudah me kike bukatar inyi daze tabbatar miki da cewa ban ta’ba son wata hallitar Allah ta jinsin mace ba bayan mahaifiyata se ke? Ina miki son da ban san adadinshi ba hayatee karki hukunta ni da laifin kallo da shishigemin da en matan kasan nan zasu min tunda ba ni ke musu ba”

Ajiyar zuciya ya sauke tare da hura mata iska cikin kunneta cikin kuma kasa da murya yace “hayateee kin kuwa san shekaru na nawa a kasarnan?” Be kula amsanta ba yace “tun da chan a lokacin da ban samu hasken zuciyata ba ban kula su ba seda na samu duniyata?” Ze kuma magana ta juyo fuskanta ta had’e bakinsu seda ta mishi wani fitinannen tongue to tongue kiss kan tace cikin kasa da murya “A gafartamin zaujii, tsoro nake ina tsoron kar watarana in Gaza ta wani fannin suyi nasaran d’aukemin kai, god forbid Allah ya sani I can’t imagine a life without you, kaine farin cikina zaujii kaine haskena, kaine duniyata, kaine murad’in raina, kaine rayuwana kaine numfashina Ina maka son da bana yiwa raina, kain.....”

Be jira ta karasa ba Don kalamanta saura kad’an su maidashi crazy ya had’e lips d’insu tare da rungumeta kaman zasu had’iye juna, da kyar suka tsayar da abinda suka tsokano suka shiga sukayi abinda ya kawosu kan suka koma gida suka d’aura daga inda suka tsaya, satinsu guda ta samu admission inda da kanshi ya mata komai da komai sati na zagayowa suka fara fita aiki.

Rayuwa sukeyi cike da ‘yanci da kulawa zata ce tunda tasa kafa ta bar Nigeria ita de bata ta’ba d’aura wani abu akan gas da sunan girki ba, ko cooku ya dafa ko su ci a waje In bata da lectures haka zata zauna office d’ishi muddin yana cikin makaranta ba company ba komai tare sukeyi sun zama jini d’aya kowa ya san irin soyayyar da suke yiwa juna.

Kwance take rub da ciki tana waya da zahra dake mitan ita ta gaji suyi su dawo Allah bazata yarda ayi aurenta basa nan ba, kallonshi tayi yana tsaye gabanta rike da kugu daga shi se boxers jira yake tazo taje ta taje mishi suma Don ba abinda basa yiwa junansu har shaving, cewa tayi “oh sweetheart Hakuri zakiyi ba yadda muka iya don ba cikin hutu za’ayi bukinki ba and kinga hammanki yace bazamu koma Nigeria ba se after five years and he mean it”

Zahra tace “Ai Hamma!! bakiga fad’an da Abba yayi ba da ya samu labarin ajiye ayyukanshi na Nigeria da yayi amma gayennan ko a jikinshi, ya tsallaka ya barmu da wahala don tunda nenne ta samu sauki muka tashi dawowa ummu ta d’auko mana hamnan nan bakiga yadda take kula da ita ba kaman basu mata laifin komai ba” cikin tausayawa tace “Eyyah Anty Hamna zahra ya kamata ki taya ummu kulawa da ita na san tana cikin mawuyacin hali” zahra tace “ni dae har tsoro take ban bata cika magana ba se ido duk abinda zaki mata sede ta biki da ido se aukin ibadah da yanzu naga ta dage dashi kullum cikin kuka” Iman tace “Allah sarki ya kamata ta dawo nan mu zauna tare” Da sauri zahra tace “wani irin zama tare Saudah?” Yaune ta farajin zahra ta kirata da saudah a rud’e kuma a firgice dariya tayi kan Tace “ta koma d’akinta mana bari zanyiwa ummu magana”.

Katse wayan taga hannunshi yayi da sauri ta kawar da kanta daga fuskanshi ganin yadda ya had’e rai kaman be ta’ba dariya ba cikin kausasa murya yace “kull karki soma na gayamiki, karkisa inyi rantsuwa akan abinda ba zan ta’ba yin kaffara ba ki fita sabgar abinda ban sa ki ba banaso” yana kai nan ya juya ya shige toilet ajiyar zuciya ta sauke, ko me ze yi sede yayi bazata zama muguwa ba, dole Hamna ta dawo d’akinta da taimakonta, ta san baze ta’ba iya ‘bata yini yana fushi da ita ba.

Ummanta ta kira Bayan sun gaisa take neman shawaranta akan abinda ta sa gaba sossai umma ta bata goyon baya ta kuma cikata da adu’a cike da karfin gwiwa ta kira baba suka gaisa ya bawa mama da yanzu taji sauki sossai sallama kawai suke jira wadda shima suna zaton nan da sati, yadda ta nemi shawaran umma haka ta nemi na Mama itama sossai ta bata goyon baya suna waya da maman ya fito ya shirya cikin suit navy blue masu bala’in kyau da tsada yayi wanka da turare fuskan nan a murtuke da sauri tayi sallama da mama ganin ya nufi kofa.

Ta sha gabanshi tare da langwa’bar da kai cikin kashe murya tace “zaujiii ka rufamin asiri kar ka fita kana mai fushi da ni, na tuba” se hawaye sharr abunda ta san baze ta’ba iya Jura ba kenan, ajiyar zuciya ya sauke kan yace “Hayatii Ai kece” rungumeshi tayi cikin shesheka tace “don nayi abinda yake daidai? Hamna fah ba ita tayi maka laifi ba zugawar mahaifiyarta ne da yanzu bata duniyar ma kaga kenan duniya ba bakin komai yake ba, kuma ba matabbata bane”

Zameta yayi yace “Hayatee bazan iya son wata a yanzu bayan ke ba bazan iya ba, karkisa na zama cikin masu tashi da shanyayyen ‘barin jiki a ranar gobe kiyama sbd rashin adalci tsakanin mata na biyu karkiyi please” yana kai nan yayi pecking d’inta a goshi ya zagayeta ya fice ajiyar zuciya ta sauke hawaye na silalo mata, Allah ya gani in tace maganan nan kad’ai da yanzu akeyi baya tunzura mata rai da kishi tayi karya amma ya zatayi? Be dace ba sam ace be mayar da Hamna ba tana er uwarshi, ko don farin cikin ummu zatayi hakan bare kuma akwai lada na musamman da ze jiraye ta ranar gobe kiyama.

Lalu’ban numbern Abba tayi ta kira ringing biyu ya d’aga cikin ladabi tace “Abba barka da rana” yace “yauwa mamana ya kuke ya bakunta?” Tace “Lafiya kalau Abba ya aiki?” Yace “Alhamdulillah” cikin sanyin murya tace “Abba alfarma nake nema” yace “tooh Alfarmar mece? Allah ya sa be fi karfina ba” ajiyar zuciya ta sauke muryanta na rawa tace “Abba Auren Hamma Abdulraheem da Anty Hamna nake so a mayar ba tare da saninshi ba” Shiru yayi cike da al’ajabi seda ya kwashe mintuna kan yace “me yasa kike so Hamna ta koma d’akinta saudah?”.

A hankali tace “Abba da hamma da Anty Hamna duk d’aya suke a wurinku na san kuma baku so sakin da ya mata ba dukda akwai laifinta dayawa a abubuwan da suka faru, Abba na tabbatar zuwa yanzu tayi nadamar duk wani abinda ta aikata na san ummu zata fi kowa farin cikin komuwan auren nan, Abba Ina so ya mayar da Hamna ta sanadiyata watakila Allah ubangiji ya yafe min wasu manyan laifukana da ban san dasu ba”.

Ta karashe tana share hawayen da yake gangaro mata, Shiru Abba yayi Tabbas tayi gaskiya sun sha zama da modibbo da mai martaba akan yadda zasu sa Abdulraheem ya maida Hamna tsoro suke sbd baud’add’en halinshi kar ya karasa sakin kowa ya huta, amma se gashi ita Iman wacce ta gaje sunanta ta nemi komen auren da kanta, cikin sanyin murya yace “Toh Saudah zan duba lamarin zamuyi shawara da mai martaba, duk yadda mukayi zakiji”.

Sallama sukayi ta kashe wayan tare da mikewa ta fad’a wanka tana iya yinta don kokarin kauda wani damuwan kishi a ranta musamman In ta tuna ita fa tazo ta samu Hamna a gidan be kamata tayi farin ciki ba don sun rabu, tana fitowa ta shirya cikin high-waist skirt dark blue na kanti me fad’i sossai ta d’auko hill black ta saka ta saka blue black top me dogon hannu se ta rataya scarf black a saman kanta bayan tayi parking gashinta pony tail, black handbag karami ta d’auka tana shirin fita taji wayanta na ringing dubawa tayi seda gabanta ya fad’i ganin me martaba, komawa tayi a sanyaye ta zauna kan ta d’aga.

Gaisawa sukayi a mutunce cikin yanayinshi na sarauta yace “Saudah babanku ya kirani yake fad’amin wani magana wadda ya fito daga gareki, kin kuwa tabbatar maganan nan zaki iya?” Murmushi me ciwo tayi cikin ladabi tace “Allah ya kara tsawon rai, zan iya In Shaa Allahu kawai a d’aura ta taho zan shawo kanshi In shaa Allah” Ajiyar zuciya me martaba ya sauke kan yace “toh shikenan za’a mayar da auren tare dana fatima” dib dib dib haka taji zuciyarta na bugawa ta de daure sukayi sallama kan ta mike ta fito driver ya d’auketa se cikin makaranta.

Basu had’u ba har ta taso tana shigowa gida wanka tayi ta saka wani sky blue half gown me hannun vest tana son ire iren shigen sbd ita koyaya tana son ta jita sake ba nauyin komai, a parlor ta zauna tana gyaran nails d’inta a lokaci d’aya tana jin karatu a wayanta, ta jima zaune nan kan taji turo kofanshi bakinshi d’auke da sallama da sauri ta mike ta nufeshi ya bud’e mata hannu ta fad’a suka rungume juna a tare suka sauke ajiyar zuciya cikin kasa da murya yace “I miss you hayatee” tace “miss you too zaujii, Sannu da dawowa” jan hannunshi tayi zuwa d’akinsu ta tayashi cire kaya kan ta jashi zuwa toilet akan yayi wanka karshe tare sukayi wankan bayan sun gama soyewarsu a toilet d’in.




🖤Gureenjo🖤


🥀NOOR IMAN🥀

*Fatima Muhammad Gurin*
*Gureenjo6763 on wattpad*

*`Yar Mutan Adamawa*

💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)

*056*

END

Bayan wattanni.

Zuwa yanzu an jima da sallaman mama taji sauki sossai se d’an abinda baza’a rasa ba na Ciwon sugar da take fama dashi, auren zahra ya kara matsowa Don yanzu haka saura sati biyu, ta ‘bangaren soyayyarsu da Abdulraheem kuwa ba abinda ya ragu se ma abinda ya karu sbd bayyanar ciki a jikinta kulan da yake bata na safe daban na rana daban na dare daban, ta tabbatar da yana da dama ko kuda baze yarda ya sauka a jikinta ba bare har tayi wani ciwo.

Kaman yau zaune take tayi nare nare tana cin grilled fish hankalinta kwance tanayi tana kallon wani film a tashar Bollywood, ringing d’in wayanta ne ya d’auke mata hankali daga kan kallon da takeyi ta duba wayan se taga ummu ce ke kira, da sauri tayi picking tare da sawa a handsfree cikin sabo da so tace “ummun mu Barka da warhaka” ummu tace “Yauwa daughter ya kk? Ya jikin?” A kunyace tace “Da sauki ummu am na warke, ya shirin buki?” Ummu tace “za de ki warke daughter, shirin buki gashinan munayi zakuyi missing bukin autana” Tace “wallahi kuma banji daad’i ba dama muna hutu” ummu tace “haka Allah ya kaddaro, kina de cin abinci yadda ya kamata kam?” Tace “eh......” katseta yayi da cewa “Ina kuwa take ci ummu kullum abincin kenan gasashen kifi na rasa yadda zanyi da ita ta dinga cin abincin” ta tsorata Don sam bataji shigowarshi ba hakan yasa ta harareshi.

Murmushi yayi jin ummu na cewa “Ina zata samu abinda zata ci a garin masu jajayen kunnennan bari ma kaji bazan bari ta haihu chan ba kula ba daga ta shiga watan haihuwa zata dawo In kaga dama kayi zamanka tunda lokacin Hamna na chan” murmushinshine ya d’auke jin magannan ummu cikin rashin fahimta yace “wani irin hamna na nan ummu?” Ya karasa yana kallonta kauda kai tayi cike da rashin gaskiya ranshi ne yaji ya fara ‘baci, cikin sanyin murya ummu tace “daughter ki kula da kanki se anjima” ta kashe wayan, duk shiru sukayi na mintuna kan ya daure yace “Saudah me hakan yake nufi?” Nan ma Shiru tayi cikin d’aga murya yace “dake nake!!!” Razana tayi don rabon da ya mata tsawa haka tun ranan a masarautar modibbo Adama.

Cikin sanyin murya tace “I’m sorry za’a mayar da aurenku da Hamna randa za’a d’aura na zahra” kankance ido yayi yana me mikewa har ze yi magana se kuma ya fasa ya wuce a zuciye zuwa d’ayan d’akin dake gidan kwanciya yayi ranshi na suya wai sun fishi sanin abinda yake so ne da zasu yanke mishi hukunci ba tare da saninshi ba? Danne ‘bacin ran yayi ta kokarin yi har bacci yayi awon gaba dashi.

Ranan haka suka yini be ce mata ci kanki ba sede ya fita ya sayo mata gasashen kifinta me zafi yazo ya ajiye mata, ze fita kenan tayi hanzarin rumgumeshi ta baya cikin kuka tace “kayi hakuri abinda ya dace ne nayi” in tana bashi hakurin nan ranshi kara suya yake yadda ya tsani hamna da uwarta ace wai za’a mayar mishi da aurenta taya ze yi adalci a tsakaninsu? Zame jikinshi yayi cikin son danne ‘bacin ranshi yace “abinda ya dace? Abinda fah ya dace kikace? Kece zaki zauna da ita In ta dawon? Kece zaki sauke mata duk wani hakkin da miji ze bata? Me yasa kika aikata abinda tun farko na haneki akai for the first time a rayuwanmu hayatee kin tsallake umarni da gargad’in da na miki aka gayamiki don Ina sonki se ya kasance duk abinda kike so shi zan yi? Bana sonta na gayamiki bana sonta......” Shiru yayi jin kukanta ya fara hawa kanshi yayi yawan da har numfashinta na fisgewa dama cikin ya bata wahala sossai.

Kan ya kuma wani maganan ta sume mishi a rud’e ya d’auketa se asibiti da hanzari aka kar’beta doctors biyu suka rufu kanta shi kuwa se zirga zirga yake yana jin tsanan hamna na kara yawa a ranshi gashi zata mishi sanadiyar yaro tunda ita duk zamansu bata bashi ba, wadda zata bashin kuma tana kokarin shiga tsakaninsu awansu biyu a kanta ta farfad’o likitan ya fito yana fad’an yace cikin nan lalla’bashi ya kamata ayi Don har yanzu barazanar zubewa yake amma sun ki ji ana barinta shiga damuwa to ya kuskura ta kuma fad’uwa haka tabbas zasuyi asarar babyn.

Da Ohk kawai ya amsawa dr ya shiga kanta ya zauna tare da rike hannunta bacci take cikin kwanciyar hankali shima ya kwantar da kanshi daidai cikinta ya jima a haka kan bacci ya fara fisganshi cikin dare yaji ana shafa kanshi a hankali, d’ago kai yayi ya kalleta hawaye na gangara a idanunta tace “I’m so sorry zaujii” mikewa yayi ya hau gadon tare da janyota jikinshi cikin kasa da murya yace “I’m sorry too hayatee” Tace “ka yafemin kaji ba wai kishinka ne banayi ba hakan shine daidai shiyasa nake son tayaka abinda yake daidai....” katseta yayi da cewa “shikenan ya isa maganan nan, na amince ta koma d’akinta sede fa a Nigeria zatayi rayuwanta ban yadda ta taka kafanta ko wani kasa ba” Shiru iman tayi hawaye na gangaro mata a haka de ya lalla’bata sukayi bacci.

Washegari aka sallameta satin bukin na zagayowa ya fara had’a kayanshi tsab ya had’e kayanshi a akwati en daidai tana dawowa daga school ta samu akwatin ajiye da mamaki ta janye runguman da ya mata tana kallon akwatin tace “wannan akwatinfa zaujii?” Cikin rashin kula yace “Nigeria zani za’ayi aure ango baya kusa ne?” Dipp haka fara’arta ya d’auke da kyar ta iya cewa “Yaushe zaka wuce?” Yace “gobe flight d’in dare zan bi” kai kawai ta gyad’a ta ajiye jakanta ta shige toilet a chan ta zauna ta sha kuka tana tunanin anya, dama haka maza suke? Ji fah yadda ya nuna mata baya son auren amma yanzu shine da azar’ba’bin zuwa bayan da na zahra ma be yi niyyan zuwa ba.

Seda ta gama shan kukanta kan tayi wanka ta fito yana zaune yana danne danne a system d’inshi hannu ya mika mata cikin sanyi ta make kafad’a juyowa yayi ya zuba mata ido har ta gama shiryawa cikin kaya marasa nauyi cikinta ya d’an fito a gaban kayan kad’an Haka, Bayan ta gama fesa turarenshi da yanzu take so bata son nata ta juyo ta kalleshi tare da murmusawa tace “kallon fah?” Yace “na soyayya ne” yana d’age mata gira murmushi kawai tayi ta karaso ta kama hannun da yake mika mata ta fad’a jikinshi ya gyara mata kwanciyan da kyau akan kirjinshi a sanyaye yace “me yasa kikayi kuka?” Da sauri ta kalleshi yace “yes tun fitowanki hayatee idanunki suka gayamin haka, ashe har yanzu akwai abinda ze saka ki kuka da damuwa hayatee? Na d’auka duk matsalanki sun kau

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login