Follow us on social media
Showing 81001 words to 84000 words out of 131683 words
Chapter 28 - NOOR IMAN Yar Baƙin Ciki BY Fatima Muhammad Gurin
bud'e mata ta shiga tana ci gaba da hawaye, shima zagayawa yayi ya shiga se ga Anty rahama itama ta shige baya suka fice.
Karatun qur'ani yayi playing suratul A'araf sheikh Abdulrahman sudais ke rero karatun, saurara take tana jin tension d'inta na sanyaya amma fah hawayen be dakata da zuba ba sede ba magana ko uhm bata iya cewa har suka isa hawaye take, shima gabad'aya yayi kalan tausayi zafin hawayen yakeji har ranshi amma ya ya iya? Dole tayi kukan wannan rashi da ze iya da ya tayata.
Mutanen da ta gani jibgi a kofan gidansu yasa kukanta fara fita da shesheka, fita yayi ya zagaya ya bud'e mata tare da rusunawa kad'an yace "kukan nan be isa haka ba saudah? Kin san fa ba lafiyace ta isheki ba kema, kiyi hakuri ki kar'bi wannan jarabawar hannu bibbiyu ko kin manta Allahn da ya bamu ya fi mu sonta? Lokacinta ne yayi Muma In tamu tazo ko munki ko mun so se mun je gareshi so why not kiyi ta mata adu'ar dacewa da rahamar ubangiji akan wannan kukan? Ko kin manta kuka karin zunubi da nauyi ne ga mamaci?".
Tafin hannunta ta sa ta share fuskanta tana gyad'a mishi kai, mikewa yayi ya kama hannunta Anty rahama da itama hawayen tausayin Iman d'in ya zubo mata ta bi bayansu, da sannu da sannu suka shige cikin gidan, mata ne ko ta ina hakan ya sa shi had'a hannunta da Anty rahama shi kuma ya ja baya, en uwa ne ko ta Ina kowa hawaye da kukan wannan rashi yake Mama mutum ce wacce ta chanchanci ayi kukan rashinta.
Ana ganin Iman kuwa aka fara Allah sarki Allah sarki wadda hakan ya kara sa Iman kuka, d'akin baba aka nuna mata alamu chan gawan maman yake, da sassarfa ta karasa d'akin tare da zubewa gaban gawan da aka mishi komai saura sallah da kaiwa makwanci, kawai se ta rungumeta ta kuma fashewa da sabon kuka "Mama dan Allah ki tashi na san baza ki mutu ki barni ni d'aya a duniyar nan ba, mama kin manta kince In Shaa Allahu se kinga jikokina kan mutuwanki, kin manta kinci burin yi min wankan jego da alkawarin ko Ina So ko bana so se naci tuwon dawa da kunun tsamiya? Mama dan Allah ki tashi bazan iya ci gaba da rayuwa ba ke ba In wani abin ya kara faruwa da ni fah? Mama kina so in mutu nima? Na san bakya so ki tashi dan Allah mamaaaa.....".
Wani irin kuka me ban tausayi take, Baba dake gefe se share hawaye yake yayinda Umma tayi saurin ficewa tana ci gaba da kuka, kaman ance saurara taji zuciyar Maman na bugawa kasa kasa, kunnenta ta kara mannawa Ai ko de ba hasashe bane da gaske ne.
Chak kukanta ya tsaya ta d'ago ta kalli baba tace "baba Mama bata mutu ba wallahi tana numfashi" girgiza kai baba yayi yace "kiyi hakuri Mamana, ke aka wa rashi dole hankalinki yafi na kowa d'agawa, na sa...." katseshi tayi tace "baba ba fa wai rud'ewa bane ko wani abu wallahi naji tana numfashi zo ka sa kunnenka kirjinta kaji yana bugawa" dukawa Anty rahama tayi ta dafa kafad'anta tana cewa "haba Iman kiyi tawakkali mana ko kin ta'ba ji Ance wadda ya mutu ya dawo ne?".
Wasu maza ne suka shigo sun kai goma mikewa baba yayi yana cewa "lokacin sallahn yayi ko?" Kai suka gyad'a, a rud'e Iman ta d'ago tana cewa "baba na rantse ina cikin hankalina Mama bata mutu ba zuciyarta na bugawa karku kashe min ita dan Allah".
"Muje kawai gigitan mutuwanne ya sa ta fita hankalinta Allah ya baki hakurin rashi Don ke aka yiwa" bappa yushe'u ya fad'a, biyo bayansu tayi Anty rahama ta riketa da karfi ta fisge har tana fad'uwa dayake ita kanta ba wani karfin ne da ita ba, da gudu ta biyosu tana fitowa tayi wani wawan tuntu'be tare da hantsilawa kad'an ya rage ta kai kasa taji an riketa.
'Dagowa tayi se taga shine cikin kuka tace "yauwa kai kam na san zaka yarda dani kazo muje Hamma kaji, wallahi naji zuciyar Mama na bugawa bata mutu ba sukace ta mutu, ka yarda dani wallahi da kunnena naji" kallonta yayi cikin tausayawa har ze ce a'a kuma se ya tuna tace ta san shi kad'ai ze yarda da ita idan yaki yarda da ita fa? She will be shattered amma kuma idan suka je ba gaskiya taji ba fa? Same thing.
Se be ki ba ya kama hannunta suka nufi su baba, Allah ya taimaka sauban ya biyosu hakan ya sa yayi mishi hannu ya taho suka karasa tare kallon baba yayi yace "baba kayi hakuri ka bari Sauban ya duba Mama I think gaskiya Saudah take fad'a" har ze Musa Iman ta zube kasa tace "dan girman mahallicinmu baba" Kai ya gyad'a sauban ya duka ya fara bud'e taburman kan ya d'an kwance likkafanin ya sa hannu ya kamo wrist d'inta na mintuna biyu duk sun daskare kowa na jiran yaji me ze ce musamman Iman da Abdul, da ya gaji da kukan matar tashi yana fata Mama bata mutu ba ko hankalinta ze kwanta.
Wani murmushi sauban ya saki yana mikewa yace "da sauran numfashinta lokacinta be yi ba muna bukatar isa asibiti da gaggawa" zubewa Iman tayi kasa tana mika godiyarta ga Allah ta hanyar sujudushukur kan ta mike ta rungume Abdul tana ta maimaita "Alhamdulillah na gode, na gode".
Breaking hug d'in yayi sanin da mutane, a take aka maida Mama cikin gida kowa matan se tambayar abinda ke faruwa sukeyi baba ne ke basu amsa da "bata mutu ba, ikon Allah" kawai suna zuwa aka cire mata likkafanin aka sanya mata kaya suka d'auketa se asibiti, ana isa akayi da ita ICU kaidarshi kuwa ba me shiga kwata kwata se doctors, hakan ya sa Malabo kama hannun Iman zuwa room d'inta har kan gado ya kai ta ta kwanta kan ya zauna gefenta yana shafa kumatunta yace "Alhamdulillah Allah shine abin godiya, lokacin mama be kai ga yi ba tukuna, yanzu hankalinki ya kwanta?" Kai ta gyad'a tana sake murmushi yace "masha Allah, to yi bacci ko zaki samu natsuwar hankali Ohk?" Gyad'a kai tayi tare da lumshe ido kumatun ya ci gaba da shafawa a hankali tun tana jinshi har bacci yayi awon gaba da ita.
Kallon su Anty kalthum yayi yace "sannunku fah" murmushi sukayi Anty rahama tace "Ai kai ne da sannu da da gaske ne maman ta rasu da Allah kad'ai ya san halin da Iman Zata shiga ciki idan ta wayi gari taga ba maman" Anty kalthum tace "Ai dole Anty kin manta shakuwa da son dake tsakaninsu?" Ze yi magana kenan aka turo kofa, family d'in Iman ne abin mamaki suka dinga shigowa suna dubata duk wadda ya zo da niyyan duba Mama yaji baza'a barshi shiga ba se baba ya fad'a musu Ai Iman ma ba lafiya tana asibitin se kuwa kaga sun shigo sun dubata.
Sossai Abin yayiwa Abdul daad'i ba kad'an ba yayi alkawari kuwa tana tashi se ya fad'a mata waenda suka zo duba ta d'aya bayan d'aya Don kowa seda ya tambayi sunanshi da alakarsu da Iman sam be manta ba suna cikin kanshi ras abinda be Saba ba, murmushi ya saki yana furta "Anything for my hayateee" yayi maganan yana kallon Anty rahama dake mishi kallon yaushe kuma ka zama haka.
Murmushi sukayi, Anty kalthum ta musu sallama ta tafi da tabbacin zata turo driver da abincin dare, godiya yayi mata tana dariya tace "haba hamma se kace bare nayiwa? Ai ko ba aure tsakaninku Iman matsayin zarah take da shi wurina" ta'be baki yayi kan yace "to maganatun ummu ke da Hafeez kam ban san waye gwara ba, na sallameki se da safe" Anty rahama tace "Da yake ta gama maka abinda kake bukata yau ko? Ai dole ka sallameta" harara ya sakarwa Anty rahama itama kuwa ba 'bata lokaci ta rama, ficewa Anty kalthum tayi tana murmushi kaman Anty rahama ta san abinda ke zuciyarta kenan tana tsoron furtawa ya ci mata.
Se bayan isha Iman ta farka yana nan zaune gefenta yana aikin kallonta d'akin ba kowa se su biyu, tun da akayi magrib Anty rahama ta tafi akan bayan isha zata turo baaaba, lumshe idanunta tayi ta kuma bud'ewa cikin nashi, murmushi ya sakar mata itama ta mayar mishi "sannu" ya furta, tace "yauwa, wai nayi bacci sossai gashi duk salloli sun wuceni" yace "dab magrib dr Ameera ta shigo na roke ta ta kara miki alluran bacci cikin drib da tayi niyan sa miki that's why kikayi baccin sossai".
Kai ta gyad'a tana sauka tace "bari Inyi alwala" da sauri ya mike yana kamata yace "kula karki illata min kanki plz, muje In raka ki na san jikinki har yanzu beyi karfi ba" seda suka fara tafiya tace "da kayi zamanka Allah zan iya" yace "you are welcome" siriryar dariya ta sake wadda ya sakashi murmushi seda ya kaita toilet d'in kan ya fito ya zauna, bayan tayi abinda zatayi tayo alwala tana fitowa ya mike ya rike mata hannu suka karasa kan taburma a kan darduma ta tsaya yace "zaki kuwa iya a tsaye?".
Tayi murmushi tace "na fa ji sauki Hamma zan iya" yana murmushi yace "to Alhamdulillah" tare da mika mata khimar sakawa tayi ta tada sallah ya koma kujera ya zauna, la'asar, magrib and isha tayi duk ta gaji ta zauna tana nike kafafunta, chak ya mike ya nufi basket da tana sallah drivern Anty kalthum ya kawo ya bud'e ya zuba mata abinci a plate dafaffen doya ne da egg sauce se pepper soup na cow tail, gyara zama tayi ya d'iba ya fara kai mata ba musu ta bud'e baki ya dinga feeding d'inta har ta koshi tayi nak.
Ganin ya ajiye spoon d'in Don kau da kanta da tayi yasa tayi saurin d'aukawa ta d'ibo kallonta yayi ta kauda kai tace "na san baka samu natsuwar cin abinci ba kaima please bud'e nima inyi feeding d'inka" for the first time tun wayonshi da wata mace zatayi feeding d'inshi, abinda ya tsana kenan Don yanzu ko ummu be yi tunanin ze yarda ta bashi abinci a baki ba amma se gashi hankali kwance yake kar'ban abinci daga hannun hayateenshi.
Kallonta kawai yake kaman ya samu Tv ita kuwa ta ki ko kallonshi abincin kawai take bashi idanunta na kan plate da spoon d'in hannunta, hannunta ya rike ta kalleshi yace "Alhamdulillah am full" a tare suka ajiye spoon d'in hannunsu cikin na juna, cire mata khimar d'in jikinta yayi kan ya mike da ita zuwa kan gadon asibitin pillow ya sa mata a bayanta ta jingina ya matsa jikinta sossai dukar da kai tayi zuciyarta na bugawa "kin san yau suwa suka zo dubaki?" Kai ta girgiza mishi, nan ya fara fad'a mata in ya kira sunan ya manta dangantakarsu se ya wani taune lips yana buga goshinshi wadda hakan ke matukan burgeta tana murmushi zata tuna mishi se ya waro ido ya had'a hannu ya buga yace "yesss" se kuma ya shagwa'be mata fuska yace "ni bana so ki barni In tuna kayana da kaina!!" Murmushi sossai take sakar mishi har fararan hakwaranta da wushiryanta su bayyana.
Wadda In hakan ya faru shagala yake da kallonta In hakan ya faru, haka sukayi a karshen lissafin nashi dariya take mishi sossai jin yadda ya kira Nizziya er bappa yushe'u da Nazza'u ne ko nizzaya wadda hakan ya bata dariya sossai, yadda ma yayi pronouncing d'in abin dariya ne bare kaga yadda yake wani 'bata fuska kaman an mishi dole, shagala yayi da kallonta a hankali ya kai hannunshi kan dimple d'inta ya shafa.
Kallonshi tayi shima kuwa dama ya zuba mata ido, zuciyarshi ne ke luguden bugawa sbd tunanin maganasu da Anty rahama dake dawo mishi, har kokon ranshi tsoro yake kar maganan ya tabbatu, yana tsoron sata cikin ciwo da damuwa, amma ya iya dole ya gwada don kawar da zargin zukatansu dashi da er uwarshi, a hankali yayi leaning suna kallon juna cikin ido ya d'aura bakinshi kan nata ya fara kissing d'inta a hankali.
Lumshe ido tayi jin hannunshi jikinta yanayi ne kawai ba Don wai ya ji daad'i ba a'a sam har rawa jikinshi yake sbd fargaban abinda ze biyo baya, kaman kuwa jira ciwo yake nan fah ta fara ja tana jan numfashinta sama, da sauri ya d'agota ya manna ta jikinshi yana jin yadda take kokuwa da numfashinta, zazzafan Hawaye ne ya gangaro kan kumatunshi kasan makoshi yake furta "innalillahi wainna ilaihi rajiun!!!!" Hannunshi ya mika ya danna telephone d'in gefen gadon ba'ayi mintuna uku ba nurses suka shigo ganin halin da take ciki yasa d'aya fita da gudu ta kira doctor, seda dr. Amira tazo kan yayi karfin halin sa'buleta jikinshi ya d'aura ta kan gadon jiki a sanyaye ya fita daga d'akin don baze iya jurar ganin irin alluran da za'a mata ba, jijiyoyin jikinshi gabad'aya sun tashi rad'a rad'a fuskanshi yayi ja ja jir tsabar 'bacin rai da damuwa, ko had'a ido aka ce kayi dashi baza ka iya ba, safa da marwa yakeyi a bakin kofan yana tunanin who the hell is after this!!!!!!!!
*Readers How far😉*
🖤Gureenjo🖤
🥀NOOR IMAN🥀
*Fatima Muhammad Gurin*
*Gureenjo6763 on Wattpad*
*'Yar Mutan Adamawa*
💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)
*ban san me zance gareku ba en Annur hausa novels da kuma Noor Iman fans, na gode sossai da adu'o'inku gareni ga wanna naku ne kuyi yadda kuke so dashi, en Wattpad Ina me baku hakuri plz ban samu fad'a muku uzurina kan lokaci ba rashin lafiya nayi ta Ulcer wadda hakan yayi sanadiyar rashin jina kwana biyu, kuyi hakuri.*
*039*
Iska me zafi yake aikin fesarwa daga bakinshi yana safa da marwa cikin tsantsan nazari da tunani, damuwa kuwa har ya rasa adadin da yake jinshi, hankalinshi In yayi dubu ya tashi bayan duk abinda aka mata a baya ashe har yanzu ba'a barta ba? Ta Ina ma ze fara da wannan jinyan nata? Fitowar dr Ameerah ne ya maido hankalinshi kanta tana share gumi tace "Anya dakta?" Murmushin karfin hali yayi yace "kar ki damu na gano matsalanta zaki iya bamu sallama ko yau In Shaa Allahu ciwon baze sake tashi ba".
Tace "za'ayi haka kuwa?" Yace "yes of course" Tace "shikenan bari inje office in rubuto muku" Kai kawai ya iya gyad'a mata yana nan tsaye be motsa ba bare yayi niyyan shiga d'akin har taje ta kawo musu takardar cikin tausayawa ta kalleshi zatayi magana yayi saurin sake murmushi yace "dr har kin kawo?" Tace "eh gashinan plz a kiyaye" dayake ba yarinya bace yasa yace "In Shaa Allahu thanks" ya kar'ba direct ya wuce yayi Settling bills d'insu na kwanakin da sukayi, daga nan ICU yayi dr dake duba Mama ya nema.
Aka nuna mishi office d'inshi a bakin kofan suka had'u da sauban da mamaki yace "har yanzu dama kana nan baka tafi ba?" Sauban yace "a'a na tsaya nan d'inne sbd hankalinka ya karkata kan Iman ka san itama tana bukatar kulawa sossai" Kai Abdul ya gyad'a tare da cewa "an ma yi discharging d'inmu yanzu zamu tafi" da mamaki yace "har ta warke?" Kai kawai Abdul ya gyad'a Don baze iya fad'awa Sauban d'in sirrinsu ba Don hakan kaman wani Sirri ne na rayuwansu shi da Iman kawai Anty rahama kad'ai ze iya fad'awa Don suyi shawara.
Murmushi sauban yayi ba Don ya yarda ba yace "Toh Alhamdulillah, dr mukhtar yayiwa Mama duk tests d'in da ya kamata daga yau har bayan two weeks ba wadda ze iya shiga kanta se an san wani irin cuta ce da ita" kai Abdul ya gyad'a yace "Ohk yanzu zan tafi da Iman gida bazan samu zuwa biyan kud'ad'en ba bari In turo maka, ko wani nurse ne se ka sa ya biya please" sauban yace "Ohk ba matsala" a take Abdul ya mishi transfern manyan kud'ad'e ya mishi godiya kan sukayi sallama suka yi hanyoyinsu.
'Dakin da Iman take ya shiga a zaune ya ganta ita kad'ai ta buga tagumi cikin tunani gadon ya karasa har ya zauna bata sani ba, hannu ya sa ya janye tagumin nata kallonshi tayi hawayen idanunta ya gangaro hakan ya sashi gane ta fahimci abinda ke faruwa kenan, matsawa yayi gabanta sossai sai kawai ta kifa kanta jikinshi ta fashe da kuka mai sauti, lumshe ido yayi yana shafa bayanta a hankali shima kaman yayi mata kukan.
"Ni kam anya Ina da rabon farin ciki kuwa a rayuwata? Me yasa ne? Upon all people of this world a rasa wacce za'a sa gaba da mugayen manufa se ni? Me yasa se ni hamma? Me yasa?" Cikin kasa da murya yace "kaddarace ki daina irin waennan kalaman kar kije kiyi sa'bo watarana, ko kin manta kar'ban kaddara me kyau ko marar kyau yana daga cikin cika cikan imani? Kika san ko ta wannan hanyan ki shiga aljannah? Ki kara hakuri watarana komai me wucewane".
Cikin rawar murya tace "kaima rabuwa zakayi dani ko?.... sbd.. bani da anfani a gareka... da ni da photo duk d'aya ne macen da baza ta iya ta'bukawa mijinta komai ba bata da anfani a ga....." tattausan hannunshi ya d'aura kan lips d'inta yace cikin taushin murya "kinfi kowacce mace yanzu anfani a rayuwata hayatee bayan ummu...." da sauri ta d'ago tana kallonshi idanunshi ya narkar cikin nata cikin tabbatarwa yace "yes ina so ki cire ran rabuwar aurenmu hayatee, auren mu yafi na zo'be karfi ko da bana kallonki muryarki kawai zanji zan iya rayuwa a haka ya wadaceni har gaban Abada".
Jikinshi ta koma tayi lub ya ci gaba "bare duk wani halin da zaki shiga hayatee se na fiki tashin hankali sau dubu fiye da naki, zan tsaya miki ko da ba ni zan anfana da lafiyanki ba har se na tabbatar kin