Follow us on social media

Showing 102001 words to 105000 words out of 131683 words

Chapter 35 - NOOR IMAN Yar Baƙin Ciki BY Fatima Muhammad Gurin

a cikin jirgi kan ya kyalesu bayan ya tabbatarwa baba in sun sauka su fito kawai zasuga dogarai sunzo to su musu magana su fad'amusu su suka zo d'auka, baba na ta mishi godiya ya wuce, baba da d'an iliminshi ne ya karasa musu abinda ba'a rasa ba cikin ikon Allah suka iso lafiya aiko suka samu dogarawa biyu tsaye karasawa garesu baba yayi ya musu sallama suka amsa "ku ne Abdulraheem ya turo d'aukanmu ko?" Nan suka sake musu fuska suna gyad'a kai da sauri suka bud'e musu mota suka shiga.

Ja sukayi suka fito basu yi fada ba direct fufore sukayi, cikin lokaci kankani suka isa ita umma gabanta se fad'uwa yake ko me suka zo yi nan ta de san ba lafiya ba ko magana ta kasa yiwa baba har suka iso, Abdul suka gani tsaye bakin get yana jiransu da fara'a ya tarbesu dogaran suka d'auki kayan zuwa ciki yayinda ya musu iso zuwa parlorn baba fufore tsoho me ran karfe.

Suna zama ummu ta shigo parlorn da sallama tana kallon Abdul ta had'e rai dama ta san be wuce shi bane ze kawo kararta har baba ya mata kiran gaggawa haka, a kasa ta zauna ta gaida baban ya mata Sannu da zuwa yana kare mata kallo tabbas zargin su Abdul d'inne ya tabbata kanta Don daga ganinta ya gane ba cikin natsuwanta take ba, a mutunce suka gaisa da su umman iman.

Baba yayi gyaran murya yace "Rashida shiga da bakuwarmu wurin hajja ku ci abinci ku huta tukun In ganku gabad'aya" amsawa tayi cikin ladabi ta mike umma ma ta mike suka shige cikin gida, abinci aka kawowa baba shima amma dukkansu suka ci.

Bayan gaisuwa hajja ta gabatar musu da abinci a ciki ma suka ci seda sukayi azahar kan suka dawo parlorn baba lokacin suma suka dawo daga massallaci, bayan sun zauna baba ya tsiyaya ruwan galon d'inshi a cup ya mikawa ummu yace "amshi sha rashida" kar'ba tayi ta Sha tana gama Shaa se murd'awan ciki nan ta kama cikin da karfi se Amai wani irin bakin amai takeyi cikin azaba da sauri Malabo ya karasa ya kama kafad'unta a rud'e yana ambatan "ummu" hannunshi ta kama taci gaba da kakari har da Hawaye tausayin mamanshi yasa idanunshi rinewa a take.

Baba da umma kam se kallon ikon Allah suke, ta kai mintuna biyar tana aman kan ya tsaya bakin kwayar idanunta suka juya zuwa farare wasu ruwan baba ya kuma d'iba ya watsa mata tayi firgigit ta mike kasa a sume hawaye ne ya gangarowa malabo akan kuncinshi da sauri ya share yana kawar da kanshi daga kan mahaifiyarshi ta jima a haka kan ta bud'e idanunta tana dafe kanta dake sarawa.

A hankali memory d'in abinda ta dingayi ya fara dawo mata tun ma kan auren yadda ta dingamishi har zuwa rana irin ta yau, hannunta dake rawa sossai ta d'ago ta d'aura akan bakinta hawaye na kwarara daga cikin idanunta tace "me nayi? Me na aikata Innalillahi wainna ilaihi rajiun Allah ya Allah" da sauri ta juyo tasa hannayenta kan cheeks d'in malabo tace "Ina take? Tana ina?" Yace "ummu wace? Hamna?" Tace "a'a saudah nake magana Noor Iman, wallahi ban san ya akayi ba ban sani ba Allah" ta fashe da kuka tana jingina da jikinshi kuka sossai tayi har seda umma tayi hawaye haka Abdul ma duk idanunshi sun rine.

Da kyar ya iya lallashinta tayi shiru baba ya dubi Umma yace "na dawo kanki, Ina so inji dalilin da yasa kika ki 'yarki kika tsangwami rayuwanta? Bana so ki min karya waraka zan nemarwa 'yarki daga wurin rabbil izzati, In baki taimaka mata yanzu ba you will regret it for ever sbd zata iya mutuwa a halin da take ciki yanzu, taimakonki kawai take bukata a yanzu In har ke kika haifeta da cikinki ki yiwa Allah ki fad'amin me ya faru?" Kuka umma ta saka Abdul yayi saurin sakin hannun ummu ya karasa gabanta ya duka yace "ki taimaki rayuwata dan Allah!!!" Ya fad'a muryanshi na rawa baba yace "dan Allah Aisha" kukanta ta karawa volume cikin rawar murya ta fara magana "Ina sonta Ina son 'yata dan Allah ka taimakeni kar ta rasa ranta zan fad'a".

Shesheka ta ja kan taci gaba "lokacin..... lokacin Ina da cikin Iman na wata shidda.............








                       🖤Gureenjo🖤


🥀NOOR IMAN🥀

*Fatima Muhammad Gurin*
*Gureenjo6763 on wattpad*

*'Yar Mutan Adamawa*

💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)

"My Meeroh this is for yhu, I love yhu so much, masoyiyar Stephen, demon da ohooo sorry fah🤣😅😅🤣🤣 Allah sarki Vampire diaries watcher ya zo please ya tayata kuka🤣😅😅😅*


*046*

"Akwai wani rana da babanta yayi tafiya bayan wata uku da aurenshi da mamansu kenan, amma gidanmu ba d'aya ba lokacin ya tafi da safe akan da yamma su hindatu zasu zo su tayani kwana, yayinda kamila zata je gidan mamansu, ban d'aura abinci ba se d'an makulashe da nayi taci se chan yamma likis na d'aura mana farar taliya da miya dama ina da miya na ajiye, bayan na dafa taliyar ta dafu na tsame ta to tafasashen ruwan ba tare da na tsaya ta huce ba na watsashi gabad'aya kuma da karfi magudanar ruwanmu da yake me girma sossai Ina watsawa ana kiran magrib so se na ajiye tukunyar na juya na rufe taliyar na d'au buta na zaga bayi seda na fito nayi noticing ashe duk abin nan da nakeyi ban rufe kaina ba a haka dae nayi alwala na shige d'akina ba wuta a d'akin sannan duhun dare be gama shigowa ba amma d'akin yayi wani irin duhu da ko tafin hannuna bana iya gani.

Lalu'ben inda zan samo torchi nake hannuna ya kai kan keken kwantar da yara da babanta ya saya don tanadin haihuwa a take na rike keken da kyau se jin kukan jinjiri nayi yana kuka da iyakar karfinshi kaman kaina ze rabe tsabar karan tayi yawa, kaman an had'a baki da en nepa suka kawo wuta cikin keken da kukan ke tashi na kalla, wani irin razanannen ihu na sake ina matsawa baya da sauri hannuna dafe da cikina, yaro ne a ciki namiji ne ko mace ban sani ba jikinshi daga kai har kafa kunan wuta ne yayi wani iri ba kyaun gani, idanunshi ba fari se bakin da ya rufe idanun gabad'aya bakinshi baki kirin har wani hucin bakin hayaki ke fita daga ciki, gashin kanshi rabi me tsawo baki har kan fuskanshi rabin kuma a aske tal, har Ina iya ganin karamin kahon dake 'bangare askakken.

Kuka na fara Ina neman kofan fita nan wutan d'akin ya fara d'aukewa da kawowa tuntu'be naci zan fad'i dafe kujera nayi ina dukawa, kuma d'ago kan da zanyi naga wata mace zaune akan plastic chair dake d'akin bayanta ta juyamin kanta kasa tana kuka gashinta a sake dayawa har kugunta faratunta zako zako dogaye bana ganin fuskanta da sauran jikinta abinda na iya gani kenan na sandara wani ihun kawai na fad'i sumammiya.

Ban san ya akayi ba nade ji kaman ana kiran sunana cikin mafarki amma da murya me amo da tsawa a firgice na tashi zaune, se naga wani rabi mutum rabi kwarangwal me girman jiki sossai da tsawo shima gashinshi kaman na matan nan me kuka a kan kujera faratunshi har sunfi nata halitta ne shi me muni da tsoratarwa har yau bana fatan sake ganin wanchan fuskan idanunshi wuta ke ci hancinshi na fitar da hayaki kaman ana kona karamin bola a take hayaki ya turnuke d'akin cikin tsawa yace "ke biladama me ya shigar dake gonata? Kin ko san waye ni?".

Cikin kuka nace "ban sani ba amma ko menene dan Allah kayi hakuri kuyi hakuri ban san me na muku ba" wani irin dariya me rugugi ya sake na minti biyu a take kuma ya had'e rai yace "tashiii!!!!!!" Jiki na rawa na mike na tsaya ya min nuni da gadon yaron "jinjirin d'ana me shekaru d'ari da biyar kika kone min da ruwan zafinki ba tare da kin mana magana mu matsa ko kin ambaci Allah ba da hakan ze hankarar damu!!! Kinga uwarshi nan Zulhaya'i tunda abin ya faru take kuka ko d'ago ido taki tayi!!! tun daga Birnin Sin aka tasoni sbd tashin hankali, Me kike tunanin zamu miki????? Me ya kamata ya zama hukuncinki? Don bazan ta'ba yafemiki ba". Cikin matsanancin tsawa yake maganan.

Zubewa nayi kasa Don bana fatan sake kallon fuskan wanchan yaron na aljani cikin kuka nace "ka taimakeni Don girman Allahn da ya hallicemu ka tausayawa d'an cikina ka yafemin dan Allah, kar ka min komai na tuba" kafewa yayi akan se fa na fad'amishi hukuncin da ze min cikin tsawa da barazana kawai yake magana, matarshi dake ta kuka ne ta d'ago ta kira sunanshi da ba zan iya cewa gashi ba, kallonta nayi da sauri na kawar da kai Ina kuka kawai ba tare da na tuna ambaton Allah ba me makon ruwan hawayen dake zuba a cikin idanunmu ita na jini takeyi zan iya cewa tafi mijin munin gabad'aya rayuwa na ranan da bazan ta'ba iya mantawa ba kenan Don naga tashin hankali iya tashin hankali.

Bud'ar bakin aljanar nan se ji nayi tace "ba zan ta'ba yafe mata ba sede In gindaya mata sharud'a ta za'ba kuma ta dena had'amu da Allah don bamu sanshi ba" tsawa mijin ya dakamin "kina ji ko????" Nace "eh naji..... naji" ba tare da aljanar ta kalli inda nake ba tace "na farko shine ki bani kyautar abinda ke cikinki kina haihuwa zanzo na d'auke kayana ko na d'aukeshi tun a ciki In raine ko ma menene a madadin kassara min d'a da kikayi....." Shiru tayi jin na kara karfin kuka na Ina girgiza kai hannuna dafe da cikina cikin tsawa tace "na biyu!!!!! In kasheki in kashe d'anki... ko erki, shine ze bawa ruhin d'ana da yanzu ya riga ya mutu salama" ban san sadda bakina ya furta "innalillahi wainna ilaihi rajiun ba" banga tasowar ko d'aya daga cikinsu ba se jin saukan mari nayi da yasa na dena ji na wucin gadi Ina dawowa hankali na naga wani shar'be'biyar wuka na yawo kan cikina kuma rungume cikin nayi cikin kuka".

Kuka ne yaci karfinta wadda hakan ya sa ta dakatawa Abdul kanshi na kasa ya kasa d'agowa shi kad'ai ya san me ke yawo kanshi yayinda baba da ummu ke hawaye ba abinda baba fufore ke yi se gyad'a kai, laifin be wuce na mu mutane bane dama yayi tunanin hakan Don basu cika shiga mutane ba tare da hujja ko dalili ba, ruwa baba ya d'auka ya bata ta kur'ba ta ajiye baba fufore kasa hakuri yayi ganin ta kuma yin Shiru yace "wanne kika za'ba ciki?".

Ci gaba tayi "Akwai na uku wadda shine na za'ba bayan na sha wahalansu, kaman dae yadda zan muku bayani yanzu... nace "na tuba!! Kuyi hakuri duk ciki ba wadda zan iya za'ba tsawa ta dakamin "ba'a katseni idan Ina magana..... na uku!!! Shine zaki haifamana ita bazamu kar'beta ba sannan kuma bazamu rabu da ita ba sede ke zaki tsaneta ta karfi da yaji se na rabaki da ita ko shi kaman yadda kika rabani da nawa d'an, kiyi mata tsanar da ze sa ta dinga zargin anya ke uwace? Ki mata tsanar da ko sau d'aya muka ga so ko tausayi cikin idanunki akanta zamuyi ajalinta har lahira ina miki rantsuwa da jinin d'ana markuzzz duk randa kika yi magana da ita na mintuna biyar se na kasheta har lahira da wukan da kike ganinshi gabanki.

Kallon wukan nayi cikin tunani na rashin natsuwa na amince da sharad'inta na uku dukda na san daga ni har 'yata ko d'ana da zan haifa zamuyi matukar wahala sbd ba uwar da zata haifi d'a a cikinta tace ta tsaneshi ko me ze mata kuwa, komai na duniyan nan da dalili sede akwai me karfi akwai kuma marar karfi na tabbatar nawa me karfin ne sbd ba uwar da zata so a kashe mata d'a ta dalilinta dukda ita tayi wahalan har zuwa kawowanshi duniya guilt baze barta ba, sannan dan Allah karkuga laifina a cikin wannan abun ni na san laifina d'aya ne, ba zan iya za'ban sharud'an farko guda biyun ba sbd duk ba na d'auka haka na d'auki na ukun sbd a ganina shine gwanda gwanda.

Sallaman su hindatu da saratu yasa aljanun 'bacewa 'bat ajiyar zuciya na sauke ina mikewa ashe har isha ya wuce da sauri na fito tsakar gidan dayake ba haske sossai se basu ga fuskana ba sannu da zuwa na musu tare da umartarsu da su isa bari nayo alwala shigewa sukayi ni kuma na d'au buta nayi alwala na wanke fuskana da kyau na dawo d'akin hindatu na aika ta had'o mana abincin ni bari inyi sallah, magrib da isha nayi se lokacin na samu natsuwar kaiwa Allah kuka na ya kawo min d'auki ya tsaremin abinda ke ciki na laifi kam na san nayi tun farko na kuskuren zubar da tafasashen ruwa da magriba.

Tun daga ranan ban sake ganinsu ba nayi ta adu'o'i Allah ya sa sun tafi kenan ba zasu kara shigomana rayuwa ba, kwanan babanta shidda ya dawo a lokacin su hindatu suka tattara suka koma gidajensu, har ga Allah nayi niyyan fad'awa babanta amma Ina bud'e baki se inga wannan wukan a daidai cikina yayinda mummunan hallitanta na tsaye jikin gini tana aikomin da harara me birkitar da hanjin ciki da manyan idanunta wadda suka fi kama da na ball.

A haka nake Shiru har cikin Iman ya kai haihuwa tun satin da zan haihun waennan aljanun ke zuwa tunamin da sharad'inmu har a cikin d'akin haihuwa kuwa hakan ya sa tsoron kar su kashemin ita yasa ko kallonta banyi ba, Allah ya taimakeni taimakon da har yau bazan ta'ba dena Jin daad'inshi ba kuma har gobe, ya d'aurawa mamansu sonta wadda nafi kowa jin daad'in hakan don na san ko me zan mata ze zo da sauki In tana da wata uwa kusa da ita.

Ban ta'ba bata nono ba sede madara da mamansu ke bata tun inna, babanta da kuma mahaifiyata na sani gaba da fad'a da masifa akan abinda nake mata suna d'auka alkunyar d'an fari ne har suka dena mamana tayi wa'azin tayi fad'an tayi nasihan har marina tayi amma ko kallo iman bata isheni ba bawai Don bana sonta ba se Don tsoron kar su kashemin ita ni kad'ai nake iya kallonsu ni kad'ai na san irin tashin hankalin da na shiga da barazanarsu akan iman wadda karfi da yaji ya daskarar min da zuciya na dena kaunarta ko son ganinta sbd su.

Inna da take mata soyayya ta tsakani da Allah da kannen mahaifinta Ina ji Ina gani a gabana aljanar nan marar imani ta kawo wata mata da tayi zubi da mahaukata kuma bokayen aljannu tayi surkullenta ta d'iba da kad'an kad'an ta turawa inna, babanta, hindatu, kamila da saratu a tsakanin zuciyarsu wani abu marar kyaun gani ruwan ganye shar, ba yadda basuyi ba don su sawa mamansu abin yaki shiga daga yaje kusa da ita se ya zube shima na tabbatar adu'ar da nake tayi a zuciyata ne Allah ya amsa min, da kad'an da kad'an su inna suka fara bayyana tsanarsu gareta ba kaman da farko da sukeji kaman su had'iyeta ba, haka nake shanye duk wani bakin cikin da zanji akan rayuwan da Iman takeyi da yadda Allah ya d'aura mata kulafucin uwa kaman me dukda irin soyayyar da take samu wurin mama, kullum baza'a wayi gari a yini banyi kuka ba kuka sossai cikin nadama da danasanin dafa wannan taliya.

Aurarrakinta da waennan mugayen aljanun ke kashewa sune suka fara min barazana da lafiyata ba tare da kowa ya sani ba har mahaifinta, kullum cikin dare Haka zan mike in hau kan sallaya In raba dare Ina mata adu'o'i, banda yadda zanyi inaga Don sun ga komai ze iya faruwa zuciyata ta fara bushewa da tsoronsu da nake na fara maida musu magana kuma nake kokarin sanar da babansu yasa sukayi kokarin kasheta a aurenta na uku ba auren kawai ba har ita sukayi niyyan kashewa amma naji daad'i sossai da adu'o'ina suka fi karfinsu har yayi tasiri kanta ya kawo mata hamza amma marasa imanin suka kasheshi.

A lokacin ne nima suka zo da wannan boka suka sa min wannan koren abu a zuciyata fiye da yawan wadda suka sawa su inna, daga lokacin ne kuma nima naji har zuciyana bana sonta daga lokacin ne na dakata da mata adu'a daga lokacin ne naji inama banyi cikinta ba da ban shiga wannan damuwa da tashin hankali na shekaru ba, a lokacin da na fita harkanta da lamuranta na dena mata adu'a na dena duk wani tsayuwan dare da nakeyi sbd ita se Allah ya amshi adu'o'ina na baya da na jima ina mata ya kawo mata Abdulraheem.

Banda Abin cewa se Alhamdulillah Alhamdulillah na gode Allah da ya kawo mata warakanta a kan wannan bawan Allah bani da abin sakamishi ko biyanshi se adu'ar Allah ya biyamishi bukatunshi na alkhairi ya sadashi da manzon tsira Annabinmu annabin rahama Muhammad Sallalahu alaihi wa sallam".

Shiru parlorn ya d'auka na fiye da mintuna goma kowa juya labarin yake cikin mamaki da al'ajabi ajiyar zuciya baba fufore ya sauke yace "menene kike ganin laifinki guda a cikin labarin nan?" Tace "zubar da ruwan zafi da magrib" yace "tabbas wannan abinda mutane dayawa suke gani ba laifi bane wallahi wallahi shine abu marar kyau da ze iya jawo musu nadama na har abada sbd shiga taskun aljannu da suka fimu karfi da komai da sukayi"

Note:-

(ba wai a littafi ba wannan ba novel bane da kawai na tsara da karan kaina da zuciyata ba seda aka tayani, ku taimaki kanku en uwana mata in kuna zubar da ruwan zafi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login