Follow us on social media

Showing 120001 words to 123000 words out of 131683 words

Chapter 41 - NOOR IMAN Yar Baƙin Ciki BY Fatima Muhammad Gurin

         🥀NOOR IMAN🥀

*Fatima Muhammad Gurin*
            *Gureenjo6763 on wattpad*

*'Yar Mutan Adamawa*

💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)

                          *053*

Tunda jirgin ya d'aga take zaune shiru gefenshi kanta kasa tana wasa da yatsun hannunta se yaji wani iri, yaji rashin dacewar tsawan da ya mata ba ita bace da laifi, hannunshi ya d'aura kan nata ta d'ago ta kalleshi idanunta na cika da hawaye a hankali yace "sorry" juya kanta tayi yace "am so sorry na d'aga miki murya ba tare da laifinki ba, I was angry and confused ne how on earth someone can be this wicked and heartless?".

Had'iye hawayen tayi tace "ba komai, amma duk da haka ai er uwarkace Hamma be kamata ka saketa ba, tunda har tayi nadama se mu ci gaba da zama da ita da zuciya d'aya kaman da" hancinta ya dangwale yana murmushi yace "you are so simple hayatii, wato ma ko kishi na bakyayi? To nayi fushi" yayi maganan yana juya mata keya kwanciya tayi jikinshi tana murmushi tace "hmmm Hamma duk wadda ya gayamaka hakan ya kamata yayi istigfari Don yayi babban karya ni kuwa nake kishinka" Da sauri ya juyo yace "so na fah?" Dariya tayi tana gyara kwanciyanta tace "bacci" ta lumshe ido murmushi yayi yana shafa fuskan ta yace "I love you" murmushi tayi.

Jirginsu na sauka suka fito suka tari taxi ya fad'i hotel d'in da za'a Kaisu suka shige tana makale dashi a lokaci d'aya tana kallon garin bata ta'ba zaton lagos ya had'u haka ba seda tazo kaman wani kasa ta fita, hotel d'in da yace a kaisun ma abin kallo ne tana ta kalle kallenta har ya sallami me taxi d'in, hannunshi ya sanya ya kama nata ta d'an kalleshi suka sakarwa juna murmushi.

Seda ya kama musu d'aki tukun suka kuma fitowa zuwa wani boutique dake gefen hotel d'in trolley ya fara saya musu kan da kanshi ya d'auka mata wasu tsinannun kayan bacci guda biyu da d'aukan ma seda ya bata kunya bare kuma ace ta saka a jikinta, ko ya ce mata kala yaja hannunta zuwa wuraren Jeans, bombshell skinny jean ya d'auka guda d'aya se ya d'auka mata long sleeve carpel outwear duster coat shima d'aya se tops biyu se wani sakakken English gown longsleeve da scarfs guda biyu.

Daga nan sukayi wuraren kayan maza ya d'auki shirt and jean designer guda se vest da boxers da turarenshi, seda ya dauki vest da boxers ya tuna be d'auker mata inners and perfume ba, nuna mata perfumes d'in yayi yace "hayatii d'auki wad'anda suka miki, one minute" ya juya ya fice wurin inners ya nufa ya d'auka mata bama ta san ya san sizes d'inta ba se ganinshi da tayi dasu kunya kaman ta nitse hannu ya sa ya kar'bi perfumes uku da ta d'auko yayi pecking kumatunta yace "thanks let's go" yayi gaba tabi bayanshi tana kallon ingarman namiji da Allah ya had'ata dashi, wani irin sonshi na kara huda zuciyarta ya iya kula da ita, ya san duk wani hanya da ze bi ya sata farin ciki, zata iya buga kirji tace tafi kowacce mace sa'an miji.

Hure idanunta da yayi ne ya sata lumshe idanu kamshin strawberry ya buge hancinta, cikin kasa da murya yace "ya de?? Ko kin fad'a ne?" Yana wani d'age mata gira, juya idanunta tayi alamun ban fahimta ba tace "inaa na fad'an?" Seda ya d'an ciza lips d'inshi tukun yace "kogin love" bata san sadda tayi dariya ba shima ya tayata tana girgiza kai ta kama hanyar fita Don ganin shi da leda alamun yayi billing, bayanta yabi da kallo kan a natse shima ya taka yabi bayanta.

Suna komawa hotel d'in ya musu order d'in abinci ya fad'a wanka bayan yayi yayi da ita su shiga tare taki ta'be baki yayi yace "In ma bakiyi yanzu ba akwai anjima hayatii" ya juya ya shige, zaune tayi tana ta gwada layin zahra yaki shiga, har ya fito tana trying layin amma yaki tafiya haka ta hakura ta mike itama tayo wanka tana fitowa ta samu har abincinsu ya karaso kan sallaya ta ganshi hakan ya sa tayi saurin saka doguwar rigar nan sakakke tayi tarha da gyalenta wadda ya kasance babba ta yafashi ne Bayan ta cire lafayan da tasa da safe.

Bayanshi ta tsaya suka rama sallahn da aka biyosu na magrib da isha bayan sun idar ya mike ya d'auko abincin da kanshi ya kawo gabanta ya tsuguna ya sa mata a plate shi kuwa coffee ya had'a ya koma bakin katon gadon d'akin ya zauna yana kunna plasma tv da remote d'in da ya d'auka kan center table, news ya kai dayake karfe tara yayi ya maida hankali yana kallo yana kur'ban tea, a lokaci d'aya kuma yana satan kallonta ganin juya abincin kawai take, seda aka gama news tukun ya mike ya koma kusa da ita ya duka yace "hayatee" kallonshi tayi yace "Lafiya kuwa? Me yasa bakya cin abinci?" Tace "to kaima Ai baka ci ba" girgiza kai yayi yace "yanzu don ban ci abinci ba kema ba zaki ci ba? Cikina a cike shine yasa kika ga banci ba, ban saba cin abinci sau uku ba se biyu that's why".

Kai ta gyad'a kan ta kai Loma bakinta tana kallonshi shima kuma ita yake kallo seda ta had'iye kan tace "Ina ta gwada layin zahra da ummu baya shiga ko lafiya?" Shrugging kafad'unshi yayi kan ya mike fuskanshi na nuna alamun da gaske baya son maganan da ze tuna mishi da hamna ko mahaifiyarta, kayan baccinshi ya saka ya haye gado ya kwanta.

Seda ta gama cin abincin kan ta mike ta shige toilet tayo brush ta kuma fitowa tana kallon gadon ganin kaman bacci ya d'aukeshi yasa ta nufi akwatin da ya saya d'azu ta bud'e ta zaro rigunan baccin da ya sayon ta kafa mishi ido a zuciyarta se masifa take ta inda zata fara saka waennan kayan duk basu da maraba da babu, kuma kallon gadon tayi still yana nan yadda yake idanunshi a lumshe, mikewa tayi da guda d'aya wadda take ganin d'an gara gara red ta shige toilet, sakawa tayi ta kalli kanta da kyau a door mirror d'in toilet d'in a hankali tace "tabdijam Allah ya kyauta yanzu fisabilillahi wani irin riga ne mutanen nan sukayi shi kuma yaje ya sayomin? In fita hakannan mana kawai ba komai jikina, Ai duk d'aya da wannan kam" bakinta ta turo gaba tana ci gaba da mitan inba asaran kud'i ba me anfanin wannan riga gashi taga yafi dubu goma.

A haka ta fito sanin yayi bacci ta janyo kofan bayin ta nufi gado ta gefenshi taje inda lamb switch yake da ma na d'akin gabad'aya da niyyan kashe bulb taje se idonta ya kyalla kan kamilallen kyakyawan fuskanshi, har bata san ta kura mishi ido tana kallo ba a hankali ta kai hannu ta shafa sajenshi da ya kwanta lub lub gwanin sha'awa zuwa kan red lips d'inshi murmushi tayi a hankali tace "you have no idea how much I love you da kake tambayana d'azu, zaujii am more than madly in love with you, your handsome face, your attractive red lips, your dark brown eyelids, your everything zaujii I love you more than anything in this world, more than my life I can't imagine a life without you" ta duka ta kai mishi peck goshi tana mikewa se charab suka had'a idanu.

Zaro nata tayi zata mike yasa hannu ya fisgota har seda ta fad'o kanshi ya sa hannu ya kashe bulb d'in d'akin yana cewa "I love you more hayatee" be jira amsanta ba ya had'e bakinsu ya fara nuna mata wani hot and dying love.

********

Bayan fitansu daga parlorn Shiru wurin yayi se kukan hamna tana maimaita "na tuba, na tuba hamma wallahi Ina sonka fiye da kaina" mikewa ummu tayi da niyyan kirawoshi mai martaba yace "koma zauna rashida" komawa tayi idanunta da har sun kumbura da kuka na kara tsiyayar da hawaye Unstoppable bata ta'ba zaton haka daga er uwarta guda da take dashi a duniya ba abin yayi mugun bugar mata zuciya sede ya ta iya? Abinda ya faru ya riga ya faru gashi tana girban abinda ta shuka.

Bayan ta zauna me martaba yace "kin san Abdulraheem in ranshi ya 'baci ze iya karasa d'ayan ma gabad'aya kowa ya huta, gwara mu barshi ya huce tukuna se ayi maganan kubran". Ze kara wani maganan kenan sukaga fad'uwar baba galadima salati aka d'auka kowa na shirin yin kanshi se nenne petel ma ta zube, a takaice wannan masarauta sunga tashin hankali Don asibitin masarauta sun kasa yin komai kanshi seda aka fita dashi FMC nan ma da kyar aka samu ya farfad'o da oxygen a kan hancinshi neman ganin me martaba da modibbo yayi suna shiga ya kama hannunsu yace "ku fad'amin yayyuna?? Ku fad'amin ta Ina na gaza da tarbiyar yarinyar nan?" Modibbo yace "baka Gaza ta ko Ina ba Abdulraheem In kuwa ka Gaza d'in to muma da iyayenmu mun gaza kenan" mai martaba ma yace "baka Gaza ba galadima ni shaida ne kayi duk wani abinda ubangiji ya umurta akan renon 'ya'yanka".

Shakuwa yayi da kyar yace "Alhamdulillah Allah kayi shedana ya rabbi in na Gaza ba tare da sanina ba ka yafemin" ci gaba da shakuwa yayi akai akai, modibbo da hawaye ya gangaro mishi yace "ka dubi girman ubangiji ka yafemata Abdulraheem ko Allah ze sa ta samu rahamanshi" girgiza kai yayi yana mai cigaba da shakuwa ganin ba zai iya wani maganan ba yasa modibbo fara maimaita la'ilaha illallah Muhammadur rasulullah salallahu alaihi wa sallam. Yana direwa baba galadima ya kar'ba dukkansu uku suka dire a tare numfashinshi na d'aukewa chak.

Duk karfin zuciya irin na mai martaba se ga hawaye ya fara zuba mishi ba kakkautawa dama tun chan yana da bala'e'en hawan jini gashi ta sanadiyar d'iyar da ya haifa ya sota fiye da komai duniya ya kare duk wani hakkinta tayi sanadiyar fad'awarshi ga ajalinshi ya koma hannun ubangijin talikai da bakin cikinta anya hajja umma anya zata ga da kyau kuwa a rayuwarta na kabari zuwa har abada?.

(Ya ubangiji ka bamu daman kiyaye duk wani hakki na iyayenmu akanmu yasa mu cika da imani😭).

Modibbo da mai martaba da kansu suka mishi wanka suka shiryashi aka ajiyeshi dole yayi kwanan keso sbd daren da yayi, a daren In ka shiga masarautar modibbo Adama zaka tabbatar da ba lafiya ba tsit ko Ina se karatun alqur'ani da ya karad'e kafatanin masarautar, ummu wani irin kukan tashin hankali da bata ta'ba yi ba tayi Abba karan kanshi seda ya girgiza da wannan mutuwa sbd yafi shakuwa da baba galadima akan ainihin ubanshi, zahra, kalthum, hafeez da rahma ne suka sata a gaba da lallashi cikin tashin hankali take girgiza musu kai bazasu gane bane ba Allah ya kar'bi ran mahaifinta Sannan mahaifiyarta na kwance rai hannun Allah er uwarta guda d'aya gata a haukace Ina ta san zata sa ranta taji sanyi?

A zuciye zahra ta mike ta nufi parlorn me martaba inda hajja umma ke kwance har yanzu a wurin har yanzu a d'aure sede bakin ya mutu sbd yunwa da ya ci karfinta Hamna na zaune gefenta se tambayar waye uban ta take yi tuntuni, zahra na isa tace "bakar munafuka Allah ya isa tsakaninmu dake umma, Allah ya saka mana yayi miki hukunci akan abinda kika aikata, Kin kashe mahaifinki ga mahaifiyarki chan rai hannun Allah ki fara kuka tun yanzu umma sbd azabar Allah me tsanani ne akan bayinsa mushirikai" tana kai nan ta juya ta fice.

Kallon Hamna umma tayi tace "kunceni zan gayamiki" cikin rashin tunani Hamna ta kwance ta a d'ari ta fice da gudu duk yadda dogarai suka so tareta kasawa sukayi har ta fice babban titin wajen masarautar a daidai nan wani katuwar tankin mai yayi kanta ya murkushe har lahira ihu hamna da ta biyota tayi wadda seda ya karad'e masarautar kan ta zube a nan kasa (Allah kai d'aya ne Allah, ya ubangiji kaine Allah, ya Allah don girman zatinka ya rabbi ka sa mufi karfin zuciyoyinmu ka hanemu da bin wani bayan kai, kayi mana tsari da bin wani katon d'an wuta kafiri (boka) bayan kai, Allah mun gode maka zamu ci gaba da gode maka da duk wani ni'ima taka a garemu, ya rabbi ka  sa mu cika da imani. Ameen ya hayyu ya qayyum).

******

Kwana gabad'aya masarautan nan sukayi ido biyu da safe aka kai Baba galadima makwancinshi na gaskiya, umma da ta gama zama kwalta aka d'an kalata abinda za'a kalata aka sallaceta aka kai aka binne, ummu kam seda ta suma sau kusan hud'u kan wayewar gari da adu'a da komai ta samu d'an natsuwa inda ta Matsa aka kaita wurin hamna da nenne petel a tare take basu duk wani kulawa.

Ta 'bangaren su Hamna kuwa washegari da safe yayi booking ma mama da Baba flight zasu tashi da yamma yayinda ya gama magana da sauban kan komai tun jiya har da asibitin da zasu gani ya gama biyansu komai ta waya daga wannan asibitin zuwa Airport se sun d'aga kan zasu fita daga hannunsu suna sauka kuma zasu shiga hannun wanchan asibitin sannan akwai wani d'an gidanshi da ya tura daga london d'in zuwa Miami akan suna sauka Kamawa Baba hotel kusa da asibitin ya tura mishi kud'i da komai sbd ance bazasu samu jirgin Miami a yau ba se washegari da safe so be ma yi booking d'in ba.

Bayan ya gama settling komai ya fara kokarin yi musu nasu booking d'in se kira ya shigo wayan shi, wani cousin brother d'inshi ne d'an gidan baba yarima d'agawa yayi suka gaisa kan yace "Abdulraheem kana Ina ne haka baka da labarin abinda yake faruwa masarauta ne?" Yace "me ya faru?" Yace "Allah yayiwa me sunanka rasuwa jiya bayan fitanka" a razane yace "innalillahi wainna ilaihi rajiun" ya kuma maimaitawa kan ya yi baya ze fad'i da sauri Iman da fitowanta toilet yanzu kenan ta rikeshi ya fad'a kan gado a razane take kiran sunanshi ganin da alamu ya fice hayyacinshi ya razana ainun ne yasa ta fara kira mishi sunan Allah.

Da kyar da taimakon Allah ta samu ya dawo hayyacinshi se hawaye rungumeshi tayi aiko ya fara mata kuka marar sauti, Allah ne kad'ai sheda akan kaunar da yakewa kakan nan nashi, Allah ya gani yafi kaunarshi fiye da mai martaba mutum ne shi kamili wadda kowa nashi ne, cikin rawar murya tace "Hamma lafiya? Me ya faru?" Cikin rawar murya yace "Saudah Allah yayiwa mai suna rasuwa ta dalilin wannan matan" da sauri ta d'agoshi tana maimaita "Innalillahi wainna ilaihi rajiun, Allahu akbar Allah ka gafarta mishi kayi mishi rahama da dukkanin muminan musulmai da suka riga mu gidan gaskiya" Ameen ya amsa tace "Ka dena mishi kuka hakanan Hamma kayi mishi adu'a kaji? Yanzu ka tashi mu koma na san duk inda umma take tana bukatanka kusa" Da kanta ta mike ta taimaka mishi ya sa kaya ta d'auki wayanshi ta duba App d'in air Max akwai jirgin yola ta fara processing sauran abinda bata sani ba ta mika mishi ya saka ta mike ta had'a musu kayansu hannunta cikin nashi kaman wani rakumi da akala Don ya zama wani iri ta musu checking out suka fice Airport ba jimawa jirginsu ya d'aga zuwa yola.



*Two pages to go*

                    🖤Gureenjo🖤


                  🥀NOOR IMAN🥀

*Fatima Muhammad Gurin*
            *Gureenjo6763 on wattpad*

*'Yar Mutan Adamawa*

💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)

  *this page is dedicated to you my deedi just want you to know that I love you and I will always be with you, take your side no matter what the situation is, you are such a wonderful and strong woman, you should stick in that love🥰🥰, you are the best sister ever and will always be*


                          *054*

Bayan kwana uku

A cikin kwanaki ukun nan masarautar modibbo Adama ya shiga wani irin yanayi da zasu ce sun manta rabon da abu makamancin haka ya faru, yau akayi sadakar ukun baba galadima da umma dukda dae dayawa har an fara mantawa da rasuwan biyu ne ba d'aya ba, duk wadda ze yi gaisuwa sede yace "Allah yaji kan galadima ya mishi rahama" Tun dawowan Abdul ya sa aka chanzawa nenne petel d'aki ya kuma janye ummu daga kan Hamna ta koma kan mahaifiyarta shima kuma anan yake yini yana bata baki Don ya lura tana cikin damuwa tun bayan da nenne petel ta farka sau d'aya mistakenly wata baiwa ta kawo musu abinci ta mata gaisuwan baba jikin ya kuma rud'ewa tun jiya da safe har yanzu bata farka ba.

Abdul yayi masifa kaman ze ari baki, me martaba da modibbo suna zuwa ko wani dare su dubata yayinda su iman sede suzo fisha su fice, dukda yana bukatan lokaci da matarshi amma ba yadda ya iya yanzu ummu tafi bukatarshi fiye da kowa se dare ya tsala yake komawa part d'insu a hakan ya kuwa taimakawa ummun sossai.

Kaman yau bayan sun dawo daga asibitin bayan tayi magrib tana azkar taga kiran ummanta na shigowa bata d'aga ba seda ta jira ya tsinke tukun ta kirata back tana d'agawa tace "ummanah Ina kewarku" umma daga 'bangarenta tace "khaih mamana yanzu sallaman taki kenan?" Baki ta tura gaba tace "ummah Assalamu alaikum" murmushi umma tayi kan tace "wa'alaikissalam ya kuke? Ya ummunku da hakurin rashi?" Tace "Alhamdulillah umma d'azu naji kunyi waya ko?" Umma tace "Ina ruwanki" kuma turo baki gaba tayi cikin shagwa'ba tace "shikenan ummah babu, Ina su ikhram Ina missing d'insu wallahi, d'azu hafsy take ce min ta shiga satin haihuwanta ko? Ni kam umma kuna waya da maman Abulkhairi kuwa ya jima ina son tambaya se in sha'afa kullum In na kira wayanta baya shiga".

Ajiyar zuciya umma ta sauke Tace "yanzu fisabilillahi wanne kike so in amsa miki? Ni kiran da na miki daban kin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login