Follow us on social media
Showing 12001 words to 15000 words out of 131683 words
Chapter 5 - NOOR IMAN Yar Baƙin Ciki BY Fatima Muhammad Gurin
kama muka mike muka fita ba tare da ta furta komai ba, har seda muka samu wurin da ba mutane sossai tukuna ta dakata, "wai me ke damunki ne haka besty? Wallahi ko makaho ya shafa fuskan nan naki ya san kina cikin damuwa kar ki kuskura kicemin ba komai, jibeki? Duk a birkice!!".
Hawaye ne ya cika min ido a zuciyata nace "baza ki gane bane" amma a fili se na kwakwulo murmushi nace "ba fa komai besty, kinga muje ki koyamin abinda akayi a class yau, kan 11 muyi Botany" zatayi magana na ja hannunta Ina sakin murmushi, ba yadda ta iya haka ta bi ni, muka koma hall d'in da mukayi lectures yanzu, ba mutane dayawa hakan yasa muka samu wuri muka zauna ta hau min bayani In taga kaman zan tafi tunani se ta san yadda tayi ta hana.
It is really fun zama da zarah tana da wani baiwa da Allah ya bata wadda baza ka ta'ba zama da ita bata saka farin ciki da nishad'i ba, ba ta da girman kai irin na yaran masu kud'in zamanin nan sam, 11 na yi mukayi second lectures d'inmu zuwa 1 tukun muka fito.
Seda nayi sallah kan na fito don gidan hafsy dake low cost zani, tuni zarah ta wuce, cikin natsuwa ta nake tafiya ina yaki da zuciyata wajen hanashi fad'awa tunanin da ze sani yin wani shirmen akan titi don na saba, a kasa na dinga tafiya har bakin gate kan na samu adaidaita na hau tare da fad'a mishi inda ze kaini.
Bamu fita layin BUK road ba wani ya tare me napep d'in dama ba shata na d'auka ba sbd bani da kud'in yin hakan mussaman irin napep na kano, wani fitinennen kamshi ne ya min sallama, wadda har seda ta sani lumshe ido na bud'e a hankali, dukda raina na bani in kalli me wannan kamshin amma ego na ya hana seda naji husky voice d'inshi na cewa "sallamu alaikum" ni da me napep d'in muka amsa, a lokaci d'aya.
Idona na sauka cikin nashi nayi saurin kawarwa na mayar kan titi, "low cost nayi" me napep d'in yace "fad'uwa ta zo daidai da zama muma chan mukayi" be kara magana ba se faskekiyar wayarshi da ya fidda ya fara dannawa, cikin seconds naji yana amsa call "yes plz kazo BUK road gefen wani mini super market zaka ga mota ta a wurin, na shiga na siya abu se kuma ta ki tashi, the key is with the securities just collect it there".
Ban ji me aka ce mishi a d'ayan 'bangaren ba se de naji yana godiya tare da kashe wayan, Shiru shiru ko motsin kirki banayi har muka kusa isa, shi kuwa ta 'bangarenshi kallo d'aya ya mata ya tabbatar ya samu irin macen da yake so, don tayi mishi d'ari bisa d'ari ga natsuwa da ya lura tana da shi.
Don sam ta kasa sakewa ji tayi ya cika mata ido sossai, ganin har ga Allah ba ze iya barin wannan daman ta wuce shi bane yasashi cewa "sunana Muhammad bashir ana ce min hammad and yhu?" Bata tabbatar da ita yakeyi ba seda ta kalleshi taga ba waya yakeyi ba, se ma murmushin da yake ta sake mata har fararen hakwaranshi na bayyana.
Itama murmushin tayi kan tace "Noor Iman" yace "wow nice name amma ba asalin suna bane ko?" Kai ta gyad'a kan tace "asalin Saudah" wani murmushi me sauti ya saki yace "sunan manya, sunan mom d'ina fa gareki" murmushi kawai tayi, a take ya ci gaba da janta da hira duk ta kasa sakewa har suka isa daidai inda zata sauka, ta cewa me napep d'in "zan sauka a nan" da "Toh hajiya" ya amsa tana shirin sauka taji Muhammad yayi saurin cewa "Noor Iman".
Waigowa tayi se taga waya yake miko mata at the same time yana murmushi yace "samun number d'inki plz ma dinga gaisawa" d'an Shiru tayi tana kallon wayan seda ya kuma cewa "dan Allah" kan ta kar'ba ta saka mishi, "thanks" yace bayan ya kira yaji ringing d'inshi a jikinta, umarnin tafiya ya ba me napep d'in don yaji tana shirin bud'e jaka don d'auko kud'i.
Girgiza kai tayi bayan wucewarsu kan ta nufi karamin kofan gidan hafsyn da sallama ta shiga a tsakar gida ta ga maman mijinta zaune tana cin goro, dukawa tayi ta gaisheta, amsawa tayi tana me kare mata kallo har Noor ta dunfari parlorn hasfy taji matar nan tace "tsaya wannan ba yayar hafsatu sarauniyar zaurawa ba? Me aure aure da ta kasa zama sbd bin maza ya bi jikinta?".
Wani irin bugu zuciyata tayi a lokaci d'aya naji Ina shirin dena gani da kyar na iya juyawa na kalleta nace "itace de, sede kar masu fad'in hakan su manta kaddara ce tana kan kowa kuma bata fi karfin kowa ba, an haihu de" salati matar ta saka, ko karasa sauraron salatin nata banyi ba na fad'a parlorn hafsa kujerar da ya fi kusa dani kawai na samu na zauna a kai Ina dafe kirji.
Abubuwa sun min yawa har ga Allah sede In na tuna Allah baya d'aurawa bawa abinda yafi karfinshi se ince "Astagfirullah wa atubu ilaih" amma Ina tunanin zuwa yanzu akwai abinda ka iya samun zuciyata don kiris ya saura ta tarwatse gabad'ayanta, "Yaya Noor ce, sannu da zuwa" muryan hafsy ya katse min bakin cikin da nake ciki murmushi na kwakulo ganin yadda take fara'a nace.
"Nice Hafsy fatan bakiyi fushi dani ba, wallahi tunda kikayi 'barin nan nake ta sa ranan zuwa dubiya Allah be yi ba se yau, Allah de ya kiyaye na gaba ya baki me anfani" tana murmushi tace "ba komai wallahi yaya noor, na gode Ai yanzu da lokacin ma duk d'aya ne tunda de kinzo. Bari na kawo miki ruwa" ta mike ta fice chan ta shigo ranta ba daad'i hannunta d'auke da katon faranti me d'auke da plate d'in jollof da ruwan pure water guda biyu.
Da mamaki nace "Lafiya kuwa hafsy?" Murmushi tayi wadda daga gani na san na yake ne tace "ba komai, ya su mama da umma? Ya school?" Kan na bata amsa se ga uwar mijinta nan da mijin shi kanshi, "au wato da nace kizo kice mata ta fice min daga gidan d'a shine kikayi biris da maganata ga shashasha nan ko? Asararriya irin wannan ballagazan yar taki".
Cewar uwar mijinta, da sauri hafsy tace "a'a hajiya wai dama nace ko ruwa ne tasha kan ta wuce, daga makaranta take kuma dubiya da jajen 'ba...." da tsawa mijin ya katseta "Hafsah da uwata kike ja In ja? Lallai ashe hajiya gaskiyanki ne wannan yar tata munafuka annamimiya itace ke shirin fara hure mata kunne amma ba haka take ba".
Kuka hafsa ta fara da sauri na mike na d'au jakata Ina danne hawayena nace "kuyi hakuri In shaa Allahu bazan sake zuwa ba bare har na hure mata kunne, hafsy dan Allah kiyi hakuri" a sama sama nake jin muryan habu yana cewa "gwara kam, kuma wallahi hafsat kika bari wanchan tsohuwar guzumar ta kara shigomin gida ba tare da izinina ba a bakin auren ki, zan kira baban don ki tabbatar uwata tafi ta kowa ta bada tarbiyya me kyau ga duka 'ya'yanta ba'ayi watsatsiyar da zata shigo ta zageta ba".
Innalillahi wainna ilaihi rajiun, Allah Astagfirullah, Allah ka dubeni, shine abinda nake ta nanatawa Ina tafiya ban san ya baba ze yi dani In yaji maganan nan ba, da ma ban zo ba, horn d'in mota da na dinga ji a bayana ne yasa ni dakatawa na kuma yi saurin goge fuskana da yayi cha'ba cha'ba da hawaye, "Noor har kin gama ziyarar?" Juyawa nayi ina kallon shi, hammad ne zaune cikin wata white Mercedes murmushi na kakalo nace "Eh" yace "Ohk shigo plz na kaiki gida" Kai na girgiza "a'a zan hau napep na gode".
Kafewa yayi, a yanayin da nake cikin nan bani da wani karfin yin musu da shi hakan yasa na bud'e gefen me zaman banza na zauna yaja yana tambayata "wace unguwa?" Nace cikin sanyin murya "gandun albasa" tafiya mukeyi Shiru shiru kan yayi breaking silence d'in da cewa "Damuwa da tunani be dace da kyakyawar fuskar nan ba sam".
🖤Gureenjo🖤
🥀NOOR IMAN🥀
*Fatima Muhammad Gurin*
•Gureenjo6763 on Wattpad•
*'yar mutan Adamawa*
💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)
*09*
"Noor magana nayi baki ce komai ba, ko zan iya sanin damuwanki? In da hali In magance miki?" Nan ma Shiru tayi, kaman bazata ce komai ba se kuma tace "damuwana yafi karfin tunaninka, ba me iya magance min ita se wadda ya busan numfashi" Shiru ya ratsa na mintuna kan yace "hkne but komai Ai yana da sila, I understand sbd baki sanni bane yasa bazaki iya fad'amin damuwanki yanzu ba.
But with time zan san me ya dameki nima zaki san me damuwana, sbd alaka ta har abada nake son kullawa dake, kallo d'aya na miki na tabbatar na samu irin macen da nake so kab duniya, Ina sonki" wani irin bugu da zuciyarta yayi seda tayi tunanin ze iya ji, inaaa bata shirya ba, bata shirya wani tozarcin ba, ba ta yadda za'ayi tayi aure yanzu wallahi.
Cikin rawar murya tace "a'a kayi hakuri dan Allah ka nemi wata" hankalinshi kwance yace "ni ke nake so ba wata ba, bazan rabu dake ba se kin ban kwakwaran dalilin yin hakan" Kai tsaye tace "ni bazawara ce" d'an Jim yayi kan yace "hakan ba dalili bane" dukda he was not expecting that, "aurena har hud'u ba d'aya ba" waro ido yayi yana kallonta har be san sadda yayi losing control ba tare da bumping wata bakar mota dake gabanshi.
Birki ya taka tare da sakin ajiyar zuciya, ba 'bata lokaci ya bud'e motar ya fita don yayiwa na gabanshi 'barna kad'an, tana nan zaune taga de yana knocking glass d'in motar ta gabansu, kuma taga an bud'e bata ji me suka tattauna ba, ta de san maganan da sukayi bata wuce na minti biyu ba, taga wanchan d'in yaja motarshi yayi gaba, bud'e kofan da hammad yayi ne yasata kallonshi har seda ya zauna kan ta d'auke kanta.
"Dan Allah ban son wasa Noor kinga abinda kika ja sbd kawai kina so in rabu dake se kicemin aurenki hud'u da kananan shekarunki?" Shiru tayi don baze fahimta ba, amma tana fatan yana ajiyeta a unguwansu a tare shi a bashi labari, nuna mishi hanya ta d'ingayi har kofan gidansu, "na gode" shine kawai abinda ta furta kan ta sa Kai ta fice, Ai ko de kaman yadda tayi tunani be fita a unguwan ba aka tareshi aka bashi labarinta na karya da gaskiya wadda yasa shi fita cikin natsuwarshi, gashi Allah ya sa mishi sonta farat d'aya a ranshi.
Ze 'boyewa mom don ya san In har ta sani bazata ta'ba yarda ya aureta ba, gashi shi kuwa baze iya rabuwa da ita ba, gida ya nufa da nufin yayi tunani ta yadda ze shawo kan mom kan tayi bincike, don haka take In har d'anta ze yi aure da kanta take bincikar halin surukarta da yanayin gidansu, sede kash yana parking mom na fitowa.
"A'a hammad ya na ganka haka? Me ke damunka?" Shiru yayi na mintuna kan yace "mom ba ko..." katseshi tayi "kul karka kuskura yaushe muka fara wasan haka da kai, zaka fad'amin ko se ranka ya 'baci?" Dayake Allah ya halliceta da son nata gata da zafi bata yarda komai ya samu d'anta bata d'au mataki ba, ba yadda ya iya hakan yasa yace "na samu matar aure".
In disbelief take kallonshi kan ta sake murmushi tana cewa "Toh shine abun tada hankali? Kode tsoron gayamata kake In shige gaba don na sanka da tsoron mata" murmushi yayi yana gyad'a kai, tace "toh ya sunanta? Kuma wani unguwa take?" Ko yayi karya se ta gane don ba halinshi bane "sunanku d'aya amma ana kiranta 'Noor iman' unguwansu kuma gandun albasa.
Tana murmushi tace "masha Allah, ka san tsari na, kar naji maganan nan a bakin mahaifinka ni da kaina zan gayamishi" sawa ranshi kawai yayi ya rasa Noor don In har mom taji abinda yaji Toh kuwa baze ta'ba aurenta ba ko mutuwa yake yana farkowa, amma kuma ance Ai ba abinda yafi karfin Allah, da wannan tunanin ya wuce part d'inshi.
*********
Tassss Tass taji saukan mari akan kuncinta hagu da dama a razane take kallonta, Umma!!! Bata ta'ba shiga harkata ba se yau, bata ta'ba d'aga hannu da sunan dukana ba se yau, "ana cewa baki da hankali da natsuwa ban ta'ba yarda ba se yau, Toh bari kiji bazata ta'ba sa'buwa ba yadda kike kashe aurenki sbd iskanci irin naki ki kashewa 'ya'yana ba, wallahi ki kiyayeni ba abinda bazan iya miki ba In har kika kuskura auren 'ya'yana yayi rawa ta dalilinki, su ba gur'batattu bane sun san me sukeyi" kan baba dake zaune gefe ta maida kanta.
"Ka jawa 'yar ka kunne Hafeez Wallahi tallahi ta kara taka kafanta zuwa gidan 'ya'yana zan yi mugun bata mamaki" bata jira cewarshi ba ta juya ta fad'a d'akinta, da kallo baba ya bi ta kan ya maida idonshi kaina, ina tsaye ne kawai amma wallahi zan iya rantsewa jini be tafiya a jijiyar jikina, i am more than shock da kalaman umma, nafi mintuna biyar kan naji zuciyata ta fara bugawa da karfi tana wani irin zafi, wasu zafafan hawaye suka fara rolling a idonanuna da kyar na taka zuwa d'akin mama, baba de be ce min komai ba se kallona da yakeyi har na kule.
Mama bata nan hakan ya bani daman fad'awa kan gadonta na fashe da wani irin kuka me ban tausayi, me tayi ne a duniyanta da take fuskantan irin wannan bakin rayuwan? Wani laifi ta aikata haka me girma da yake hunting d'inta like this? Innalillahi wainna ilaihi rajiun uwa de da ta haifeta a cikinta, ta raine ta na wata tara tasha wahalan nakuda amma shine take mata haka?.
Me babancin dake tsakanina da 'yan uwana da har za'a fifita su sama dani? A kuma raba tsakaninmu, me nayiwa umma ne?? Da irin wannan tunanukan take kuka tambayoyi ne fal a raina akan rayuwata sede banda wacce zan iya tambaya, sede tayi kuka me isanta kan ta mike ta fad'a toilet tayi wanka, seda ta fito daga wanka kan taga mama murmushi ta kakalo tace "sannu da dawowa mama".
"Yauwa Iman lafiya kuwa na ganki wata iri" ba tare da ta kalli maman ba tace "Lafiya bacci na d'anyi" girgiza kai kawai mama tayi don ta san ba haka bane, kallo ta dinga binta dashi har ta shirya cikin normal English gown tare da zura hijab, seda ta tada sallah kan maman ta d'auke kanta daga kallonta, tana nan zaune har ta idar da sallah, ta juyo tace "me za'a d'aura mama?" Mama tace "babanku ya kawo aleyaho se kiyi miyan da tuwon shinkafa" da Toh ta amsa tana mikewa da hula a hannu ta fice.
***********
"Ai rayuwar gidan Abdul ba karamin gyara bane a cikinshi, da wannan matar tashi da da ita da babu duk d'aya" cewar Anty Rumah kanta na kan bama d'anta Arfat nono, Kallon Abdul d'in dake kwance kan doguwar kujera Kalthum tayi tana son yin magana tana tsoron kar ya zageta amma ganin idanunshi a lumshe kaman ba magananshi ake yi ba yasa ta cewa.
"Wallahi kau Anty Rumah baki ga da na shiga gidanta da safe ba, ko wurin zama na kirki babu tsabar tarkace da datti, wai da na mata magana shine take neman yi min rashin kunya kaman ba shekara na bata ba" Hamma Hafeez yana dariya yace "Toh sarauniyar son girma, amma Ina suna da namiji cleaner?".
Zarah da ta fito daga kitchen hannunta d'auke da tray da cups na smoothie akai flavor kala kala dayake kowa da irin flavorn da yake so, tana ajiyewa tace "hmm ina ko ze iya zama da masifan Anty hamna" Anty Rumah tace "Da gwara macece ma amma Ina shegen kishinta na tsiya ze iya bari ta nemi me aiki mace", Hamma Hafeez kai tsaye yace "Da nine Abba wallahi aure zan karamishi" Anty Rumah na dariya tace "Se kace baka san halin gayen ba? Ai ko Abban ne se yaga dama ya amshi matan, balle kuma kai da kace da kai ne, Ai magana ta 'baci".
Zarah tace "Da kuwa na za'ba mishi nitsatsiyar matar da babu irinta" kaman daga sama sukaji muryan ummu tana cewa "Lallai yaran nan kun cika, Yanzu fisabilillahi akan 'yar uwarku kuke irin wannan mugun fatan? Kar fah ku manta da ni da uwarta uwarmu d'aya ubanmu d'aya, to bari kuji in fad'a muku hamna ita kad'ai zata zauna a gidan Abdulraheem In har na isa dashi, kuma kuyi ku tattara ku fice min a gida tunda kune masu hure mishi kunne.
Shima In ba shashasha ba taya za'ayi ya zauna kuna zagin matarshi yana ji be kare ta ba, to Abdulraheem kajini da kyau In har Ina numfashi matarka d'aya hamnah" daga bakin kofa sukaji Abba yace "A'a Rashida Ina miki rantsuwa da Allah a yau Babana ya kawo wata macen yace yana so in aura mishi, Toh fah se inda karfina ya kare, Allah ne fah ya bashi daman zama da mace fin d'aya In har baya jin daad'in na farkon, karki zata ban san duk halin da yake ciki da matar tashi ba Ina sane, sannan 'yan uwanshi nada gaskiya dole su zauna su nema ma d'an uwansu mafita In har da gaske suna sonshi, ban ga dalilin d'aukan zafi akan abinda ba shine ba" kallo kawai ummu ke bin Abba dashi kan ta juya ta haura a zuciye a ganinta 'ya'yanta Da mijinta sun tsani 'yar 'yar uwarta tunda har zasu iya cewa a yi mata kishiya su kuma suna zaune gidajensu su kad'ai, Toh kuwa zata ga uban da ya isa yi ma Abdulraheem aure tunda d'anta ne, tana da hakki a kanshi kaman yadda shi Abban