Follow us on social media
Showing 48001 words to 51000 words out of 131683 words
Chapter 17 - NOOR IMAN Yar Baƙin Ciki BY Fatima Muhammad Gurin
karfin yinki kai ko uwarki.........” Shigowar Abdul ne yasa tayi shiru da bakinta.
Kasa Iman tayi ta kanta tare da janyo mayafinta tayi saurin yafawa Anty kalthum da ta mike tsaye ta kalleshi don san tabbatar da yaji abinda hamna take cewa ko be ji ba, aiko expression na fuskanshi ya tabbatar mata yaji, ko kallon inda hamna take be yi ba ya duka gaban iman tare da d’age gyalenta se suka had’a ido murmushi ya sakar mata ganin ba d’igon hawaye fuskanta.
Itama bata san sadda tayi murmushin ba, kafad’unta ya kama ta mike tsaye, ya gangaro da hannunshi ya sanya cikin nata lumshe idanu sukayi a tare jin wani irin electric shock ya ratsa su a lokaci d’aya taushin hannayen junansu ya nemi rikitar da su, ciki kasa da murya yace “Kalthum kira ummu mu wuce” daga nan ya ja hannunta suka nufi kasa, ko kallon inda hamna take be yi ba bare ya san anyi wata hallita wurin.
Wani irin murmushi kalthum ta saki tare da sake gud’a tana nufan d’akin ummu tana wakar “er yarinya..... kin ji haushine....” tanayi tana kid’an da bakinta, wasu irin hawaye ne suka zubowa hamna kutmelesi ita Abdul ze wa wulakanci a gaban kucakar amaryarshi? Lallai daga ita har shi basu nemi zaman lafiya ba kuma wallahi bashi suka ci se tayi maganinsu, zarah ce ta fito cikin shirinta sanye da green lace tayi matukar kyau janye da trolley d’inta tana kallon Hamna tace “Anty Ina besty?”.
Cikin fad’a hamna tace “ban sani ba ko Ajiyar ta kika bani?” Ta’be baki zahra tayi kan tace “ahh ba ni na kar zomon ba” Anty kalthum da ta fito daga room d’in ummu tace “ko ratayar ma ba’a baki ba auta am, mu tafi su ya Abdul suna jiranmu a tsakar gida” ta janye trolleyn ummu ta fice zarah ta bi bayanta suka bar hamna da haushi, tana nan tsaye ummu ta fito lullu’be da gyalenta kallon hamna tayi tace “lafiya kuwa?” Shiru tayi ma ummun kaman wata sa’anta kan ta juya ta shige d’akin da ummu ta sauketa ta d’auko trolley d’inta da bakin gyalenta tsiriri dashi iya wuya ta yafa tare da d’aukan black handbag d’inta ta fito.
Mota uku sukayi Abba, ummu da Hafeez a d’aya, Abdul, Iman da hamna a d’aya sun sashi tsakiya, se kalthum da zarah a d’aya duk drivers ke jansu suka nufi hanyar Airport a hanya su zarah suka rabu dasu sukayi wurin maymz don d’auko sauran kayayyakin Iman, a harabar Airport d’in suka sauka drivers d’inne suka janye trolleys d’insu zuwa ciki.
A mota suka ci gaba da zama Hafeez da hamna ne suka fice zuwa arrivals hamna ta zauna shi kuma ya shige inda Abba ya aikeshi, Shiru suke zaune a motan kanta kasa yayinda shi kuma yake danna wayanshi be matsa daga gareta ba sam cinyoyinsu na gogan juna kamshinshi duk ya cikata ga fargaba da take ciki jikinta se rawa yake zuciyarta na aikin bugu.
Suna nan zaune har su zarah suka karaso suka shige ciki, tana nan de zaune da ta gaji da sunkuyar da kan se ta d’ago tare da juyawa tana kallon window tana kallo su Abba suka sauka suka shige ciki, satan kallonshi tayi yana nan yana aikin danna wayanshi, ajiyar zuciya ta sauke tare da maida kanta kasa ta janyo gyalenta yadda yake, se da yaji ana sanarwar jirginsu kan ya matsa ya bud’e ya fita ya cire babbar rigar kam daga shi se na ciki da wando se hula dake kafe kanshi.
Zagayawa yayi ya bud’e mata ta zuro kafanta ta sauko tafiya ya fara a hankali ta fara bin bayanshi dakatawa yayi tare da juyowa ya dawo dab da ita har tana jin numfashinshi ya sanya hannu ya janye gyalenta zuwa baya, d’ago ido tayi se suka had’a ido d’auke kai yayi tare da sanya hannunshi cikin nata suka fara tafiya majestically har ciki, da suka je hawa stairs na jirgi ne ta dakata tare da matse hannunshi cikin nata hakan ne ya sanyashi tuna ashe bata ta’ba hawa jirgi ba.
Sake hannunta yayi batayi aune ba se jin hannunshi tayi a kwankwasonta ya zagayeta tare da d’aura kanta kan kafad’anshi suka ci gaba da tafiya duk yadda take so haka yakeyi sbd takalmin kafanta In tace zatayi garaje fad’uwa zatayi tunda bata saba ba, duk ido kansu ya dawo ko a jikinshi seda suka had’a ido da ummu ne ya d’an sunkuyar da kai ganin irin hararan da take jefanshi dashi, hamna ma kaman zata fashe kuma se aka ci sa’a sit d’insu Manne da na juna, Sbd basu samu VIP ba don sunyi late booking seda ta zauna tukun ya tsallaka ya zauna daga jikin window da hannunshi ya sanya mata belt zarah da kalthum se kus kus sukeyi suna dariya, da akayi sanarwar kashe waya ma shi ya bud’e jakanta ya d’auko nata tare da jujjuyawa se kuma ya danna ya kashe tare da jefata aljihunshi itade tsabar kunya ko iya d’ago kai ta kasa.
Dirin tashin jirgin da taji ne yasa tayi saurin kama hannunshi dake hannun sit gam murmushi ya saki kan ya maida nata cikin nashi lumshe ido tayi har jirgin ya daidaita a sama kan ta bud’e nan ya saketa ya sanya ear pods tare da jingina da jikin kujeran ya lumshe ido, har suka sauka be d’ago ba, manyan motoci da dogarai da masu busa da ganga irin ta sarauta ne suka cika Airport d’in daga ji zaka san ba kananan mutane bane suka sauko garin ba ‘bata lokaci sukayi checking aka tattari kayansu zuwa mota, wannan karon da zarah ya kyaleta yayi gaba don baze iya tafiyar hawainiyar nan ba, se tsokannata Zarah take har suka shiga mota se Unguwan lamid’o.
🖤Gureenjo🖤
🥀NOOR IMAN🥀
*Fatima Muhammad Gurin*
•Gureenjo6763 on Wattpad•
*'Yar Mutan Adamawa*
💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)
*026*
Nenne ce da kanta tazo ta tarbeta hannunta ta kama har part d'inta kanta a kasa so bata samu damar karewa masarautar kallo ba amma de ta tabbatar Allah yayisu da yawan kuyangu ko bayi don duk inda suka bi gaisuwa ce kawai ke tashi amma ba wadda ke amsawa wadda hakan ya sata jin ba daad'i bata san haka gidan sarauta yake ba.
Ke'bantaccen d'aki babba sossai nenne ta kai ta zarah de na binsu a baya Ummu da Abba kam tuni sunyi site d'insu yayinda hamna tayi wurin nenne petel don a chan sukayi zasu had'u da ummanta, Hafeez da Abdul kowa site d'inshi ya tafi, "Feel at Home Ohk?" Nenne ta furtawa Iman, gyad'a kai iman tayi tana murmushi, ko ba'a fad'a mata ba ta gane wannan itace nenne mahaifiyar Abba, tsohuwa me mutunci da sanin ya kamata.
Fita tayi wasu mata suka shigo d'auke da manyan trolleys har guda uku, zarah dake mata masifar ta bud'e kanta haka ta sha iska ta dakata tare da juyawa ta kallesu, a tare suka ce "barkanku da isowa, Hajiya Nenne ce ta turo mu don fara yiwa Amarya abinda ya kamata" murmushi zarah tayi kan ta gyad'a kai tana janye gyalen fuskan Iman "Toh madam se ki mike za'a fara miki gyara" kallon matan tayi kan tayi murmushi suma suka mayar mata.
Akwati d'ayar ta bud'e ta d'auko wani silk farin riga da iyakarshi be wuce gwiwar ta ba ta bata "ranki shi dad'e bismillah" kar'ba tayi ta kalli rigan ta kuma kallon rigan ita zata saka wannan a gaban mutanen nan? 'Bata fuska tayi zatayi musu zarah tace "wallahi if I hear pim Nenne zan kira" Sarai ta san halin zarah hakan yasa ta mike ta shiga toilet ta sako da kyar ta fito ya kuwa amshi jikinta se tattakurewa take gashi hannunshi irin na vest.
Zama tayi bakin gadon tana kallonsu dariya zarah ta kwashe dashi bata san sadda ta banka mata harara ba, d'ayar ce ta katsesu da cewa "ranki shi dad'e In ba matsala zan iya bud'e kanki?" Kai ta gyad'a matar ta matso ta bud'e kanta ba laifi gashinta na da tsawo sossai zuwa de wuyanta kuma ba datti amma dukda haka matar tace "ranki shi dad'e kan yana bukatar wanki zamu iya karasawa toilet?" Wani irin abu iman ke ji In manya mutane irinsu suna mata magana haka cike da girmamawa kuma se suyi maganan kaman neman izini suke.
Mikewa tayi ta bita suka shiga bayin tas ta wanke mata kai cikin natsuwa ba hayaniya zata iya rantsewa bata ji ko alamun zafi ba haka ruwa ko kad'an be hau kanta ba, suna fitowa taga d'ayar ta had'a wani karamin kujera gefen sockets bismillah tayi mata kan ta karasa ta zauna, wacce ta wanke mata kai d'ince ta fiddo hand dryer ta had'a ta fara busar mata da kai yayinda d'ayar ta d'auko lallen da bata san sadda aka kwa'ba ba ja da baki ta fara mata jan.
Yayinda d'ayar ta fiddo wasu abubuwa kaman kurkur da su madarar turaruka ta fara had'awa, mikewa zarah tayi tana yafa gyalenta tace "Bestie bari inje sashin baba yarima yanzu zan dawo" Kai iman ta gyad'a itafa yanzu bakin magana ma bata dashi, abinda ya kamata ace a gidansu kuma 'yan uwanta ne sun mata se gashi en uwan miji sun had'a gabad'aya sunayi, tsoronta ma kar hakan ya zama abin gori a gareta gashi gidan sarauta yadda take jin labarinsu kad'ai abin tsora ne bare kuma ta zama topic of discussion.
Cikin awannin da basu wuce uku ba an gama mata had'ad'en lalle ja da baki har an kankare, gashinta an zuba mata nyinyirin two step kaman ka lashe tsabar had'uwar kitson da kankantarshi, jikinta An mulkeshi da dilka, 'yan mata ne hud'u a d'akin bayan zarah, Nabeeha, Ameerah, teemah da zee yaran baba yariman ne kuma kusan sa'anni ne da zarah, musu suke akan wacce ta fi kyau tsakanin Hamna da Iman duk d'akin ya kaure da hayaniya Zee ce tace "wallahi Iman tafi kyau ku tsaya kuji hujjojina" Shiru sukayi suna sauraranta ta d'aura da.
"Kunga Iman na da wushirya Adda hamna bata dashi" kallonsu tayi tace "kuce d'aya mana" suka had'a baki suka ce "d'aya" ta kara da "Iman na da dimple Adda hamna bata dashi" sukace "biyu" ta d'aura "Iman na da manyan boobs dukda ba har chan ba amma tafi Adda hamna" sunkuyar da kai Iman tayi cike da kunya su ko ko a jikinsu se cewa "uku" da sukayi, "yauwa Dukda Adda hamna tafi Iman bombom, iman ta fi ta hips me d'aukan hankali" shewa sukayi kan suka ce "hud'u" "kai hasken fata ne fah kawai Adda hamna zata nunawa Iman da baka ce se a hankali, ga yangan tsiya kaman wacce ta fi kowa, abu na karshe da ya zama hujja na shine ku lura da kyau Idanun Iman sexy eyes ne irin na Hamma Abdul banbancin kawai nata black nashi kuma brown yayinda idon Adda hamna suka kasance kanana kaman na 'yan China".
Dariya suka sa har Iman Lallai a gaishe da zee, hiransu suka ci gaba dayi iyakaci iman tayi dariya In sunyi abun dariya sede sam bata sa musu baki ba, ta sani ko min lalacewar d'an uwanka fa baza ka so a zageshi a gabanka ba tana da wannan wayon hakan yasa duk Aibata hamna da suke bata saka musu baki ba, tsab matarnan ta dirje ta har halawa tayi mata sega Iman an fito Amarya sak se wani yalki take, se lokacin en matan suka mike akan zasuje suyi wanka su shirya zuwa walima don sune manyan kawayen Amarya.
Ficewa sukayi aka barta da zarah kad'ai se lokacin tayi magana "su kuma ya kuke dasu bestie?" Zarah tace "yaran baba yarima ne matanshi hud'u hakan yasa duk su hud'u aka haifesu shekara d'aya sede banbancin kwanaki, Inda baba yarima ya burgeni ya tsaya a gidanshi sossai irin sossai d'in nan, shiyasa Kika gansu kaman 'yan hud'u ko kawaye, Ai kin gane sunayensu ko?" Iman tace "Eh na gane, bari inyi wanka ruwan yana hucewa" wacce ta mata dilka ce ta had'a mata ruwan wanka me had'e da turaruka kala kala, seda ta lumshe ido da ta shiga ruwan ita karan kanta ta san ta chanza ba se wani ya fad'a mata ba, ji take kaman lallenta kar ya ta'ba gogewa har Abada tsabar yadda ya tsaru.
********
"Umma cewa fah kike inyi hakuri In baki lokaci ni wallahi na gaji da jin wannan kalaman, ko kallo fah ban isheshi ba" kuka ta fashe dashi tana cewa "a gaban mahaifiyarshi fah yayi rantsuwar ban ta'ba shiga zuciyarshi ba kuma bazan shiga ba" umma tace "Haba Hamna me yasa kike abu se kace ba 'yar da na haifa a cikina ba? Nace ki bar komai a hannuna da Sannu duk zasuyi jawabi kuma ki dena musu kuka se su mai dake sakarya.
Kaman yadda na fad'amiki tare zamu koma, mu bud'ewa 'yar iska wuta se ta gaji ta gudu da kafanta, kafin mu tafi kuma zamu je mambila mu samu boka ya rufemana bakin duk wadda ze ga aibun zamana gidanki, ke har shi yayi iya yinshi ya taimaka ko me zamu iya kashewa ya kasa kusantar yarinyar nan yaji tana mugun wari yaji ya tsaneta" dariya Hamna ta sake tana cewa "that's my mom idea d'inki yayi Allah ya sa ya tafi daidai" Umma tace "aaa damu za'ayi? An isa a ta'bamin 'ya a zauna lafiya ne".
Hamna zatayi magana kenan Nenne Petel ta shigo wadda hakan ya sata yin Shiru, zama tayi bakin gadon d'akin tace "kubra" hamna ta amsa da "na'am" Tace "Ina ta so inja hankalinki, auren nan da Me suna yayi ba shine yake nuna baya sonki ba, kaman yadda Allah ya bawa duk wani namiji umarni ze iya auren mace daga d'aya zuwa hud'u In har ze yi adalci a zaman nasu, haka sunna ne sbd fiyayyen halitta matanshi sunfi goma haka sahabbanshi da wuya ki samu me mata d'aya kinga kenan ke wacece da Baza'a miki Kishiya ki zauna da ita ba? Ki guji tada fitina a gidanki dan Allah, ki kiyaye duk abinda ze zama tashin hankali a tsakaninku, banda yawan kai kara sbd yana janye kimar mace a idanun mijinta haka kuma banda kishi irin na jahilci, kai ya waye yanzu ba'a kishi irin na hauka se na hankali akan miji zaki nuna kishinki ba'a kan Kishiya ba, sannan ki za......" mikewa Hamna tayi tana waro ido "laaaaa Nenne petel yi hakuri plz ina zuwa minti d'aya ashe ya Abdul yace In kaimishi fruit salad na manta" ta fice da sauri.
Murmushi umma ta saki ta san karya ce kawai hamna ta shirga don ta gaji da jin wa'azin Nenne petel d'in, kuma bata ga laifinta ba haka kawai adakeka a hanaka kuka, shigowar ummu ne ya katsewa umma tunaninta bata san sadda ta ja tsaki ba ganin yadda Nenne petel ke farin ciki da ganinta "lafiya?" Ummu ta tambaya umma tace "kalau" mikewa Nenne petel tayi tana cewa "Rashida biyoni yanzu babanku ya gama magananki yace In kin shigo inyi maza In kaiki wurinshi" murmushi ummu tayi tana cewa "Allah sarki babana nayi kewanshi muje Nenne petel" fita sukayi da harara umma tabi bayansu tana ta'be baki.
********
Karfe uku daidai ya musu a kofar masarautar lamid'on Adamawa ganin inda suke shirin shiga yasa inna cewa "Kai dreba Lafiya kuwa? Ina kake shirin kaimu?" Yace "gidan su Angon ba hajjiya, ko be gayamiki shi jikan sarkin Adamawa bane?" Goggo saratu Tace "Kai haba dallah jikan sarki a ina? Alfarmar alqur'ani ka kaimu inda muka gama wassafawa zamu gani ba nan ba ta Ina zata ga jikan sarki har ta aureshi?" Goggo kamila tace "aiko kya tayani tambaya".
Wata daga chan baya tace "tooh ko de da gaske yake tunda Ai shi aka ce ya d'aukomu kuma ya san inda ze kaimu ku bari ya shiga inma 'Batan kai yayi shi ze daku a wurin dogarai Ina ruwanmu" murmushi ya saki yana girgiza kai tunda suka kamo hanya yake jin yadda suke aibata wannan Amarya tun be san sunanta ba har ya rike tun yana ganin kaman gaskiya suke fad'a har ya dawo kokonton karya ne ko gaskiya don abinda suke fad'a be yi kama da gaskiya ba, yana Jin yadda kowa ke wassafa yadda ze yi In yaje ya kasa cin miyar kukar da dangin ango zasuyi, dukda an tsaya gombe sunci abinci ba ko sisinsu Abba ne ya ciyar dasu bayan yayi magana da me shagalinku restaurant duk abinda suke so a basu shi ze biya kud'in don wawanci irin nasu ba wadda ya tambayi nawa ne kud'in ko wa ya biya suka ci suka gyatse suka hau mota suka ci gaba da tafiya, yana ga ko sun zata kyauta ake rabarwa oho! Toh ga karshen hassada.
Bud'e get d'in da akayine ya sasu maida hankali bakin kofan dogaran dake wurin sun kai ashirin da wasu polices suka fito suka dudduba motan suka tabbatar wadda Abba ya fad'a ne kan suka musu hannu suka shige, baki wangale suke kallon katoton masarautar had'ad'e kaman a wata kasa suke, kuyangi da Bayi ke ta aikin kai kawo, saukowa sukayi suna rarraba idanu kaman waenda sukayiwa sarki karya.
Wasu mata biyu da shigar alfarma suka gani sun nufosu bayansu kuyangi ne akallah zasu yi goma, har gabansu suka karaso suna murmushi suka ce "barkanku da zuwa masarautar Modibbo Adama, ni sunana Dada nice uwargidar wazirin masarautar nan" d'ayar tace "zaku iya kirana nenne petel uwargidan Galidiman masarautar nan kuma kaka ta 'bangaren uwa a wurin Surukinku" gaishesu suka kuma yi suka amsa, kan d'aya daga cikin kuyangin tace "barkanku da zuwa ku biyomu don ganin masaukinku, nice shugabar kuyangin nan gabad'aya sunana sahura mu ke da alhakin kulawa daku cinku, shanku da makwancinku daga yanzu har randa zakuyi sallama da masarautarmu me albarka".
Inna de ido fah ya raina fata hausawa suka ce d'an hakin da ka raina...... bin bayansu sukayi kowa gwiwa a sage yhu guys know