Follow us on social media
Showing 51001 words to 54000 words out of 131683 words
Chapter 18 - NOOR IMAN Yar Baƙin Ciki BY Fatima Muhammad Gurin
that feeling right? Irin feeling d'innan da zaka gama sa ranka ga abinda zaka kalla se kaga akasin haka🤣 masaukinsu aka kaisu part guda aka ware musu me cike da komai na jin daad'in rayuwa Ac da Tv kad'ai inna ta sani a duk cikin kayan alatun part d'in se ta zama 'yar kauye musamman da ta shiga bayin.
"Zakuyi wanka ku shirya yanzu akwai taron da za'ayiwa Amarya har ta gama shiri ma" goggo hindatu tace "ta gama shiri fah kikace? Mu da muka barta kano?" Murmushi sahura tayi kan tace "Ai su jirgin sama sukabi sun iso tun safe" salati suka saka se kace wasu en kauye inna tace "wannan Ai bakin hali ne da wariya mu se aka turomu a mota muka yini muna tafiya ita kuma aka d'aurata a jirgi, Toh bakar munafuka dad'in abin ma nima na ta'ba hawa jirgin nan tunda naje kasar da bata ta'ba zuwa ba, kum..."
Goggo hindatu ce ta katseta tana kallon sahura tace "zaki iya tafiya, yanzu zamu Shirya" fita tayi tana mamakin en uwan Amaryar nan kaman ba danginsu ba? Abinku da masarauta me kunnuwa tuni zance ya fara yawo Ai Amaryar yarima Abdulraheem mujiya ce cikin en uwanta.
Cikin lokaci kankani sukayi wanka suka shirya suka ci abinci kan suka fito da niyyar tafiya taron da za'ayin a mota aka d'aukesu inna ta kasa Shiru Tace "har Ina ne za'ayi taron malam? Yanzu fah muka baro kan hanya kafafu na har sun kumbura kuma a kara d'aukarmu zuwa wani wurin?" Yace "Ba nisa nan cikin masarautar ne amma bazaku iya zuwa a kasa ba shiyasa aka turo mu d'aukeku" Shiru duk sukayi har suka isa katon hall d'in dake bayan masarautar wadda daga waje ma zaka ga irin kayatuwar da yayi.
Yaji decoration har ya gaji zallan mata ne wurin manya masu ji da kud'i da mulki duk kuma family ne, abinda ya sa aka yi saurin cika kuma aka zozzo sbd Nenne ce da kanta ta aikawa kowa katin gayyata wadda be zo ba kuwa ba abinda ze hanata kiranshi ta ci mishi mutunci, Mama da yaranta gabad'aya zaune a 'bangare d'aya, 'bari d'aya aka warewa 'yan uwan Amarya chan aka musu iso suka zazzauna.
Basu jima da zama ba na hango wasu gayya sun kutso kai waro ido nayi a fili nace "ikon Allah su kuma waennan wa ya musu iso zuwa nan?" Gayyan en ANNUR HAUSA NOVELS ne gaba sanye da ankonsu na jallabiyoyi masu kyau da tsari duk milk amma design daban daban kowacce ta yafa gyalenta gwanin sha'awa, Ummu Ameer, Ummu haneef, Ummu Aslam da Adama Aliyu ne gaba se wani cin magani suke irin ba rainin nan, Anty kalthum ce ta karasa dasu wurin zamansu suka zazzauna suna jiran walima, har na d'aga kafa Don zuwa garesu na kara gani wasu gayyan na MU KARU DA JUNA Maman khalil, kawata Aisha da Khadijah Queen da Maijidda ne gaba sanye suke suma da ankonsu na jin wa'azi wato jallabiya suma wurinsu aka basu suka kame ba raini sun had'u.
Basu jima da zama ba kuyangi suka fara shigowa suna watsa flowers a hanyan suna kuma fesa turare baya baya sukeyi inda Iman ta bayyana sanye da Ash fitted gown irin na amare yaji design kana ganinshi zaka san ba karamin kud'i yaci ba fuskantan nan ya sha makeup d'in zarah taci d'auri da ash head, Ash pose da Ash hill shoe ta sanya saman kayan kuma alqyabba ce Baki da Ash wayyo had'uwa, tayi kyau har ta gaji su Inna kam kasa ganeta sukayi har Goggo saratu ke cewa "wannan kam watakila itace sarauniyar masarautar".
Inna tace "ze iya yiwuwa bakiga irin kyaun da tayi ba? Ga fadanci kam kaman za'a mata sujada" goggo hindatuce tace "inna Noor iman ce fah" waro ido sukayi Ai kuwa ita d'ince tsaki inna taja tana kallon su zarah da suka biyu bayan ta suma sunyi kyau dukda ba anko bane jikinsu amma sunyi matukar kyau, kan wani tattausan carpet irin na masarauta aka zaunar da ita kan su teema suka zagayeta, wata malama ce ta shigo ta zauna akan kujera kwara d'aya dake saman stage d'in ta fara zanzaro wa'azi. Daga chan karshe na hango en Wattpad ma fah sun natsu suna jin wa'azi suna gyad'a kai😅.
🖤Gureenjo🖤
🥀NOOR IMAN🥀
*Fatima Muhammad Gurin*
•Gureenjo6763 on wattpad•
*`Yar Mutan Adamawa*
💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)
*027*
Walima akeyi me class wadda ya ratsa duk wani me sauran imani kan a tashi kuyangi suka fara shigowa da abinci kala kala suna rabawa da souvenirs da ban san sadda akayi ba, a cikin paper bag me d’auke da hotunansu su biyu rike da hannun juna ita kanta bata san sadda akayi ba, cikin jakan kuma dardumar sallah ce babba me tsadar da azkar wadda ya had’a na safe dana yamma se na bacci da bayan sallah a jikin ba hotonsu sede sunayensu, se memo me d’auke da hotonsu kala kala masu kyau.
Dukwadda ya taka kafanshi wurin seda ya san eh fah wannan walimar ta had’u, ‘yan Annur hausa novels harda fad’a wurin karbar souvenirs bayan nenne ta fad’a musu kowa ze samu😜, ana tashi zarah ta kama hannun Iman suka fice bata bari sunyi magana da en uwanta ba sbd kar su ‘bata mata rai ranar farin cikinta, mota suka shiga aka wuce dasu, cikin sanyin murya iman tace “Zarah Ina son ki kaini wurin nenne”.
Kallon drivern zarah tayi tace “Part d’in Fulani” yace “An gama ranki shi dad’e” murmushi Iman tayi tace kasa kasa “er air se kace gaske na lura kema jinin sarautar nan na yawo kanki kaman d’an hayakin yayanki” ta karasa kasa kasa kaman batayi niyyar fad’a ba, dariya zarah tayi tana cewa itama kasa kasa “Eyyeh Lallai ma matarnan yayan nawa ne kanshi ke hayaki?” Dariya Iman tayi zatayi magana zarah ta d’aura da “ba dole ba kin san aka ce In kazo inda aka san waye kai ka kama ajinka da girman ka sbd bama son raini ya shigo ciki, sannan abinda kika fad’a kaman a kunnen yayana kuwa don wannan sako ne”.
Girgiza kai Iman tayi tana waro ido zatayi magana kenan motar ta tsaya, se kuma wasu dogarai suka bud’e musu, fita sukayi zuwa kofan part d’in nennen, Shiru kaman ba me rai a ciki dukda en bukin da suka cika gidan amma ba kowa part d’inta sbd ita bata son hayaniya da yawan mutane a wuri, iso suka nema kuyangarta ta shiga ta nemo izini aka ce su shiga.
Babban parlor ne da ya amsa sunansa kafatanin rayuwar iman zata iya cewa bata ta’ba shiga parlor irin wannan ba, dukda a part d’in ta sauka amma ‘bangare daban daga chan baya me karamin parlor da bedroom d’in da suke da zarah, bata karaso nan ba balle ta san ya yake kuma ta chan be cika yawan dogarai da kuyangi kaman nan ba, room d’in dake facing d’insu zarah ta mata jagora zuwa ciki, kamilalliyar tsohuwar na kishingid’e akan tuntu d’akin karan kanshi duniya ne komai na ciki na asalin gidan sarauta ne.
Wasu kuyangi ke mata tausa, murmushi ta sakarwa Iman wadda ya bayyanar da hakorin makkanta me kyau da yalki, hannu ta ma kuyangin suka fice, da sassarfa Iman ta karaso gabanta ta duka se kuma ta fashe da kuka, ita da zarah duk ido suka zubata kan Nenne ta mike ta iso gabanta batayi zato ba taji tsohuwar tayi hugging d’inta wani sihirtaccen kamshi me sanyi da zata ce bata ta’ba jin turare me kwantar da hankali ba irin wannan ke tashi a jikinta.
“Gimbiyarmu meke faruwa ne? Ko wani ne ya ‘bata miki?” Kai Iman ta girgiza tace “Kin min abinda duk duniya ba wadda ya isa ya min, kin farantamin kin kankaro darajata a idon en uwana da masarautar nan, ni kuwa nenne me zanyi in biyaki wannan alkhairan naki gareni?” Murmushi nenne tayi kan ta saketa tayi baya kad’an zuwa kan tattausan carpet irin na sarauta ta kishingid’a kan tace “Ba abinda zakimin da ya wuce adu’a tun dana ji labarinki daga bakin Zarah naji wani irin tausayi da soyayyarki ya shigeni, rashin kulawar uwa ba karamin illa bane ga ‘ya musamman mace, Ina so ki d’aukeni a matsayin uwa wacce zaki dinga fad’awa damuwarki a ko yaushe kinji?”.
Kai Iman ta gyad’a kan Tace “In shaa Allahu Nenne zan ci gaba da yi miki adu’a har karshen rayuwana Allah ya biyaki ya saka miki da gidan Aljannah” da Amin ta amsa, kan ta harari zarah, baki zarah ta zum’buro tare da cewa “aaa ya da harara ni kuma me nayi?” Tace “wayace ki kawota nan, bayan kin san kuna da shirin dinner a gabanku? Oya tashi kuje tayi sallah ku fara shiri sannan ki tabbatar taci abinci”.
Kai zarah ta gyad’a tare da cewa “Nenne Ina tsohon mijinkin nan me ran karfe?” Murmushi nenne tayi kan tace “yarinya kau da idanunki akan shi kin san yafi karfinki, ana fakewa da ce mishi tsoho bayan sonshi ake kaman za’a mutu” Turo baki gaba zarah tayi tana ‘bata fuska iman bata san sadda murmushi ya su’buce mata ba, nenne ma murmushi tayi dama abinda take son gani kenan.
Hakan yasata cewa “ko kefa ‘yata ki dinga murmushi, baki ga yadda take miki kyau ba” ‘boye fuskanta tayi tana kara sakin wani murmushin a zuciye zarah ta mike zata fita nenne tace “Eh dai ko me zakiyi kiyi, baza ki gane min miji ba ehe” mikewa Iman tayi tana ci gaba da murmushi tace “mun barki lafiya ranki shi dad’e” Kai ta gyad’a, itakuma tabi bayan zarah.
Tana fitowa ta fara dariya me sauti wallahi zarah ta bata dariya itace da tambaya sanan ita ce ke fushi, musamman yadda take ta ‘bata fuska yafi komai bata dariya bata kula ba, alkyabbar jikinta ya tad’iyeta abinka da ba sabon ba, shikenan yau kam fad’uwa zatayi ta karya kafa ko hannu Don wannan tiles d’in ta tabbatar ta kai kasa ba abinda ze hanata karyewa.
Wani wawan ajiyar zuciya ta sauke jinta a hannun mutum, dayake da tazo fad’uwa hulan alkyabbar tayi gaba zuwa kan fuskanta so bata ga wadda ya taimaketa ba amma kuma kamshin tabbas ta sanshi, a hankali ta d’ago kanta jin har yanzu be saketa ba hannunshi d’aya zagaye da kwankwasonta d’ayar kuma a kafad’anta, tana d’agowa suka had’a ido.
Bazata iya jurar kalllon cikin kwayar idonshi ba hakan yasa tayi saurin kawar da kanta tana daidaita tsayuwarta, saketa yayi ba tare da yayi mata magana ba ya zagayeta ya shige d’akin nenne abinshi, bata san ta rike numfashi ba seda ya wuce taji tana shirin mutuwa ba shiri ta saki numfashi me karfi, d’ago kai tayi se suka had’a ido da zarah da sauri ta sunne kai yayinda zarah ta kwashe da dariya.
Gaba tayi ta barta nan tana kunkuni, har suka zagaya inda ta sauka zarah bata bar dariya ba tana cewa “osheeee yau naga wani irin love” suna shiga Iman ta fad’a toilet ta barta nan da surutunta, wanka tayi da ruwan d’umi sossai Don duk a gajiye take jin kanta, kan tayo alwala ta fito, tana tunani da mama aka zo amma bata ganta ba ko me dalili? Gashi tunda ya d’auki wayanta a jirgi be dawo mata dashi ba, se yanzu ta tuna duk had’uwansu bata ta’ba gaidashi ba fah kar ya d’auka bata da kunya.
Zarah ce tace “tunanin me kike ne matar yaya?” Harara ta sakar mata “zarah ki fita idona in rufe, wannan kuma wani irin suna ne?” Dariya Zarah ta saki tana cewa “karya nayi? Ko ke ba matar yayanan bane? Kingama daga yau sunan da zan dinga kiranki dashi kenan, matar yaya” kanta Iman ta nufa da gudu ta yi toilet tana cewa “tuba nake matar yaya” murmushi iman tayi tana girgiza kai.
Cikin kayan da nenne ta aikomata d’azu ta zabo wani cotton duguwar riga me guntun hannu ta saka tare da zaro hijab ta tada sallah, magrib tayi ta ci gaba da zama tana azkar dayake ta haddace, Haka kawai taji tana sonyi dama ba kullum takeyi ba se ta bushi iska, tana nan zaune zarah ta fito itama tayi wanka sede da towel ta zauna bayan ta shafa mai, ta bud’e makeup kit d’inta ta fara goge brushes d’inta dayake tana fashin sallah.
Ganin ta gama azakar se kawai ta fara karatun qur’ani da ka, tun daga Nasi ta fara tana cikin izu na biyu aka kira isha, ta mike ta gabatar tana sallamewa ana sallama kofa wasu kuyangi ne suka shigo bayan zarah ta basu umarnin shigowa da manyan trays a hannunsu na abinci seda suka ajiye kan suka duka suka kwashi gaisuwa zarah ta amsa tana wani ‘bata fuska.
Suka mike suka fice bayan ta basu umarni, kallon iman tayi dake kallonta tace “Lafiya matar yaya? Why are yhu eying me?” Murmushi kawai Iman tayi kan ta mike ta ninke sallayar da hijabin ta isa gaban trays d’in ta bud’e kular farko couscous ne a ciki me rai da lafiya da yaji veggies ta d’iba kad’an tare da bud’e kula na biyu pepper chicken ne part d’aya ta d’auka ta d’aura gefen couscous d’in ta nufi gado ta zauna.
Allah sarki en uwa se ta fara tunanin ko en uwanta sunci abinci? Tsintar kanta tayi da adu’ar Allah ya sa irin abinda aka kawo mata aka kai musu suma suci daad’i, tana gamawa suka fara kwalliya da zarah se lokacin take tambayarta “Ina Su teema ne?” Zarah tace “suna chan suna makeup, yanzu anko zamuyi Don akwai wani yadi haka me yanayi da less da Mommy ta d’inka mana dukkanmu so ban saka nawa ba suna basu saka ba sbd munyi se sallah ne zamuyi anfani dashi tunda kinga azumi ya gabato, toh kuma se ga bukinki zamu saka shi as anko, ga colors d’in blue and pink ne ke!! Hasko had’uwarmu kawai”.
Iman tace tana ta’be baki “dukde abunku baza ki kaini ba” zarah Tace “eyeeeh Lallai ma wannan Amaryar marar kunyace ashe?” Dariya iman tayi zarah na tayata, a haka suka gama kwalliyar suna gamawa Su teema na shigowa sun kuwa fito kaman ka sace kowacce makeup d’inta abin yabawa ne, cikin Jin haushi zarah tace “wato nice kashin baya an barni da towel Ina yawo kowa ya shirya, Toh Amarya de bazata fita ba In har ban gama ba”.
Nabeeha tace “kin isa yarinya?” Zee tace “har ta wuce ma kin manta itace angon? Ko mata na fita bada izinin mijinta bane?” Teema tace “Ina fah In ba so take tagamu da fushin Allah ba?” Ameerah ta d’an duka kaman yadda kuyangi ke yi tace “Allah ya ja zamanin yarima jikan sarki, gaba sayaki baya sayaki, me tafi....” hannu zarah ta d’aga mata kaman yadda sukewa kuyangi, kan tace cikin yatsina “fad’i damuwarki” kara dukawa Ameerah tayi tace “Ranka shi dad’e muna neman izinin tafiya da matarka ne zuwa wajen dinner tare da umarnin Fulani” d’an Shiru Zarah tayi kan tace cikin yatsina “ku jira daga waje zan duba” dariya suka kwashe dashi har Iman abin ya bata dariya sossai, wato ma sun san irin mulkin da suke shimfid’awa bayi.
Teemah tace “er Air kin ko yi kama da hamma Abdul sossai da kina shakiyancin nan” zarah tace “Sweetheart” tana kallon Ameerah, Ameerah Tace “Eh za’a cuceni kenan, fad’i Ina jinki” zarah tace “plz love ki taimaka ki mata head bari nayi makeup kar a barni baya, plzzzz” hararanta tayi kan tace “ba don halinki ba” zarah tace “thanks” mikewa Iman tayi ta zura doguwar rigar ta milk da Flowers kanana kanana golden, rigan yayi wani irin amsan jikinta ne ba d’inkin kawai abin kallo ne.
Head d’inta golden Ameerah ta d’aura mata ya kuwa fita d’as ya zauna, a jikin saman d’an kwalin ta Makala mata gyalenta milk an zagaje bakin da flowers golden irin na rigar me d’an girma, sarka da d’an kunneta Teema ta sakamata suma golden yayinda Zee ta saka mata takalminta shima golden, hill ne abinda Iman bata so Don zuwa yanzu kafanta har kumbura ya fara abinda ba sabon ba haka de ta sanya.
Zarah na gama shiryawa wata babbar mace ta shigo, duk Sannu suka mata suna ce mata mommy, Iman ma gaisheta tayi ta amsa da fara’a kan ta bud’e handbag d’in hannunta ta fiddo turaruka masu asalin kamshi ta feshe Iman dasu har seda taji sun fara hawa mata kai, kallonsu zarah tayi tace “kuyi gaba, yanzu zamu taho da Amaryar In kun isa kada ku shiga ku jira isowarta” suka amsa da Toh kan suka fice.
Motoci ne kala kala a harabar gidan ba na kananan mutane duk ciki, tuni jama’a dayawa sun fice wurin dinnern, har su Inna sun tafi ba yadda ba’ayi da itaba ta zauna su tafi ta ki tace se ta je, mama dake ta kallonsu goggo saratu ta kalla tace “wai lafiya kuwa Anty? Se naga kaman tunda muka zo bakya jin daad’i ga idanunki duk sun suuntuma” goggo hindatu tace “Ai ko de, jiya na lura ko Waliman nan bata samu zuwa ba” Mama ta kirkiro murmushi kan Tace “wallahi zazza’bi ne da gajiyar hanya suka had’umin amma yanzu na ji sauki sede bazan je dinner d’in nan ba” goggo kamila tace “Allah ya kara sauki” suka amsa da amin, kan suka fice suka barta anan part d’in suna fita ta fashe da kukan da na rasa dalili, ikon Allah.
Mommy da wata da taji mommyn ta kira da Anty Dada suka fito da Iman d’in zuwa jikin wata arniyar Bakar mota suka bud’e mata ta shiga, tare da rufowa, suma duk suka shishige motocin dake wurin a jere motocin amaryar suka nufi fita dayake ba cikin masarautar suka shirya event d’in ba, a razane ta d’ago jin kamshinshi ya subhanallah yana motar shima zaune a gefenta ya jingina da jikin kujera.
Sanye da milk shadda da yaji ado da milk zare, irin