Follow us on social media
Showing 36001 words to 39000 words out of 131683 words
Chapter 13 - NOOR IMAN Yar Baƙin Ciki BY Fatima Muhammad Gurin
me jiran gado duk sun watse wasu har a kasashen waje ma suke aiki a cikinsu akwai barristers, doctors, engineers se Abba da ya kasance business tycoon, matan kuma d'aya na aure Sokoto gidan sarautar chan d'aya na aure Abuja se yaran hajiya mama da uku sunyi aure d'aya na gabanta duk cikin yola sukayi aure.
Auren ummu na shekaru hud'u ta samu haihuwar Anty Rahma bayanta da two years aka haifi Hamma Abdulraheem wadda ya ci sunan baba galadima da kanshi ya hana a 'boye mishi suna, se Hamma Muhammad wadda muke kira hafeez, se a lokacin Hajiya mama tayi aure da kyar ta auri wani mai rufin asiri ba don ta so ba, se don Baba galadima ne ya za'ba mata mijin da kanshi ba don ta so ba de don gidan sarautanmu ba'a jayayya da za'bin iyaye yasa ta hakura ta aureshi.
Amma be da sakat a gidanshi se abinda tace sannan za'ayi bata shekara ba ta haifi kubra wacce suke kira hamna, bayan haihuwa Anty hamna da one year ummu ta haifi Anty kathum, haihuwar Anty Kalthum da three years aka haifeni, tunda hamna ta tashi koyaushe tana hanyar kano da sunan hutu ko mahaifinta baya son zuwanta se hajiya umma ta sata gaba ta kawota ba yadda ya iya, Allah ya d'aura mata son ya Hafeez sede shi duniya In akwai wacce ya tsana to ya biyo bayanta sbd shegen iyayinta da nuna isa kaman 'yar wani ga rashin kunya, abinda yasa basa shiri kwata kwata da Hamma Abdul kenan sbd baya son masu irin halin nan nata.
Dukda ma yana gama secondary ya bar kasan se in yazo ne itama ta zo suke had'uwa a haka ma kullum fad'a don in har yana wuri tayi abu se ya hantareta cewa yake bani na iyanta yawa ne dashi, bamu san ya akayi daga baya ta koma son Hamma Abdul ba, shima ya tashi da son business amma se karatunshi ya banbanta da abinda yake so, zallar Bsc. biology ya karanta degree d'inshi se ya koma Entomology yayi Masters da phd d'inshi wato study of insects anan ya ci gaba da musu aiki a matsayin lecturer dukda ba so yake ba.
Ganin zamanshi a London d'in ya fi yawa ne yasa Abba had'a hannu dashi suka bud'e kafanin fata wato de suna sarrafa fatun dabbobi, gabad'aya natsuwarshi ya tattara ya ba companyn yana jin daad'in aiki da turawan sossai sbd basu da wani hali irin na 'yan nijeria, In ji shi da fad'a. Bayan ha'baka companyn da yayi ne ya ajiye aiki da university d'inshi ya koma harkar companynshi.
Nan Hajiya umma ta bawa ummu shawarar had'a su aure da hamna don wai zaman mutum a kasar waje ba mata matsala ne a lokacin kuma tana AUN wadda Abba ne ke biya mata tana karantar Economics, ummu ne ta tilasta Ya Abdul auren hamna da kyar ya yarda sbd shi mutum ne me murd'ad'en hali seda Tayi barazanar tsine mishi kan ya yarda akayi auren amma yaki yarda ta bishi London a nan unguwanmu ya sayi gida ya ajiyeta ba yadda basuyi ba yaki, sede ya dinga zuwa.
Da hakan tayi anfani da Abba tasa aka tilasta mishi dawowa Nigeria wai ita baza ta iya ya dinga zuwa yana komawa ba tunda yaki ta bishi, Abba ya bashi za'bin ko ta bishi ko ya dawo Nigeria da zama se ya za'bi dawowa nigeria inda BUK da kansu suka nemi yayi aiki da su daga jin labarin ze dawo nigeria suma ki yayi wai bazeyi lecturing ba musamman a nigeria seda Abba ya sa baki kan ya kar'bi offer d'in, nan Abba ya bashi Director na steel companinshi dake nan kano wadda ya Hafeez ke jagoranta kasancewarshi business ya karanta.
Anty Rahma tayi aure da jimawa da yaranta uku suna nan cikin kano da zama a hotoro se Anty kalthum da bata jima da yin aure ba tana zaune ne a zoo road da d'anta d'aya, Anty hamna na running business manyan shagunan kayayyakin mata da yara take dashi a nan BUK road, "To Kinji yadda muke" gyad'a kai iman tayi tace "masha Allah, Zanso wataran in je Adamawan nan don wallahi Ina son fulani" zarah na dariya tace "zakije ne har ki gaji da zuwa" ta karasa maganan tana mikewa "uhm bari Inzo In tafi kafin ummu ta fara kirana don tace ta gaji da yinin da nakeyi waje, yauwa bari In kirata tace in nazo In kirata ta gaisheki da jiki".
Iman tace "plz karki kirata" zarah tace "au bakya son magana da ummun tamu?" Iman tace "ba haka bane wallahi wani iri nake ji In zanyi waya da babban mutum bazaki ga..." sa mata waya zarah tayi a kunne wadda sallaman ummu ya sata yin shiru ba shiri, tana hararan zarah tace "ummu barka da rana" ummu tace "yauwa Iman ya jiki?" Tace "da sauki Alhamdulillah, an sallamemu ma" ummu tace "masha Allah, Allah ya kara sauki yasa kaffara ne" iman tace "Ameen Ameen mun gode" sukayi sallama ta ba zarah wayan zarah ta sanar da ummu tana nan dawowa yanzu.
Tana kashewa tace "saura Abba" waro ido iman tayi tare da mikewa tayi kan zarah tana kokarin kwace wayan Ai zarah da gudu ta mike tayi waje yayinda iman ta rufa mata baya seda suka zagaya parlorn maman sau biyu kan iman ta zube a kan kujera tana haki hannunta dafe da kai, da sauri zarah ta yo kanta tana cewa "ba kinga ba, mutum beda gashin wacce yace ze yi kitson wacce da de kina lafiya ne se muyi tayi har gobe ma ni be dameni b.." bata karasa ba iman ta damke hannunta ta fisge wayan tare da mikewa da gudu ta fad'a d'akin mama tare da rufe kofa tana sauke numfashi harda "wayyo wayyo" take had'awa.
Tana kan sauke numfashi tace "zarah wallahi na kamaki zaki gayawa 'yan garinku Haka kawai kisa mutum gudun da be shirya ba, da fuskanki kaman na dr. Malabo a wurin masu farin larabawa kawai, wayyo Allahna" tana jin zarah na dariya tana cewa In ba tsoro ba ki bud'e mana ta shareta tare da kallon wayan, duba fuskan wayar zarahn da zatayi se taga "Blood💞💞" dubawa ta karayi da kyau se taga ba kira ake ba call ne ke reading duration d'in ma ya kai 5mins waro ido tayi tana sa hannu a baki tace.
"Ke zarah waye blood kinga mun kira garin shiriritarmu na san se magana yake be ji komai ba se shirme" zarah tace "credit na kashe kashe da kyar ya Hafeez ya sa min cati jiya wai Ina shirmen banza dashi" iman tace "ke dallah tambayarki fa nayi waye blood bazan kashe ba se kin fad'amin, ma bazan kashe ba punishment d'in gudun da kika sani kenan" zarah tace "Toh wallahi Ya Abdul ne kuma...." kan ta karasa taji salatin iman ta san zuwa yanzu ta kashe Ai ko de tun bata karasa cewa Abdul ba tayi hanzarin kashewa tana salati.
"Zarah kin kasheni, Allah ya sa be ji nace da fuskanku iri d'aya ba, da kuma farin ku kaman na larabawa ba" dariya zarah ta kwace dashi tana cewa "gen gen gen shikenan yaji, mutum da carry over kuma sun kulla abota gashi 3credit unit, ba ruwana" cikin muryan kuka iman tace "shikenan na shiga uku" dariya zarah ta ci gaba da yi tana tsokanarta se da taji da gaske kukan take kan ta lalla'beta ta bud'e mata kofan ta fara aikin rarrashi don sossai hankalin iman ya tashi.
*******
Murmushi ya dinga sakewa yana girgiza kai wato yaran nan daad'i ne ya musu yawa harda gujel gujel, wani lalatacciyar dariya ya saki tuna wai da fuskan zarah kaman nashi a wurin, Da kuma farinsu kaman na larabawa a fili yace "zaki maimaita ne yarinya" tare da mikewa ya koma d'akin hotel d'inshi dama waje ya fita shan iska se kuma yaga kiran zarah d'in duk haukan da suka dingayi a kan kunnenshi ko ba komai yaji daad'in samun lafiyanta, shirin tafiya kano ya fara don jirgin yamma ze bi ya koma gida.
*******
Da kyar zarah ta lalla'bata tayi shiru, tare da mata sallama akan zata koma gida da yamma zata je d'auko malabo a airport, se de su had'u gobe In ta dawo daga lectures, iman tace "gobe akwai Lectures ne?" Zarah tace "Eh akwai na ya Abdul" iman ta waro ido kan Tace "zanje In shaa Allahu Ina ni da missing class d'inshi" zarah tace "baki fah warke ba baza ki kara haku..." katseta Iman tayi da cewa "ke karma ki 'bata nyaun bakinki se naji, samun ma in mishi maganan test d'in da yayi Allah na, Allah ya sa kar ya ki yimin" suna tafiya zuwa waje suke maganan.
Parlorn umma suka shiga tayiwa mama da umma sallama mama se godiya takeyi kan Iman ta rakota jikin mota suna d'agawa juna hannu ta wuce.
🖤Gureenjo🖤
🥀NOOR IMAN🥀
*Fatima Muhammad Gurin*
•Gureenjo6763 on Wattpad•
*'yar Mutan Adamawa*
💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)
*021*
Se da ta kwanta bacci tukun tunanin auren da baba yace za'a d'aura mata a jibi ya dawo mata, ta fara tunanin ko da wani irin miji kuma Allah ze had'ata? Me mutunci ne ko akasin haka, shi yace yana sonta ko baba ne ya roke shi ya aureta? Har ga Allah tana tsoro sossai irin sossai d'in nan wadda take so yake sonta ma ya aka kare bare kuma wadda bata sani ba be santa ba? Hawaye ne ya gangaro mata da sauri ta goge ta furta a fili "na gaji da kukan nan haka" ta mike ta fad'a toilet tayo alwala tare da fitowa ta tada sallah.
Ta jima tana nafilfili In tayi sujjada se tafi minti ashirin tana yiwa Allah kirari tana kai mishi kukanta seda taji ta samu natsuwa kan ta mike ta hau gado ba 'bata lokaci kuwa bacci ya saceta, ta manta when last tayi bacci cikin kwanciyar hankali taji baccin ya mata daad'i irin yau da kyar ta tashi sallan asuba ta lalla'ba tayi kan ta mike mama ce da girki hakan yasata nufan kitchen kai tsaye aiko ta samu har ta hura icce har kasa ta duka "Ina kwana mama?" Mama tace "Lafiya klau iman ya kika fito yanzu kije ki kwanta ki huta na san har yanzu jikinki be yi karfi ba".
Murmushi tayi kan tace "Mama na ji sauki fah, school ma zan shiga ina da aji karfe takwas" Mama tace "a'a wani makaranta kuma iman? Yaushe aka sallamoki daga asibitin? Baza ki kara hutawa ba" Shagwa'be fuska tayi tace "Mama na warke fah In ban je ba akwai matsala wallahi gashi yayi test ina asibiti" Mama ta girgiza kai kan tace "ke kika sani, kije ki zauna In fara sa miki ruwan wanka In yaso kika juye se in d'aura sanwar" juyawa tayi ta d'auki tsintsiya ta fara share kasar gidan.
Tsab tayi shara mai kyau ta gama kan ma ta gama Mama ta juye mata ruwan a bucket ta d'auka ta shige toilet bata wani 'bata lokaci ba ta fito ta shirya duk de kayanta yawanci materials ne atampha In za'a mata se na dubu ko dubu da biyar wato robber kenan shiyasa gwara ta d'inga material d'inta, cikin wani fari da jan material ta shirya dayake ta d'an yi rama se rigan ya nemi yi mata yawa.
A haka de ta sanya ta sa red robber himar d'inta ta fito da farin flat shoe d'inta da kuma karamin hand made side bag d'inta, sama sama ta sha kunun da mama tayi bata ma tsaya jiran d'umame ba ta fice, In tace zata hau keke napep ba abinda ze hanata makara hakan yasata hau machine takwas saura minti uku ya sauketa a kusan hall d'in da zasuyi lectures d'in.
Waro ido tayi ganin shi a kafa da alamu ya d'an tsaya office kuma a chan ya bar motan, da hanzari yake tafiya irin de tafiyar maza masu ji da jini a jika Ai bata san sadda ta fara gudu ba har yayi stepping kafanshi cikin class ya juya da nufin rufe kofa kenan ya hangota tana gudu se ya dakata tana isowa ya kauce ta shige kan ya ja kofanshi a bayanta ajiyar zuciya ta sauke tana hakki, se kuma ta d'aga kai don kallonshi se carab suka had'a ido, ko second idonshi be kai cikin nata ba ya kawar da kanshi tare da haurawa stage.
Da mamaki ta karasa ta zauna me ke damunshi haka? Ko de ita ne take ganin kaman 'bacin rai shimfid'e a fuskanshi? Kallonshi ta ci gaba da yi as usual black pants ne jikinshi da Armani shirt baki se wasu shegun timberland suma bakake sanye a kafanshi gashin nan ya sha gyara har ya gaji se yau taga abinda d'alibai da wasu lecturers d'in ke kiranshi yayi daidai da yanayin shi da komanshi. a kan lips d'inta ta furta.
"Youngest biologists" bata hangi zarah ba duk jujjuyawan da tayi kuwa se kawai ta bud'e littafinta ta fara jotting abinda yakeyi, tabbas ranshi a 'bace yake ranan Kuma cike yake da damuwa sbd jiya bayan isowanshi hamna ta iso, dukda yayi mamakin ganinta amma se be nuna ba, sema shareta yayi yaci gaba da harkokinshi dayake da ya dawo be shiga gida ba yasa bayan isha yayi wankanshi tare da shiryawa ya fito parlorn sama.
Nan ya ganta tana kallo ba tare da ya kula ta ba ya nufi sauka, wani irin turirin bakin ciki ne ya taso mata yanzu fah wurin buduruwarshi zashi ko? Ga wani fitinanne kamshi irin nashi da ya bule parlorn tun kan ya fito haka zashi wurinta? Bata san sadda ta sha gabanshi ba, se kawai ganin mutum yayi kerere rike da kwankwaso cikin rashin kunya tace "Ina zaka?".
With so much surprise yace "wow!! Yaushe muka fara wasan haka dake ban sani ba?" Tace cikin rigima irin nata "Ai haka zaka ce tunda zaka je wajen buduruwarka ba ko kuma ince karuwarka maci amana kawai Ai na ji labari, baka san an dena kiwon dabba yanzu se mutum ba?" Girgiza kai yayi dukda zafin karuwarka da ta fad'a na sashi jin kaman ya d'auke ta mari haka ya danne ya ra'ba ta gefenta ze wuce se yaji ta rike mai riga tana fad'in.
"Wallahi ba inda zaka je ba wurin wata shegiyar da zaka, 'yar iska 'yar gidan mayu wallahi ta kuskura ta shigo gidan nan sede gawanta wallahi se na da'ba mata wuka In kuma da'bawa kaina komai ze faru sede ya faru, munafuka 'yar gidan munafuk...." Tass ya d'auketa da mari ya kuma kara mata, bata san sadda ta sakeshi ba cikin kaushin murya yace "nan gidan shine gidan zamanta na har abada do your worst, wawiya marar hankali kawai".
Ya wuce ya fice abinshi ihu ta kwala kaman wata mahaukaciya tare da nufan d'aki daga ita se wani banzan crazy jeans da crop top a hakan ta d'auki hula ta sa a kanta tare da zaran keyn mota ta fice da gudu kaman wata mahaukaciya se yanzu ta tabbatar auren ze yi da kokonto da maganan boka takeyi.
Direct gidan Abba tayi da kuka da komai ta shiga se kuwa ta ganshi zaune parlorn kasan da umma da kuma Hafeez, me makon tayi shiru se ta kara karfin ihunta taje gabanshi ta tsaya "baka isa ba wallahi, baka isa ba azzalumi macuci kawai baka isa ba Abdulraheem...." ta karashe da matsanancin kuka a zuciye ya mike ya nufi gaban stand d'in ummu ya fisgo wayoyin wutan dake wurin yayi kanta.
Ihun da ta tsala yasa Abba shigowa da sauri dama yana kusan shigowa cikin parlorn da sauri ya rike hannun Abdul da ke shirin sauke mata bulalar "subhanallah, hasbunallahu wani'imal wakeel, Abdulraheem??? Matarka ta sunna?" Tsabar baccin rai jikinshi har rawa yake yace "Abba na gaji wallahi na gaji da halin kubra wata rana zan iya karyata In bata kiyayeni ba" Ummu tace cikin mamaki "Lallai Abdulraheem ka cika, a gabana ka kalli cikin idanuna kace zaka karya 'yar uwarka kuma matar aurenka? Ke hamna me ya had'aku?" Hamna dake jikin ummu take aikin kuka tace "ummu aure naji ana ta magana a gari ze yi, Da na tambayeshi shine..... shine ya wankamin maruka har biyu and he said I should do my worst......" ta karasa da kuka sossai.
Cikin tsananin shock ummu tace "Aure Abdulraheem? Da gaske take?" Shiru Malabo yayi cikin tsawa tace "Aure? Da izinin uban wa?" Abba yace "enough rashida, Aure ze yi kuma jibi In Allah ya kaimu ba da izinin kowa ba se na mahaifinshi and In na isa dake yhu should just sit back and watch, and yhu also" ya karasa maganar da maida akalarshi kan Hamna.
"Baze yi ba wallahi Ahmad Ai ba kai kad'ai ka haifeshi ba" ba Abba kad'ai ba Abdulraheem, Hafeez da zarah da ke saukowa seda suka kad'u da jin furucin umma basu ta'ba ji ba duk tsawon rayuwarsu basu ta'ba ji ta d'aga murya saman na mijinta ba se yau and the worst part she even call him with his name without even respect or something.
Abba karan kanshi ze iya cewa be ta'ba ji ta kira sunanshi haka ba se yau danne mamakinshi yayi yace "Na rantse da ubangiji Abdulraheem se ya auri Saudah duk duniya ba wadda ya isa hanani se mahaliccina, ko da kuwa shi Abdulraheem ne ko kuma me martaba, wallahi duk kuwa Abdulraheem be zama mijinta ba ki tabbatar kuma yaranki su shaida ni ni Ahmad Muhammad Malabo se na zama mijinta, mark my words".
Juyowa yayi kan Abdulraheem yace "and yhu wallahi duk sadda naji ko a labari ka kara d'aga hannu ka daki matarka se na mugun sa'ba maka senayi mugun 'bata maka rai, wawayen maza marasa daraja sune masu dukan matansu" se kuma ya sassauta murya yace "Allah mad'aukakin sarki seda ya gindaya sharudda uku kan ya kai ya duka dukan ma ba irin wannan ba na san ka sani so plz ka kiyaye" ya juya kan hamna yace "Kubra" Tace "na'am" yace "Kin san baki fi karfin In Zane ki ba ko? Toh duk