Follow us on social media

Showing 30001 words to 33000 words out of 131683 words

Chapter 11 - NOOR IMAN Yar Baƙin Ciki BY Fatima Muhammad Gurin

nuna suna sona ma basu iya rikeni ba se wadda za'a bashi sadakata, be san darajata da komai nawa ba?" Zarah tace "karki manta ba abinda yafi karfin Allah, da yardarshi mijin da zaki aura yanzu shine mijinki na har aljannah" cikin sanyin murya tace "Allah yasa, na gode zarah na gode da kika maida damuwata naki, and plz karki ce zaki nemi hammad ki kyaleshi da dalilin hakan na sani" tsaki zarah taja, tana kau da maganan da cewa.

"Batun Umma da baba kuma besty kina ganin anya Haka kawai ne?" Se yanzu ma noor ta tuna da ashe tun shekaranjiya da baba ya zo da dare be sake zuwa ba har yau, ya samu an d'auke mishi nauyinta Ai shi a daad'inshi, girgiza kai tayi kan tace "ba wani besty son ransu kawai suke aikatawa bazan d'auki hakkin wani da wannan tunanin ba beside waye ze musu asiri don su tsaneni ni d'aya tal duk cikin 'ya'yansu?".

Zarah tayi Shiru na mintuna kan tace "hakane kuma amm....." ringing d'in wayanta ne ya sata fasa fad'an abinda zata fad'a, kokarin fidda wayan tayi daga cikin jaka kan ta d'aga ma ya tsinke, ganin Hamma Abdul ne yasata sake kira "Assalamu alaikum Hamma barka da rana" yace "wa'alaikissalam warahmatullah kina Ina gaaji? Kin san 4 zan tafi shine kika tafi yawonki ko?" shagwa'be fuska tayi tace "Ayya Hamma am kaima ka san bazan iya tafiya yawo inyi nisa ba bayan na san zakayi tafiya, ganinan zuwa yanzu" yace "Ohk ki sameni gidana na riga na sallami su ummu" Tace "In shaa Allahu" kan suka tsinke wayan.

Mikewa tayi tana kallon noor tace "kinga besty bari In tafi Hamma Abdul ze yi tafiya gashi mun saba tun Ina karama In har ze yi tafiya ni kad'ai ke raka shi har airport" murmushi noor iman tayi tace "Ohk se gobe In kin zo, na gode" tayi maganan tana d'agawa zarahn hannu, har zarah ta fita ta dawo da sauri ta d'auki wayan noor ta bud'e ta d'auki numbern hammad ta fice tana cewa "bye take care besty" murmushi kawai noor tayi.

*****

Tana isa ya fito dama an riga da an sa mishi karamar jakanshi a mota so car d'in da zai kaisu airport kawai suka shige, duk a baya suka zauna, kallo d'aya ya mata yace "me ya faru kika yi kuka auta?" 'Dan Shiru tayi ita ba abin tayi karya ba tsab se ya gane, and bata son mishi maganan noor sbd se ta kara mishi bayani sossai kan ya ganeta dukda yana da gane mutane ta san wani sa'in har da iyayi.

Da waswasi tace "ka tuna friend d'ina na abitin su ya sauban? Har nake ce maka kaman tana cikin da...." yace "yes Saudah right?" Da mamaki ta kalleshi, yace "uhm me ya faru? Rasuwa tayi?" Shagwa'be fuska tayi tace "wani irin fata ne wannan Hamma dan Allah?" Yace "Toh na sani? Me ze saki kuka kanta In ba rasuwa tayi ba?" Nan ta fara bashi labarin noor iman, ba wai don tona asiri ba ko rashin sirri kawai sbd duk rayuwanta shine kawai abokinta kawarta kan ta san Noor, wani irin shakuwa ne tsakaninsu me wuyar fassaruwa, tas ta bashi labarin noor daga farko zuwa yanzu yadda noor ta bata.

Yanzun d'inma da hawaye ta karasa, tana gamawa ana sanarwan 'this is the last and final call for passengers traveling on Air max flight AI 104 to lagos' ba tare da ya bari ta kalli fuskanshi ba yace "bye habeebty take care, we will talk about her when am back" ya fice da sauri, yana zama a sit d'inshi hawayen da ya cika idonshi na gangarowa da sauri yasa hannu ya share, tare da kwanciya ya lumshe ido shi kad'ai ya san abinda ke yawo ranshi har jirginshi ya d'aga.





                     🖤Gureenjo🖤


🥀NOOR IMAN🥀


*Fatima Muhammad Gurin*
              •Gureenjo6763 on Wattpad•


*'yar mutan Adamawa*

💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)

*duk naga comments d'inku na gode and na hakura, Allah ya bar kauna, and this page is dedicated to yhu guys, duk me yin Noor iman Ina yinshi irin over d'innnan, thnks*


                         *018*

Allah sarki baiwar Allah ashe haka tayi rayuwa shiyasa kullum tana cikin damuwa, tunanin wani irin uba da uwa Allah ya bata kawai yakeyi, har ya sauka a Lagos tunanin mafita yakeyi, seda ya shiga taxi tukun ya sake wani kayattaccen murmushi a fili yace "I will see how heartless yhu are, I will definitely see how much yhu dislike your daughter" yayi maganan yana danna kiran Abba.

Bayan sun gaisa ya tabbatar mishi yana da wani magana me matukar muhimmanci randa ya dawo zasuyi, direct room d'in da aka mishi booking ya wuce bayan ajiye shi da me taxi yayi a harabar hotel d'in, wanka yayi ya shirya tare da zubewa kan gado ya janyo wayanshi ya kira sauban, "hey dude ya kk?" Sauban yace "am good how is your trip?" Malabo yace "Alhamdulillah, plz ina neman alfarma ko yarinyar nan ta warke karka sallameta se nan da four days, Ohk?" Sauban yace "ko menene dalili?" Malabo yace "we will talk about it when am back kaima ka san I will definitely tell yhu, so plz just do as I said" sauban yace "Ohk" sallama sukayi.

******

"How dare yhu treat such a humble soul like that? Did yhu know how broken and hurt she is? Ka kuwa san wahalan da ta sha a rayuwa shine zaka saka mata da rabuwa while yhu know she is in need of yhu?" Hammad yace "I'm sorry ma'am who are yhu referring to? Wait who are yhu?" Cikin masifa zarah tace "what!! Mannin hauka kai, baka san wacce kayi broken heart d'inta ba? Dole kace haka Ai tunda ka ji daad'in soyayya da wata har ta baka abinda ita iman bata baka ba".

Ajiyar zuciya ya sauke yana dafe kai yace "na shiga uku, am sorry plz" wani irin dariya tayi kan tace "ba uku kad'ai ba har tara ka shiga, yhu don't have to, yes sbd sorry ba abinda yake ragewa se ma karawa, yhu definitely don't know how mess yhu are in se munyi ido hud'u da kai" in disbelief ya saki murmushi me sauti a zuciyarshi yace 'toooh ko dawa kuma Allah ya had'ani?' Cikin masifa tace "are yhu just laughing at me? Wato ganan mahaukaciya ko?" Shiru yayi ta dinga masifa kaman wata uwar mata, kuma ta fi bragging akan In suka had'u ba, cikin murmushi yace.

"Why not mu had'un yadda zaki samu yin masifanki da kyau, In ma dukan ne se in kwantar da kai amin, tunda sorry be wadatar ba by the way na san nayi laifi but yhu have to calm down and hear me out Ohk? Please" ya karasa da muryan roko, ajiyar zuciya ta sauke kan tace "Ohk Ina zamu had'u?" Yace "cilantro restaurant" Tace "Ohk tomorrow by 4pm" har ze kashe tace "wait! Wait!! Wait!! Ba fa wai na yarda ne don in yi sparing life d'inka ba trust me in silly reason gareka a wurin zaka san ka ta'bo untouchable lady".

Kit ta kashe wayan, wayan yabi da kallo murmushi na su'buce mishi, se kuma ya girgiza kai ya ci gaba da abinda yakeyi a office d'inshi.

******

"Dr. Na warke ba za'a sallameni haka ba?" Yace "no da saura se naga kinyi garas kaman normal mutane kan zan sallameki" shagwa'be fuska tayi tace "but am normal yanzu ma fah" yace "nooo har yanzu da damuwa a ranki and bp d'inki be koma daidai ba" a sanyaye kuma tace "Ai baze ta'ba komawa normal ba, damuwa a jini na yake" kallonta yayi na mintuna kan yace "zan sallameki but se nan da three days" zatayi magana yace "shhhh no but's" murmushi tayi ganin yadda yayi kaman wani da yaro karami yake dealing shima murmushi yayi kan ya juya ya fice.

Mama ce ta shigo bayan fitanshi fuskanta da alamun damuwa zama tayi tana kallon noor tace "iman inace kin fad'awa Muhammad d'innan ya turo ne?" Noor tace "na fad'a mishi mama" mama tace "to kin fad'amishi ya akayi har yanzu Shiru ko zaki sake tuna mishi?" Shiru noor tayi na mintuna kan tace "wani abun ne ya faru? Inna, baba ko umma? Me sukace?" Mama tace "inna ta kawo calandar hotonki baki gani ba abin takaici".

Wani paper haka dogo mama ta fiddo daga cikin jakanta a nannad'e ta mikawa noor, kar'ba tayi hannunta na wani irin rawa zuciyarta a tsinke ta bud'e, hotonta ta fara cin karo dashi daga sama an rubuta 'sadaka! Sadaka!! Sadaka!!!' Daga kasa aka rubuta "Ni malam Hafeez Musa Muhammad Ina me farin cikin sanar daku nayi sadaka da 'yata Saudatu hafeez fisabilillahi, aurenta hud'u duk wadda yaga ze iya yazo ya aureta ba tare da ko sisi ba, har sadaki na d'auke mishi"

Cikin kuka noor tace "Mama wa yayi abun nan amma ba baba ba ne ko?" Mama tace "Da safen nan inna ta kawo mishi tace gudumawarta" wayanta ta janyo ta fara kiran layin baban rabon da ta kirashi da wayanta ta manta, seda ya kusa tsinkewa ya d'aga "Lafiya??" Shine sallaman da ya mata cikin matsanancin kuka tace "baba kaji kaina, ka tausayamin ko da sau d'aya ne a rayuwana dan Allah kar ka raba abinnan, naji na yarda zan zauna da duk wadda kaga ya dace dani amma ka dubi Allah ka kona papers d'in Innan nan, ba don halina ba" Shiru yayi na mintuna kan yace "taya kike tunanin zan banzantar da fad'in uwata sbd ke?" Cikin kukan tace "ka tausayamin rashin soyayyarku gareni kad'ai ya isheni baba, ba se ka kara sawa mijin da zan aura da kuma 'yan uwanshi rashin ganin darajata ba Dan Allah baba".

Ba tare da ya amsa mata ba ya kashe wayanshi, kuka taci gaba da yi kaman ranta ze fita, Mama tayi ta bata baki amma sam ta kasa Shiru ranta ya 'baci da abinda innan nan tayi kuma baba yaki amsa mata yanzu wannan abun ze rabarwa mutane kaman zamanin da? Yanzu da gaske ana abu haka a fili ba a labari ko hikaya ba? Wayanta ta kuma d'agawa ta kira Zarah.

Tana d'agawa tace "Zarah Dan Allah ki zo, Ina bukatar shawararki, yanzu plz" bata jira cewar zarah ba ta kashe wayanta ta ci gaba da kukanta, har zarah ta shigo kuka take cikin damuwa zarah ta zauna tana tambayar Mama lafiya? Mama da lokacin tayi Shiru tana ta aikin kallon iman d'in tace "toh zarah gashinan dai lafiyan yayi karanci bari In barku ku tattauna" ta mike ta d'auki taburma ta fita.

Kafad'anta zarah ta dafa ganinta cikin situation d'innan kawai yasa idonta cika tab da hawaye tace "besty menene ya faru kuma?" Cikin kuka noor iman tace "Zarah inaga duniya zan shiga" waro ido zarah tayi tace "what??? Noo baza ki shiga duniya ba besty kina tunanin don iyayenki sun miki laifi don kawai basu baki soyayya ba shi ze sa Allah ya kasa kamaki da hakkinsu In kin shiga duniya? Tukuna ma me ya faru?".

Calendar d'in ta mika mata kar'ba tayi ta bud'e bata san sadda ta zauna ba, dafe kai tayi kan ta d'ago ta kalli Iman da itama kallon nata takeyi tace "Wa yayi wannan abin?" Iman ta kauda kanta cikin takaici tace "inna, and ta sa baba dole wai se ya rabarwa mutane massalatai massalatai I even call him begging him not to do that, but se hanging min wayan yayi a kunne, Zarah menene shawaranki?".

Zarah tace "ki kwantar da hankalinki In shaa Allahu zan samo mana mafita baze raba ba da yardar Allah" hawaye ne kawai yaci gaba da gangara a idonta tana girgiza kai tace "zarah baki san baba bane, tunda har inna ce ta saka shi Toh fah baze lankwas...." Zarah ne ta katseta "In shaa Allahu zamu samu mafita, I will seek advice from a trust person of mine kuma zakiga munyi nasara, plz ki kwantar da hankalinki ki dena kukan nan kin san de bpnki har yanzu be sauka ba, Bari kiga In kira ya sauban yazo ya kara miki allura samun ki huta kukan nan ya isa haka plz".

Kiran dr sauban tayi a waya ya tabbatar mata baya nan amma ze turo nurse tayi mata allura, kashewa tayi ba'ayi minti goma ba se ga nurse tazo ta mata allura nan kuwa bacci ya tafi da ita, mikewa zarah tayi ta fita cike da damuwa hannunta rike da calandern, a mota ta zauna tana dafe kai, ta jima a haka kan ta d'aga wayanta ta yi snapping calendern, tare da shiga WhatsApp ta turawa Malabo, kiranshi tayi yana d'agawa ta fashe da kuka.

A rud'e yace "zarah lafiya? Me ya sameki me ya faru kike kuka?" Ganin ya shiga damuwa yasa tace "ka duba whatsapp se muyi magana" kashewa yayi a take ya kunna data ya hau kan sunanta da yayi saving da 'fav. Sis❤️' hoto ya gani hakan yasa yayi downloading, mikewa tsaye yayi yana kara karanta rubutun dake jikin calendern, da sauri ya fita ya shiga calls ya kira Zarah.

Tana d'agawa yace "Allah ya sa basu rabar ba" zarah tace "I don't think Hamma, plz me kake gani zamuyi mu taimaka mata bakaga irin halin da ta shiga ba sbd wannan tozarcin da ake shirin mata" d'an Shiru yayi na seconds can yace "I know what to do karki damu, and plz stay with her ki kwantar mata da hankali" sbd saninshi da tausayi da tayi yasa bata kawo komai a ranta ba tace "Toh Hamma" yace "bye" tare da kashe wayan.

********

Safa da marwa ya fara tare da dunkule d'aya hannunshi yana bugawa a tafin d'ayan, ba plan d'inshi ba kenan duk wannan seminar ne ya hanashi aiwatar da plan d'inshi yadda ya tsara, yanzu me ze yi don baba ya fasa raba abun nan? Kanshi ya d'an bubbuga yana cewa "think! Think plz" had'a yatsunshi biyu yayi ya murd'e suka bada sautin 'dasss' kan yace "yess that's what am going to do" wayanshi ya d'auka ya kira Abba.

Bayan ya d'aga cikin ladabi suka gaisa kan yayi gyaran murya cikin natsuwa ya baiwa Abba labarin noor iman kab ba abinda ya 'boye sbd be son Abba yaje aiwatar mishi da idean d'inshi a samu wani wadda ze gayamishi karya da gaskiya yace ya fasa don ya san Abba mutum ne in yace yes ba wadda ya isa maidashi no haka in yace no to ba wadda ya isa maidashi Yes.

Kaman yadda ya zata sossai Abba ya tausayawa noor balle kuma da yaji karamar yarinyace da irin wannan kaddaran, cikin sanyin murya yace "Toh babana kai yanzu me kake gani shine zamuyi mu taimaketa sbd taimakon irin wannan jahadi ne, dukda ni ba mutum bane me yarda da tsubacce tsubacce ba wai nace babu ba amma yanzu samun na gaskiyan wuya ne dashi, se In ga kaman yarinyar ba'a barta haka ba, ko da ba mutum ba ze iya yiwuwa tana da aljannu, taya akayi baiwar Allahn nan ta rayu da irin wannan kalubale da in wani me karamin zuciya ne da ya dad'e da mutuwa, Ko kuwa ta shiga duniya ta aikata abinda ake jefanta dashi da kyau yadda za'a samu hujja".

Hmm kawai malabo yayi yana girgiza kai shi kad'ai ya san irin tausayin da yake ji akan yarinyar cikin karfin gwiwa yace "Abba aurenta nake so inyi" ya zata Abba baze yarda ba se kuma yaji yace "masha Allah that's wonderful idea" Abdul yace "and Abba bana so mu nunawa iyayenta dukiyarmu yanzu I mean if possible muje musu a talakawa marasa karfi, ni karan kaina in je musu a matsayin mashayi, I want to see how extent ya kai da kin yarinyar nan" Abba yace "Allah na gode ma, Allah yayi muku albarka" malabo yace "Ameen, Abba plz kaje wajenshi yau samun kar ya raba hotunan tozarcin nan and plz it should be secret ko ummu kar ta samu labarin auren nan sbd ka santa In abu yazo da maganan ta'bo hamna" a haka suka ajiye kan sukayi sallama.

******

"Assalamu alaiki hajiyar fad'a ban sani ba amma zuciyana na bani daidai na chanka, duk toshewar nan sbd a mazge ni ne?" Ya fad'a da zolaya, kara had'e rai tayi dukda dariya da magananshin ya bata, se kawai tace "wa'alaikassalam" zama yayi ya koma serious kan yace "Zarah right? In ba na manta ba" zarah tace "hkne uhm Ina jin reason d'inka" yace "zarah baza ki gane yadda nake son iman ba amma ba yadda na iya Allah be za'beta a matsayin matata ba, zarah ya kike so d'an da uwarshi tayi rantsuwa sau uku tace muddin ya auri yarinyar da yake mutuwar so bata yafe ba duniya da lahira ko da kuwa bayan ranta ne?" Ya karashe idonshi na kad'awa.

Cire glass d'in idonta tayi tana kallonshi se kuma ya bata tausayi she can feel it sincerity d'inshi yake gayamata, ya d'aura da "kiyi hakuri sannan ki tayani ba iman hakuri ban san hawan jini da heart attack ke damunta ba seda na furta mata kalmar rabuwa, tabbas na so bari se ta warke In gayamata amma mom tace zata je har asibitin ta sameta tsoron kar taje ta tozartata yasani gayamata, na so jin ko labari iman ne ko da ba da aure bane in ga in zan iya taimaka mata amma yanzu bazan iya fuskantanta ba".

Hawayen da ya zubo mishi ne yayi saurin d'aukewa, a sanyaye zarah ta fara bashi labarin Iman se ga hammad ya rufe fuska da handkerchief har ta gama be iya bud'ewa ba ya jima a haka yana jin yadda zarah take fitar da nata kukan kan ya goge fuskanshi ya fiddo wani ya mika mata, kar'ba tayi tana goge fuskanta ganin hankalin wasu ya fara yowa kansu, ya jima sossia kan ya iya magana "kina ganin hammanki ze iya taimaka mata?" Tace "kwarai kuwa Ina da tabbacin hakan, ko da ba ze iya ba bazan so ka sake shiga magananta ba don ta riga ta kokarta cire ka a zuciya Allah ya sa ba wai ta fad'a dayawa bane, sannan ko bata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login