Follow us on social media
Showing 60001 words to 63000 words out of 131683 words
Chapter 21 - NOOR IMAN Yar Baƙin Ciki BY Fatima Muhammad Gurin
ba tare da ta sani ba, kuyangin kofa ne suka sanar da isowansu kan shigansu ciki, a parlor suka samu familyn baje, murnan ganin en uwanta ne ya kamata yayinda su kuma suke wani yatsina fuska, har kasa ya duka ya gaidasu suka amsa kaman basa so musamman inna, itama gaishesu tayi basu amsa ba se d'aid'aiku karfin hali tayi tace "ina Mama?" Wata daga ciki tace "tana d'aki bata da lafiya kwa iya shiga" shiga sukayi tana kwance kan gado lullu'be da blanket.
Da sauri iman ta karasa kanta tana hawaye tace "Mama me ya sameki haka? Me ke damunki? Mama me yasa baki fad'amin ba?" Murmushi tayi kan tace "Da sauki Iman karki damu kinji? Zazza'bi ne kawai" Abdul ma gaisheta yayi yana mata Sannu da jiki ta amsa kan ta d'aura da "Abdulraheem ga amanar Iman na baka duniya da lahira yanzu bata da kowa sama da kai dan Allah ka riketa amana, kayi mata adalci a rayuwanta ka zama daban cikin saraun mazanta".
Yace "In shaa Allahu Mama zaki sameni me cika alkawari" godiya ta mishi tana murmushi Tace "kayya iman me kuma na kukan nan eye? Naji sauki tashi maza kibi mijinki kiyi mishi biyayya iya iyawarki, ki zama mata ta gari ki tabbatar kinyi anfani da maganganun da na jima Ina gayamiki akan rayuwar duniya da kuma zaman aure na Sanki da hakuri ki kara akan na da, kinji? Allah ya miki albarka".
Kuka sossai Iman ke yi ya mike yana cewa "Mama za'azo a kaki asibiti, Allah ubangiji ya baki lafiya" Da Ameen ta amsa, hannunta ya kama suka fito parlorn tana me ci gaba da kukanta har sun nufi kofa Inna tace "ke saude dakata" tsayawa sukayi ta juyo shikam ko motsi be yi ba, goggo saratu tace "Allah sarki bawan Allah abin tausayi baya cikin hayyacinshi" goggo kamila tace "wallahi kuwa daga gani ka san aikin asiri ne" inna tace "wani irin boka kike anfani dashi ne Saude? Allah wadaran naki ya lalace yanzu duk mazan da kika aura kika kashe wasu kika kassara wasu be isheki ba se kin had'a da wannan kamilallen da bai Dace dake ba?".
Iman zatayi magana kenan taji yace "Allah sarki baby Ashe boka kika samu ya mallakeni? Da kuwa zan ganshi da na kara mishi kud'i ya kara mallaka miki ni se yadda kikayi dani" gira ya d'aga mata yana wani murmushi yace "Bazaki san irin son da nake miki ba Allah, sonki kaman ze huda nan ya fito" ya karasa yana nuna mata kirjinshi, waro ido tayi ya kashe mata ido yana me jan hannunta jikinshi ya zagaye kwankwasonta da d'ayan yace "bazan ta'ba iya rayuwa ba ke ba, don't you ever think of leaving me Ohk?" Tsantsar mamaki ne ya sata d'aga kai bata ma sani ba juyawa yayi ya sakarwa su inna murmushi kan ya jata sukayi waje wayyo ina wuta Inna ta saka Abdulraheem🤣🤣🤣, dama zargin dole aka mata sukeyi to gashi ya basu kunya ya watsa musu tulin kasa a ido.
🖤Gureenjo🖤
🥀NOOR IMAN🥀
*Fatima Muhammad Gurin*
•Gureenjo6763 on Wattpad•
*'Yar Mutan Adamawa*
💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)
*030*
Suna fita ya saketa yana jan karamin tsaki, karamin murmushi tayi se yanzu ta gane sbd su yayi Don ya nuna musu ba auren tushe aka mishi ba, kuma ba laifi taji daad'in hakan, mota suka shiga aka wuce da su part d'insu dake kusa sossai da part d'in su Abba, babban parlor ne irin babban nan, a ciki katon kitchen d'insu yake guda d'aya se d'akuna guda uku a jere na hagun ya nufa itama tabi bayanshi har ciki, wow royal set ne a d'akin komai da komai golden, sossai d'akin ya mata kyau kasancewarta me son royal sets, a tsakiyar d'akin ya dakata kan ya juyo ya kalleta se ta dukar da kai.
"Ga room d'inki nan Zarah zata kawo miki kayanki gobe in Allah ya kaimu zamu wuce sbd school d'inki" a hankali tace "Toh na gode" fita yayi itakuma ta zare alkyabbar jikinta da d'ankwalin kanta tana zama bakin gado, yanzu wai nan ne d'akinta? Na garin nan kenan da zuwa kawai zasu dingayi Ina kuma na kano da Abba ya d'auki nauyin yi mata kayan d'aki? Tana nan zaune Zarah ta shigo.
Murmushi suka sakarwa juna kan tace "se yanzu kika gama kwalliyar kenan?" Zarah tace "bazaki gane bane, yanzu ga Akwatinki nan duk abinda zaki bukata yana ciki, bari In wuce" hararanta Iman tayi tace "zuwa Ina? Zama zakiyi madam ni kad'ai zaki bari nan?" Dariya zarah ta saka tana cewa "Lallai matarnan dama tare zamu zauna? Kinga tafiyata bye bye se mun had'u gobe a kulamin da yayana" da sauri Iman ta tashi zata riketa da gudu zarah ta fice tana dariya.
Dawowa tayi tana dafe Kai ta zauna bakin gadon again, har Tv me d'auke da receiver da kuma Fridge akwai a d'akin da kujera dogo royal guda d'aya gabanshi akwai center table shima de cikin sets d'in royal d'inne, se gadonta da wall to wall drawer d'inta me madubi tsakiya, d'ayan 'bangaren kuma kusa da wani kofa dressing mirror ne me azababben kyau.
Ga dukkan alamu kofan na toilet ne, mikewa tayi ta cire kayan jikintan Don ya isheta akwati ta bud'e ta d'auko towel d'inta da a jiya komai na ciki ta fara anfani da su, d'aurawa tayi ta nad'e kayan ta ajiye bakin gado ta d'auki sponge da liquid soap da shima jiya nenne ta had'o mata ta fad'a toilet wanka tayi, dayake a jiyan Zarah ta nuna mata duk yadda zatayi anfani da irin toilet d'insu, toilet d'inma kanshi abin kallo ne.
Sanin ita kad'aice kuma ba shigowa ze yi ba yasa ta fito da towel abinta, shafa mai tayi ta feshe jikinta da turaruka kan ta d'auko wata doguwar rigar atampha straight gown ta saka ya amshi jikinta sossai ta fito a amaryarta, dayake ta iya d'auri sossai haka ta kafashi a kanta, wayanta ta d'auka tayi kiran Mama seda ya kusa katsewa kan taji an d'aga "hello mama ya jikin? An kaiki asibitin" muryanshi taji yace "an mata allura she's sleeping" da mamakin taya akayi wayan Mama ya shiga hannunshi tace "kuna asibitin ne?" Yace "yeah but drip d'in da aka sa mata na karewa zamu taho" Tace "Toh Allah ya kara sauki" Da Ameen ya amsa kan ya kashe wayan.
So take tace zata zo amma tana tsoro, tv ta kunna ta fara kallo ganin shima be mata ba yasa ta mike ta fito parlor a kan kujera ta kwanta tana tunanin inda rayuwa ya kawota, har bata san bacci yayi awon gaba da itaba, se da akayi azahar kan ya nufo part d'inshi duk a gajiye yake bukin nan ba karamin gajiyar dashi yayi ba gashi har yanzu be huta ba, tsaki ya ja yana tura kofan parlorn.
Ba abinda ke tashi a parlorn se kamshin turaren wuta me sanyi, direct d'akinshi ya nufa ba tare da ya lura da tana parlorn ba, wanka yayi yayo alwala ya fito tunanin Ummunshi kawai yake anya ze iya jurar fushinta a kanshi? Shi kad'ai ya san irin azabtuwar da yakeyi wallahi, kanshi dake sarawa ya dafe ya jima a haka kan ya sake kan ya fara shafa mai bayan ya gama ya bud'e closet d'inshi da tunda ya zo ya cire kayan akwatinshi ya mayar ciki sbd shi be iya anfani da kaya a cikin akwati.
Bakaken kananan kaya ya sanya as usual ya feshe jikinshi da turarukanshi Bvlgari man in black da Aqua di jio (Armani) take d'akin ya bule da fitinannen kamshinshi, wayanshi d'aya kawai ya d'auka ya fito da nufin tafiya masallaci se kuma ya ga dacewar ya dubata yaga lafiyanta, d'akinta ya nufa kanshi tsaye ya shige ciki da mamaki yaga ba kowa a ciki d'an tsayawa yayi yaji ko ze ji karan ruwa a toilet nan ma Shiru be ji komai ba.
Fitowa yayi yana tunanin Ina itakuma tayi har ya wuce ya sake dawowa ya zagayo cikin parlorn dayake ta bayan kujerun hanyar d'akukansu suke, ganinta yayi tana baccinta hankali kwance akan doguwar kujera, da ido ya kafeta fuskanta fayau ba ko d'igon kwalliya se tafi mishi kyau akan da kwalliya, lura yayi da tana jin daad'in baccinta sossi hakan ya sa yaki tashinta ya juya ze tafi kenan tayi wani irin juyi saura kad'an ta hantsilo da azama ya tareta chak ya d'agata ba tare da tunanin komai ba ya kaita d'aki kan gado ya shimfid'eta yana zame mata d'ankwalin kanta.
Ya shafa kan a hankali kan ya mike ya fito yayi tafiyarshi masallaci, daga nan part d'in me martaba yayi a babban parlornshi ya sameshi zaune bayan an mishi iso, a kasa ya zauna yana gaida dattijon Amsawa yayi yana tambayarshi Ina amaryarshi dariya kawai Abdul yayi, suka fara hira da kakan nashi akan matsalan Noor ne duk hiran ya karkata inda yake fad'amishi yaji labarinta gabad'aya a wurin nenne why not kan su wuce su je fufore wurin malam.
Abdul yace "mai martaba tafiyarmu fuforen nan da wuya tana makaranta lectures dayawa zuwa yanzu sun wuceta, and ni a ganina hasashen nenne ne kawai, bawa kaddara be isa fad'amishi ba seda asiri? Amma In kana ganin muje d'in zamu je idan munzo sallah karama tunda azumi ya gabato" mai martaba ya d'anyi shiru yana nazari tabbas maganan nenne ba hasashe bane akwai ayar tambaya akan Matar tashi amma tunda yace In sun zo azumi zasu je shikenan.
"Toh Allah ya kaimu da rai da lafiya" Abdul ya amsa da ameen ya Allah, Abba ne da baba yarima da kuma baba galadima suka shigo a tare da sallama, mai martaba da malabo suka amsa a tare, zama sukayi duk a kasa suna kara gaida mai martaba amsawa yayi da fara'a, basu jima da zama ba nenne da mama suka shigo, Se ga Nenne petel ma ta shigo duk gaisuwa suka mikawa mai martaba ummu ce karshen shigowa itada rahama suka shigo.
Suka gaida iyayensu yayinda Abdul ya gaisheta kaman bata ji ba haka tayi kanshi ya dukar cikin kunar rai, gyaran murya me martaba yayi kan yace "Ina uwargidan nawa?" Yayi maganan yana duban Abdul cikin sanyin murya yace "Allah sene banda masaniyar inda take rabona da ita tunda muka shigo masarautar nan" kwafa nenne tayi baba galadima ya kalli nenne petel yace "suna ina ne?".
Nenne petel tace "A min aikin gafara mai martaba banda masaniyar bada izinin mijinta take zaune part d'ina ba, tun safe suka fita da mahaifiyarta akan zasu je yanzu su dawo har yanzu basu dawo ba kuma wayoyinsu duk basa shiga" girgiza kai mai martaba yayi kan ya kalli ummu yace "Rashida" d'agowa tayi tana furta "Allah ya kara tsawon rai" yace "menene matsalarki akan auren Abdulraheem?" Gyara zama tayi tace "mai martaba yarinyar fa aurenta biyar sannan na samu labarin duk inda ta zauna se ta raba kan mutane da munafurci irin nata musamman uwar miji da shi mijin da take aure".
Murmushi irin na manya yayi kan yace "Shine dalilin da yasa kika ce d'anki kar ya kara nuna miki fuskanshi?" Kai ta gyad'a tana karawa da "mai martaba har fa ciki ta zubar kwanan nan" Baba galadima yace "Rashida ki kiyayeni kin tabbatar?" Zatayi magana mai martaba yace "Abdulraheem" Malabo da baba galadima a tare suka d'ago yana kallon Malabo yace "kirawo matarka" mikewa Abdul yayi ya fita.
Mota ya hau zuwa part din shi don be san ko ta tashi daga baccinta ba In ma ta tashi be da tabbacin In ya kirata a waya zata iya kawo kanta sashin me martaba, da sauri ya shiga d'akinta har yanzu bacci takeyi, kanta yayi a hankali yake d'an bubbuga hanunta yace "Saudah! Saudah!!" Idanunta ta bud'e ta zuba mishi da sauri ya kawar da nashi jin wani abu ya tsarga mishi sbd ganin sleeping eyes d'inta.
"Tashi me martaba na son ganinki" da sauri ta mike zaune zatayi mishi tamabaya yace "ina jiranki parlor" yana kai nan ya fita, bayi ta shiga ta wanke fuskanta da sauri ta fito ta d'auki d'ankwalinta ta d'aura tare da d'aukan alkyabbar d'azu ta saka ta zuro flat shoe ta fito, dafe da Kai ta ganshi har ta iso kusa dashi be sani ba seda tace "hamma muje" kan ya d'ago ya d'an kalleta ya kau da kai.
Gabanta ne yayi mummunar fad'uwa ganin yadda idonshi yayi ja, be bata daman tambaya ba har suka iso se sake sake kawai take, a tare suka zauna tana mika gaisuwanta zuwa ga mai martaba ya amsa da fara'a kan ta gaida sauran mutane parlorn duk sun amsa banda ummu, mai martaba yace "Saudah zaki iya bamu labarinki?" Ajiyar zuciya ta sauke kan ta fara bayarwa a hankali tun muryanta na rawa har ta fara Hawaye tun tana hawaye har ya koma kuka sossai.
Wani irin tsuma jikin malabo ke yi dukda ya ji daga bakin zarah amma se yanzu da take fad'a da bakinta yaji tafi bashi ainihin tausayi be san sadda ya d'aura hannu a bayanta yana shafawa a hankali ba, har ta kai aya, matan ma seda suka kuma mata hawaye banda Ummu da mama da suke ta ta'be baki, mai martaba kanshi ya tausaya mata, kallon ummu yayi yace "yanzu yarinyar da ta fuskanci irin wannan taskun kike son kara d'aura mata wani? Kiji tausayinta mana rashida yanzu idan Zarah ce ta fuskanci irin wannan ibtila'in baza ki so uwar mijinta ta so ta ba?".
Shiru duk sukayi zatayi magana Baba galadima ya daka mata tsawa "Rashida Anya kuwa? Kina kuwa son gamawa da duniya lafiya? Kar fa ki kasance cikin waenda Allah yayi maganarsu a hadisi zaki ga suna aikata aiki na gari se mutuwa ya riskesu su aikata akasin haka su shiga wuta, Toh ki maida hankalinki kiji da kyau Wallahi wallahi wallahi duk randa kika sa me suna ya rabu da matarshi ki tabbatar kaman kin rabu da mu ne har abada, kallon Abba yayi yace "Ahmad" Abba ya amsa yana kallon matar tashi dake kuka tana ganin fa kaman duk baza su fahimci abinda take jiyewa d'anta ba.
Gani take kaman duk labarin da Iman ta bayar karya ne ita ta tsara kayanta ta fad'a, "For the first time a rayuwana zan rokeka alfarma" Abba yace "baba ka fad'i duk abinda kake so in Allah ya yarda ni me cika maka umarninka ne" Baba galadima yace "Ina so ka fad'a da bakinka mu zama sheda duk randa ta sa d'anta sakin matarshi a bakin aurenta, In ta ga dama kar ta amsa gaisuwarshi har abada".
Iman sossai ta shiga tashin hankali fahimtar abinda ke faruwa anan Ummu bata sonta bata son aurenta da Abdul, kallonshi tayi kenan shine sanadin damuwanshi mahaifiyarshi bata amsa mishi magana, cikin rawar murya ta bud'e baki zatayi magana nenne dake gefenta ta kama hannunta kallonta tayi se ta girgiza mata kai alamun kar ta ce komai shiru tayi ba don tayi niyya ba, tana ji Abba ya maimaitawa ummu.
Mai martaba ne ya fara mata nasiha da duk ba fahimta take ba itafa Iman ta zama mata annoba a family d'inta tunda duk sbd ita suka za'ba ba wadda ke goya mata baya, yana gama nasiharshi ta tashi ta fice ba tare da ta bada hakuri ba bare ta nuna taji, Nenne petel ce ta share hawayen fuskanta tana gyad'a kai yanzu ta tabbatar da abinda take zargi In ba aljannu bane suka shigi Rashida to fa asiri ne a kanta, zata bi duk hanyar da zatabi taga er ta ta koma kanta In shaa Allahu.
Sallamansu me martaba yayi bayan kowa ya d'an kwantarwa da Abdul hankali akan kar ya damu mahaifiyarshi zata sauko ne da kanta, mikewa yayi Iman ta mike suka fice har suka isa part d'insu kuka take cikin rud'ani yanzu ta raba shi da mahaifiyarshi? Duk irin son da zarah ta fad'amata sunayiwa juna tayi ajalinshi Innalillahi wainna ilaihi rajiun nan kuma matsalar kenan?.
A parlorn ya zube yana kuma dafe kanshi bayan damuwanshi, kukanta yake ji har kasan zuciyarshi, a gabanshi ta zauna ta ci gaba da kukanta, wani irin tsawa ya dakata "will you just shut up and leave me alone? Haba da wanne kike so naji?" Me makon tayi yadda yace se ta fad'a jikinshi ta kuma rushewa da kuka runtse idanunshi yayi tare da amsanta ya zagayeta a hannayenshi, batayi aune ba taji bakinshi cikin nata, tsit kakeji kukan ya tsaya se numfashin da take ta ajiyewa, shi kuwa yayi hakanne don tayi shiru ne amma kuma se yaji abin na neman fin tunaninshi.
🖤Gureenjo🖤
🥀NOOR IMAN🥀
*Fatima Muhammad Gurin*
•Gureenjo6763 On Wattpad•
*'Yar Mutan Adamawa*
💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)
*Wannan page d'in naku ne masoya wannan littafin, Ina godiya kuma Ina jin daad'in comments d'inku, Allah ya bar kauna*
*031*
A hankali ya d'agota yana kallonta da tsantsar mamaki wai bacci tayi d'an girgizata yayi yaga fa tsakaninta da Allah bacci tayi a fili ya furta "ikon Allah" kan ya mike da ita a hannunshi yaje ya kwantar da ita se kuma ya tuna batayi sallahn azahar ba, fuskanta ya fara shafawa yana kiran sunanta a hankali, da kyar ta bud'e sexy eyes d'inta ta zuba mishi idanunshi ya kawar yace "tashi kiyi sallah kici abinci se kiyi baccin" yana kai nan ya mike ya fice, da kyar ta mike tayo alwala tazo tayi sallah kanta kaman ze tsage haka take jinshi.
Sallama taji anayi wadda hakan yasa ta mike ta fito parlorn ko d'an kwali bata d'aura ba, kuyangu ne rike da trays sunyi hud'u, kan dining dake gefen parlorn ta nuna musu suka ajiye, godiya ta musu kan suka