Follow us on social media

Showing 6001 words to 9000 words out of 131683 words

Chapter 3 - NOOR IMAN Yar Baƙin Ciki BY Fatima Muhammad Gurin

dake 18 and half wallahi tafi hamna iya duk wani aiki na 'ya mace a gidan aurenta.

Hakurinshi ya kai makura akan hamna wallahi mafita kawai yake nema ko ta wacce hanya, bud'e kofan part d'inshi da akayine ya dawo dashi cikin tunaninshi, kurawa kofan brown oily eyes d'inshi yayi kaman me nazartar wani abu, se kuwa gata ta shigo to my biggest surprise Zarah ce tana kallonshi tace "Ya Abdul gani" tsaki yaja kan ya harareta yace "Ai ban da ido, gyaramin part d'in nan".

Tura baki gaba tayi zata fara diddira kafafu ya watsa mata harara da idanunshin nan nasa masu firgita 'yan mata da gigitasu da fidda su cikin natsuwarsu kai har wasu mazan ma, da sauri ta zare gyalen jikinta ta nufi corridor d'in site d'in don dubo kayan da zatayi anfani dasu a zuciyarta se mita takeyi.

Mutum da matanshi amma itace baiwa komai yake so lil kaza Lil kaza bata isa yin musu ba yaci ubanta In na muguntan na kusa dukda shi ba mutum bane me saurin kai hannu amma yana da zafi fiye da tunanin me tunani, ga riko amma In ka sanshi kuma yana da sanyi da tausayi fiye da zato haka kuma yana son 'yan uwanshi son da baya had'ashi da kowa, musamman ummu.

Ya tsani karya da munafunci haka baya da shishigi akan harkar da ba'a sanyashi ciki ba kai ko da kuwa na cikin gidansu ne. Dr. Abdulraheem Ahmad malabo kenan AKA Dr. Malabo sunan da friends d'inshi da students ke kiranshi.

A natse tayi komai har ta gama a gajiye sossai sbd ko gida bata karasa ba daga makaranta ya kirata yace tazo haka tasa driver pasa shiga layinsu yayi kwana ya shige layin gidan yayan nata dake duk cikin unguwa d'aya wato Nasarawa GRA, kwance ta ganshi akan duguwar kujera kafafunshi na lilo sabida tsawonshi da ya zarta kujerar idanunshi a lumshe hannunshi kwance kan flat tummy d'inshi.

Ita har ga Allah tausayi yake bata ace mutum da aurenka da komai amma kai baka san daad'in mata ba? Ajiyar zuciya ta sauke tace "hamma mi timmini, d'ume bo a yid'i?"(Hamma na gama me kuma kake so?) bud'e idanunshi yayi ya kura mata na mintuna kan yace cikin slang fulatancin shi "wala, dillo tan mi andi a somi, yah sewtu"(nothing, tafi kawai na san kin gaji, je ki huta).

Kai ta gyad'a kan ta fice ta shige mota driver yaja ya fice da ita zuwa gida, a gajiye ta shiga ciki a parlorn kasa taga hamma Hafeez da ummu zaune suna hira, zubewa tayi a jikin ummu tana cewa "wayyo ummu am na gaji" kyakyawar bafulatanan mace da tajiku da kud'i, don jikinta kawai ka kalla zaka tabbatar da haka photocopy d'in Abdulraheem don ba abunda ya bar mata kyakyawace ta ajin karshe dukda she's at her early 50's.

Tace "Eyyah autana sannu, je kiyi wanka ko za kiji karfi se ki zo In miki tausa" murmushi me kyau ta saki tana mikewa tace "Ohk ummu bari nayi sauri, Hamma Hafeez barka da gida" bata jira amsanshi ba ta haura sama.

********

"Hammad wallahi na gaji da magana akan rashin auren nan naka, haba mutum ka girma baka san ka girma ba? Shekaru Talatin da biyar bakayi aure ba kam wai se yaushe zakayi? Am fed up na baka nan da three months ko ka kawo mata ko kuma na za'ba maka duk wacce raina ke so, haba!!!!"

Wadda aka kira da hammad ne naga ya d'ago a marairaice yace "am sorry dad ba nufi na In 'bata muku rai ba don Allah kuyi hakuri" tsaki dad din ya ja cikin yanayin fushi yace "just get lost na gama magana na" kallon mom hammad yayi da nufin ta sa baki se ta ta'be bakin nufin ba ruwana, tare da ci gaba da taunan chewing gum d'inta.

Ba yadda ya iya  hakan yasa ya mike ya fita cikin damuwan 'bacin ran da ya sa iyayenshi, shi fa ba wai auren ne baya so ba, ba kuma sha'awar ne baya ji ba, kawai de shi har yanzu be ga wacce ta mishi bane sam a duniyarshi kuma yana ci gaba da adu'ar Allah ya had'ashi da irin matar da ya dad'e yana mafarkin aure.

Kaninshi na uku ma yanzu d'a d'aya gareshi amma gashi shi har yanzu zaune a matsayin tuzuru, motanshi ya fad'a tare da figanta ya fice a guje direct Zoo road yayi gidan Amininshi Uwais wadda yaranshi uku yanzu kuma sa'annin juna ne, da sallama ya shiga parlorn yaran dake wasa tsakiyar parlorn suka taso da gudu suka rungumeshi suna "oyoyo Uncle, oyoyo" karamin ya d'aga sama ya shilla tare da ca'bewa yana fad'ad'a fara'arshi.

Yace "Ina Abba da mama?" Babbar tace "suna kitchen suna mana dinner" kama baki hammad yayi kan yace "manya!! Oya Abida kira min Abba kice ya sameni a mota" fita yayi niyyar yi bayan ya ajiye Aiman akan kujera yaro kam ba se ya wangale baki ya hau kuka ba, murmushi hammad ya kuma sakewa dukda ba'a rabashi da murmushi sam a rayuwanshi amma In yana tare da yara se ya d'inga jin kaman Aljannah aka mishi bushara dashi sbd tsabar soyayyarshi da yara.

Duk inda ya ga yaro tofah da kuka da komai yaron ze rabu dashi tsabar yadda ya iya tafiyar da su, Uwais ne ya fito sanye da apron abun gwanin ban dariya duk filawa a fuskanshi da jikin apron, hakan yasa yaran da hammad kwashewa da dariya had'e rai yayi yana zare apron yace "ban cike da halin iskanci hammad ka kiyayeni na gayama, Abida oya kama kannenki kuyi d'aki har Aiman".

Kama hannun Aiman tayi ze yi rigima Uwais ya zaro mishi idanu a take yabi yarshin da tafiyanshi da yayi kwari sossai, zama uwais yayi yana cewa "man ya kaman kana cikin damuwa?" Hammad yace "sossai ma Dad ya bani wata uku In fiddo mata ko ayimin auren dole" dariya Uwais ya kwashe dashi ganin yadda hammad ya karasa maganan, zeyi magana kenan matarshi Hajara ta shigo da lullu'binta hannunta rike da tray wadda aka d'aura drinks da snacks akai ta ajiye gaban hammad tana gaidashi at same time.

A ladabce suka gaisa kan ta wuce zuwa d'akin yaranta don ganin me sukeyi, "wallahi dad yayi min daidai, banza tuzuru kawai Ai hakan shine maganinka Haka kawai mutum ya ki aure ya kuma zauna yana aikin shan lemun tsami da lipton wallahi In kayi wasa dad zan kira ince ya matso da watanni ukun da ya baka zuwa sati biyu".

Cewar uwais "aaaaa Kwana d'aya ne ka manta ya za'ayi In zo maka da damuwa na amma se ka zauna kana wani surutun da ba shine ba, Wallahi ni Uwais har yanzu banga macen da ta min ba, kaima ka san macen da nake burin aure" tsaki Uwais yaja kan yace "ba wani abinda na sani mace de sunan ta mace yanzu Inba iskanci ba ace duk matan kano baka ga wacce tayi maka ba? Haba Aboki ni yanxu ba abinda zance sede kaima ka san waye dad tunda ya furta se ya aikata gwara ka bazama neman mata ehe".

Tsaki hammad yaja yana mikewa yace "ba anfanin zuwa wurinka wallahi kaga se anjima" be jira cewar Uwais ba ya fice abin shi shrugging kafad'a Uwais yayi kan ya mike ya nufi neman matarshi.

*****

"Wallahi na gaji da ganinki? Don kawai ba yadda na iya ne da maganan inna wallahi da se de ki nemi gidan wani uban, haba ga mace har mace amma se d'an banzan bakin hali to wallahi na gaji, hotonki zan d'auka In kai massallaci duk wadda yaga kin mishi ko wanene, makaho, kuturu, gurgu, almajiri kai ko menene aura miki shi zanyi in rabu da banzan iri, aikin banza kawai, mtsewwwww".

Baba kenan ke zuba wannan sababin daga gaisuwa, uban da ya haifeni ya kasa yarda da qaddarata Toh wa ze yi? Kallon ummata nayi dake tankad'en garin tuwo daga gefe ko kallon inda muke batayiba hankalinta kwance harda 'yar wakarta da fillanci, hawayen idona na goge ina me tuna mutuwar aurena na karshe, wadda a lokacin ne kad'ai umma ta iya bud'e baki tace "Allah ya kyauta" bayan na dawo gida.

Isma'il da uwarshi da kannenshi suka had'u suka min dukan mutuwa don baba ne ya kawoshi kuma yace kar na fad'a mishi komai akan rayuwata ya riga ya mishi bayani soyayya sama sama mukayi don irin mutanen nan ne masu zafin zuciya da bakin hali, yana son kowa ya dinga jin tsoronshi cikin har matar aurenshi matarshi d'aya da yara hud'u, had'uwarmu da auren be fi sati biyu ba, ba yadda na iya sbd bana sonshi amma baba ya nace haka akayi aure.

Har nayi sati biyu a gidanshi a lokacin ne ya fara jin jita jitan mutane a kaina ashe ba tun ranan ya fara ji ba, wani abokinshi ya ta'ba fad'a mishi amma se ya karyata abokin ya kuma tabbatar mishi duk randa ya kusanceni to wallahi mutuwa ze yi don haka aka ce (kuji sharrin bil adama) hakan yasa ko d'akinta baya shiga tun be yarda ba har ya samu shedu dayawa a kaina wadda duk na karya ne don ba wadda ya san waceceni se ni kaina.

'Yan uwanshi ya gayawa ni da ubana mun munafurceshi haka suka min dukan mutuwa suka kuma koreni ba tare da sun ban ko sisi na kud'in mota ba daga katsina zuwa kano, a rayuwata ban ta'ba roko ba se a lokacin na zama marokiyar karfi da yaji, da kyar na samu d'ari hud'u na taka zuwa KSTA na sami kano line suma da kyar da wulakanci suka d'aukeni sbd kud'in be cika ba.

Haka da muka iso kano da kafa na dinga takawa har gidanmu na ci azaba kafana kaman ze 'balle da kuka da komai na ba su baba labarin abinda ya faru a lokacin ne umma tace "Allah ya kyauta" tayi tafiyarta inda mama ta dage akan ba me ta'ba ni haka yayyun baba suka ce a barni ba laifina bane laifinshine wannan karon ga wahalan da na sha.


*satin nan gabad'aya baza kujini ba daga gobe in shaa Allahu sbd Ina da wasu jiga jigan exams guda biyu kuyi hakuri mu had'u Friday*


                    🖤Gureenjo🖤

🥀NOOR IMAN🥀

*Fatima Muhammad Gurin*
•Gureenjo6763 on wattpad•

*`Yar Mutan Adamawa*

💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)

*Alhamdulillah🙏🙏 thnks for your prayers*

*06*

Bappa Mu’azu da kanshi ya kirani a waya yace in same shi a gidanshi dayake babban d’an kasuwane kuma ba laifi ya tara kud’i don duk cikin su baba ya fi kowa kud’i, bayan naje mun gaisa da matanshi sama sama don duk basu yarda nayi hulda da su bare yaransu da suke ‘yan uwana wai zan ‘bata su, har parlornshi ya kirani mu biyu kad’ai.

Nasiha sossai yayi min wadda na yarda na kuma tabbatar shine kad’ai me tausayina cikin ‘yan uwan baban, daga karshe ya ce “me kike so a duniyan nan mamana?” Wani irin farin ciki marar misaltuwa ne ya rufeni na manta da duk wani ‘bacin rai da damuwana inda ba ‘bata lokaci nace “makaranta bappa” kai ya gyad’a cikin tabbatarwa yace.

“Na miki alkawari zakiyi karatu yadda kike so in sha Allahu kiyi ta adu’a sannan ki maida hankali banda abinda ba shine ba, zan san yadda zanyi convincing inna, don ta Amadu ba matsala bane” godiya sossai na mishi inda ya ban kudad’e ya kuma fad’amin yaranshi ‘yan mata biyu zasuyi jamb so ze biya mana tare tunda Ina da neco da waec d’ina.

Cikin jin daad’i na dawo gida duk wadda ya kalleni a lokacin ze tabbatar da cewa Ina cikin farin ciki marar misaltuwa, mama kad’ai na ba labarin ta ji daad’i sossai kuma she was glad zan cika burina, maganan da naken nan a lokacin anyi auren duk ‘yan uwana biyu mata, a lokacin da maganan yazo kunnen baba kin yarda yayi sossai suka kai ruwa rana da yayan nashi har seda inna ta sa baki kan ya amince nayi jamb.

Inda naci sossai ba ‘bata lokaci ya nema min Admission a nan BUK na kuwa samu course d’in da nake so wato Bsc.Ed biology, bappa mu’azu shi ya bani kud’in yin komai har sabbin kayan sawa irin de na fita reni, haka duk sati yake turomin dubu biyar don baba ya rantse biyar nashi baze shiga cikin karatuna ba......

Hmmmm wannan shine labarina “SAUDA AHMAD” (NOOR IMAN)

*********

“Duk inda kike ki tabbatar kin dawo gida before fad’uwar ranar gobe” kitt ya kashe wayanshi tare da jefarwa kan kujera, ya gaji wallahi da hali irin na hamna amma ya ze yi tana da goyon bayan su ummu, komai tayi shine me laifi.

Ta ‘bangarenta kuwa tsaki tayi tana kallon best friend d’inta Jawahir tace “wallahi mutumin nan ya takurawa rayuwata, haba!! Mutum ya tashi a turai yayi rayuwa a turai amma se ya d’inga yin wani abu irin na dakikan kauyawan Nigerians, if not because Ina son Abdul wallahi da na rabu dashi.”

Jawahir tayi murmushi tana sipping cocktail d’inta tace “hmm Ai duk laifinki ne hamna ace mutum yayi ta baki shawara bakya d’auka!! Da nine da Allah se Abdul ya rena kansa, mutum se d’an banzan gadara da fi’ili?” Dariya hamna tayi kaman ba mijinta aka zaga ba tana danna wayanta tace “hmm ban san me yasa jinin ku be zo d’aya da boo ba, bari kiga Inyi booking flight na san na kai mutumin karshe tunda har yayi magana In ban koma ba ma matsala ne”.

Hararanta jawahir tayi “ke kam haka zaki kare wallahi, aikin banza In nice bazan koman ba inga abinda ze faru” waro ido hamna tayi tana girgiza kai “uhm uhm jawahir duk iskanci na wallahi Ina tsoron Malabo baki san halinshi bane shiyasa, kuma baza ki gane ba” mikewa jawahir tayi tayi gaba tana cewa “Allah ya hanani sani mtseww”.

Booking flight hamna tayi kan ta bi bayan kawarta tana murmushi itama ko ba komai tayi missing d’in jikinshi sossai sati kusan uku rabonta da nigeria.

*****

“Wato baka ji fad’an dad d’inka ba ko?” Shagwa’be fuska hammad yayi kan yace “plzzz mom na san zaki iya ki rokar min shi don Allah ya kara min time” ta’be baki tayi kan tace “na fa riga na gama magana dad d’inku ya gama hakurin da ze yi da kai, ko na je korata ze yi” ajiyar zuciya ya sauke kan ya ci gaba da cin abinci jiki asanyaye, dole ya nemi mata cikin watannin nan.

Don Allah ya gani ba ze iya bari dad ya za’bar mishi wata kuchaka ba, da irin tunanin nan ya gama cin abinci ya mike ya fita, mota kawai yaja ya fara zaga gari yana neman mata, abin ma dariya yake bashi wallahi, duk wacce ya gani se ya kare mata kallo amma ba wacce keda quality d’in da yake so 100% ya zagaya har ya gaji ya dawo gida ran nan a chunkushe, part d’inshi kawai ya shige yayi kwance kan gado yana tunanin mafita.

*******

“Iman zo In aikeki gidan inna” cewar mama dake zaune a parlor tana kirgen kud’in da aka kawo mata yanzu na bashi, fitowa nayi ina tura baki nace “dan Allah de mama, nide ban son zuwa gidan Allah sbd kin san halinta Sarai a gareni” hararata mama tayi kan tace “Toh bari na yafa mayafi na je da kaina” daga jin yadda tayi maganan zaka san gatse ne, hakan yasa na koma d’aki na sanyo khimar kan doguwar rigana na material hannuna rike da takalami na fito na kar’bi sakon.

Tare da kud’in napep na fice, umma dake zaune kofanta tana gyaran farce na kalla nace “umma naje gidan inna” dukda na san ba amsani zatayi ba amma hakan ya zama kaman al’ada bana iya fita ban mata sallama ba ko da kuwa baza ta amsa ba, da kafa na taka zuwa bakin hanya, bana kallon kowa balle takaici ya kamani na zund’e ko ko kana nan magan ganun mutane.

Me makon na tari napep kaman yadda na kar’bi kud’in kawai se na tsinci kaina da hawa machine muka nufi court road, daidai wuraren BUK holdup ya rike mutane ga me machine d’in nawa se kutsa kai cikin ababen hawa yake duk ban lura ba sbd tunani na ya tafi gabad’aya wurin irin wulakancin da inna zata min a gidanta.

Kiiiii naji taka birkin d’an acha’ban a hankali nace “kayi a hankali malam Dan Allah” ba tare da yace komai ba ya taka birki ya tsaya, kaman ance In waiga se ko idona ya fad’a cikin nashi da sauri na kawar da kaina ina jin gabana na fad’uwa, hakan be hanani tuno wulakancin da ya min ba, ban san yadda akayi na tura baki gaba Ina kunkuni da ni kaina ban san me nake cewa ba.

Ta ‘bangarenshi kuma kallo biyu ya mata ya kau da kai, Sarai ya ganeta itace ta shigo mishi class sau biyu bayan ya shiga, yadda ta tura baki tana kunkuni ya bashi dariya sbd ya san haushinshi take ji, hakan ya sashi sakin murmushi, “hasbunallahu wani’imal wakeel” ya furta akan la’bbanshi ganin yadda me acha’ban da take kai ya figi machine d’in kaman zasu kife sbd bada hannun da akayi.

Sake had’a idanu sukayi Ai ko ya sakar mata harara kan ya kau da kanshi shi har ga Allah haushin masu acha’ban nan yake ji da masu hawa Haka kawai suyi ta risking life d’inka a banza yanzu dan Allah duba amma ita ko a jikinta yayi tsaki yafi abinda yafi kan ya karasa cikin BUK ran nan a ‘bace, wadda ya rasa dalili.

Ta’be baki tayi a zuciyarta tace ko me na mishi da ze wani harareni? Mtsewww, ba ‘bata lokaci suka karasa layin gidan inna ta sauka ta sallami me machine d’in ta shige gidan cikin fad’uwar gaba, daga bakin get take jin hawaniyar yara hakan ya tabbatar mata da akwai gwagwaninta da suke nan aiko tana karasa kutsa kai ta hangi goggo hindatu da kamila zaune cikin runfa suna lissafin kud’i, daga chan gefe inna

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login