Follow us on social media
Showing 105001 words to 108000 words out of 131683 words
Chapter 36 - NOOR IMAN Yar Baƙin Ciki BY Fatima Muhammad Gurin
ko da safe ko da rana ko da magrib ko da dare a kasa ku dena ku ajiyeshi se yayi sanyi inko ya kama dole ku ambaci sunan Allah kan zubarwan, akwai mutane dayawa da na sani ko naji labari wasu sun haukace, wasu sun mutu, wasu an kassara su, wasu sun shiga duniya wasu sun zama se adu'a sbd irin wannan dalili, sannan shiga wanka a lokacin da magrib ta ratso wato lokacinta ta shiga shima ba karamin hatsari bane ga ke ya ke er uwata mace dan Allah mu kiyaye waennan halittu ba ganinsu muke ba sannan In sun samu galabar shiga jikin baiwa na Allah ba daad'i zataji ba, ba kuma daad'i takeji ba bare kuma ace irin su marid, ifrit, duna da sauransu da sede su nufeka da sharri ba alkhairi kwata kwata a sha'aninsu, ko kuma Ashiq da ze aureki sbd son da yake miki wadda shi ze hanaki auren wani namiji jinsinki kaman kowacce mace 'yar uwarki, In basuyi a kanki ba zasu iya yi ga 'ya'yanki don Allah mu kula).
Ihun da sukaji yasasu duk mikewa Abdulraheem baba ya kalla yace "sune sun samu galabar shigomin cikin gida suna mugaye tabbas wannan shine kuskure mafi girma da suka aikata gabad'aya rayuwansu, d'aukomin abubuwan nan muje" wasu maguguna da baban ya mishi nuni da su ya d'iba, bayan shi da kanshi ya d'ibi wasu da sauri suka fice.
🖤Gureenjo🖤
🥀NOOR IMAN🥀
*Fatima Muhammad Gurin*
*Gureenjo6763 on wattpad*
*'Yar Mutan Adamawa*
💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)
*047*
Daga bakin kofan d'akin ya taka birki yana ambaton Innalillahi wainna ilaihi rajiun a lokaci d'aya yana lumshe idanunshi he's not that strong In aka zo batun Iman baze iya ba, baze iya ganin irin wannan azabtarwa da suke mata ba, baba ya mikawa magungunan ya sa kafanshi da niyyar juyawa baba fufore yace "Abdulraheem" dakatawa yayi zuciyarshi na tsananta bugawa, "shigo se ka taimaka mini" juyowa yayi ya shigo yana kau da kai, mama da ummu da kuma hajja gana kuka kawai suke.
Wani irin sauyawa halittarta yayi idanunta sun koma jajajir kaman an zuba musu ruwan borkono bakin kuma ya koma Ash bakinta baki kirin hannayenta da kafafunta duk a juye kitson kanta da kanshi ya dinga warwarewa gashin na bazuwa, cikin d'aga murya baba ya fara magana "Tun muna daad'i daad'i daku ku tattara ku fita harkar bayin Allah nan laifi ne sun muku amma shekaru ashirin da hud'u yaci ace kun gama d'aukar fansarku karku shiga hakkinsu kuma, ku fice tun kafin na fara kona ku da ayoyin Allah" wani irin dariya cikin murya marar daad'i ta sake har tana d'aura hannu kan baki tsabar dariya gashi muryan a shake kuma na maza.
Murmushi baba ma yayi yace "Ohk fine abinda kuka za'ba kenan? Alright" Wasu adu'o'i ya fara yana kai aya ya kama ayoyin Allah kaman na cikin suratul baqarah, saffat, A'araf da jinni da dai sauransu nan fah tun suna dariya har ta fara ihu na fitar hankali tana d'agawa sama tana fad'owa ita kad'ai In tayi ihu se d'akin yayi wani girgiza duk wani abu na fashewa seda suka fashe a d'akin komai seda ya juya upside down, cikin muryan maza me amo da karfi ta fara magana "dakata!!!! ka dakata!!!! Ka dakata naceee!!!" Kin shiru yayi se ma wani kwal'ba da ya bud'e wadda had'i ne na abubuwa dayawa irin su za'afaran, zaitun, habbatussauda, khaltuffa, dawa'ujinni da dai sauransu ya watsa mata wani kara tayi ta d'agu sama ta bugu da gini ta sake dawowa kan gadon ta fad'i tare da murd'ewa kaman maciji se ga Malabo na hawaye.
Cikin muryanta na asali tace "wayyo hamma" tana mika mishi hannu da sauri ya kama hannun yace "hayatee kece?" Tace "ka taimakeni ciwo wayyo" baba fufore yace "kauce Abdulraheem ba ita bace duk cikin munafurcinsu ne yau ko ni ko ku" Abdulraheem ze yi musu Don ganin yadda take kuka tana ta nanata wayyo wayyo se yaji muryan farko kaman ta mazan nan tace "ba fa zan barta ba Ina rantsuwa da jinin d'ana da kuma namijina yadda uwarta ta rabani dasu se na rabata itama da nata, sandin mutuwar markuzz mijina ma ya mutu Don haka se na ga bayansu".
Baya Abdulraheem ya matsa hawaye na ci gaba da zuba mishi yana gogewa duk wani me imani baze juri ganin yadda suke mata be zub da hawaye ba gabad'aya ta fice a hankalinta da kamanninta kaman ba ita ba, artabu aka ci gaba dayi tsakanin baba da wannan aljana Zulhaya'i seda suka kai ruwa rana gabad'aya ta wahalardasu Don daga baya neman illata baban ta fara amma dayake yace Allah so ba yadda ta iya dashi daga karshe ta fara kuka a galabaice tana neman ya tsaya zata fita kar ya gama koneta ta tuba.
Se sannan ya dakata yace "toh bismillah muna jiranki, ta Ina zaki fita? Tace "zan fita ta hanci" yace "kiyi alkawari bazaki kara ra'banta ko dawowa inda suke ba" Tace "nayi.... nayi" yace "ni kuma nayi alkawarin duk radda kika sake kusantar zuri'ar nan se na kasheki har lahira da ayoyin Allah" Kai ta dinga gyad'awa kan iman ta saki wani wawan atishawa har sau hud'u a jere kan ta koma ta fad'i kan gado, zama Malabo yayi bakin gadon tare da kama hannunta yayi kissing wasu Hawayen tausayinta na sake zuba akan kuncinshi, ajiyar zuciya manyan suka sauke baba ya kalli baba fufore yace "mun gode Allah ya saka maka ya biyaka da gidan Aljanna" murmushi yayi yace "kaman yadda Abdulraheem yake jika gareni Haka itama don haka ba godiya don nayiwa jikata Abu, yanzu shikenan Sun rabu da ita da izinin Allah, kai Abdulraheem zan baku wasu magunguna ka tabbatar tana anfani dasu zuwa en wasu lokuta kad'an".
Kai Abdul ya gyad'a Don shi magana ma yanzu ji yake baze iya ba, ficewa baba da baba modibbo sukayi suka bar matan se Abdul da har yanzu be saki hannun matar tashi ba, ummu tace "khaih Allah ya mana tsari da irin mugayen nan" umma da hajja sukace "Ameen" hajja ta fice umma ma tabi bayanta suka zauna a parlor suna ci gaba da tattaunawa akan matsala irin haka, "Abdulraheem ka yafemin dan Allah" sake hannun Iman yayi yazo ya kama na mahaifiyarshi yana dukawa gabanta yace "ni ummu baki min komai ba sema ni da na miki, na kasa nema miki lafiya kan lokaci da na san wani abin aka miki da tun farko na kawoki nan wurin baba ki yafemin na rashin kula da hakkinki" kanshi ta shafa tana murmushi Tace "Allah yayi maka albarka yayi muku gabad'aya, sede Babana kana tunanin waye ze min irin wannan abu akan ku? Me nayiwa wannan bawan Allahn da ya so sani kassara rayuwan 'ya'yana da na d'iyar wasu?".
Shiru yayi na mintuna kan yace "Allah masani ki dena damuwa akan hakan ummu In Shaa Allahu Allah ze ci gaba da kareki sannan Ai Allah ba azzalumin bawansa ba baya barin hakkin wani akan wani shi ze yi mana sakayya, karkiyi zato sbd zato zunubi ne babba kinji?" Kai ta gyad'a mishi, tace "kaga Ango, daughter na fa ta kular min da kai kaga yadda kayi wani fresh da kiba?" Mikewa yayi yana murmushi yace "ummu zaki fara ba" dariya tayi shima ya taya ta kan yace "I miss yhu ummu" Tace "miss yhu more, uhmm bari Inje In samarwa daughter na abinda zata ci d'azu naji kanacewa tun jiya bata farka ba ko?" Kai ya gyad'a yace "tunda muka zo ko ruwa bata sha ba" girgiza kai tayi tana mikewa bayan ta ajiye gyalenta ta fice.
Komawa gefen matanshi yayi ya zauna yana maida hannuwansu cikin na juna idanunshi akan fuskanta Allah kad'ai yasan abinda yake ji akan yarinyar nan, zuciyarshi kaman zata fito tsabar yadda take bugawa da sunanta yana mata son da a rayuwanshi be ta'ba zaton ze yiwa wata halitta ba, wayanshi ya fiddo yana kau da kai daga kallonta zahra ya fara kira tana d'agawa yace "Albishir Auta" Tace "goro" yace "ummu ta samu lafiya" wani irin ihu tayi da yasashi saurin kashe waya yana murmushi, Haka ya kira kalthum da hafeez ya gayamusu rahamace dae suka d'an jima suna waya har ya bata labarin gabad'aya abinda ya faru yau sossai tayi kuka cikin tausaya musu, dama idanunshi akan ta yake sede safa da marwa yake so da ya jima ta bayanta yana kan bawa Anty rahama labari kaman ance ya dawo ta gabanta yaga hawaye nata gangara daga cikin idanunta da suke a rufe.
Da sauri yace "we talk later sis bye" ya kashe wayan gabanta yaje ya zauna yasa tattausan tafin hannunshi yana share mata hawaye yace cikin taushin murya "hayatee" kawai se ta mike kad'an ta rungumeshi zama yayi da kyau yana sanyata jikinshi yana jin kukan da ta fashe dashi kaman sukan mashi a kirjinshi, jikinta har rawa yake kab taji labarin da ya ba Anty rahama daga farko har karshe ta tsorata sossai da lamarin abin ya zo mata bazata dama abunda ya faru kenan? Allah sarki ummanta sossai take squeezing hannunta a jikinshi tana kuka.
Tsam ya kuma rungumanta yana cewa "is Ohk hayatee, is ohk i got yhu!!" Cikin rawan murya tace "hamma Ina ummuna? Tana ina don Allah?" Yace "ki dena kukan nan haka se in kaiki wurinta ok?" Da sauri ta zame daga jikinshi tana share hawayenta hannu bibbiyu with adoration yake kallonta kaman wata small baby, "kaga na dena" tana maganan ne wasu hawayen na kuma zuba.
Mikewa yayi yana kama hannunta yace "sauko to muj..." "Ahhhh" da tayi ya katse mishi magananshi da sauri yace "menene? Me ya sameki?" Ya fad'a a rud'e yana dubanta, yadda ya rud'e din se ya bata dariya har ta murmusa cikin kuka girgiza kai yayi yace "ke ko?" Ta shagwa'be tace "hamma jikina ciwo..." yace "sorry dear" ya tabbatar ko don bubbuguwan da tayi dole jikinta yayi mata ciwo tunda ba sabawa tayi ba.
Sake hannunta yayi yana dawowa, d'an dukawa yayi ya saka hannunshi yana mayar mata gashin da ya hauro kan goshinta baya yace "kiyi zamanki anan bari In je In kiramiki umman from there zan fita In samo miki drugs ohk?" Kai ta gyad'a mishi yayi pecking goshinta yace "take care and don't cry" murmushi tayi ya juya ya fice, yana fita parlorn yace "umma hayatee na son ganinki jikinta na ciwo bazata iya fitowa ba" Kai umma ta dukar a kunyace shi ko ko a jikinshi sema hajja da ya kalla yace "hajja Ina ummu?" Murmushi tayi tace "tana chan kitchen tana had'awa matarka abinci, se kace mu en gidan bamu iya girki ba" murmushi yayi yana kashe mata ido yace "Ai kin san mu na special ne seda haka" Tace "ja'irin yaro ko ba sepecil ba" dariya ya fashe dashi yana kama baki ze yi magana tace "wuce ka bani wuri bana son ji" kitchen d'inta ya nufa yana dariya wai sepecil ga mijinta gwani a boko amma ita batayi karatun ba sbd yanayin wasu iyayen na da da basu yarda da boko ba.
A bayanta ya tsaya yana leka tukunya kaman yadda takeyi juyowan da zatayi kenan suka kusa cin karo "subhanallah" ta furta a tsorace baya ya matsa yana dariya ludayin hannunta ta d'aga da nufin kwad'a mishi da sauri ya rike hannunta yana cewa "sorry ummu, I'm sorry" cikin dariya murmushi tayi tace "Da alamu yau kana cikin farin ciki" yace "yes sure, I'm the happiest person in the world today, ummuna is back likewise my hayatee" Tace "tafi marar kunya kawai se na hanaka hayateen naka inga ta tsiya" shagwa'bewa yayi yace "sorry" murmushi kawai tayi ta juyawa girkinta da taci karfinshi, yace "ummu zan je dubawa Hayatee maganin ciwon jiki bye" Tace "Ohk Son, take care" ficewa yayi cikin nishad'i da farin ciki.
Ta 'bangaren umma kuwa seda hajja ta kuma magana kan ta mike ta shige d'akin cikin zakuwar son rungume 'yarta for the first time a rayuwa tun haihuwarta, iman da ta lalla'ba ta sauko da kafafunta daga saman gadon ta zauna da kyau tana ganinta ta mika mata hannu tana cewa "ummaanah" Da sauri umma ta karaso suka rungume juna suna kuka a tare, d'agowa umma tayi tana shafa fuskanta zuwa kanta cikin kuka tana cewa "my baby!!!" Se ta kuma rungumeta. (Awwwn so pitiful)
Itama se ta kuma cewa "ummanah" daga karshe ta kwanta a jikinta umman na shafa gashinta zuwa bayanta wani irin soyayyar uwa da d'iya suke shearing soyayyar da yafi ko wani irin soyayya a duniya sun jima a haka kowacce na son fara magana amma this awkward feeling na rashin sabo ya hana, daga karshe umma ta nisa tace "ki yafemin Saudah" for the very first time a rayuwarta Da taji umma ta kirata da asalin sunanta se ta kara narkewa hawaye na kuma zubo mata se ta turo baki Don shine ya fad'o mata yace kar tayi kuka bayan ya San definitely se tayi d'in, a shagwa'be tace, "Umma ni wallahi ban ta'ba rikeki a zuciyana ba ko shed'an ya rayamin mummunar abu akanki da sauri nake tuba in nema mana gafarar ubangiji gabad'ayanmu Don nice ya kamata in nemi yafiyarki ki yafemin umma abubuwa dayawa sun faru ta sanadiyata" d'agota umma tayi tana kallonta tace "ni ba Abinda kika min ke 'ya ce ta gari wacce ko wace uwa zatayi alfaharin samu Allah yayi miki albarka" kuma rungume umman tayi se ji sukayi ance "I'm really jealous here ni baza a rungumeni ba?" Da sauri Iman ta d'ago tana kallon ummu Allah ya gani tsoronta take se kuma take ganin abun kaman a mafarki ko de kunnenta ne suka jiye mata ba daidai ba? Ummu na matsowa tace "com'n come gimme a hug" hannun umma iman ta matse tana kallonta se ta gyad'a mata kai tana matsawa ummu ta maye gurbinta ta rungumeta tace "I'm so sorry dear ki yafemin ba laifina bane it was a sihr akan ki da my beloved son ban san aikin waye ba, kiyi hakuri dan Allah wallahi duk wani mummunan abu da na ta'ba miki na tuna har kunyar had'a ido dake nake, dan Allah ki yafemin.... d...." da sauri Iman ta katseta tace "ummuuuu....... Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah Allah na gode maka da ka nunamin wannan rana, rana ce da bazan tam'ba mantawa ba All thanks to Allah he brought all my ummu's back" ta kuma lafewa jikin ummu murmushi kwance a fuskanta, d'agota ummu tayi tace "banji kince kin yafewa ummun taki ba to" Tace "ummuna Allah ya yafemana bakimin komai ba wallahi tun da chan ban rikeki ba, Ai d'a nagari baya ta'ba fushi da iyayenshi" kuma rungumeta ummu tayi tace "so proud of yhu binty" kan ta mike tana cewa "bari In kawo miki special dishes da nayi sbd ke na san kina jin yunwa".
Ita ta ma manta da rayuwan cikinta se yanzu da akayi maganan abinci dama tun chan yake mata kukan yunwa, ummu na fita ta matso gangan umma ta kwanta jikinta nan suka fara hira a hankali kan kuce kwabo sun sake ana ta shan hira gwanin shawa'a.
************
NIGER
Wani kungurmin daji da suka shigo da seda sukayi tafiyan kusan awa uku a machine bayan sun ajiye motansu bakin hanya duk sunyi lugub sun gaji kaman waenda aka yi musu jibgan kare, da kyar suka iya sauka bayan machine d'in ya tsaya dab gidan bokan sede me............
🖤Gureenjo🖤
🥀NOOR IMAN🥀
*Fatima Muhammad Gurin*
*Gureenjoh6763 on wattpad*
*'Yar Mutan Adamawa*
💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)
*Am so sorry for keeping you guys waiting🙏*
*048*
Layi ne a wurin na bala'i abin mamakin kuma matane karankatakap ba namiji ko d'aya a galabaice Mama ta dubi jawahir tace "ke dama haka ake cin uban wuya kan a samu ganinshi? Yanzu kina nufin se mun jira duka wannan layin kan mu ganshi?" Murmushi jawahir tayi tace "no inde da kud'ad'e wannan layin ba komai bane yanzu zamu iya ganinshi" umma tace "ko nawa ne dan Allah muyi mu hanzarta" Hamna dake ta nyamutsa fuska tana kallon wurin tace "yanzu anan mutum yake rayuwa? Tabb" ba wadda ya amsata se d'an waya da jawahir tayi nan da nan wani yazo ya bi dasu ta baya har bukkan boka.
Wani mummunan bakin kafiri mushriki ne zube a wurin kato irin giant d'innan shirgege da uban tumbi zaune idanunshi a rufe hannayenshi a bud'e kaman dae yana wani bautansu dae na shirka, duk zama sukayi cikin dakakkiyar muryanshi yace "me ke tafe daku?" Umma ce tayi gyaran murya tace "ni dae 'ya'yan 'yar uwata ne nake so duk su wulakanta su zama abin Allah sarki sbd komai da suka fini, mijinta kuma a nakastashi, tunda har ya kasa aurena ya aureta se 'yata gatanan tana auren d'aya daga cikin yaran ne Abdulraheem muna so ya zama a tafin hannunta se yadda ta juyashi kawai, sannan munafukar d'ayar matarshi a haukata ta haukan da za'a rasa warakanshi har abada"
Shiru yayi na mintuna akallah talatin har sun kosa duk se kara gyara zama suke kan ya fad'i wata kalma se ga kwarya a gabansu da wani jan abu ciki wani abin ya kuma fad'a se ga Iman nan kwance a jikin ummanta tana mata surutu ita umman murmushi kawai take sakewa, had'e rai Hamna tayi In da itace tayi magana ma wallahi da cewa zatayi a kasheta har lahira kawai dae tana tsoron wannan gabjejen mutum ne.
Yace "ita?" Umma tayi saurin cewa "kwarai kuwa boka" kai ya gyad'a ya sake fad'an wata kalma da wani yare da bama su sani ba se ga wani kulli gaban hamna fari da baki da wasu garin magani gasunan dai kore kore yellow yellow, yace "ba'kin shi zakiyi wanka dashi a tsakiyar d'akinta ki kirayi