Follow us on social media

Showing 90001 words to 93000 words out of 131683 words

Chapter 31 - NOOR IMAN Yar Baƙin Ciki BY Fatima Muhammad Gurin

nan tsaye Baba ya fito "a'a Abdulraheem kai bako ne da zaka zo ka tsaya daga waje? Maza maza karaso ciki" murmushi yayi yabi bayan baban da be tsaya sauraranshi ba yayi gaba, darduma aka shimfid'a mishi akan taburman dake kasan inuwan Almond tree d'insu, se da ya zauna tukun suka gaisa da baban, umma ce ta fito sanye da hijabi itama ya gaisheta yana mamakin kamansu da Iman yadda har ya 'baci kawai de iman chocolate color ce yayinda Umma fara.

Ba yabo ba fallasa ta amsa ta mike ta koma ciki, bayani yayiwa baba akan abinda ya kawo shi da maganan da sukayi da sauban ya yanke shawarar ze kaita Miami shine ya zo kar'ban passport d'inta Don mata shirye shiryen tafiyan, sannan kuma yana so a had'ata da mutum d'aya da ze na kula da ita, godiya sossai baba ya mishi kan yaje d'akinta ya d'auko passports d'inta ya kawo mishi seda ya zauna tukun yace "tafiyan na san ana bukatar mace ne er uwarta ko?" Girgiza kai yayi yace "a'a baba ko namiji ma ze iya sbd ba'a kwana akan marar lafiya su zasu kula da komai nata, mutum d'ayan ma munaso ne kawai kar ace an rasa wani nata kusa, ni da Saudah ba zama zamuyi ba muna ajiyeta wasu kasashen zamu wuce".

Gyad'a kai baba yake cike da al'ajabi wai yau mijin  Noor Iman ne ze musu irin wannan hidimar ba Don shi ba kam sede Mama ta mutu a yadda take dukda ya san mutuwa da rayuwa duk na Allah ne, har zuciyanshi ya fara da na sanin abinda ya dinga mata gashi yanzu Allah ya mata za'bi na gari zata huce duk wani takaici da suka kunsa mata har gwara shi da mahaifiyarta ya rasa dalilin da akayi yasa ya tsangwami ershi mafi soyuwa cikin yaranshi. Maganan Ikram ne ya dawo dashi daga duniyar tunanin da ya tafi inda tace "laaaaaa Ashe da gaskiyar Ikhlas bature Adda Iman ta aura???" Tayi maganan tana kama baki kaman wata babba.

Dariya baba da Abdul sukayi a tare baba yace "haba ikhram ba gaisuwa ba komai?" Tace "good afternoon" murmushi yayi kan yace "Lafiya kalau ikram ya makaranta?" Waro ido tayi tana kama ha'ba tace "ashe turawa ma sun iya hausa??" Dariya again yayi yana kallonta ita ta fi iklas kama da iman amma duk basu da kyaunta, zatayi magana umma ta kwala mata kira daga d'aki da gudu ta juya tayi d'akin.

Abdulraheem cikin murmushi yace "baba Ina ga ba se an tsaya tunane tunane ba In har de zaka samu leave a aiki se mu tafi da kai Ina ga ze fi" murmushi baba yayi yana cewa "za'ayi haka?" Abdul yace "In Shaa Allahu" baba yace "zasu bani In na nema Don ina jimawa sossai ban nemi wani hutu ba" passport d'inshi yaje ya d'auko mishi yana ta zuba godiya, Abdul yace "ba komai baba Ai an zama d'aya yadda zan d'auki ummu da Abbana Haka kuma zan d'aukeku" dukda Haka sossai yayi godiya sukayi sallama ya raka shi har jikin motanshi ya wuce.

Tsaye take tana kwashe had'ad'en miyan d'anyen ku'bewanta da ta aika Bala me bawa flowers ruwa ya sayo mata, yaji nama da kifi yayi shar da shi da kaurinshi, har seda na had'iyi nyau tsabar kyaun miyan, bayan ta gama ta rufe coolern ta d'auka ta kai dining anan na ga babban na tuwon Don gulma seda na bud'e tuwon semo ne da aka d'auresu a ledojin d'aura tuwo sun tuku sossai gwanin sha'awa.

Komawa tayi kitchen d'in ta bud'e fridge na ciki ta d'auko babban jug d'in zobonta ta kai fridge d'in wurin dining sbd a na kitchen ze iya yin kankara, dubawa tayi komai intact da plates da serving spoon da ruwan wanke hannu duk ta had'a, ajiyar zuciya ta sauke ta juya d'akinta, tun da ta shigo ta fad'a gado tayi kukanta me isanta ta mike taje ta wanke fuskanta tayo alwala sbd azahar da taji ake kira Bayan ta idar ta mike ta fito ganin ba alamun d'aura wani abu a gidan yasata tuna ashe fah ita zata kar'bi girki so dole ta tar'bi mijinta da yamman nan, komawa d'aki tayi ta d'auko kud'i tare da sanyo hijabi ta fito har kasa ta aika aka sayo mata abinda zata bukata ta dawo ta fara tuka tuwonta kan ma ya dawo ta had'a ruwan miya kawai yanka ku'bewanta tayi ta daka da kanwa, tana gamawa ta had'a zobo.

Wayanta da yake haske tayi saurin nufa ta d'auka ganin baba ya sanya ta zauna tana cewa "Assalamu alaikum baba Ina yini?" Yace "wa'alaikissalam warahmatullah mun yini lafiya?" Ta amsa da "Lafiya kalau Alhamdulillah ya su umma da ikhlas?" Yace "suna nan lafiya mamana yanzu mijinki ya bar nan" wani irin rasss gabanta yayi tana ambaton Innalillahi wainna ilaihi rajiun a zuciyarta ta d'auka wani abin ne ze faru da ita se taji baba yana cewa "ki taya mu yi mishi godiya ze fitar da mamanki jinya wata kasa tare zamuje da ni da ke da kuma shi" wani wawan ajiyar zuciya ta sauke kan ta sake murmushi tana cewa "Alhamdulillah, Masha Allah" yace "kin samu miji me hankali da sanin ya kamata fiye da sauran mazajenki dan Allah mamana kiyi iya kokarinki wajen kulawa da shi ki gani ki ki gani ki ji kiyi kaman baki ji ba se a zauna lafiya".

Tace "In Shaa Allahu baba bazan baka kunya ba" yace "Toh Allah miki albarka" tare da kashe wayan amsawa tayi da Ameen tana saukewa daga kunnenta hawaye na silala na farin ciki, da sauri ta mike tana sake murmushi ta fad'a toilet wanka ta tsalla tare da alwala bayan ta gabatar da la'asar cikin kayanta ta shiga ta nemi wani riga da skirt d'in wata maroon and ash atampha ta saka wow zo kuga yadda kayan nan ya zauna mata kaman a jikinta aka hallicesu tsam skirt d'in ya fito da duk wani shape na jikinta.

Kallon kanta tayi anya zata iya tsayawa gabanshi haka? Rigan off shoulder ce hakan ya sa kirjinta ya d'an fito daga sama kunyace ta kamata lumshe ido tayi tana sauke ajiyar zuciya dole ne kawai a haka zata fita gabanshi sbd tana son bawa kanta wani gur'bi na musamman a zuciyarshi wadda In ya fita ze ji wajen ya koma mishi kaman rana yana dawowa gareta ya ji shi kaman a ni'imtaccen inuwa mafi sanyi, daad'i, kamshi da kayatuwa a duniyarshi.

'Daurinta ta kafa ya kuwa fito d'as dashi dama tun kan su fita ta gyara d'akunansu gadonta ne ma a d'an 'bace gyarawa tayi ta sanya turaren wuta ta koma nashima ta saka mishi ta kuma saka a parlorn saman kamshi nan take ya bule ko Ina, hijab ta sanya tana jin haushin mantawa da tayi bata mikawa su baba mai gadi da kuma bala da audu driver Abinci ba Bayan ta saka musu.

'Dauka tayi ta fice zuwa kasa daga bakin kofa ta kira bala ya zo ya kar'ba yana ta zuba godiya, komawa tayi saman ta gyara d'aurinta ta d'an saka powder ta d'auko red lipstick ta sanya se kwalli a cikin idanunta dayake ita ba me yawan kwalliya bace amma In tayi d'an kad'an d'in matsanancin kyau yake mata.

Bayan ya bar gidansu ya fara tunanin me ze sayamata tsaraba ya kai mata, shi ba sanin abinda ta fi so yayi ba har ya wuce wurin masu fruits se ya dawo baya ya saya fruits d'in da d'an yawa yayi gaba ya sake tsayawa wurin da ake gashin kaza ya sayi uku manya da su, aka sanya mishi a leda ya wuto be san ko hakan yayi ko be yi ba haka de ya karasa gida da sake sake horn ya danna aka wangale mishi gate ya shige, yayi parking ya bud'e baya ya d'auko ledojin da ya taho dasu har ya sa kafa ze sauka se kuma ya fasa ya gyara zama tare da d'auko wayanshi ya danna kiran baba fufore bayan ya d'auka suka gaisa cikin raha da dariya kan a natse ya mishi bayanin abinda yake damun Iman da kuma abinda suka lura dashi sossai ya shiga alhini da damuwa inda yace duk yadda za'ayi ya kawota wurinshi nan kusa yayi.

Godiya sossai ya mishi kan shima ya fad'amishi d'azu ya bukaci ganin mamansu kuma ta tabbatar mishi a jibi In Shaa Allahu zata bayyana gidanshi komai ze daidaita In shaa Allah, godiya ya mishi sukayi sallama kan ya sauka ya nufi cikin gidan tun kan ya haura saman yake jin wani sassanyar kamshi na tashi lumshe idanunshi yayi ya bud'e su a hankali ya haura matakalar ya karasa parlorn sanyin ac da kamshin na sa shi jin wani kasala ya rufe shi.

Direct d'akinta ya nufa tare da tura kofan bayanta kawai ya kalla amma seda gabashi ya fad'i a natse yake takawa zuwa asalin uwar d'akin, cikin sanyinshi yace "Saudah" juyowa tayi tana sakar mishi murmushi tare da mikewa wani wawan ajiyar zuciya ya sauke har be san sadda ya karasa ya rungumeta ba suka sake sake ajiyar zuciya a tare, Ina ma Ina ma? Ina ma lafiyanta kalau taga ruwan kaunar da yake mata? Wani 'bangare na zuciyarshi yace me kake sauri komai ze daidaita In shaa Allah.

Gyaran murya yayi yace "I've been calling you several times amma baki amsa ba" Tace "subhanallah I'm so sorry wallahi wayan na silent" sake juna sukayi da sauri ta d'auki wayan ta duba Ai kuwa six miscalls d'inshi fuskan tausayi tayi ta kalleshi yace "is Ohk sede please kar ki sake sa wayanki a silent in ba kina so hankali na ya tashi ba" Tace "Toh" ido ya tsuramata yana aikin kallo har seda matsanancin kunya ya rufeta kara hugging d'inta yayi yace "you look so cute, beautiful and super awesome my hayatee" Wani murmushin jin daad'i ta sake tana mikewa tace "thank yhu" a saman lips d'inta se ji tayi ya had'e bakin da nashi.........







                        🖤Gureenjo🖤



                  🥀NOOR IMAN🥀

*Fatima Muhammad Gurin*
          *Gureenjo6763 on wattpad*

*'Yar Mutan Adamawa*

💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers association)

                           *042*

Seda yayi kissing d'inta son ranshi kan  ya janye jikinshi yana kallon fuskanta, wani kunya ne ya rufeta hakan ya sa ta mayar da kanta chest d'inshi tana sunne kai, sossai yayi murmushi tace cikin sanyin muryanta "Na gode kwarai hamma Allah ya biyaka da mafificin alkhairi" d'agota yayi jin har muryanta ya fara rawa yace "da akayi me ne hayatee?" Tace "batun jikin Mama b......" katse ta yayi "mama ta wuce haka a wurina hayatee sbd ita ta kularmin dake ta kuma rainar min ke tun daga yarintarki har na zo na d'auke kayana so kinga anything for her".

Wani irin blushing take sakewa da ya mugun mishi kyau hakan ya sa shi kama lips d'inshi na kasa yana tsotsa a hankali yana kallonta se kuma kunya ya kamata tasa hannu ta rufe fuskanta, murmushi ya saki kan ya 'bata fuska yace "wayyo hayatee yunwa ze kashe miki ni.." waro ido tayi tace "laaa sorry wallahi na manta shap muje please inyi serving d'inka" yana taune lips cikin tsokana yace "kina nan kina soyayyarki Ina zaki tuna" da sassarfa ta fice yana murmushi ya bi bayanta yana mata wani irin kallo.

Serving d'inshi tayi nan fa ya sa mata darun shi kam hannunshi na ciwo baze iya ci ba haka ta zage ta bashi da da spoon zata bashi nan ma yace baya so da hannunta yake so ta bashi a haka ta bashi da ya koshi maimakon ya ce mata ya koshi se In ta sa mishi ya dinga cizan hannunta kad'an kad'an daga baya kam ma se ya d'an mata da karfi "Ahhhhsss" tace tana yarfa hannunta kallon sha'awa kawai yake binta dashi shagwa'bewa tayi tsakani da Allah har da d'an hawayenta.

Da sauri ya rike hannun yasa a bakinshi ya fara tsotse mata razana tayi zata mike yaki sakinta se ma kafanshi da ya janyo ta, wow sossai yanayin ya ma ko wannensu daad'i da kyar ya lalla'bata ya bata abincin shima da hannunshi, a nan suka shantake har aka kira magrib ya mugun kasheta da soyayyarshi me daad'i da sanyaya rai ba surutu sede kawai actions ita kuwa ta cire kunya ta bashi duk wani irin kulawan da yake so daga ita har shi ji sukayi kaman su zauna su dawwama haka.

Kan ya fita seda ya gaya mata daga masallaci asibiti ze wuce wurin Abba, ta kuwa bashi sakon gaisuwa tace ya ce ma Abban se gobe in Shaa Allahu zata zo ta dubashi seda yayi hugging d'inta again kan ya fice, taji daad'i da bai tambayi abinda ya sa ta bar asibiti bata jirashi kaman yadda yace ba, kaman yadda shima yaji daad'i sossai har ranshi da bata nuna mishi komai akan damuwan da mahaifiyarshi ta sanyata ba, kimarta da darajarta ne suka ninku a ranshi.

Da wannan tunanukan ya karasa asibiti ya samu jikin Abba da sauki sossai su rahama da kalthum suna nan har zahra da hafeez suna nan umma, ummu da kuma hamna ne basa nan seda yaji wani iri da a da ne Abba be da Lafiya haka ummu baza ta ta'ba iya barin kusa da shi ba amma ji bata zo da wuri ba haka tayi tafiyanta, fita yayi ya samu doctor yace a sallami Abban tunda jinin ya d'an sauka in Shaa Allahu ze samu kulawa a gida har ya gama warwarewa haka dae ba Don doctorn ya so ba ya bashi sallama ya kuma tabbatarwa Abdul d'in su tabbatar basu barshi yayi skipping pills d'inshi ba, godiya ya mishi ya taho.

Yana tahowa ya samu mijin Anty rahama da na Anty kalthum sun zo duba jikin Abban da sha tara na arziki gaisawa sukayi cikin mutunci kan yayi musu bayanin an ma sallami Abban ai shi karan kanshi seda yaji daad'i dama ba zaman asibitin yake so ba Hafeez da Zahra ne sukayi jigilan kai komai d'insu mota daga nan Abba ya sauko yana tafiya a natsenshi jere suke da Abdul yayinda sauran suka biyo bayansu har motan Abdul d'in.

Ya bud'e mishi baya ya shiga, su Anty kalthum suka mishi sallama da Allah ya kara afuwa inda ya gargad'esu kar ya ga kafan ko wacce a gidanshi gobe In ma zasu zo su bari se zuwa jibi ko gata a haka dae su da mazajensu suka ja motocinsu sukayi gaba, zahra ta shiga motan hafeez su ma suka nufi gida Abdul a gaba suna binshi a baya, bayan sun isa sunyi parking suka raka Abban nasu har part d'inshi Abdul na kallon zarah yace.

"Auta zan baki amanan Abba, ga magungunanshi pls safe, rana dare ki tabbatar ke kika mishi girki da hannunki kika kawo mishi ya ci ko kad'an ne ki bashi magungunanshi kar fa ki barshi be sha magani ba kinji?" Murmushi duk sukayi har Abban seda ma yace "to baba Abdul" duk dariya suka sake har Abdulraheem d'in, Hafeez ya wuce side d'inshi don hutawa haka ma zarah fita tayi ya saura Abdul da Abba Anan ne cikin sanyinshi yayiwa Abba bayanin ciwon Iman Don fa shi a rayuwanshi baya iya 'boyewa Iyayenshi komai irin dae d'abi'ar wadda yayi rayuwar waje fad'awa iyayinka duk abinda ya shafi rayuwanka ba komai bane, kuma irin ya tashi da hakan iyayenshi sun d'aukeshi friends akwai tsananin biyayya da shakuwa tsakaninsu.

Sossai Abba yayi jimamin abin, inda ya tambayeshi to yanzu wani irin mataki ya d'auka, ya sanar dashi ya fad'awa baba fufore yace suyi hanzari zuwa so zasu wuce jibi Don a gobe ba jirgin yola da ze d'aga, Adu'a sossai Abba yayi mata tausayinta na kara kamashi anan yayi wa Abdul d'in bayanin hankalinta da yadda ta kula dashi a jiya, shi be ma san taya akayi ta biya kud'in magungunan ba, amma yana gani aka koreta be iya cewa komai ba tsabar a lokacin be san yadda ze yi da ummun bane, sossai ya yabi hankalinta da natsuwarta ya kuma roki Abdul da ko baya sonta ya san yadda ze yi ya sata a zuciya ya kula da ita fiye da duk wasu mata na duniya bayan mahaifiyarshi.

Sallama sukayi akan ze kwanta ya huta seda Abdul ya tabbatar ya sha maganinshi ya kuma sha fruit salad sossai da zahra ta had'o mishi kan ya tafi, da sake saken Ina su ummu suka tafi ya dawo abin mamaki se ya samesu a parlorn su na sama baje suna hira kazan da ya kawo d'azu baje suna ci ana hira harda jawahir, kaman wasu friends se kuma pottage na Irish da ya gaggani a plates d'insu sunci rabi sun babbari gashi yaji kayan had'i.

Karasawa yayi yana kallon ummu yace "ummu ashe kina nan har an sallami Abba ya koma gida" tace "au laifine Don na zo nan d'in?" Yace "a'a ko d'aya" kan ya nufi room d'inshi se kuma yaji ta kira sunanshi tsayawa yayi kan ya juyo ta nuna mishi umma tace "wannan kam ba uwarka bane da bazaka iya gaidata ba?" Yace "sannu hajiya" ta amsa a d'age ya juya ya fad'a d'akin Iman zaune take bakin gado ta dafe kai hawaye na silala a idanunta bata san ya shigo ba seda ya kira sunanta da sauri ta goge fuskanta tare da kakalo murmushi tace "har ka dawo? Ya jikin Abban?".

Wani irin tausayinta ne ya kuma rufeshi gashi bata so ya san tana cikin damuwa macen arziki kenan tana iya kokarin ta wurin 'boye damuwanta Don farantawa nata mijin rai, yace "Abba jiki da sauki hayatee an sallameshi ma" jin daa'inta ta nuna sossai tace "masha Allah, Allah ya ci gaba da bashi lafiya gobe In Allah ya kaimu zanje na dubashi pls???" Tayi maganan tana karya wuya.

Yace "to hayatee Allah ya kaimu" tayi murmushi yace "me yasa kikayi wani girkin bayan naga tuwon d'azu dayawa ze ishesu?" Tayi murmushi tace "ummu ke son Irish pottage shiyasa kayi hakuri na bawa su bala sauran abincin zasu iya kaiwa iyalansu" karkata kai yayi kaman yadda takeyi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login