Follow us on social media
Showing 1 words to 3000 words out of 131683 words
Chapter 1 - NOOR IMAN Yar Baƙin Ciki BY Fatima Muhammad Gurin
🥀NOOR IMAN🥀
*Fatima Muhammad Gurin*
•Gureenjo6763 on Wattpad•
*'Yar mutan Adamawa*
💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)
*01*
Tafiya kawai nakeyi sam ban san inda nake jefa kafana ba bare na kula da hanya, hawaye kawai ke kwaranya daga cikin kurmin idona zuwa kan kumatu na.
Tsananin damuwan da nake ciki be sa na kula da kan hanya na jefa kaina ba seda naji wani wawan bugu yayinda students na arean suka saki salati wasu na ihu, runtse kyawawan idanuna kanana nayi cikin jin zafin bugun tun daga kafana har tsakiyar kwakwalwana amma ko kad'an zafin be kai na zuciyata ba.
A hankali na waiga na kurawa bakar meserati wadda gabad'ayanshi baki ne har glasses d'in ido don ganin ko ze fito ya bani hakuri amma ko motsi kofan motar be yi ba bare ayi alamun bud'ewa.
Mikewa nayi na d'ingisa kafana da nasan yayi mugun buguwa na koma gefe na zauna, wasu na min sannu wasu kuma cewa suke Allah ya kara dama yarinyan kullum tana tafiya kaman mahaukaciya sam bata da hankali a kanta me makon a kaita psychiatric amma an kawo ta nan makaranta ko me zata d'auka oho.
Kuma runtse ido na nayi ba su kad'ai ba duk inda zan gilma sau d'aya sau biyu zasu ce psycho ce ni ba wai dan wai yanayin shigar jikina ba, a'a tsantsar rashin natsuwa da damuwan dake d'auke a yanayina da fuskana ke sa su zaton haka duk da sanyi na a abubuwa dayawa.
Karan wucewar motar da speed shi ya dawo dani daga duniyar tunani na, kafana na riqe da zarazaran yatsotsin hannuna na dinga matsawa har naji dama dama amma na tabbatar akwai matsala jin irin azabar dake shigana.
Agogon dake d'aure a tsintsiyar hannuna na kalla 7:50 ajiyar zuciya na sauke kan na mike na ci gaba da tafiya a hankali Ina d'ingisa kafan na nufi auditorium sbd achan nake da lectures karfe takwas gashi yanzu 7:50.
Ban isa auditorium ba se takwas da kusan mintuna takwas hall d'in tsit kaman anyi ruwa an d'auke a hankali na tura kofan na shiga bakina d'auke da sallaman da iyakarshi pink lips d'ina a hankali na ci gaba da takawa da nufin karasawa ciki In samu wurin zama.
Seda nayi tsakiyar hall d'in kan naji an ce "who the heck did yhu think yhu are!!! Will you get out of my class jor" sam muryanshi bata da hayaniya dukda tsawa yayi ba don microphone da yake amfani da ita ba ko rabin ajin baza su ji tsawar nashi ba bare lectures d'inshi.
Juyawa nayi na mishi kallo d'aya yayinda shi kuwa idonshi ke kan damin lecture note d'in hannunshi.
'Fa tabarakallahu ahsanul khalki' na furta akan lips dina ban kara gangancin kallonshi ba na juya na fita a sanyaye still cikin d'ingishi kujeru irin na zaman d'alibai dake gaban hall d'in na samu na zauna Ina sauke ajiyar zuciya.
A rayuwana ban ta'ba ganin namiji me irin kyaunshi a fili ba sede a tv, tv d'inma se tashoshin larabawa ko indiyawa kwata kwata ban san yadda zan fasalta kyaun shi ba sede na san yana da bala'e'en kyau ga fari me d'aukan hankali.
Share tunaninshi nayi sbd damuwana ya fi karfin tunanin kyaun wani halitta, ya zanyi da rayuwana, wai laifin me na aikata da ake hukunta ni da abunda ban san hawanshi ba bare saukanshi? Why always me? A shekaruna na 23 a duniya nayi aure sau hud'u duk ba wadda na mishi kyakyawar wattanni biyar.
Yes inada kyau daidai misali amma kyauna ba me d'aukan hankali bane sbd fata me duhun haske ce dani wato 'chocolate' color ba kallo d'aya zakamin ka fahimci kyaun da surar da Allah ya bani ba shiyasa tun ina shekaru sha takwas a duniya samari suka min rutututu kowa so yake ya mallakeni.
Ashe ni kam maza sune kaddarana ganin kullum za'ayi sallama ace ana kiran Noor Iman yasa baba na yanke shawaran In fidda miji ya min aure.
Dukda bana so sbd Ina matukar son karatu kan aure amma ba yadda na iya kasancewata me tsananin biyayya yasa na fidda wani saurayina da ya nace min tun Ina jss class ba 'bata lokaci a randa na cika sha takwas cib a ranar aka d'aura min aure da bello sede abun takaici a ranar da aka kaini gidanshi a ranar Bello ya dankara min saki har uku ba tare da na san laifi na ba.
Cikin tsananin tashin hankali na dawo gida da safiyar ranan amma se babana da 'yan uwanshi suka rufu akaina da duka ba tare da sunji ta bakina ba, ba don mama ba 'yaddiko na, wato kishiyar mahaifiyata' da inaga ban yi rai ba a ranan.
Bakaken maganganun da na sha ko seda nayi dana sanin zuwa na duniya dayawa suna cewa rashin kai budurcina gidan mijina yasa ya min wannan wulakncin yayinda maganan yayi tasiri akayi ta yad'ata unguwa da 'yan uwa.
Amma abun takaici ko kallo ban ishi umma na ba, bare sannu ko kuma ta ajiye ni taji damuwa ta hakan yafi komai yimin ciwo a rayuwa ban san daad'in uwa ba, ban san abinda ake cewa uwa ba a kaina kam sede Ina ganin yadda take kula da kannena kaman zata maida su ciki.
Abun na min ciwo fiye da tunanin me tunani, mutuwar aurena na farko yayi sanadiyar tashinmu a rijiyar lemu, muka koma gadon kaya da zama sbd ban isa fita ba haka 'yan gidanmu, Babana na matukar sona kan faruwan mutuwar aurena na farko, wani irin so yake min da ban san iyakarshi ba.
Sbd tausayin da nake bashi, komai sede kishiyar uwata ta min, tun Ina karama umma ke banzantar da ni wai ita alkunyar 'yar fari a yadda baba ya fad'amin kenan amma har yau ban yarda ba sbd abun yayi yawa.
Ban san kula ba se a wurin mama, ban san yadda ake shagwa'ba a gaban uwa ba se a gabanta, ban da wadda zan kaiwa kuka na se mama, da farin cikina da bakin cikina duk tare muke rabawa se ince ta fini shiga damuwa akan mace macen aurena.
Hayaniyar d'alibai masu fitowa daga auditorium hall ya tabbatar min da an gama lectures d'in, d'ago idon da zanyi se ya fad'a cikin nashi ko second idonshi be yi a kaina ba ya manna bakin space akan sparkling brown eyes d'inshi tare da nufar motanshi cikin takun isa da kasaita, se a lokacin na gane ashe wadda ya kad'e ni a hanyar shigowata shine lecturer d'inmu na yau.
Kallonshi nake yadda farinshi ke d'aukan ido ga baki wuluk d'in gashin kanshi dake kwance lublub har kasan keyanshi se sheki yakeyi, irin gashinne cike da giranshi haka sune gargasan dake kwance a hannunshi zuwa saman kirjinshi da ya fito kad'an sbd V neck black shirt da ya saka.
Ina mamakin wannan bawan Allahn anya d'an nijeria ne? Bakaken kananan kayan dake sanye a jikinshi ya kara fitar da farin fatarshi, kananan maganganun da d'alibai suka fara akanshi ne yasa ni kauda kaina daga kallonshi na mayar kasa Ina me kokarin sake zundumawa duniyar tunani na naji an zauna gefe na.
A hankali na waiga se naga wata kyakyawar matashiyar yarinyar da tunda na fara zuwa makarantan take yawan ce min sannu bayan ita ban ta'ba magana da wani d'an ajinmu ba, alhalin Ina cikin sati na hud'u kenan da na fara zuwa makarantan ta BUK inda nake karantar B.sc Ed Biology.
"Sunana Zarah Ahmad Malabo and yhu?" Da kyar na iya yi mata yake don murmushi wahala yake min nace "Saudah Hafeez ana kirana Noor Iman".
*•Assalamu alaikum 'yan uwa ga fah Gureenjoh da sabuwar littafi hope zaku so shi kaman sauran books d'ina, promise yhu will never regret reading my book, in shaa Allah, comments for more pages•*
🖤Gureenjo🖤
🥀NOOR IMAN🥀
*Fatima Muhammad Gurin*
•Gureenjo6763 on Wattpad•
*`yar mutan Adamawa*
💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)
*02*
“Wow nice name, kiyi hakuri fah da abinda Dr. Abdurraheem ya miki haka yake da wulakanci ga dizgi wai shi In har ya shiga aji to ba me shiga a bayanshi, amma ke baki jima da fara zuwa ba ko? Gashi an ci rabin semester na san baki yi catching up wasu abubuwan ba, zan dinga koya miki karki damu daga yau mun zama friends”.
Lord!! Wannan bade surutu ba mutum kaman aku, na raya a raina a fili kuwa murmushi na mata Ina son inyi karatu sossai inga na zama wata a duniyan nan yanzu ban son aure ban son wani magananshi karatu kawai hakan yasa nake son yin kokarin yaki da zuciyata In kuma kau da tasiri da maganan mutane ke min inyi karatu tukuru.
Dama asalina me surutu da kazar kazar ce rayuwa ne ya maida ni miskilar karfi da yaji, kallonta nayi nace “yanzu d’an wannan yaron ne doctor kina nufin ya kammala doctoring degree d’inshi?” Zarah ta ta’be baki kan tace “kwarai kuwa ke abunki da wadda be yi karatu a nigeria ba firrrrrr ya tafi ba wani delay balle strike duk degrees d’inshi a kasar waje yayi kuma daban daban”
Jinjina kai nayi don son kawar da magananshi na ce “Toh yaushe zaki fara koyamin karatun?” Tace “duk sadda muke da interval tsakanin lectures se mu dingayi ko In mun gama da wuri kuma bamu da wani se mu d’an yi kan mu tafi” wannan karon murmushin da na mata tun daga cikin zuciyata ya fito, wara brown eyes d’inta kad’an tayi kan itama ta saki murmushi tace “wow I like your dimple and your wushirya” na kuma yin murmushi nace “nice meeting yhu zarah”.
Tace “same here” hira ta ci gaba damin ni kam se nodding da d’an murmushi tunda na shiga 18 zan iya rantsewa ban ta’ba mintuna biyu ba tare da damuwa ko tunani ba amma gashi yau samun mutum a kusa dani kuma me faran faran ya sani sakewa da ita sossai har na manta da damuwana na wani lokaci.
Eleven nayi muka shiga another lectures na chemistry sossai na maida hankali kuma ba laifi na fahimta don ni d’in ba laifi me d’an kwakwalwa ce.
Karfe d’aya muka fito muna fitowa zarah ta kalleni tace “har anzo d’aukana muje mu sauke ki a gida ko Ina Gandun albasa kike kikace?” Kai na gyad’a mata Ina d’an murmushi nace “nop ke kam yi wucewarki, se in mun had’u gobe” na san irin gulman mutane yanzu a fara rad’e rad’en na fara bin maza ana saukeni a manyan cars dama yanzu ma ban tsira ba.
Ba yadda zarah batayi ba amma naki haka ta tafi ni kuma na ci gaba da takawa a hankali sbd kafana da ya d’an suntuma zuwa lokacin, ban wani ‘bata lokaci ba na tare napep na shige tare da fad’a mishi inda zani.
Bayan mun iso na sallameshi na fara takawa cikin taka tsantsan kaina a kasa kaman kullum daga gefe majilisan ‘yan unguwa ne na samari gaba kad’an kan gidanmu na tsoffi.
Kullum In har zan bi ta wurin na wuce se na zub da kwalla dayake mutuwar aurena har biyu a unguwan na Gandun albasa ne, ‘ka ganta nan ashawon, ta fito yawon karuwanci da sunan makaranta’ runtse ido nayi Ina jin zafin sunan amma daga yanzu nayi alqawarin bazan kara yi musu kuka ba.
Ina jin wani daga ciki yace ‘wai itace me aure auren?’ Wani yace ‘kwarai kuwa aurenta na farko sako ta akayi a daren farko sbd bata kai budurcinta ba’ da sassarfa na karasa wucewa dukda zafin da kafana ke yi, haka zuciyata kaman an saka a tukuban tsire.
Ina isa wurin manyan mutanen na duka har kasa na gaidasu suka amsa ba yabo ba fallasa amma nayi musu farin sani na san ina bada baya za’a dasa maganata dukda ba koyaushe sukeyi yadda zanji ba amma sun hana ‘ya’yansu kap huld’a dani wai zan ‘bata su.
Ina shiga gida hawayen da nake rikewa ya fara gangara umma ta na tsaye jikin igiya tana shanya baba zaune a kan taburma kasan bishiyar umbrella (almond) yana shan iska don ya dena fita majalisa sbd habaice habaice da bakar maganganun da ake ya’ba mishi gashi ya ci alwashin baze ta’ba chanza wani unguwan ba sbd ni, rijiyar lemo da Gadon kaya sun isa.
“Umma barka da gida” da “yauwa” kawai ta amsa ni ba tare da ta ko kalle ni ba, girgiza kai nayi inajin hawayena na karuwa na rasa dalilin kasa sabawa da wannan hali na ummana a shekaruna na 23 a duniya.
Har kasa na duka gefen taburman baba nace “sannu baba Ina yini?” Kau da kaina nayi daga kallon banzan da yake watsa min Ina jin yadda ya ja dogon tsaki, gwiwa a sage na mike na karasa kofan mama nayi sallama daga ciki ta amsa ni tana cewa “lale lale ‘yar albarka barka da dawowa” murmushin yake nayi na karasa parlorn na zauna.
Ikhram da ikhlas dake zaune saman kujera suka ce “sannu da dawowa yaya iman” nace “yauwa” mama ce ta fito tana kallona tace “naga kaman duk kin gaji tashi kije kiyi wanka ki zo ga abinci nan kizo kici” wani yaken nayi Ina mikewa nace “Toh mama na gode” taku d’aya biyu nayi naji ta saki salati tsayawa nayi na san sbd kafana ne itace kad’ai!!
Itace kad’ai a duniyata da zata ganni da damuwa ta magance min, ita ce kad’ai me sona nan duniya haka nima Ina sonta har raina sbd son da take min ban damu da kasancewarta kishiyar uwata ba “na shiga uku Iman me ya samu kafankin?” Na juyo Ina murmushi nace “mama bugewa nayi” tace “ashsha zo muga” wurinta na koma tana gani ta waro ido “maza juya mu fice gidan malam iro ya gyara miki daga gani gurd’ewa ce ko tsagewar kashi”.
Baki na turo Ina shirin mata musu har ta shige d’aki tana fitowa ta sani a gaba muka fice zuwa tsakar gida ta kalli baba tace “malam yarinyarnan Noor Iman ta samu matsala a kafanta bari muje gidan malam iro ya duba mata” bata jira cewar shi ba muka wuce don ta tabbatar ba amsa ze bata ba inde akan maganan da ya shafeni ne kaman yadda nima na san da hakan.
Muna isa ya tabbatar da gocewar kashi ne a rike ni ya gyara da kuka da komai aka gyara mama se mita take wai na cika ragwanci, biyanshi tayi muka fito muka dawo gida ina share hawaye, wanka nayi na shirya cikin riga marar nauyi duk a d’akin mama komai na yake don ban ci darajar a bani d’aki na ni kad’ai kaman sauran ‘yan matan gidan da yanzu suke gidan mazajensu ba.
Ido na a lumshe nake taryo rayuwarmu na baya, Malam Musa Muhammad d’an asalin kauyen wudil ne na nan jahar kano yana da mata d’aya da yara takwas ya jima yana sana’an driver kuma har Allah ya kar’bi rayuwanshi sana’anshi kenan, da Sana’an ya sayi gida anan hayin rigasa suka dawo nan da zama anan cikin kano gabad’aya yaranshi sukayi karatu kasancewarshi me son boko, dukda shi be yi ba, baba shine na hud’u a cikin ‘ya’yanshi yana da kanne hud’u.
Goggo Kamila, goggo saratu, goggo hindatu, se bappa Audu.
Yayyunshi uku duk maza ne bappa Yushe’u, se bappa Mu’azu se bappa sama’ila kan baba, duk mazan sunyi karatu daidai gwargwado iyawar mahaifinsu kan rasuwarshi inda babana yayi diploma d’inshi a fannin mass com, ya auri ummana (Aisha) ne a chan garin malumfashi na nan katsina inda ta kasance ‘ya d’aya tilo a wurin iyayenta batayi wani karatun kirki ba iyayenta suka cireta suka aurar da ita.
A lokacin ya fara aiki a matsayin karamin ma’aikaci a gidan rediyon freedom, suna son junansu don zaman amana da soyayya sukeyi wadda jigonshi ya kasance hakuri, har ummana ta shekara hud’u bata ta’ba koda ‘Batan wata ba, hakan yasa su goggonina da inna mahaifiyar baba suka matsa ya karo aure yaki sam amma se suka fi karfinshi inda ya auri kanwar matar bappa yushe’u.
🖤Gureenjo🖤
🥀NOOR IMAN🥀
*Fatima Muhammad Gurin*
•Gureenjo on wattpad•
*'yar mutan Adamawa*
💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)
*03*
Hadiza wato mama kenan, zuwan mama da kwanaki kad'an ciki ya bayyana a jikin ummana sossai baba ya d'auki son duniya ya d'aura akan cikin, su inna kam da suka ji labari se kunyan yadda suka dinga mata ya baibayesu suka dawo suna son cikin suma kaman su janyo ran haihuwanshi.
Kwarai umma ta wahala a wurin haihuwa na har Allah ya sa ta sauka lafiya inda ta sameni ba karamin farin ciki su inna da baba sukayi da hakan ba, har mama kaman zata had'iyeni zan iya cewa son da take min yafi na ummana a ganina fa kenan, aka saka min sunan inna "saudah" yayinda mama ta saka min inkiya "Noor Iman" shekaruna biyu a duniya ummana ta kara haihuwa nan ma mace "hafsa" sunan mahaifiyarta ce bata yarda kuma a boye mata suna ba.
Bayan hafsy da shekaru biyu ta haifi Nafeesah daga ita da shekaru biyu ta samu Al'amin se Ihlam yayinda ikhlas ta kasance auta, har rana yi ta yau mama bata samu haihuwa ba kuma sam bata nuna damuwanta akan hakan tunda ta d'aukemu a matsayin 'ya'yanta itama karshe ma kyauntana sukutum baba ya bata ganin yadda take kulawa da ni kamar ita ta tsuguna ta haifeni.
Mun girma da son boko kaman yadda baba ya tusa mana ra'ayin kanmu a had'e yake da sauran 'yan uwana mata yayinda suke tausayamin ganin yadda umma ke nuna halin ko In kula da rayuwana zan iya cewa ban ta'ba mintuna biyu cikakke muna magana da ita ba kwata kwata bata san komai nawa ba.
A haka har na girma nayi wayo maimakon In ji na tsaneta amma sonta da son ta kulani suka shigeni, se in dinga shishige mata tana hantarana watarana har dukana