Showing 21001 words to 24000 words out of 124573 words
Chapter 8 - Sangartacce Book Complete Pdf by Maman AbdulShakur.pdf
dauko shi namai addu'a nabashi magun guna anan, to ubangiji Allah ya kara mana katanga
da makiyan mu, ko lokacin dana bata addu'an nace mata inhar sihiri ne dazaran yasha zai
karya ashe kam sihirin ne" Abba ya girgiza kai cike da damuwa yace "bamusan waye ke neman
shi da shairi hakaba, amma muna kan rokon Allah daya bayyana mana gaskiya" Baba yace "ai
wanan ba matsala bace zan bashi addu'o'i dazai dingayi kullum safe da maraice in sha Allah
babu abinda zasuyi dazai kara kamashi da izinin Allah kuwa dan kariya ce" Abba da kaman
yazuba ruwa akasa yasha yace "mun gode, mun gode akaramakallahu, Allah ya biya bukata"
sukadan yi shiru shidai Ayaan kanshi akasa Allah Allah kawai yake Pops yagama surutun shi
sutafi, gashi yakasa daddana waya hakanan yaji malam ya cikamai ido, maganan Abba ne
yadawo dashi daga zancen zucin dayake yi. "Malam ina diyar naka Bilkisu zanzo mu ganta mu
kara yimata godiya idan ba damuwa" murmushi Baba yay yace "tana makaranta chan dogon
bauchi, dayake na rana takeyi sai biyar da rabi zata dawo" Abba yay shiru chan yace "inba
damuwa zamu jirata tadawo Malam" Malam yace "babu komi ai tama kusa tunda gashi yanzu
hudu saura" nan fa hira yakachame tsakanin Abba da Malam da Baba Suleman kaman sunsan
juna ataba nan ataba chan, suna yin la'asar Muji yamusu sallama yatafi nan Umma ta gabatar
musu da abincin da aka dafa musu farar shinkafa da jar miya bayan ta gaisa dasu ta fita,
abincin su Abba sukaci sosai abinsu dan wlh yay dadi.
Wuraren biyar da rabi ta shigo gidan nasu da sallama a gajiye, tun awaje take mamakin babar
motar data gani a pake akofar gidan su, gashi kuma gidansu nawani fitinannen bakon kamshi,
abakin kofar su ta zaunar ta ijiye jakan makarantar ta agefe tana kokarin cire takalmi da safa
dan bama ta lura da takalman dake gaban kofar dakin Baba ba, cikin yar siriyar muryan ta ta
kwalama Maman su kira "Mama nadawo" safan tacire tarike su ahannu tana kallonsu ganin
sunyi datti yasa ta taka farar kafarta datama jan lallin salatef jiya dayay kyau sosai zuwa wajen
botikin dake gefen rijiya ta wurga zafan tajuya zata shiga daki taji muryan Baba daga dakinshi
yana kiranta. "Bilkisu" "Na'am Baba" tajuya zata tafi da sauri Raiyana dake falo zaune tace
"Baby bakine fa kizo ki chanza kaya" turus tai a tsakar gidan tana kallon takalman da sauri
tadawo daki hijabin makarantar kawai tacire sanan tadau pink hijab dinta data goge dake
makale ajikin kusa tasaka, har kasa hijabin ya kaimata mai hula aiko bakaramin kyau yamata ba
yafitar da baby face dinta sosai, ko silifas bata sakaba tai hanyar dakin Baba, abakin kofa tai
sallama sanan ta shiga, gani tai kowa na dakin ita yake kallo banda mutum daya da kanshi ke
kasa, murmushi tadan kakalo daya lobar da dimple dinta sanan ta shiga tsakar falon, dukawa
tayi tafara gaida wanda bata ganin fuskarshi danya dukar dakai, sanan tadan matsa batare data
jira amsar shiba ta gaida tsohon na tsakiyan su wanda tunda ta shigo yake kallonta yana washe
baki ahankali tace "ina yini Abba" murmushi Abba yay yace "andawo yan makaranta Bilkisu ya
karatu?" a kunyace ta sunnar dakai tace "Alhamdulillah Abba" sanan tagaida Baba Sule da
shima ya amsa mata cike da fara'a kafin ta koma gaban Baba ta tsugunna kusa dashi tace "gani
Baba" Baba da tunda tashigo yake kallonta yadan nisa yace "wajen ki akazo?" dan zaro ido tayi
dan bataga wanda tasani cikin suba hakan yasa Baba ya gyara zaman shi ya fuskanceta da
kyau yace "yaushe kika faramin karya Bilkisu? Maisa baki gayamin gaskiya ba ranan dakika zo
kika karbi addu'an nan? Eh? Inda nasan gaskiyar zancen aidana hadaki dasu Isyaka kun
kawoshi nadinga mai magani agida" rasa abinda zatace yasa tafashe da kuka mara sauti, jikinta
ta har rawa yake tasa bayan hannu ta goge idanunta ahankali tace "Baba kayakuri, tsoro nakeji
na dauka xakamin fadane" takarashe maganan cikin kuka, akaro nafarko kenan daya dago kai
yadan saci kallonta da sauri ya kawad dakai kuma. Malam ya nisa yace "shikenan ya wuce
haka Allah ya kaddara faruwan lamarin, gashin nan shida iyayen shi zunzo yimana godiya tun
dazu ke suke jira ki dawo daga makaranta, daga kano suke"Juyo dakai tai tadan saci kallon su
daidai lokacin shima yasake dago kanshi suka hada ido da sauri ta janye nata kirjinta na
bugawa, yanzu wanne ne dama mahaukacin nan kai anya kuwa. Maganan Baba yadawo da ita
daga duniyar tunani ya kalli su Abba yace "bari indan leka yaran nan Alaji" Abba yace "to
Malam, saimun fito muma" fita Baba yayi Abba ya gyara zama ya kalleta yace "yar arziki Allah
yamiki albarka y'ata, yabiya miki bukatun ki duniya da lahira, duk mai taimako baya tabewa
ladanki na wajen Allah, Allah ubangiji ya baki duk abinda kikeso anan duniya da lahira banda
abinda xan ce miki Bilkisu amma nagode, nagode, Ayaan yafadan mana abinda kika mai shine
mukazo mu gode miki, Allah ya saka da alheri" wani irin kunya ne ya lullube ta mutumin da
yamafi Baba tsufa ne yaketa gode mata haka lullube fuskar tai da hijabi kanta akasa hakan
yasa Abba yay murmushi sosai ya kalli Baba Suleman yace "kaga yar albarkan kunyamu take ji,
zomu basu waje sabida shima yamata tasa godiyar" yay maganan yana hararan Ayaan dake
kallonshi kaman zaiyi ihu, fita sukai daga dakin sukai zaure wajen Baba, hakan yasa dakin yay
shiru tamaki dago kai sai wasa take da yatsunta dasuka sha jan lalle a kumba.
Daga chan tsakar gida Raiyana ta kwala mata kira. "Anty Baby kizo wai" tashi tayi ahankali
batare data kalleshi ba tafita daga dakin, Raiyana dake wurin zaure tace "Baba yace kikai mai
charbin shi" tana fadin haka tafice daga gidan ahankali tajuya jiki asanyaye tai hanyar dakin
Baban idanunta ne suka sauka akan Layla dake labe a kitchen tana mata game da waya, "lalala
wayata Layla jeki ijiye kafin kija arufemin sim" tai maganan tana tafiya, tana kaiwa bakin kofar
Baba takara juyowa ta kalli kitchen din dan taga ko Layla ta ijiye wayar ganin bata ganta ba
yasa tahau kan dakalin da zaka tsallake ka shiga dakin Baba, ta kama labulen ta rike gam kafin
ta daga kafa tana leken kitchen din ta window ko ta labene awani wajen, daidai lokacin shikuma
yazo zai fita yasa hannu yakama labulen yaja zai bude, jan labulen dayayi yasa kafarta ta
turgude tayo baya gabaki daya tafada jikinshi tabaya tareda sakin labulen yakoma jikin kofa,
mugun firgitan datayi ne yasa takasa motsi saima sauke ajiyar zuciya datake yi jin kirjinta
kaman zai fado waje gashi takasa juyowa takuma kasa barin jikinshi, kafarta datasha jan lallin
salataf yabi da kallo yana kallon gashi gashin ta daya leko ta hular hijabin ta zufan datayi yasa
sun kwanta luplup, yafita tsawo sosai hakan yasa har kwakwalwanta yana gani, hannu yasa ya
juyo da ita atsorace ta kallai, daure fuska yay kaman baitaba dariya ba yace "banason rawan
kai, ki natsu, karki sake barin irin haka yasake faruwa" yay maganan yana mata wani irin kallo
sanan yawuce yafita daga dakin cike da izza duk takun dazaiyi saitaji a kirjinta harta dena
ganinshi, tafi minti biyu a tsaye a wurin sanan ta share yan guntun hawayen dasuka zubomata
ta rufo kofar tafito tai dakinsu.
Sai bayan sallan magrib suka tafi Baba yamusu rakiya har wurin mota sanan yakoma ciki, ba'a
dadeba saiga amajirai sun kawoma malam manya manya ledoji da rapan kudi yan dubu daidai
guda biyu malam baiyi niyar karbaba yafita waje da sauri dan ya maida musu amma harsun tafi
haka yadawo yabama su Isyaka leda daya su rarraba tunda kayan kwalama ne dayan ledan
kuma ya shiga gida dashi da kudin.
Abba ne zaune gefen Ayaan dayay bacci abinshi a dakinshi na hotel yay tagumi yana kallon
fuskar Ayaan yayinda dayar hanunshi ke shafa kwantacen gashin shi, sosai ya zurfi a tunani
hoton Balkisu yakasa barin ranshi, for d first a duniyar nan yaji lokaci yayi da Ayaan zai ijiye
mata ya ijiye iyali zaizo yaga jikokin shi kafin yabar duniyar nan, yana mugun kwadayin ma
Ayaan Bilkisu, yarinya hafiza, ga ilimi natsuwa da kunya ai itace tafi dacewa da Ayaan
sanadinta hala ya natsu. Sai wajajen karfe daya sanan yabar dakin Ayaan din yawuce nashi.
Misalin karfe biyar na yamma suka fito daga cikin school dan anatashi su biyar ne na yamma,
suka jero ita Aisha shehu, Walawa, Fa'iza dakuma Fatima, itace a tsakiyar su cikin dogon farin
hijabin ta dayasha guga da wandonta purple kafarta sanye da farar safa tasaka brown takalmin
makaranta mai igiya, babu komi a fuskar ta sai kwalli dakuma mai data shafa a lips dinta bayan
sallan la'asar wanda yasa har yanzu pink lips dinta ke shining sosai da black din abin sai yay
kaman tasa jan baki, murmushi dukan su sukeyi dan Fa'iza ke basu labarin yanda sukai da
saurayinta jiya dayazo tadi sunata murmushi, bayan Fa'iza tagama duk sukai dariya, takara yin
wani irin murmushi daya lobar da dimple dinta tana dan tunani tace "niko jiya da Isyaka yazo ko"
sai kuma tai shiru tana fari da ido hakan yasa Walawa ta dafata tace "fada mana yar malam
meya faru dayazo ke badai ya mammatse kiba" hararan ta tayi tace "Allah kyauta bama iskanci
mu" murmushi duk sukayi suna kallonta, sai kuma tasake yin fari da ido tace "anbiya shi kudin
aikin hannu shaddan dayayi aiko ya siyomin ice cream jiya, muka sha nida su Raiyana" ihu
suka hau yi suna tafi. "woh ke woh ke, ashe dai ustaxai sun iya soyewa su isyaku an iya sawo
ice-cream" dariya tai kafin ta dauke kai tace "an sa fa, nan da 2weeks da some days ne?"
"mene!" dukan su suka tambayeta atare Aisha Shehu ce tace "amma kin cika yar iska Billyn
Malam, keda kikace mana sai bayan kun gama exam?" kaman zatai kuka tace "wlh bahaka
bake fa, Babane yace ranan walimar shi kawai ahada da auren" duk shiru sukayi suna tafiya
ahankali saikace ba gida zasu ba sai kallon su take tana murmushi, chan Walawa tace "inko
hakane bazamu yarda ba wlh dole mutaba mu mulmula su kafin Isyaka yataba" ihu sosai tayi da
saida sauran daliban gabansu suka juyo ta arce da gudu sosai tana dariya saida ta musu nisa
sosai dan har bata hangosu sosai sanan ta jingina dawani mota tana mayar da numfashi tana
dariya tana kallon layin data kusa kurewa da gudu, kirjinta ta dafe tace "wayyo Allah na" jin
yanda ya wani irin buga sanan tacigaba da nishi tareda lumshe ido tana kokarin saita numfashin
ta, wani irin kamshin turaren kamshi daya daki hancin ta yasa ta bude ido ahankali ta saukesu
akanshi ya tsaya agaban ta yay folding hannu akirji yana sanye cikin wani black bodyhug daya
kama shi dan kana ganin layi layin six pack dinshi, da fadadden kirjinshi dake nan kaman ya
rabe biyu, sanan hannun rigar yakama muscle í ½í²ª dinshi jijiyoyin sun fito, kafara shi cikin wani
original tomford sneakers, ya sanya wani dan iskan crazy jeans dayay tokin rigar aciki sanan
yasaka belt mai bala'in kyau, kana iya hango sarka dake kyalli ta wuyarshi gawani sheken dan
kunne na diamond wanda maza ke makalawa da gum, dan dan kunnen da gum dinshi yake
zuwa, idanunshi sanye cikin dark shade da bata iya tantance mema yake kallo, yanda ya tsaya
a gabanta sosai yasa tama kasa janye jikinta daga motar dan go tafiya daya kacal tayi zata iya
gogan jikinshi ta lafe ajikin motar numfashin ta nafita da sauri da sauri, hannu yasa a aljihun
bayan wandon shi yazaro bandir din kudi yan dubu daidai ya rike kudin kafin ya kalleta, kanta
akasa tana wasa da bakin hijabin ta, wurgamata kudin yay a fuska wanda har saida ya bugi
bakinta kafin ya fadi akasa tsakakanin kafanta, yabi kudin da kallo sanan ya tabe baki yace
"Pops ne yadaman nabiyo ki school dinku namiki kyauta, so here u go" yajuya yay inda ya paka
mota zai shiga, bin kudin tai da kallo ranta ya mugun baci da sauri ta share hawayen dataji ya
zubomata ta tsugunna ta dauki kudin ta mike ta kalli motar daya shiga ganin baibar wurinba
yasa tai wurin motar, kai tsaye tabude daidai lokacin ya dauko bottle water ya bude zaikai baki,
ajiye mai kudin tai akan cinya ahankali tace "nagode amma ni bana bukatar wani abu daga
wurin ka" tajuya zata tafi karaf taji yarike wutsiyar hanunta, da sauri ta juyo taga bama ita yake
kallo ba saima kai bottle din dayay bakinshi yana shan ruwan shi a natse, duk iya karfinta
takasa kwance hanun gashi duk yan makarantar su dazasu wuce nata kallonsu duddu su
Walawa basu riga sun karaso ba, zafin dataji hannun nayi yasa hawaye ya gangaro mata a
kunci, saida yagama shan ruwan sanan ya ijiye bottle din ya juyo da kanshi ya kalleta tareda
cire bakin glass din idonshi ya ijiye a gefe ya kafeta da idanu da sauri ta janye nata ta cigaba da
kokarin fizge hanunta, muryar ta har rawa yake tace "ka sakeni natafi gid..." "ke!" ya daka mata
tsawan da batasan lokacin data fashe da kuka ba ta hadiye sauran maganan, wani irin mugun
kallo yamata dayasa ta hadiye hawayen tarasa mesa take shakan shi haka, cikin wata irin
kakkausar murya yace "kinsan wayeni kuwa?" dan murmushin gefen baki yayi dayawani irin
karamai kyau kafin yasake damke fuska yace "Am Dr Ayaan, a doctor, double degree holder,
masters holder and PhD holder, am a surgeon and a pathologist, mace bata kawomin wargi,
babu abinda bansani ba na mace, so ki kula! Ki natsu! I don't take shit! dan haka pick dis money
and get out of my sight" yafada cikin tsawa tareda jawo hanunta daya damke tun dazu ya daura
kan kudin yamata wani irin kallo dayasa ta bude hannun da sauri ta dauke kudin sanan ya
turata dahar saida tafadi kasa yaja motar dawani irin gudu yabar wajen yana tsaki, baisan mesa
Popsy kemai wanan abinba wlh me zaiwani sa yazo nan, thank God yau zasu bar garin.
[7/15, 12:21 PM] Ummi Tandama: [7/13, 10:15 PM] +234 802 916 3341: ♦♦ *SANGARTATTCE*
♦♦
Maman Abd Shakur
23 - 24
*For Sell! idan baka biyaba dont F*ck*ng read it in Ayaan voice. Aha*
Hawaye ta share tabi wutsiyar hanun nata da kallo yanda yay ja abunku da farar fata ahankali
tace "kuma ban yafeba mugu kawai" ta tashi da gudu tana kuka tai bakin titi batare data waigi
su Walawa dake kiranta ba, ta tare Bus ta shige tana share kwalla ahaka har gida. Tana zuwa
gida kofar gidan su tai turus tana kallon baban trailer company Uniform, suna sauke katipu irin
na boarding school dinan ankawo ma almajirai kowa daidai, aiko sai tsalle suke suna murna
wajen ya kacame da hayaniyan su, karasawa tai wajen Baba dake tsaye yay shiru yana kallon
masu sauke katifar tace "Baba waya aiko da wayan nan katipun?" "mutanen dasuka zo jiya ne
suka aikoma dalibai dashi, wai suna Allah kadai zai iya biyan mu amma ga wanan abama
dalibai" shiru tayi tama rasa yanda zatayi tabama Baba kudin daya bata dan kunya takeji fada
zai mata mesa ta karba hakan yasa ta wuce cikin gida tana satan kallon Isyaka dake rubutu a
allo yana binta da kallo shima, murguda mai baki tayi tana nunamai allon ta shiga gida tana
dariya, da sauri yabi allon da kallo yaga ashe afarar rigarshi yay rubutun baima saniba garin
kallon ta muurmushi yay ya shafa gemunshi daya cika kaman wani babba sosai yacigaba da
rubutun dayake yi. Tana shiga ta debo ruwa daga rijiya ta shiga tai wanka tadawo daure da
zani, tana bubbuga kunenta dan ruwa ya shiga gajiya tayi da goge kunen kafin ta zauna gefen
mama hanunta Mama tabi da kallo yanda yay ja tace "maiya sameki a hannu?" girgiza kai tayi
tace "bakomi bugewa nai a school" kofin magani Mama tabata ta karba tasha sanan a ijiye tana
yatsine baki, jakarta tadauko taciro bandir din kudin ta ijiye kusa da Mama tace "Mama mutumin
nan najiya nahadu dashi a makarantar mu yabani wanan" kudin Mama tabi da kallo tace "aisai
ki kaima Baban ki tunda kinada hannun amsa ni meruwa na" kaman zatai kuka tace "Mama dan
Allah kibashi nidai tsoro nakeji, fada zemin wlh" tai kaman zatai kuka ta mike ta shige uwar daka
dan saka kaya.
*******
Yau kwanan su biyu kenan da dawowa daga kano.
Mami dake kwance kan gadon Abba danyau ita keda girki ta kalli agogon bangon dakin taga
karfe biyu har da rabi nadare kafin tasake kallon Alaji, tun wuraren goma Alaji ke kan dadduma
sai salla yake yana addu'o'i data rasa name, kasa hakura tayi ta sakko itama ta shiga bayi ta
dauro alwala tafito tadau hijabi ta bishi, bayan sun sallame ta dafa shi, juyo dakai yayi ya
kalleta, murmushi tamai dake sanyaya mai rai tace "Alaji matsalar mekake dashi haka? Meke
damunka tunda kadawo daga zaria naganka duk wani irin wats d matter talk to me, kasan state
of health dinka bai kamata kanasa damuwa aranka ba" dan ajiyar zuciya tayi kafin ta maida
kanta kan kafadar shi ahankali tace "meke damun mijina abin alfahari na haka?" murmushin
dabai shirya yiba yasaki Firdausi daban ce, koyaya yake cikin damuwa kobai fadi mataba zata
gane, duk wani hanyar sanyaya mai rai tasani, murmushi yasakeyi kafin ahankali yace "akan
dan mu nake addu'an nan" tabe baki Mami tayi hakan yasa ya girgiza mata kai yace "ba abinda
kike tunani bane wlh" yadan gyara zama alamun serious yace "tunda naje zaria naga Bilkisu
zancen ta ya tsayamin arai, duk sakan sai maganar ta yazomin rai, ina son Ayaan da yarinyar
nan fiye da yanda kike tunani, yarinyar akwai natsuwa ga ilimi, ta sauke fa takuma kusa gama
hada hadda inji baban ta, ga taimako, ayanda Boy yake yanzu mace