Showing 33001 words to 36000 words out of 124573 words

Chapter 12 - Sangartacce Book Complete Pdf by Maman AbdulShakur.pdf

M Shakur   

09 Nov 2025

3879

ki rakani" tashi Reema tayi tadau gyalen ta saba
akafada suka fita bayan ta kara jan gyalen ta tarufe fuskar ta.

Tunda suka fito daga gidan kanta ke kasa sabida yanda taga maza sun cika layin alamun
andaura auren kenen, ahaka har suka shiga cikin gidansu aiko ana ganin ta matan dasuka cika
tsakar gidan suka hau guda ayyiririri ga amarya ga amarya, kara lullube fuskar ta tayi har suka
shiga dakin Umma da Layla ta nuna musu, Umma ce dake daga bakin kofa ta yaye mata gyalen
data rufe fuska dashi tace "ai sai abude fuskar ko tunda kin shigo amarya, ga baki kinyi daga
kano iyayen Ayaan ne" dukda bata gane waye Ayaan din da Umma ke fadi ba hakan bai hanata
dago kai ta kalli manyan mata biyu dake zaune akan doguwar kujeran ran Umma da aka

wadata su da abincin biki agaban suba suma ita suke kallo a kunyace ta dukar dakai ta
tsugunna tana wasa da hannayenta dasuka sha lallin amare ahankali tace "ina yinin ku Mumy
kunzo lpy" atare Big Mummy da Mami suka amsa mata da lpy lau tareda yima ta godiya akan
abinda tama Ayaan, sai a lokacin ma tagane ashe iyayen mara mutuncin mahaukacin nanne,
suka mata fatan alheri tareda addu'a zama lpy duk kanta nakasa dan bata yarda sun sake hada
ido ba dan kunyan su takeji sosai, Mami ma takasa daina kallonta har kasan ranta takeji kam
inama ace Ayaan ya sameta din ya aura da tai farin ciki sosai yarinya mai natsuwa haka da
kunya. Ganin takasa tashi yasa Umma tace "to tashi kuje ku koma wajen kawayen ku" ahankali
ta mike tsaye tadan kallesu kafin tasake dukar dakai tace "mungode Mummy Allah kiyaye
hanya" tajuya da sauri tafita Reema tabiyota abaya tana murmushi suka fito zaure zasu fita
waje, tsayawa tayi tana kara lullube fuskar ta da gyale sanan suka fita suka koma gidan party.

Sai bayan sallan la'asar dan lokacin hartai sallan la'asar har an chanza mata kaya wanan karan
amtapa ne ajikin ta milk colour anmai kwalliyan black ajiki, wayyo Allah bakaramin kyau Bilkisu
tayi ba tasa takalmin dazu baki da gyalen da jakan tana zaune cikin su Walawa daketa mata
tsiya Baaba da wata kawarta sukazo gidan, gyalenta suka saka mata sukai mata lullube sanan
suka kalli kawayen Baaba tace "kudan bamu aronta" suka fice tana biye dasu abaya har gidan
Baaba da babu mutane saidai su Mama, Umma, da bakin dazu na kano datake iya hangosu ta
huji hujin gyalen dake jikinta, sallama ababban falon Baaba taji Baaba tayi ta shiga da ita ta
zaunar da ita kusa da mutum dabata san kowaye ba, saikuma taji Baaba ta cire gyalen daga
kanta ta maida mata dashi kafada kafin tajuya tafita daga dakin, tasami su Mama dasu Mami da
ita suke jira duk suka fita daga gidan dan komawa gidan su, kana ganin fuskar Mami kaga farin
ciki lullube akan fuskarta, Baba dashi kadaine zaune adakin da Ayaan da aka ijiye Bilkisu kusa
dashi dan su Abba basu dade da fita daga gidanba sunje dauko wasu abokan shi daya kira ya
fadi musu zancen auren Ayaan, ajiyar zuciya Baba yayi yana tausayin yanda ma zai fadama yar
tashi abinda Isyaka yayi hakanan dai ya tatataro jarumtar shi ya fuskanceta yakira sunanta
"Bilkisu" dago kai tayi ta kalli Baban nata tace "na'am Baba" yace "inaso ki zama jaruma mai
karban kaddara aduk yanda tazo mata, karki sa komi aranka ki dauka komi yafaru ne ayanda
Allah yakeso, ahaka Allah ya tsara tun kafin ma a hallice mu" yadanyi shiru kafin ya nisa yace
"yau awurin daurin aure Isyaka ya tashi agaban kowa" saikuma yay shiru kafin yay murmushi
me ciwo yace "yace yafasa auren ki baya sonki yajuya yama fita daga masallacin abinshi" tunda
yafara maganan ta dago kai take kallon mahaifin nata badadan shi bane ke gayamata maganan
nanba da wlh zata iya cewa karyane Isyakan ta bazai taba yimata hakaba, yace "bazai aure
kiba, shine dama mahaifin Ayaan yataba zuba nemama danshi auren ki lokacin ankusa bikin ki
da Isyaka, shine yau bayan abin yafaru Ayaan yace shi abashi yana sonki shine nasa aka daura
auren ki da Ayaan ga sadakin ki nan" ya daura mata kudin ajiki, kaman ma bata duniyar nan
haka takejin ta Isyaka yace bazai aureta ba, andaura mata aure da Ayaan din dabama tasan
wayeshi ba, dan bilhakki takara manta wani Ayaan, Isyaka na ne yace "bazai aureni ba?" da
sauri ta kalli Baba da rinannun idanunta dasuka cicciko da hawaye dan shima ita yake kallo
tace "Baba Isyaku nane yace bazai aureni ba? Menamai Baba, wlh banmai komiba dan Allah
kace yayakuri Baba" tafashe da kuka sosai kaman zata mutu, Baba ya girgiza mata kai yace "i
shiru ki manta da zancen isyaka danke matar wani ce yanzu, nasan ban kyauta miki ba dan
banji ta bakinki ba, amma a matsayina na uba zan iya zaba miki miji nagari daga ganin Ayaan

yaron ne dan gidan arziki, ga mahaifin shi da kirki da daraja musulmai, nariga na musu bayanin
jarabawan da zaki zana sun amince daki zauna agida bayan gama jarabawan saiki tare, yanzu
dai bari na barku tare kudan tattauna ni natafi wajen su mahaifin ka" yay maganan yana kallon
Ayaan da kanshi ke kasa tun dazu, dago kai yayi ya kakalo murmushi yace "to Abba" Baba
yafita yana kallon Bilkisu dake wani irin kuka dake tabamai zuciya gidan yarage daga shi sai ita.

Baba nafita tamike tsaye zata fita dan bama tason ganin koma waye mijin da Abba yace
yamata, hanyar fita daga dakin tayi cikin kuka fuuu taji an wani irin fincikota danhar saida
gyalenta yafadi kasa saura kiris tafada kanshi amma ganin wanda take shirin fadawa jikinshi
yasa ta dage ta tare kanta tafadi agabanshi tana kuka, wanan mugun Baba ya aura mata dama,
wutsiyar hanunta daya kama tabi da kallo, hawaye masu dumi suka zubomata tafara kokarin
fizge hanun nata amma yaki sakinta saima wani irin matsiyacin kallo dayay yace "Ke! bazaki
natsu ba" ko kallon shi bataiba saima daddagewa data keyi zata fizge hannun, hannun yabi da
kallo ba karamin kyau lallen yayiba barinma yatsunan ta da dogayen kumbunan ta da aka
zagaye su da ja, yasake mata wani irin kallon yadanyi murmushin gefen baki yace "bakiji dadi
bama na taimaka miki? Wanan kazamin yaron yace baya sonki shine nace ni bari indan rufamiki
asiri sabida tausayin mahaifin ki danaga hawan jini yana neman kamashi za'ai abun kunya,
shine na taimaki rayuwan ki inda bahaka ba mezanyi dake jibeki fa dan Allah" wani irin bakin
ciki da maganganun shi yasa taji yasa ta daddage taja wata shegiyar tsaki. "mtswwww" fizgota
yay wanan karan saida tafado a kirjinshi, gabaki daya hanunta daya rike yamaida shi ta baya ya
lankwasa hakan yasa tai wani irin ihu. "wayyo Allah Mama zai kasheni" tafashe da kuka mara
sauti jikinta ko ina rawa yake, dan lumshe ido yayi jin yanda numfashin ta na kuka ke sauka
akan fuskarshi kafin ya budesu ya sauke akan hawayen dakebin kuncinta ba kakkautawa ya
daure fuska tamau tareda sake matse hannun tabaya ihu tayi sosai har saida ta bankare ta
daura dayan hanunta akan kafadarshi duk cikin azaba, hanun yabi dawani irin kallo da sauri ta
janye tana kuka sosai tana yarfe hannun harda shesheka, sakinta yayi tareda tureta harsaida ta
fadi akasan wajen ta tashi ta zauna da sauri ta kamo hanun daya kama tana kallon yanda yay ja
takara fashewa da kuka tana hurama hanun iskan bakinta dan zafi yake mata, tsaki yay yafita
daga dakin, akofar gidan yaga su Abba da abokanen shi dasuka zo tareda Malam ya gaidasu
sanan yaja Abban shi gefe kaman zaiyi kuka yace "Pops am going to the hotel nidai nagaji wlh i
need to sleep" da sauri Pops yataba kanshi yace "shikenan Mah Boy jeka huta muma dasu
maman ka Anjima bayan Isha zamu dawo hotel din, gobe da safe zamu dawo akara gaishe
gaishe da sanin juna kafin mu wuce kano ko" gyada kai kawai yayi yawuce ya shiga mota yaja
yabar wajen.
[7/15, 12:21 PM] Ummi Tandama: ♦♦ *SANGARTATTCE* ♦♦


Maman Abd Shakur

31 - 32

Anan falon Baaba taci kukan ta ta koshi, ji take kaman tahadi yi zuciya ta mutu maisa Baba
yamata haka tunda Isyaka yace bayayi basai abarta ba anwani hadata da wanan basamuden

mugun, ahaka bacci yay awon gaba da ita a wurin.
Hayaniyan dataji yatada ita daga baccin daya dauketa Baaba tagani zaune da wasu bakin
gidansu dasuka zo daga kauye anata hiran rabon kudin da Abba yay tayi, fashewa tai da kuka
hakan yasa suka lura ma tatashi Baaba tace "hakuri zakiyi ai Isyaku duniya ce tanada girma
yama kanshi, ki yakuri ba gashi Allah ya musanya miki ba mai sonki wanda kika taimaka, ni wlh
inxakiji ta tawama kinfi dacewa dashi, tashi kije kiyo salla kici abincin ki karfe sha biyu fa" tashi
tayi ta karbi toculan da Baaba ke mikamata ta karba tafita daga dakin ta wuce yo alwala.

Misalin karfe takwas na safe tafito daga wanka daure da zani a kirji Baaba dake zaune gaban
murhu ta bita da kallo yanda take uban sheki, murmushi tayi tajuya tacigaba da dama kokon
datake yi, daki ta shiga ta shafa mai ta shirya cikin doguwar rigan kampala shaddan purple da
fari da Baaba ta iniye mata aiko yay mata shegen kyau tana cikin fama da daurin dankwalin dan
takasa sabida dan kwalin yay kaba kaba Baaba ta shigo tace "ke imaza yapa gyalen tunda kin
kasa daurin kije Baban ki ya aiko Muji ya kiraki iyayen mijin ki suna hanya zakuyi sallama su
tafi, mike" Baaba ta dagata ganin bamata da niyyar tashi tadau gyalen ta yafa mata tace "imaza
tafi nima ganinan zuwa" fita tayi daga gidan jikinta duk asake har gidan su da babu wasu
mutane sosai dan yan uwan su kadanne suka rage dakinsu tayi tana shiga uwar daka tafada
kan Maman su tafashe da kuka sosai dagota Mama tayi ta share mata hawayen dasuke
zubowa tace "kiyakuri Baby, nasan yanda kikeji, haka Allah ya kaddara zai faru dama chan
Isyaka ba mijin ki bane, bahakanan Allah ke hadaka da wani arayuwa ba rana daya ba, kin
hadu da Ayaan ta dalili ne, asheko shine wanan mijinki, ki yakuri kinji anriga andaura babu
yanda zakiyi" cikin kuka tabude baki zatai magana Mama ta girgiza mata kai tace "banison ji"
sallaman da akayi yasa Mama ta amsa ta fita ganin Mami ce itakadai dan sauran duk sun shiga
falon Baba yasa Mama tai murmushi tace "barka da zuwa kun iso, shigo" shigowa Mami tai
tasami waje ta zauna tace "ina kwana ya gajiyan bik" Mama tace "lpy lau ya taku gajiyar"
murmushi Mami tayi tace "Alhamdulillah ina yar tawa?" murmushi sosai Mama tayi tace "tana
ciki bari nakira miki ita" da sauri Mami tace "a'a kibarshi dan Allah ni nashiga?" a kunyace
Mama tace "kai dan Allah keda yarki kike wani tambayana, ni kinga ma tafiyata bari naje
agaggaisa" Mama tadau hijabi ta fice zuwa dakin Baba, Mami ta daga labulen da sallama ta
shiga dakin, a kunyace ta mike tsaye dan taji Mama na magana bama ta tsaya ta saurara ba
sabida kukan ta take, tsugunnawa tayi tanadan murmushi ahankali tace "ina kwana Mumy"
hannu Mami tasa ta dagota sama kafin ta sumbaci gaban goshin ta, lumshe ido tai a kunyace
dan bata sababa, Mami ta zauna da ita akan gado kafin ta zauna agefenta tana murmushi tace
"Allah miki albarka Bilkisu kiyakuri kinji, Ayaan zai kula dake karkija komi zamu rikeki amana"
jakar hannunta ta bude ta ciro wata sabuwar Samsung ta mika mata kin karba tayi saima kara
sunnar da kanta kasa datayi tana wasa da bakin gyalenta, ajiye mata wayar Mami tai agefe tace
"ga wayar kinan nasamiki number na aciki, zan dinga kiranki, kiyi karatun jarabawa da kyau kinji
Allah yabada sa'a" ahankali tace "nagode Mumy" shafa kuncinta Mami tayi kafin ta tashi tafita
daga dakin itama ta shiga falon Baba anata magana.
Fadawa tayi kan gado tafashe da kuka sosai tarasa inda zatasaka ranta taji dadi, zumbur
tamike kaman an tsikareta tafito daga dakin Maman ahankali tai hanyar zaure tana tafiya sadaf
sadaf tana bude kofa tafita zaure saida tadan labe abayan kofa kafin tadan leka kofar gidan
kosu Baba nanan awaje ganin babu kowa sai kusan motoci uku dake fake akofar gidan nasu

akukkule yasa tai wuf tafito, tana waige waige ganin lallai ba kowa dan ko almajiri daya babu
yasa ta gyara gyalen kanta tareda tattare doguwar rigar dan tadan mata tsawo ta arce a guje.
Ayaan da tunda take leke leken ta daga bayan kofa yake kallon ta dan yana cikin mota ya
kunna AC yana sha, gajiya yay da surutan su yay fitowar shi waje, dayake glass din motar
tinted ne saisa bata lura dashi ba, gyara zama yay ya kalli madubin window motar yanda take
tafiya gudu gudu, sauri sauri ya kafeta da ido tareda hade hannayen shi biyu ya dunkule yakai
karamar yatsan shi daya yadaura akan lips dinshi kaman mai tunani, ganin tasha layin tai
kwana yasa ya kunna motar yaja yabita.

Babban wuri ne haka da akamai runfa sabida asamu inuwa, mutane ne zazzaune daketa aikin
hannu, wasu na sakan hula wasu kuma na aikin wuyar shadda, da sauri da sauri take karasawa
wajen fatanta Allah yasa ta ganshi anan dan tasan baida wajen zuwa sai nan, anan duka
abokan shi suke, tsayawa awurin tayi tana kalle kalle ganin bashi awurin kaman ance ta daga
kai ta hangoshi kan bencin dake gaban wani shagon dake gefen wajen, ga yar jaka agabanshi
yanata diban kayanshi dake gefenshi akan bencin yana jerasu acikin jakar, da gudu tai wurin
tana share hawayen dataji yafara kwararowa, kaman daga sama yaji ance "mena maka kafasa
aure na?" dago kai yayi asanyaye ya kalleta gani tayi idanunshi sunyi jajir suma harma sun
kumbura, kasa daurewa tayi tafashe da kuka sosai tasa gyalenta tana sharewa bata ma damu
da mutanen dake shiga shagon siyan abu bama cikin kuka tace "maiya sameka idanunka sukai
haka? Mena maka? Maiya sa kace kafasa aure ne kasan illar da hakan yamun kuwa? Inda
kasan baka sona maiya sa tuntuni baka fadaba sai a wurin daurin aure? Maisa kamin haka eh?"
baki yabude zaiyi magana saikuma yafasa yay shiru taga ya kurama bayanta ido, da sauri ta
juya dan taga maiyake kallo Ayaan ne acikin mota yay wining glass down idanunshi sanye cikin
bakin glasses, daure fuska yay tamau ya kalleta babu alamun wasa atattare dashi yace "get in"
kaman bada ita yake ba ta juya ta kalli Isyaka daya cigaba da hada kaya abinshi kaman bashi a
wurin tace "kasan yanda nake sonka kuwa shine ka cutar dani haka ko, maiya sa kamin abinda
kami..." tsawan dataji yasa takasa karashe maganan datake yi. "are u deaf nace kishiga mota
mutafi" yay maganan har lokacin yana zaune cikin mota afirgice ta juyo tafashe da kuka sosai
batare data shiga motar ba mutane sai kallon su suke, bude kofar yayi yafito yana wani irin taku
da duk taku daya saitaji har a kokon ranta, da sauri ta runtse ido sabida wani irin mugun tsoron
dataji yana shigan ta, hanunta dataji ya fizga kaman zai katsa yasa ta bude ido janta yayi ya
bude mota ya wurgarta ciki kafin ya koma ta dayan side din yanama Isyaka dasuka hada ido
wani irin kallo, da sauri Isyaka yadau jakar ya juyama motar baya kirjinshi na bugawa, wani irin
dan iskan murmushi yayi kafin ya bude motar ya shiga ya bata wuta, kuka take kaman ranta zai
fita kanta nakan cinya.

Bai tsaya ko inaba sai gidan dam, wurin babu kowa gashi very peaceful sai iskan bishiyoyin
daketa kadawa da kukan tsintsaye dake wucewa, zagayawa yay ya bude side din datake har
lokacin kanta nakan cinyanta kuka take sosai cikin kakkausar murya yace "fito" ko dago kai
batayi ba balle yasa ran zata fito, hakan yasa ya jawota da karfi luuu ta taho zata fada kanshi
dan ko karfi daya bataji dan rabonta da abinci tun jiya ya matsa gefe da sauri hakan yasa ta
zube akasa, wani wahalanlen kuka tasaki ahankali tana share guwiwar hannunta daya bugu da
kasa, ya dawo ta gabanta yay wani irin tsugunnawa daya karamai kyau yana karkada key motar

dake hanunshi yana mata wani irin kallo yace "baki da natsuwa ko, bakisan kinada aure ba
zakije kina ma wanchan dan kauyen magana" turo baki tai cikin kunci tace "Isyaka na niba dan
kauye bane karka sake cemai dan kauye" takarashe maganan tana wani lankawasa wuya
gawasu sababbin hawaye dasuka zubo mata tsabagen takaici, dagota yay da karfi ya jingineta
jikin mota ya kafeta da ido da sauri ta kawad dakai tareda sa bayan hannu tana goge kwallan
yace "ke ki natsu fa banason raini ko kadan wlh, auren taimako nayi, na taimake ki da mahaifin
ki danaga hawan jini na neman kamashi da almajirin chan yace yafasa auren ki" murguda mai
baki tayi dan wlh yakaita bango tace "eh almajirin ne aidai Allah ya halicce shi, kuma ahaka
nakeson abuna har yanz..." bakinta daya kaima duka da karfi yasa tai shiru ta fashe da kuka,
hanunta ya kama yakai baya ya murde hakan yasa ta bankare tana ihu. "wayyo Allah na Mama
zai ciremin hannu" hadata yay da mota ya matseta danhar jikinsu na gogan juna ya kalli kwayar
idonta yace "wlh idan kika sakemin rashin kunya sai namiki abinda zaki dinga kuka tunda ga
yau har ranan daza'a kawoki gidana".....
[7/17, 11:57 AM] +234 814 359 8303: ♦♦ *SANGARTATTCE* ♦♦


Maman Abd Shakur

33 - 34

Ya ja hanunta ya bude side dinta ya wurgata ciki kafin ya koma mazaunin driver ya shiga ya
yatada motar yabar wajen, duk tacika mai mota da kuka abakin layin su yay niyar sauketa
hango su Abba da Malam awaje yasa yawani dakamata tsawa. "ke!" atsorace ta dago kai ta
kallai hannu ya daura akan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login