Follow us on social media

Showing 78001 words to 81000 words out of 124573 words

Chapter 27 - Sangartacce Book Complete Complete Hausa Novel by M Shakur

M Shakur   

09 Nov 2025

5103

har office din inspector dake zaune yana jiran
su sanan yafita, inspector na ganinta ya mike tsaye cike da mamaki kafin ma suyi magana yace
"am coming ku zazxauna" fita yayi yay upstairs office din CP, yana shiga ya kame yay saluting
CP sanan yafada mishi abinda yagani Cp yabiyo shi suna zuwa office din tsayawa yayi baice

komiba yana kallon Bilkisu take fama da bude goran ruwa saikuma yasa hannu a aljihu yaciro
wayarshi ya duba yaga ai yarinyar hoton nanne wacce akai kidnapping wani irin shan mur yayi
ya kalli su Aaman dake kallonsu yace "su waye ku? And waccece yarinyar nan? A ina kuka
samota? Menene hadinku da ita?" kafin ma Aaman yace wani abu Dr ya mike yaciro ID card
dinshi yace "am Dr Ameenu and my Friend here is Barrister Aaman, nan ya shiga basu labarin
komi tundaga kan yanda Ayaan ya tsinceta da lokacin daya kawota hospital yagama sanan ya
bashi file din medical record dinta. Saida Cp yagama dubawa yay wani irin hamdala ya mika
musu hannu yana godiya sanan yace sutashi suje office dinshi dan gaskiya wanan good news
gwara Alhaji ya gani a office dinshi ba'a office din inspecta ba yau ya tabbata sabuwar mota da
kujeran maka zai samu, office suka tafi suka zazzauna sanan yadau waya yakira Abba.


Alhaji dasu Baba da Baba Sulaiman wanda yadawo jiya jiyan nan sabida kiran da Mami tamai
dan Alhaji ma ciwo ne yarufe shi, yaudai duk dauriyan da Abba yakeyi kasawa yayi yafashe da
kuka sosai, babba dashi amma kuka yake ganin abinda yafi soyuwa agareshi, aduniyar nan
gabaki daya ma Ayaan baimasan wake kanshi ba, gashi yaki yarda a kaishi asibiti agida Dr
Ibrahim yazo yamai allura yamishi fixing drip, Mami dai fita daga dakin tayi ta shiga nata tana
kuka sosai, Baba ne ke kanshi yanamai addu'a aka, shikuma Baba Sulaiman yana calming
Abba down, ringing da wayar Abba yayi yasa Baba Sulaiman ya mike ya dauko wayar daga kan
gadon da Ayaan yake a kwance ganin Cp ne yasa ya mikama Abba yace "ka dauka Cp ne Allah
sa Muji alkairi" goge idanunshi yayi da bakin malummalum din dake jikinshi ya kalli Ayaan da
aka sakama oxygen dan baya iya numfashi da kyau ya sake girgiza kai yana kokarin tsayar da
hawayen dakeson zubomai, yay picking call din tareda yin sallama ahankali, zumbur yamike
tsaye yana neman fadi Baba Sulaiman ya taroshi bakinshi har rawa yake yace "Cp kace
anganta, Bilkisu Bilkisun mudai?" kowa na dakin kallonshi yake tsabagen murna ma jefar da
wayan yahi ya tsugunna yay sujjada sanan yayo gadon baima bi takan Baba Sulaiman dake
tambayan shiba yay cupping fuskar Ayaan da idanunshi ke lumshe yana girgiza shi hawaye na
gangarowa daga idanunshi na farin ciki yace "Boy, Boy tashi muje police headquarter anga
Bilkisu Boy, anga matar ka" da kyar ya bude idanunshi dasuka kankance ya rike hannun Abba
da karfi yana kallon fuskar shi batare daya iya magana ba, gyadamai kai Abba yayi yace "yes,
yes my baby Boy, anga matar ka, i love u Boy so so much, oya get up let's go get ur wife" da
taimakon Abba da Baba yatashi har lokacin kallon Abba yake dan gani yake kaman zafin
zazzabi yasa yakejin Abba nakiran anga Bilkisu, ciremai robar oxygen din Abba yayi sanan
yacire mai drip din ya kalli Baba Sulaiman yace "ban rigan shi" clean white t-shirt ya mikomai
Abba ya dauramai akan singlet din jikinshi suka mikar dashi yay mugun haske lips dinshi jajir ga
rama saidai bai hana kyanshi fitowa ba, takalmin yasaka da kyar Abba da Baba suka fitar dashi
shikuma Baba Sulaiman ya shiga dakin da Mami take yace "anga Bilkisu kije gida kuyi girki dan
zamu dawo da bakin da suka kawota, kibar kuka Boy ya warke haha" yay dariya kafin ma Mami
ta jefamai wata tambaya haryabi bayan su Abba da gudu duk suka shiga mota sai headquarter.

Tun kafin suyi parking suka hango Cp yana washe musu baki dan kasa hakura yayi ya zauna
aciki so kawai yake dashi Alhaji ma zasu fara haduwa, fito da Ayaan sukayi dake bude ido da
kyar Cp yakara so wajen yana kallon Ayaan dake kallonshi da idanunshi dasuka kankance yace

"ciwo ya kare, muje Alhaji suna office dina" yana gaba suna biye dashi abaya har upstairs Cp
ne yabude office din ya shiga suna biye dashi, daidai lokacin Bilkisu ta daura hanunta akan
kafadar Aaman tanason ta leka meyake nunama Dr Ameenu awayan shi dayan hanunta kuma
rike da pringles takai baki tana gutsura. Dukansu binta sukai da kallo harda Ayaan daya kara
bude ido da kyau yana kallonta tundaga yatsar kafarta har zuwa kanta, dago dakai sukayi jin
anbude kofa da sauri Aaman ya ture hanunta daga kafadar shi suka mimmike tsaye shida Dr
dan daga ganin su sun gane family tane sabida manyan kayan dasuka sa, hannu suka mika ma
su Abba daduk Bilkisu suke kallo barinma Ayaan dako kyafta ido bayayi, itakuma tana zaune
tanacin pringles dinta batare datama kallesu ba, ga teddy ta agefe, ajiye pringles dinta tayi
tadau bottle wata dinta ta mike tsaye ta kusa da Aaman kaman zata shiga jikinshi ta mikamai
ruwan kaman zatai kuka tace "sweetheart budemini" wani irin mugun tari da Ayaan yafara yasa
ta juyo dakai tana kallonsu barinma mai tarin da manyan mutanen ke kokarin rikeshi ganin yana
neman shidewa, da sauri ta boye abayan Aaman tasa hannu ta dafashi ta leko dakai tana kallon
mutanen dai dai, hada ido suk sakeyi da me tarin da idanunshi sukai jajir yana tari yana kallonta
jijiyoyin kanshi duk sun fito shikuma Aaman sai kokarin tureta yake daga bayan shi amma taki
saima kara rirrike mai riga datayi tabaya tana make kafada tana "oh'oh" shikuma yacigaba da
tureta, wani irin kallo Ayaan yama Aaman kirjinshi na wani irin zafi kaman an juye garwashin
wuta daidai lokacin wani dan Sanda ya shigo dakin hanunshi rike da kulki, fizge jikinshi Ayaan
yayi daga hannun Abba da duka karfin dayazo mai, yatako ya fizge kulkin hanun dan sandan
daya shigo azuciye yay kan Aaman.
♦♦ *SANGARTATTCE* ♦♦



Maman Abd Shakur

67 - 68

Da sauri Cp da dan sanan daya fizge Mullin daga hanunshi harda Baba Sulaiman suka rike
gam gam, Baba Sulaiman yace "Ayaan are u okay" kokarin watsa dasu yake yana ma Aaman
wani irin kallo shima Aaman kallon shi yake irin kallon wanne wanan Kuma, Abba ne ya karbe
kulkin daga hanun nashi ya zaunar dashi da kyar ya zauna akan kujeran amma gabaki daya
baida natsuwa ahankali Abba ke tofamai addu'a Cp kuma ya kalli su Aaman da har lokacin suke
tsaye ga Bilkisu dahar lokacin ke tsaye abayan shi ta rike mai riga yace "ku zauna" Baba dai har
lokacin yakasa daina kallon Bilkisu mamakin yanda tarike wani namiji agabanshi ko kunyar shi
da tsoron shi ma da bataji ba shiya hanashi magana, he's totally shock, dauko file dinta dake
kan table Cp yayi yazo har gaban Abba dake gayama Ayaan da kanshi ke kasa yana wani irin
numfarfashi magana a kunne ya mikama Abba file din yace "gashi Alhaji medical record dinta
ne, sanadi yar faduwar nan datayi tasami tabin kwakwalwa banda haka tasami memory loss" da
sauri Ayaan yadago kai da jajayen idanunshi ya kalli Cp da sauri ya karbi record din ya bude file
din yana duddubawa yana karanatawa hanunshi har rawa yake saida yagama karance wa tass
sanan yadago kai ya kalleta tana kusa kusa da Aaman kaman zata shige jikinshi tadau teddy
tanata jijjigata tana wasa, wani irin zafi dayaji zuciyarshi nayi yasa yaji wasu irin zafafan hawaye

naso su xubomai, Abba daya gama karantan dan nashi tsaf ya mike tsaye murmushi kwance
akan fuskarshi ya karasa gaban su Aaman ya mika musu hannu yace "mungode, mungode,
ubangiji Allah ya biyaku, dan Allah karku cemin a'a kuzo muje gida munsa muku girki dan Allah
ya'yana karkuce bazakuba" yay maganan yana kallon su harda Dr, sosai nauyin Abba ya
kamasu hakan yasa yace "to Abba" Cp ya mikama police din daya shigo plain sheet da pen ya
kalli Aaman yace "zaka iya suffan tamana samari biyar dasuka fito da ita daga bakin motar" dan
shiru yayi saikuma yace "yea" nan ya dinga siffanta su police din na zanasu saiko ga sketch din
fuskar su Abba ya karba yana kallo babu wanda ya gane cikin su daga nan Abba yace sutafi,
mikewa yayi da sauri tamike itama tana kokarin rikoshi Baba ya daka mata wani irin tsawa.
"Bilkisu kewai mehaka" dago kai tayi ta kalli Baba saikuma ta murguda baki tana bobboyewa
abayan Aaman tace "ni sunana Ameerah ko sweetheart" baya Ayaan yayi zai fadi sabida wani
irin jiri dayake dibanshi da sauri Abba ya rikeshi ya kalli Baba yace "kasan bata hayyacin ta
karka ga laifin ta" ya kalli Aaman dake faman tureta daga bayanshi yace "kumu tafi yan albarka"
murmushi yayi yace "to Abba" su Abba suka rike Ayaan suka fita dashi. Da sauri Aaman ya juyo
ranshi ya mugun baci yace "d next time dakika rikeni ko shigewa jikinta saina mareki naughty
girl" yay gaba da sauri tsabagen haushi, Dr ya kalleta yanda take goge kwalla ahankali yace
"muje" murguda mai baki tayi tana goge kwalla tabi bayan shi suka fita daga office din. Suna
kaiwa waje Aaman ya nuna mata motan su Abba yace "jeki shiga motan su Abba" kallon su
Abba tayi yanda duk suka tsatsaya suna kallonta barin ma Ayaan kaman zai hadiye ta, ta
murguda musu baki tace "oh'oh ni namu zamu shiga" murmushi Abba yayi yace "bakomi
kabarta anan muje" da sauri tabude baya ta shiga sukuma suka shiga gaba Abba ya kalli Ayaan
yanda yake kallon su ahankali yace "Boy control your heart kar zuciyan ka ta buga haba dan
Allah zaka halaka kanka ne jibi yanda kirjinka ke bugu, let's go" bude mota yayi ya saka shi ciki
sanan ya shiga shima driver yajasu sukabar wajen motar su Aaman biye da ita har gidansu
sukai horn security yabude, sukai parking suka fiffito tana makale kusa da Aaman har suka je
part din Mami dayake Big Mummy taje bikin yar kawarta sai Kalle Kallen gidan take tana washe
baki tana kallon fuskar Aaman murya chan tace "sweetheart nanne garin namu" ko kallonta
baiyiba, babban falon Mami Abba yamusu iso suka zazzauna tana kusa da Aaman, ahankali
Mami ke saukowa daga sama cikin shiga ta alfarma idanunta akan Bilkisu dake zaune kusa da
wani tana wasa ta teddy Ayaan sai kallonta yake kaman ya hadiye ta, su Abba ma duk ita suke
kallo har gabanta Mami tazo zata rungumeta da sauri ta matsa kusa da Aaman tana make
kafada hakan yasa Mami tace "Bilkisu" murguda baki tayi tace "Ameerah sunana" tai maganan
kaman zatai kuka, kasa magana Mami tayi ta tsaya tana kallonta Abba ne yay jarumtar cewa.
"batada lafiya ne Firdausi, je akawo musu abinci" tadade tana kallon Bilkisu gaisuwar dasu
Aaman kemata ne yasa ta farka ta amsa musu tana murmushi kafin ta juya tai kitchen nan
tasaka yan aiki suka wadata su da abinci da abubuwan sha amma sun kasa ci sabida kunya
drinks kawai suka sha shidai Ayaan jingina yay da kujera ya lumshe ido kaman mai bacci amma
Bilkisu yake kallo bakaramin daurewa yayiba danji yake kaman ya kashe wanan mutumin
datake ta manne mawa, Abba ne yay gyaran murya yace "godiya zan kara muku yarana yanda
kuka taimaka mana kuka taimaki yarmu kuka sakamu acikin farin ciki ubangiji Allah ya faran ta
muku haka ranan gobe kiyama" ya nuna malam yace "wanan shine mahaifin Bilkisu, ga
Sulaimanu shikuma kanina ne, nikuma nine mahaifin mijin Bilkisu" wani irin bugawa kirjin
Aaman yayi kafin ya farka daga hakan Abba yanuna Ayaan dake kusa dashi yace "gakuma

mijin ta nan" saiya nuna Mami dake zaune gefen Baba Sulaiman yace "ga mahaifiyar shi chan"
innalillahi wa innalillahi raji'un kawai Aaman ke ambata aranshi, da hikima batare dawani ya lura
ba yakara matsawa daga kusa da ita yanda ta shige mai, wani irin zafi zuciyarshi keyi wasu irin
hawaye masu dumi ne suka taru a idonshi ya saci kallon Dr da shiyake kallo shima, ahankali ya
girgiza mai kai hakan yasa ya hadiye hawayen da kyar ya kakalo murmushi yadan kalli Ayaan
aranshi yace no wonder dazu yayo kanshi baikawo komi dazu ba dan yazaci hala mutumin ya
dauka sune suka saceta saisa yay haka ashe shine mijinta, ashe Ameerah matar aure ce,
maganar Bilkisu ce yasa yadawo daga dogon zancen zucin dayake ta matso kusa dashi sosai
tana nunamai pin din gyalen da Ummy tasaka mata takama rolling gyalen dashi ashagwbe tace
"Sweetheart remove it for m..." bata karashe maganan ba sabida wani irin mugun tari daya
turnike Ayaan akaro nabiyu da sauri Abba ya dau goran ruwa ya bude yabashi ture ruwan yayi
azuciye yanaso ya mike tsaye Abba ya take kafarshi yasan halin danshi koba komi shiya
taimaketa kuma Bilkisu bata hayyacin ta. "sweetheart plz cire" takara matso da kanta tanaso
tamai kuka da sauri ya mike tsaye ya kalli su Abba yana kakalo murmushin dole yace "zamu
koma yanzu karmuyi dare" kafin Abba dasu Baba da Mami dasuka Mike tsaye suma suyi
magana Bilkisu tace "yeee zamu tafi, uhnn sweetheart fitsari nakeji jirani nayi" saikuma takara
matsowa kusa dashi tace "where is d restroom" da kyar ya tattaro kalaman dake bakinshi dayay
nauyi sosai ya nuna mata Mami yace "ga Mum nan je ta kaiki kiyi" kallon fuskarshi tayi jin yanda
yay magana saikuma ta washe mai baki tace "okay wait for me" ta sakamai teddy ta ahannu
tace "hold my teddy" da sauri tai wurin Mami dake kallonta ta washe mata baki tace "Mum muje"
hanunta Mami takama suka hau stairs sai juyowa take tana kallon Aaman tana washe baki har
sukai sama da kyar ya kakalo murmushi yace "mutafi Abba kafin tafito" rakasu su Abba sukayi
har waje suka karbi number su shidai Ayaan yana zaune falo suna fita ya mike da kyar yay
upstairs yay dakin Mami yabude kofa ya shiga Mami ce kadai adakin zaune tana jiranta tana
ganinshi ta mike tsaye tai murmushi tace "bari naje nahado mata abinci bataci komiba" tafita
daga dakin, kimono ta da gyalen ta dake kan gadon yabi da kallo ahankali ya zauna akan
gadon yadau kimono ya rungume sosai yana shakan kamshin dasuke fitarwa, karan bude kofar
bathroom dayaji yasa ya zame rigan daya fuskarshi bama ta lura dashi ba tafito tana kokarin jan
straight skirt dinta data tattare ta barshi a cinya zuwa kasa, tundaga kai yake kallonta har yatsa,
kallon black body hug din da tasa yayi ba karamin kyau yamata ba gashi ya kamata yabi jikinta
hakan saiya kara bayyana cikan kirjinta dago dakai tayi bayan tagama jan skirt din yakai kasa ta
kalleshi bata damu da ganinshi ba amma ganin rigan ta da gyalen ta a hanunshi yasa ta daure
fuska a tsiwace ta rike kugu tana hararan shi, dan lumshe ido yayi yakara budesu ya sauke
akan fuskar ta, cike da masifa tayo cikin dakin agaban shi ta tsaya ta murguda mai baki ta
mikamai hannu tace "bani rigana aiba naka bane, sweetheart yasaimin" wani irin fizgota dayayi
saida tafado jikinshi, gyara mata zama yayi ajikinshi tana mutsu mutsun ta sauka ya sakala
hanunshi ta bayanta ya riketa gam yana numfashi da sauri da sauri yana kallon kwayar idonta,
murguda mai baki take iya karfin ta tana kokarin kwace kanta ganin takasa yasa tace "leave
me" tai maganan tana kokarin kwace kanta, ganin yaki sakinta sai wani irin kallo dayake yasa ta
daddage takai bakinta saitin kafadar shi ta daddage ta sakinmai cizo mai shegen zafi da kanta
tasaki fatar tashi ta dago kai tana kallon fuskarshi ganin ko gezau baiyiba ita yake kallon har
lokacin idanunshi sunyi jajir, ahankali yadaura kanshi akan kirjinta wlh takusa suma ya kankame
ta sosai muryan shi nawani irin rawa yace "am sorry wife, am sorry, I've done alot of things to

you, please kiyafe min am sorr..." yakasa karashe maganan sai kuka, cusa kanshi yayi a kirjinta
sosai yafashe da kuka irin wanda daga shi sai ita zasu dinga jin karan, duk hankalin ta yatashi
me haka wanan mutumin yakeyi yawani daura kanshi akan nonon ta yana kuka, jikinta nema
yafara rawa tasa hannu tana ture kanshi tace "leave me, let go off me" dago jajayen idanunshi
yayi ya kalleta dasu, kara ware ido tayi ta bude baki tana kallonshi cike da mamaki hawayen
data gani, ahankali takai karama yatsar ta ta dangwalo hawayen dake gangarawa kuncinshi ta
kalla hawaye ne da gaske ware ido tayi tace "laaaa dama babba na kuka, nidai ka sakeni kai, I
want to go, mehaka mtsww" tai tsaki tana ballamai harara, wani irin kuka dayaji yasake zuwan
mai yasa yasake maida kanshi jikinta ya rungumota sosai kaman zai maidata ciki yace "am
sorr..." sosai yafashe da kuka yakasa magana, shi kadai yasan yanda yakeji aranshi. Tureshi ta
shiga yi dukta rude tafashe da kuka sosai ta kwala ihu. "wayyo Allah na Sweetheart come" dago
rinannun idanunshi yayi yasa hannu ya buge bakinta, kama bakinta tayi tafashe da kuka sosai
tana kokarin tashi daga jikinshi, hanunta yakama ya daura akan kirjinshi dudda kukan datake
saida yanda taji kirjinshi na wani irin bugu ya bata tsoro, rungume ta yayi sosai yakai bakinshi
saitin kunenta da muryan shi da bata fita sosai yace "please wife karki kara kiranshi sweetheart
wlh zan iya mutuwa yanda zuciyata ke zafi" tureshi tayi da karfi cikin kuka ta make mai kafada
tareda lankwashe kai tana hararan shi tace "saina kirashi din, Sweetheart dinane kuma kabani
rigana naje wurin sweetheart mutafi gidan mu" wani irin tari yafara yana dafe kirjinshi yana
kallonta, zaro ido tayi atsorace tana kallonshi yanda yake tari, sadaf sadaf ta tako tazo gabanshi
zata zari rigarta dake kan jikinshi ya rike mata hannu ya fizgota dawani irin karfi yana tarin
yafada kan gado kaman zai mutu yakeji ya matseta sosai ajikinshi bama ya iya bude ido da
kyau,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login