Follow us on social media

Showing 12001 words to 15000 words out of 124573 words

Chapter 5 - Sangartacce Book Complete Complete Hausa Novel by M Shakur

M Shakur   

09 Nov 2025

5067

kafin yakara sa bude ido gabaki daya yana karema wurin kallo daya cika da hasken rana,
bin gabaki daya wajen yay da kallo kafin ya sauke idonshi a inda kanshi yake da sauri ya janye
kanshi daga kan kirjin wata faran kakkywan yarinya dayaga ta takure abango gawasu busassun
hawaye dasukai layi layi a fuskarta, da sauri ya mike tsaye ganin ajikinta yake yabi gabaki
dayan wurin da kallo yana kare hancin shi sabida wani irin wari dayaji wurin nayi, yana komawa
da baya da baya, champal dayaji akafan shi yasa ya kalli kafar da sauri yaga kafarshi cikin amai
yasa yay wani irin ihu "Fuck! Wah! Ewww" yawani yatsine fuska, afirgice ta bude ido jin ihu tabi
wurin da kallo kafin ta sauke kanta akan mahaukacin dataga sai kallon kanshi yake yana mikar
da hanunshi sama yana kallon hanun nashi dama duka jikinshi gabaki daya, kokarin tashi tayi
amma takasa sabida yanda kafarta yay mugun tsami dan kafarta alankwashe suke daya
kankameta jiya, kiciniyar tashi datake yi takasa yasa yajuyo kai ya zuba mata idanun dayasa taji
kirjinta yabada wani irin duma dum! Zuwa wajen yay azuciye yawani irin fizgota har saida tai
kara sabida yanda kafarta yay kara tace "wayyo Allah kafata" kawad da kanshi yayi tareda saka
hannu daya yana kare hanci saikace kashine yazo gabanshi, dan matsawa yay nesa da ita

yana kakkare hanci tareda mata wani irin banzar kallo dayasa taji kaman zatai fitsari, nuna ta
yay daga sama har kasa da yatsa yace "who d f*ck are u?".
[7/15, 12:18 PM] Ummi Tandama: ♦♦ *SANGARTATTCE*♦♦


Maman Abd Shakur

11 - 12

Kasa bashi amsa tai ganin maganin Baba yay aiki gashi yaji sauki, bayan hannu tasa to goge
hawayen dasuka zubo ta juya ahankali tana dingisawa batare data sake kallonshi ba ta
tsugunna da kyar sabida kafarta tadau hijabin ta dake kan carpet tasaka tai hanyar fita daga
dakin, wani irin fizgota taji anyi arude tajuyo baiyi watawata ba ya dauke ta da mari mai kyau
hakan yasa tafasa wani irin uban ihu ta dafe kuncinta tana wani irin kuka, nuna kanshi yay da
yatsa yana kallon fuskarta cikin husky voice dinshi yace "ke kinsan wayeni ina miki magana and
u dare walk out of me, F*ck!" yawani dunkule hannu ya daki iska, Muji da tuntuni yake tsaye
abakin kofa ya shigo da sauri yazo wajen dan tun jiya da daddare ake nemanta agida, hankalin
kowa yatashi, dazu dasafe ma su Umma sukazo duba ko agidansu ta kwana, kotadawo da latti
tsoro yasa ta kwana amma batanan hankalin Baaba duk yabi yatashi, yanajin haka yadau keke
yafito batare da kowa yaganshi ba hakanan zuciyar shi yace yazo yadubata anan. Karasa
shigowa yay yabita da kallo yanda take kuka sosai ga hanunta akan kuncinta da sauri Muji ya
kama hanun ya cire daga kan kuncinta ya kalla yanda wajen yay ja duk shatin hanunshi sunfito,
fadawa kan Muji tayi tana sheshekan kuka da kyar ta iya cewa "mutafi Ya Muji yariga ya warke"
Cireta Muji yay daga jikinshi ya kalli Mahaukacin dasu yake kallo, azuciye Muji yace "uban me
kanwata tama ka mare ta haka eh adam, butulu kawai, kasan irin dawainiyar datai dakaine
mahauka..." da sauri tarufe mai baki tana kuka tace "dan Allah nidai mutafi gida, yaji sauki
shikenan ai" ture ta Muji yayi hartana neman faduwa cike da masifa yace "wlh karki bari na
daura miki wani marin nima, tun dazu na tsaya anan ina ganin abunda yamiki uban wayeshi
dazai mareki haka? aida kinbarshi anan yacigaba dacin abincin bola banza dakiki mai dukan
mata" cakumo shi yayi azuciye da idanunshi dasukai mugun ja ya shake Muji sosai, Muji yafara
tari abunku daba karfi daya ba, tashi tayi daga tsugunen datake tana kuka tafara dukan
kakkarfan hannunshi da karfi tana kuka. "ka sakeshi, ka saken min wana, wlh ka sakeshi, zaka
kashe shi" cire hanunshi daya yay daga kwalar rigar Muji yasa hannun ya hankadeta tafadi
kasa, wani irin mukurkusu tayi sabida ciwon ta daya kama mata tafasa ihu sosai. "wayyo Allah
na cikina, Ya Muji zan mutu, zan mutu wayyo" juyo da kai yay ya kalli Muji da tsabagen wuya
idanunshi sunyi ja sosai, jijiyoyin kanshi sun fiffito yace "duk randa ka kara haduwa dani watch
ur tongue and know how u speak to me, bana tolerating raini one single bit get it?" ya tambaye
shi fuskarshi a mugun daure dan ranshi yay tsananin baci, gyadamai kai Muji yayi ahankali dan
ya shaku wlh, hakan yasa ya sake shi yana kai hanun hancin shi yana tsaki, da sauri Muji yay
kanta ganin yanda take kuka kaman zata mutu, dagota yay da karfi tareda saka hanunta daya
ta bayan wuyan shi ya taimaka mata ta mike tsaye da kyar, fasa ihu tasake yi zata koma kasa.
"Ya Muji bazan iya tashi ba, cikina, Wayyo Allah na jama'a, wayyo na shiga uku na lalace ku
taimakeni" ta rirrike shi, Muji dayake ji da bakin cikinta dan ita tajamai wanan muguwan shakan

gakuma tausayin ganin yanda dukta rikice, ahankali yace "toyi tafiya ahankali muje waje mu
shiga napep muje gida" girgiza mai kai tayi tafashe da kuka sosai tace "ni kadauke ni idan nai
tafiya barkewa ciwon zaiyi ayanda nakejin yakemini" kwalalo ido Muji yay ya harareta yace "to
ta ina zan iya daukan ki wai Balkisu, kinga wlh ko kiyi tafiya konabarki anan baruwa na
narantse" kara maida hanun nata bayan wuyanshi yayi tana kuka, ya jata da karfi dayaji kaman
zasu fadi dan kin tafiya tayi sabida ciwon dake mata sosai, yafita da ita daga ginin ya sakata a
keken yana hararan ta yace "ai Allah yakara uwar taimakon cikin ma yafashe banziya kawai" ya
watsa mata mugun hararan jiyake kaman ya gwabje ta, ya shiga gaba azuciye danhar yana
buge kai, harya kunna keken yakasa hakura ganin yanda take kuka daga gani bakaramin buge
ciwon tayiba gakuma wuyan shi daya rikemai dan har yanzu bai dena zafiba. Wlh bazan yarda
ba" fita yay daga keken yay hanyar ginin daidai shima mahaukacin yana fitowa sai wani
kyankyani kyankyani yake yana kallon kuturun takalmin kafarshi injishi, ganin bolan wajen yasa
yay turus ya tsaya yana tunanin yanda zaibi ya wuce, ganin Muji yadawo yasa ya zubamai
mayun idanunshi masu kama dana mage, dan komawa baya kadan Muji yayi dan yaune rana
tafarko dayaji mahaukacin nan ya mugun cikamai ido, sanan ya kallai yace "wlh Allah ya isa
bamu yafema ba dukan mu dakayi, kaga yarinyar chan daka tado mata da ciwo" ya nuna Bilkisu
dake cikin keke ta cusa kanta a cinya tana kuka yace "da kana mahaukacin ka, duk uban dattin
dakayi bata kyamace kaba ta kula dakai, ta gyara inda kake zama, tasaka ledar dakake kwana
dinchan aciki wanda tundaga gida ta dauko, kullu yaumin saita debo abinci daga gida takawo
ma kaci sabida dukan ka ake idan kasatoma yan shaguna buredi, tafasa asusun ta tasiyo ma
wanan takalmin dake kafarka sabida yankewa dakayi akafa sabida rashin takalmi, tasaima
wanan rigar jikin naka dan na jikin ka yagama yawo, sanan ta karboma addu'a wajen Baban ta,
tabaka kasha ka warke shine ka zanemu ko, to Allah ya isanmana wlh, da marinta da shakeni
dakuma fama mata ciwon ta bamu yafeba" yana fadin haka yajuya da gudun bala'i ya shige
keken dayariga ya kunna yabar wajen dan gani yay kaman zai biyosu.


Wani irin dogon tsaki yaja kafin yakara kallon bolan yana rufe hanci yafi minti uku ahaka yana
tunanin yanda zai tsallaka da kyar yabi bolan tareda runtse ido "jeez, i hate dis sh*t" saida ya
tsallake sanan ya bude ido tareda sauke ajiyar zuciya yana tofar ya yawu, kallon dogon layin
yayi yana tunanin yanda zai iya tafiya akafa ya shanye layin, sanan ya kalli kayan jikinshi, sake
runtse ido yayi tareda shafo kanshi da duka hannu biyu, abinda yatuna na karshe shine yana
garden yanacin white rice da pepper soup. Ajiyar zuciya yakara saukewa mai sauti kafin yafara
tafiya ahankali dan gabaki daya jinshi yake very very weak ko rabin layin bai shanye ba ya
zauna akan wani dakali yana mayar da numfashi, cije lips dinshi yayi kafin ya dunkule hannu
yadaki iska. "f*uck wats all dis sh*t?" tunda yake baitaba dogon tafiya akasa hakaba, maganan
yaran dayaji agabanshi yan kananu haka suna leken fuskar shi yasa yabude ido ya kallesu,
sunata mai dariya suna waka "waye barawon buredi?" sauran suna amshi "mahaukacin nan
shine barawon buredin shagon malam liti mai shayi" saisuyi dariya suna mai gwalo, binsu yay
da kallo kafin ahankali ya yunkura zai tashi aiko suka kwasa a guje suna ihu "wayyo
mahaukacin yabiyomu Maman mu" bai sake kallon suba yacigaba da tafiya aiko yaran suka
cigaba da binshi sunamai wakan mahaukata, ahaka haryakai bakin titi yarasa inda xaisa kanshi
baimasan wani gari ne nanba saida garin bai mishi kama da kano ba, haka yadinga tafiya yana

tare abin hawa babu wanda ya kulashi, yafi awa biyu dan harya fidda rai saiga wani dan xpress
ya tsaya daga ganinshi kasan dan wiwi ne yace "kai yane mahaukaci lpy ka tsaya akan titi?
Kosai wani ya kwashe ka ya aikaka lahira?" wani irin kallo yama dan Xpress din hakan yasa mai
machine din yace "wayihuhu kai wlh kafadama aljanun kanka nafi karfinsu dasuke min wanga
kallo dama na tsaya ne nazaci ko wani abu kakeso dan naga tuntuni kake tsaye anan ashe duk
cikin haukan ne" burga machine dinshi yayi zaitafi, ganin shine only hope dinshi yace "tsaya"
authoritatively yay maganan, kallonshi dan acaban yayi yace "kace mene kai mahaukaci?" dan
shiru yay rasa maima zaice, shi baisama roko ba, bai iya neman taimako ba, jin karan ya kunna
machine zai wuce yasa yasake kallonshi yace "inane nan wurin?" "kaman ya inane nan wurin,
bakin titi mana?" dan lumshe ido yayi kafin yabude su ahankali yace "wani gari ne nan?" "zaria"
dan acaban ya bashi amsa atakaice yana fito "ya muje ne" yanama wani singnal dake tsallake
ko tafiya ne yaje sutafi, mayar da dubanshi yay kanshi, kai tsaye yace "ban aran wayan ka?"
karkato bakin glass daya saka a idonshi yayi ya kalleshi yace "wayyo ni iskokan kanshi na sona,
kai mahaukaci ni wayata na wajen chaji aida nabaka naga uban me mahaukaci na iya da waya"
runtse ido yayi jin maganganun shi gakuma zafin rana dake dafamai fata, gakuma gajiya,
atsanake ya bude idon ya saukesu akan mai machine din yace "zaka kaini kano chan GRA?"
yay maganan yana dafe kanshi sabida saramai dayayi, bin shi da kallo mai machine din yayi
yace "ka warke newai? Naga kanata min magana kaman mai hankali, nafa saba ganin ka dan
liti nacin ubanka idan kasato mai buredi, yanzu kai to da baka da kosisi mezaka bani idan zan
kaika Kanon?" tattaba aljihun shi yayi kafin ya shafa wuyanshi jin chain dinshi na nan yasa
yaciro da sauri ya mikama mai machine din yace "24 karat gold chain ne, made in Austria 🇦🇹,
worth millions, gashi ka rike ka kaini kano yanzu" hanunshi mai machine din har rawa yake ya
karba yana dubawa, gold ne har gold, ga chain din doguwa sosai irin ta maza dinan yan iska,
kasa rufe baki yayi ya kalleshi yace "hau, hau muje tasha inada aboki mai mota nasaka aciki mu
kaika" kiri kiri yakasa hawa machine din dan baitaba hawa machine arayuwan shiba tunda aka
haifeshi, ganin hakan yasa mai machine din yace "dafani saika ware kafarka kahau" dafashin
yayi kaman bayaso yana kallon rigar jikinshi da tsabagen datti tai annakiya sanan yay yanda
yace saida yakusa fadin da machine din da kyar mai machine din yay controlling ya gyara
zaman shi yace "kai kacika karfi" sanan yatada machine din yawani jaa machine din tareda yin
awizo ganin yana neman faduwa yasa ya dafa kafadar mai machine din yana yatsine fuska,
wani gareje suka je suka sauka mai machine din yay parking machine din suka karasa wajen
wani mota, cikin minti goma suka tada motar suka ce ya shigo ya shiga sai kano.
[7/15, 12:18 PM] Ummi Tandama: ♦♦ *SANGARTATTCE* ♦♦


Maman Abd Shakur

13 - 14

Daidai kofar gidansu Muji yay parking keken, lokacin duk daliban sun fita bara dan karfe goma
dama ake tashin su, Baba da Isyaka ne duk a tsaye a kofar gidan sunje dogon bauchi
makarantar su tsakanin jiya da yau yafi sau hudu nemanta, amma duk basu ganta ba, ganin
keken Muji ya paka ga Bilkisun sai rusa uban kuka take yasa Baba yay azamar zuwa wajen

daidai Muji yafito daga keken, anatse Baba ya kallai yace "a ina ka ganta Mujittapa?" kame
kame Muji yafara yama rasa wani karya zai shararo da sauri ya juya yafara kokarin fito da ita
yace "chan hanyar gidan kawarsu na ganta awani lungu asume Baba" "subhanallah" yafada
yana kokarin cirota daga keken da kyar suka fito da ita dan kasa tsayuwa tayi sabida cikin, da
taimakon Baba da Muji sukai cikin gida da ita, Isyaka yabisu hankali atashe dan bazai iya
daurewa ba ya shiga gidan ganin duka matayen tsaye a tsakar gidan ba lullubi yasa yajuya da
sauri yakoma zaure danba karamin kunyan su Mama yakeba.

"La'ilaha illallahu maiya sameta malam?" Baaba tai magana kafin ta kalli Mama dake gefenta
tace "dauko tabarma Amina a shinfideta akai" daki Mama takoma ta fito da tabarma ta shinfida
anan bakin kofa sabida nanne da inuwa, nan Baba da Muji suka kwantar da ita, da kyar ta
kwanta dan kafe musu tai a tsaye wai zafi, Baba zai juya yaje daki yadebo ruwan addu'an daya
mata ta kamo hanunshi gam tarike. "Baba, Baba to ina zaka wlh azaba yakemin yamafi na
ranan nan, dan Allah ka tsaya kusa dani kaji Baba" tafara daddaga dayar hanunta saman tana
neman ruko wani, dan haka take inhar tana rashin lpy to bata barin mutane tabuka komi duk
kakkama su zatayi ta rike muku hannu hakan nasata jin kaman ciwon ya ragu, hannun Baaba
takamo ta rike gam cikin kuka tace "Baaba kene ko rikeni to, dan Allah kema karki tafi" tasake
sakin wani ihun tareda damke hannayen nasu gam. "wayyo Allah na Mama, Mamaaa, Raiyana,
na shiga uku Umma, Umma Umma zo kibude min cikin yasha iska" jiki a sanyaye Umma ta
tsugunna ta nannade mata rigar makarantar zuwa sama aikuwa wajen yadan kumburo kaman
tahadiye karamin kwai a wurin, tagumi Mama tai ta zubama Baaba ido hakan yasa ahankali
Baba ta juyo ta kalli Malam dake gefenta ya tsugunna yana mata addu'a sanan ta kalli Muji
dake kallon yanda Bilkisu ke kuka tace "wuce katafi nema zataji sauki kaji dan arziki" fita yay
daga gidan jiki asake, Malam nagama tofa mata addu'an ya mike tsaye zai shiga daki hakan
yasa Baaba tabi bayanshi, sallama tai yabata izinin shiga, zama duk sukayi sanan tafara
koromai zance anatse. "Malam wata yar magana nakeson nama dama, bawai inaja da Allah
bane kokuma inaso nama shishigi ba, zancen ciwon Bilkisun ne dama, naga tun fa tana
shekara sha bakwai abinnan yafara fitomata dan karami kullum saidai aita mata addu'a aruwa
tasha ya lapa, gashi har yanzu tana sha takwas amma ana kan abu daya saima kara girma
yake, ni dama cha nayi ko za agwada na turawa ne mugani koya kagani malam?" shiru yayi
yanadan dogon tunani kafin yace "da yardan Allah haka za'ayi amma akwai wani maganin
gargajiya dazan karbo mata wajen wani abokina anjima inhar tasha babu chanji to zamuje
asibitin" murmushi jin dadi tayi ganin Allah ya dorata akanshi dan Maman Bilkisu tasha fama
dashi akai yarinyar asibiti yaki yarda hakan yasa tafito daga dakin rai fes ta sakan musu
murmushi tareda kallon Bilkisun dake baccin wahala har wani irin nishi takeyi abaccin.


*************************

*Kano*
Agaban wani Mansion yasa sukai parking, wanda girman gidan kadai yayi girman wani anguwa
fita yay daga motar, su dan acaban sai kallon gidan suke hakadai suka kunna mota sukabar
unguwar, tunkarar gate din yayi wanda securities sunfi biyar biyu agaban gate sauran kuma

suna tsattsaye akowani bangare na wajen duk shi suke kallo, hanyar gate yay zai shiga
securities din suka tareshi da fuskokin su da babu alamun wasa sukace "wakake nema agidan
nan?" wani irin kallo yamusu tareda rungume hanunshi akirji ya zuba musu mayun idanunshi,
dayan ne yafara cewa "innalillahi, kai sir ne, he is back" gabaki dayan su tsugunnawa sukai
suna bashi hakuri baiko sake kallonsu ba yatabe baki ya shige cikin gida. Bababan gidane dake
dauke da motoci kala kala, different part ne agidan har hudu, da sauri yay part din parents
dinshi yana kwalama baban shi kira. "Popsy, Popsy" Abba dake zaune a bedroom dinshi ga
karin ruwa a hanunshi wanda yakusa karewa ya kalli Mami dake zauna a gefenshi tana bashi
yankanken fruits abaki dayake ci da kyar dukya fita hayyacin shi, kaman daga sama sukaji
muryan shi. "Popsy" hakan yasa ya ware ido tareda dagama Mami hannu dan yaji ko gizo
kunenshi kemai jin muryan Ayaan, sake jin muryan shi yana "Popsy" yasa yamike ya cizge karin
ruwan daga hanunshi yafice daga dakin Mami na biye dashi itama.

Shigowa katafaren falon mai kama da aljannar duniya yayi, yan aikin dake sanye da uniform
suna kokarin gyara dining suka bishi da kallon waye wanan ammadai basuyi magana ba.
"Popsy, Popsy" yakara kwalama baban nashi kira, baki zai bude yakara kiranshi sai yay turus
yana kallon fuskar shi ta jikin uban show glass din dake falon da aka jera wasu hadaddun
verses aciki, madubi ne gabaki daya, yanda gashin kanshi suka wani mummurde kaman dada
ga gemushi busu busu da yanda fatar shi tai wani irin mugun baki ya tsaya kallo shi kanshi yana
mamakin shine haka, dan yama kasa gane shine. "Boy!" yaji Abba yakira shi da irin muryan
manya dinan wayanda suka kwana biyu aduniya da sauri ya juya yaga Abba akan stairs ya
tsaya tareda kama karfen stairs din dan baida karfin tsayawa complete ga Mami itama tsaye a
gefenshi duk sun kafeshi da ido.
"Pops" yafada kaman zaiyi kuka yay hanyar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login