Showing 63001 words to 66000 words out of 124573 words

Chapter 22 - Sangartacce Book Complete Pdf by Maman AbdulShakur.pdf

M Shakur   

09 Nov 2025

3894

murmushi gefen baki
yakara saita bakinshi saitin kunenta yace "open ur eyes ki kalli abinda ya wahalar dake haka, is
not me" sake kankame idonta tayi wasu sababin hawayen kaman famfo suna zubowa, lakatan
hancin ta yayi da murya chan kasa makoshi yace "lazy gurl" dan murmushi yayi kafin ya mika
hannu yadauko soft sponge din dayake wanka dashi yasaka a ruwan sanan yaciro batare daya
rabata da jikinshi ba yadaura abayanta yafara wanketa ya wanke bayan tass, sanan ya juyo da
ita yay relaxing bayanta ajikinshi yafara wanke ta tundaga cikinta dayazo wajen kirjinta sai kuma
ajiye sponge din yadan kalli fuskarta ganin har lokacin idanunta a kulle suke hawaye sai fita
suke ta gefe yasa yahau wasa da kayanshi, saida yaga gari yasoma haske yasa yay maza yay
nashi wankan yasa tai wankan tsaki shima yayi sanan ya nannado ta a bathrobe dinshi shikuma
ya dauro towel ya dauketa kaman jaririya yafito da ita daga bayin, shi da kanshi yaje dakinta ya
dauko wata yar figigiyar riga white kaman shimi da dogon hijabi sanan yadawo yasame ta tana
zaune inda ya ijiyeta abakin gado har lokacin kuka take, daure fuska yay tamau yace "ke stop
dat silly cry" shiru tayi tana goge kwallan ya zauna kusa da ita dagata yayi yana kallon fuskarta
ya daurata akan jikinshi yacire mata bathrobe din ya saka mata rigar daya dauko sanan yasaka
mata hijabin ya koma gaban wardrobe yasaka doguwar jallabiya ya shimfida musu dadduma
yazo hanunta ya kama ya mikar da ita tsaye yajata kafa ta daga tai tafiya da kyar tai maza
maza ta goge hawayen azaban dasuka zubo, daukarta yayi yadaura ta kan dadduma shiya jasu
sallan asuba bakaramin mamaki tayiba ganin yay salla daidai itadai a iya sanin ta ko mistake
daya bataga yayiba ashe yadan san wani abu a addini shine yake iskanci. Hijabin ya cire mata
ya dauketa ya kwantar da ita akan kujera, zanin gadon da bargon yakoma yacire ya je yasaka
su a washing machine sanan yadawo ya shimfida wani sabon zanin gadon da kyar yana nishi
dudda bawani yi da kyau yayi ba dawowa yay wurin kujeran yaga har wani wahalallen bacci yay
gaba da ita, ahankali ya dauketa ya kwantar da ita akan gadon yana tunanin yanda zaiyi ya
kaita gidansu ahaka yau, kwanciya yay gefenta ya rungumeta ahaka shima wani baccin yay
gaba dashi.
Wuraren daya na rana ringing din wayarshi ya farkar dasu da kyar yadau wayar yaduba yaga
Mami ce, ahankali yay picking anatse yace "Mami na" batare data amsa shiba tace "bakaga
daman kawomin itan bane kana sane jirgin karfe shidan yamma Baffan ka zaibi ko" ahankali
yace "zamuzo dan anjima kadan Mami damafa kafarta ke ciw..." da sauri Mami ta katse wayar.
*Wolla Ayaan baida kunya, anyways something is about to happen*.

[7/25, 9:18 PM] 0mmer Farouk: ♦♦ *SANGARTATTCE* ♦♦




Maman Abd Shakur

59 - 60

Ajiye wayar yayi ya juyo da kanshi yana kallonta idonta biyu saidai ta lumshe ido sabida yanda
ya rungumeta yasa takasa tashi, dan matso da kanshi daidai saitin fuskarta yayi ya huramata
iska a fuska hakan yasa takara kankame idanunta, hada forehead dinshi yay da nata yana goga
hancinshi akan nata dudda haka taki bude idon, murya chan ciki yace "hey open ur eyes" kin
bude idon tayi sai numfashin da take da sauri da sauri, kara daura hancinshi da kyau yay kan
nata yana shakan numfashin ta itama nashi na shiga nata, batare daya raba fuskar nasu ba ya
mikar da hannunshi yana lalubo nata, akan cinyarta yaji hannun nata hakan yasa ya rike ya
bude tafin hanun yana murza tsakiyan dake jike da zufa yana kallon fuskar ta ganin taki bude
ido yasa murya chan kasa yace "alright u asked for it" chakulkuli yamata da sauri ta bude ido
tana neman yin dariya amma ta daure ta hana kanta dariyar, fuskarta yabi da kallo kafin yatashi
daga gadon ya sunkuceta sukai bayi, nanma suka kara bata lokaci dan saida ya gasata sanan
sukai wanka bayan yay wasa da ita son ranshi, kafin su fito ya zaunar da ita abakin gado yana
goge jikinshi da towel sanan ya zauna agefenta yana kallon fuskar ta yanda idonta ke kasa
sanan ya kalli gashinta daya hargitse ahankali yace "jeki shirya mufita Mami na jiranmu" yay
maganan calmly, tashi tayi daga kan gadon ahankali tana tafiya kadan kadan sabida zafi tafita
daga dakin dan lumshe ido yayi kafin ya mike yay wajen wardrobe.

Tana shiga daki tafara share hawaye da kyar tai salla sanan tai parking hargitsassen gashinta
da ribbon, wani hadadden lace ta dauko royal blue tasaka an mata dinkin riga da skirt daya
mata chas chass ajiki ta zauna akan stool ahankali, tajawo hoda ta shafa ta rangada kwali a
idonta da har yanzu basu gama washewa ba tsabagen kuka, ta shafa lip gloss a lips dinta
dasuka sa lips dinta yay wani irin kyau pink din yafito sosai bakin ma haka abin saiyay kaman
tasaka janvaki, tai carving giranta da brush sanan ta tadau dan babban mayafinta black mai
shegen kyau tasaka takalmi medan tsini kadan black shima sanan tadau jakarta data saka
wayarta kadai aciki ta zauna abakin gado, ko minti daya batayi da zama ba shima ya shigo
sanye da royal blue shadda gizna sai kyalli take yamata dinkin half jumber yasanya black cover
shoes mai masifar kyau hakanan yau yaji yanajin saka manyan kaya bakaramin kyau yayiba ya
tsaya abakin kofa turus yana kallonta hanunshi rike da tea dayan hanun kuma tablet yarike,
dan murmushi yayi ganin yanda taketa wasa da bakin gyalen ta, ya shigo dakin yazo kusa da
ita ya zauna har jikinsu na gogan juna yana kallon fuskarta yabata tea ahankali yace "sha
mutafi" karba tayi hanunta na rawa takai baki tasha kadan tacire abaki, saida tasha kusan rabi
sanan ya saka mata maganin abaki ta hadiye sanan ta shanye sauran tea ya karbi cup din kafin
ya mikar da ita tsaye yana kallonta, hanunta yarike sanan yajata yanabinta ahankali suka fita
daga dakin da sukazo wajen stairs da kanshi ya dauketa sukai kasa bayan ya ijiye cup din a

kitchen yafito da ita ya kulle gidan har compound, saida ya bude bangaren ta yasaka ta ciki
sanan ya rufo ya zagaya ta dayan side dinshi ya shiga motar ya kunna suka fita daga gidan,
wakar celine dion na if walls could talk ke tashi a motar sai binta yake kaman shiya raira wakar
kana ganinshi kasan yana cikin nishadi haka sukakai har gaban babban gidansu horn yayi yana
rage karan music din sabida kiranshi da akai a waya, daukar Wayan yayi da hannu daya ya
kara a kunne yana tuki da hannu daya ya shiga cikin gidan nasu bayan anbude gate.

Tun kafin yay parking take kallon daya daga cikin securities din gidan data ganshi kusa da
flowers din gidan ya tsugunna ya rike wasu maguna masu kyau farare guda biyu, kana ganinsu
kasan yarane ba'a dade da haihuwar suba ya kafa kansu acikin wata yar karaman bowl suna
lasan madara daya dama musu, parking yayi a inda ake parking motoci ya kashe motar har
lokacin waya yakeyi wacce bamatajin abinda yake fadi sosai bata damuba tabude kofar motar
tayi ta sauka, ko rufe kofar batayi ba tana tafiya ahankali tana dan dingisawa ahakanma wai ta
saita tafiyan sosai tai wajen magunan yabita da kallo ta madubin mota, tsayawa tayi agaban
security dake basu madaran tana kallon fararen magen tana murmushi ahankali tace "naka ne?
Sunada kyau" security dasai a lokacin ya lura da ita dan hankalinshi yay nisa akan magunan
yace "barka da zuwa madam" ganin magen taketa kallo yasa yay murmushi ya shafa kan daya
daga cikinsu yace "kin gansu nan Mamar su itake tayani gadi duk randa nake duty shine fa last
week data haifesu ta mutu wlh banji dadi ba" kaman zatai kuka tace "to ka saka musu suna?"
girgiza mata kai yayi hankalin shi nakan wacce tadena shan madaran, da sauri tace "ka samusu
Sameer da Sameera tunda naga ai mace da namiji ne ko?" dago kai yayi yasake kallon fuskar
ta yana murmushi yace "eh" ganin yanda gabaki daya hankalin ta yana kan magunan yasa yace
"kozaki dauke sune" da sauri ta gyada mai kai tana murmushi ta mikomai hannu tace "dan Allah
kaban daya natafi da ita gida" daidai lokacin shima ya mikomata magen harta daura hannunta
tadaura akan magen gyalenta ya sauka daga kanta yakoma kafada sabida iskar dayakada
kawai karan saukan mari sukaji, Ayaan ya tallama security wani hadadden Mari wanda yasa shi
sakin magen arude da sauri ta rike magen karta fadi kasa ta karye jikinta na rawa ganin
tsantsan bala'i a idonshi, kama kwalan rigar shi Ayaan yayi yana jijjigashi "dan ubanka ubanwa
yabaka izinin magana da Matata eh" arude security kanshi akasa yace "sorry sir" tureshi Ayaan
yayi da karfin tsiya saida yakusa fadi ya nunashi da yatsa da tsanin bacin rai yace "u are fired
kabar gidan nan yanzun nan" security nabashi hakuri ko kallonshi baiyiba yajuyo ya kalleta da
jajayen idonshi, gabaki daya jikinta rawa yake, fizgota yayi da karfin bala'i yana maida gyalen da
sauri ta saki magen tai tsalle ta shige cikin flowers shikuma yay hanyar shashin Mami rike da
hanunta, arude tace "dan Allah kayakuri karka koreshi" wani irin mugun kallo yamata zuciyar shi
natafasa dan jiyake zai iya kashe koma waye yaga yana kallonta koyi mata murmushi (to fah,
mutumin naku wanan kishi haka).
Fashewa tai da kuka sosai ganin yanda yake kallonta kaman zai daketa, dunkule hanunshi yayi
ya daki jikin bangon daya jinginata akai kafin ya daka mata tsawa. "shut up and wipe those
tears" da sauri ta share hawayen tass sanan yarike mata hannu suna tafiya ahankali ya bude
kofar suka shiga ciki ganin kowa na falo zazzaune akasa anata hira, ana ganinsu kowa ya
washe baki yana kallonsu yasa tafara kokarin fizge hanunta sabida tsananin kunya da nauyin
su Abba datakeji shiko ko ajikinshi saima tafiya daya fara ahankali sabida ita sukai cikin dakin
itama tabishi ta daddage iya karfin ta ta saita tafiyar ta sabida kar agane, daidai wajen Mami

yasaki hanunta ganin wani irin kallo datake mai da sauri ta tsugunna ta wajen kafan Mami dake
kan kujera tana gaida kowa kanta akasa.
Sun jima afalon suna hira itadai tana kusa da Mami kanta akasa shiko yana jikin Abba sai
shagwaba yake zubawa, Abba na wani irin riritashi kaman kwai, akai akai yake satan kallonta.
Big Mummy ne ta tashi bayan wayarta yay ringing ta kalli Mami tace "Munari ta iso bari naje"
murmushi Mami tamata tace "tadan huta tukun anjima na shigo mu gaisa nima" to Big Mummy
tace tafice daga dakin sai Mami ta kalli Bilkisu datai shiru ita kadai ganin mazan duk sun natsu
kallon news suke yasa Mami tace "tashi muje sama daughter" ahankali ta mike Mami ta kama
hanunta da kanta dan tun shigowan su tagane komi sama sukayi yabisu da kallo asace.
Suna shiga dakin Mami tai kasa zata zauna hararan ta Mami tayi tace "kinga zamu batafa in
kinamin wanan kunyan niba maman ki bane?" gyada mata kai tayi tana dan murmushi gado
Mami ta nuna mata tace "to tashi daga kasa ki zauna akan gado" ahankali ta tashi ta zauna
Mami kuma tafita daga dakin tace "ina zuwa" Mama Jummai tabama kudi ta aikata wani wuri
cikin minti talatin saiga Mama Jummai tadawo da sakon karba Mami tayi takoma daki ta shiga
bayi tahada mata ruwan zafi sosai dawasu magunguna aciki sanan tafito ta kalleta ahankali
tace "daughter shiga bayi ki zauna a ruwan dana hada miki ina zuwa" Mami tafita daga dakin
dan tabata sarari, kaman zata nutse da kunya haka takeji mikewa tsaye tayi da kyar ta shiga
bayin kaman yanda Mami tace ta shiga ruwan bakaramin dadi tajiba ko, tadade aciki sanan
tafito daure da alwala ganin ankira la'asar tana fitowa tazo tayi, ta zauna akan gado daidai
lokacin Mami ta shigo ta mika mata wayarta tace "ga Baaba" cike da farin ciki ta karbi wayan
Mami tajuya tafita, sun dade suna magana da Baaba kafin Baaba ta mikama Raiyana dake
kusa da ita dukta dameta, da sauri Raiyana ta karba tai uwar dakan Baaba tace "Anty Baby
labari zan baki" dariya Bilkisu tayi sosai tace "ina jinki bani nasha" Raiyana cikin murna tace
"Anty Baby kinayin aure nafara samari daban daban amma duk cikin su nafison copper dake
koyarwa a school dinmu kuma yazo wajen Baba yace zaima jirani har nagama ss3 kafin nan
yagama service dinshi yasamu aiki, wlh Anty Baby ina sonshi" hanun mutum dataji akan cikinta
yasa ta daga kai a tsorace wani irin kallo yake mata hakan yasa takasa magana ta sauke idonta
kasa Raiyana tace "hello Anty Baby" zama yayi kan gadon ya dauketa yasata ajikinshi tareda
daura kanshi ta wajen wayan, Raiyana tace "hello Anty Baby kinji labarin kuwa" da kyar tace
"eh" kafin ahankali tace "ke kinji dadi ai kinsami wanda kikeso Baba kuma zai hadaki dashi, niko
saidai naji sabon zance ranan bikina" da sauri ta share hawayen daya zubo mata ahankali tace
"ki gaidamin da Mama da Umma" ta katse wayar da sauri tana wasa da yatsun ta kama hanunta
yayi yana kallon fuskar ta yace "ke" kin dago kai tayi hakan yasa ya daura fuskar shi akan nata
yana mata wani irin kallota yace "ke" bude kofar da akayi yasa yadago kai Mami ce ta shigo
dakin dauke da tray ahanunta na abinci da sauri ta tashi daga kan jikinshi shima ya mike tsaye
ya karbi tray yana kallon fuskar ta ahankali yace "sannu da aiki Mami na" nunamai Bilkisu tai
tace "abincin tane" sai a lokacin ma ya kalli plate din tuwo ne da miyan kuka dayasha namomi
tabe fuska yayi ya ijiye mata agaban ta, tana ganin abincin batasan lokacin data saki murmushi
ba daya lobar da dimple dinta numfashin shi yakusa ya tsaya, ta kalli Mami data bude wardrobe
kaman tana neman abu tace "nagode Mami na" yunkura wa tayi zata sakko kasa da sauri ya
riketa dauke kai tayi ya saukar da ita kasan, zama tayi akasan ahankali ya dauko tray ya ijiye
mata agabanta, shikuma ya kwanta akan gadon Mamin, wanke hanunta tayi da ruwan da Mami
tasako mata atray din sanan tafara ci har wani lumshe ido sabida dadi gashi harda man shanu a

kukan, juyowa Mami tayi ta kallesu kafin ta mayar da hankalin ta duka kan Ayaan dake kallonta
kaman zai cinyeta itako bama tasan yanayi ba, dan gyaran murya Mami tayi tace "bakai da
Abban ka zaku kai Baba Sulaiman airport bawai kazo ka kwanta anan?" dan sosa kai yayi
yamike tsaye yace "na manta ma" fita yayi yadan saci kallonta sai tuwonta takeci.
Bayan sallan isha suka dawo gidan shida Abba side din Big Mummy yayi shikuma Abba yawuce
bangaren shi dan adakin Mami yake yau, yadade a side din big Mummy l yana hira da big
Mummy da bakuwar ta Munari dataxo daga giada sanan yamusu sallama yafito yay part dinsu,
tana kwance kan gadon Mami sanye da doguwar rigan da Mami ta bata daidai jikinta na atampa
sai hira suke ita da Mami tuni ta saki jikinta tajita garau, da sallama ya shigo dakin yadan saci
kallonta kafin ya zauna agefen Mami yana mata murmushi yace "Mami na nadawo" murmushi
tamai tace "akawo ma abinci" girgiza kai yayi yace "naci a part din Big Mum" ya kalli Bilkisu
datun shigowan shi tai shiru kaman ba ita ke surutu ba yace "tashi mutafi" wani kallo Mami
tamai tace "kutafi ina? Tana nan babu inda zata zatamin kwana biyu tukun" duk wani walwala
da murmushin dake kan fuskarshi bacewa yayi kaman zaiyi kuka yace "Mamiii" gyada mai kai
tayi tace "am serious fa" tashi yayi yafita daga dakin azuciye tundaga bakin kofa yake kwalama
Abba kira. "Pops, Popsy, Pops" arude Abba yafito daga dakinshi shigewa jikin Abba yayi Abba
dukya rude ya dafashi jin yanda kirjinshi ke bugawa yace "menene Boy waya batama rai haka
heart dinka ke beating fast?" kaman zaiyi kuka yace "Mami ne wai bazan tafi da matata ba"
"tace hakan?" Abba yay tambayan ranshi abace, gyadamai kai yayi, Abba yay kwafa yace "je
mota ka jirata gatanan zuwa kutafi, ai kafin kai auren tafi kowa damun mutane yanzu kuma
dakayi zata dauke ma mata, tafi mota abinka gatanan zuwa" juyawa yayi ya sauka downstairs
rai fess yay waje abinshi, Abba ya bude dakin Mami ya shiga ko Mami bai kalla ba ya kalli
Bilkisu yace "yar arziki tashi kije mijinki na jiranki a mota kutafi gidan ku" dukar dakai tayi sabida
yanda takejin nauyin Abba ta sauko tadau hijabin ta da jakanta ta saka, Mami tace "Allah miki
albarka zan kiranki gobe kinji" gyada ma Mami kai tayi tana kokarin hadiye hawayen dakeson
zubowa wlh batason gidan, Abba dai juyawa yayi yafita da sauri tafada jikin Mami ta rungumeta
ahankali tace "Mami zakizo kiduba ni gobe?" dan dariya Mami tayi jin yarinyar take har ranta
kaman yar da ta haifa, hakan yasa ta gyada mata kai tace "eh oya tafi kinga goma saura" sakin
Mami tayi tafita daga dakin ahankali har tsakar gida yana tsaye a parking lot jingine da motar
shi hanunshi zube cikin aljihu tunda tafito yake kallonta harta karaso wurin motar batace mai
komiba ta tazo zata wuce ta gabanshi ta zaga ta dayan side din ta zauna ya kamo hanunta,
ahankali yajawo ta yasata ajikinshi ya rungumeta wani irin siririn kuka tasaka mai, ajiyar zuciya
yasauke sanan yadan duko dakai yakawo shi daidai saitin kunenta yace "kina son ki zauna da
Mami?" gyada mai kai tayi hakan yasa yasake sassauta murya yace "ok next time dazamu zo
saiki kwana, now stop crying" cirota yay daga jikinshi hannunshi daya abayanta yarike
kwankwason ta yasa dayan hanun yaciro handky daga aljihun shi mai taushi da kamshi ya
daura akan kuncinta ya share mata hawayen dayabi ya bata mata fuska yana kallon idonta
yanda tai kasa dasu taki bari su hada

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login