Showing 99001 words to 102000 words out of 124573 words

Chapter 34 - Sangartacce Book Complete Pdf by Maman AbdulShakur.pdf

M Shakur   

09 Nov 2025

3897

zauna yace "Ya kake ji dafatan zaka iya amsa
tambayoyi na" gyadamai kai Isya yayi Cp yace "good, meya faru fadamin" nan ya basu labarin
duka abinda yafaru yakara da "amma lokacin daya yankamini cinya dannace kana gidan Abba
cemin yayi karyane Hajiya tacemai kuna nan" da sauri Ayaan yamike tsaye yace "Hajiya kace?"
gyadamai kai yayi, hannu Ayaan ya daura akan kirjinshi dake wani irin bugawa da sauri CP ya
dafashi yace "lafiya kasan hajiyar ne? If u know anything tell us sabida mukai karshen case
dinan" wani irin dunkule hannu Ayaan yayi ya daki iska yace "f*ck" dafa kafadar shi da karfi CP
yayi yace "calm down, sit" zama yay da kyar CP yace "wacece hajiyar wakake suspecting?"
shafa kanshi yayi ya fuzar da iska yace "Big Mum, Hajiya Saratu, but my question is me Bilkisu
tamata why did she wanna kill her?" yana gama maganar ya mike tsaye da sauri yafara
maganan zuci "yes, ranan da aka dauke Bilkisu dudda he was talking to Dr Ibrahim awaya yaga
yanda Bilkisu tafito daga shashin Big Mum arude, and apart from that tanata damun shi amota
cewa zata fadamai wani magana har suka kai gida, suna kaiwa gida before he could listen to
wat she was trying to tell him big Mum takira wai batada lpy, yatafi, kafin yadawo babu Bilkisu
saidai jini a stairs, and ranan nan yakamata tana shirin kasheta could all dis be coincident? No"
dafashi da akayi yasa yadago jajayen idonshi ya kalli Cp, ahankali Cp yace "mesa step mum
dinka ce suspect dinka" "sabida itace" nan yabama CP labarin komi yagama da. "ita takirani jiya
tana tambayana muna inane nace mata muna gida because I don't trust her tun kamatan danayi
lokacin tana shirin kashe Bilkisu" girgiza kai CP yayi yace "mutafi gidan ku, dan from all this she
is a suspect so dole zamu mata tambayoyi ta amsa mu" ahankali Ayaan yace "nasa Mike yamin
fixing CCTV camera a Palo da falon sama ta tun randa takusa kashe min matata" Cp ya gyada
kai yace "good hakan zai taimaki aikin mu sosai, meanwhile zan kira once angama gyara
kafarsu achan headquarter amini interrogating dinsu muji wani information zamu samu a
wurinsu, muje" fita sukayi daga dakin bayan su bar police biyu tareda Isya motocin suka shiga
shikuma ya wuce tashi sukai gidansu


Ana kiran sallan asuba suka isa anguwan su horn sukayi securities suka bude parking sukayi
suka fiffito da saurin su sukai part din big Mum ga mamakin su abude sukaga kofar awangale

da sauri Ayaan yay sama dakinta ya bude babu kowa ciki sai uban kayan data zuba akan gado
ga wardrobe abude, da sauri yafita ya shiga sauran dakunan babu kowa, sakkowa yay da sauri
ya kalli Cp yace "batanan" da sauri CP yace "what" sa yaranshi yayi su dadduba ko'ina shikuma
Ayaan yay waje yana kwalama Mike kira da sauri Mike dake bacci yafito wasu keys yakarba
daga hanun Mike daidai lokacin CP sun fito Ayaan ya wurgamai key yace "ga key dakin da
computer CCTV suke ciki Mike kaisu, bari naduba Mami na" yay shashin Mamin shi da saurin
shi ga mamakin shi abude yaga itama kofar, ciki yay da gudu sai yaga yan aikin su guda biyu
azaune kan dining sunyi zugum wani irin tsawa ya daka musu yace "ina Mami na?" arude
sukace "sir hanayi yan su yatashe mu daga bacci ita da hajiya saratu kaman fada sukayi,
saikuma mukaga hajiya saratu ta taso Mom dinka agaba suka fita bamusan inda sukaje ba"
"innalillahi wa innalillahi raji'un, wai wat is happening ne, Big mum!" fita yayi da gudu yay dakin
Computers din yasame su suna a daidai inda Big Mum ta tura Mami cikin mota takafa mata
bindiga tabaya tayanda su kadaine sukasan da bindigar, innalillahi wa innalillahi raji'un kawai
Ayaan ke maimaita wa baima farga daga tashin hankalin ba wayarshi tai ringing kasama dauka
yayi saida CP yace yadauka sanan ya dauka, sunan Big Mum ne baro baro ya bayyana agaban
screen din hakan yasa ta kafe screen din da ido da sauri CP yace "waye ke kira itane?" gyada
kai yayi da sauri CP yace "dauka sa a speaker muji mezata ce" ahankali yay picking yasaka a
speaker tsabar bakin ciki yakasa magana ma, wani irin dariya big mum tayi tace "Ayaan, Ayaan,
yaro man kaza! Well nakira ne nafada maka abu biyu zuwa uku dan nasan karkiga kasan koni
waccece yanzu dan nasan yarana dakuka kama sun kira sunana" tai wani irin murmushi dasuke
iyajin sautin shi tace "inhar kanaso ka kara saka mahaifiyar ka a ido abu nafarko danake so kayi
shine duka kamfanin Alhaji da dukiyoyin shi daya maida sunanka kamaida su sunanan wato su
zama mallaki na, nabiyu inaso yarana dakuka kama dan nasan yanzu haka police natare dakai
asake min su, na uku wanda yake na karshe inhar kana son ka kara saka mahaifiyar ka da
mahaifin ka wanda yanzu haka yakusa isowa hannuna a id...." da sauri ya katse ta ta hanyar
cewa "Pops" yafada yana dafe kirji, murmushi tayi tace "kwarai kuwa Pops, pilot din Alhaji
hmmm" tai wani irin murmushi dazan kirashi dana keta, tace "pilot din Alhaji yanda kasan tip da
taya haka muke, shikemini komi dan baban ka karfi yakare kuma gani nikuma da kuzari ta" wani
irin runtse ido Ayaan yayi jijiyoyin kanshi na fitowa tace "mahaifin ka nakiranshi yace yazo suzo
sutafi nigeria akwai matsala yakirani, kafin yakirani Bala yariga yafada min halin da ake ciki,
yanzu haka ubanka na cikin jirgi baisan inda kanshi yakeba anmai wata alluran bacci" kara
danne kirji Ayaan yayi zaiyi magana CP ya girgiza mai kai, Big Mum tace "abu na uku inhar
kanaso ka kara ganin mahaifin ka da mahaifiyar ka shine zaka bani Bilkisu amadadin su" "wat!"
Ayaan yay wani irin ihu tareda dukan computer dake kan desk jikake kakakakak sun tarwatse,
da sauri CP ya girgiza mai kai, Big Mum tai wani irin dariya tace "daka natsu dayafi shinema
abu mafi alkairi, Bilkisu wato matar ka itace silar komi ya bacin mini haka har asirina yatonu,
dan haka dolene na kasheta ita tafara jiyo asiri na aranan na kiraka itakuma natura aka dauketa
akaje Bauchi aka yarda ita, saikawai gata tadawo saisa naso na kasheta ranan kafin tafadi komi
amma ka kamani, Ayaan ka ganni nan akan dukiya zan iya komi wlh, bazan iya hakura bane
uban dukiyar mahaifinka ka gaje komi ba, my initial plan was nakamo ka kamin signing komi
yadawo nawa saina kasheka kai kadai, bayan ka mutu kaga ai bakin cikin rashin ka shizai
halaka tsohon mahaifinka, uwarka kuma nabarta da ranta dan babu abinda zata iyamin, shine
fa makirar matar ka tabata mini komi, Ayaan!" ta kirashi dawani irin kakausar murya tace "inhar

kanason ka kara ganin Pops da Mami kamaida dukiya komi yadawo nawa, kasa asaki yaran
aikina, sanan ka bani matar ka Bilkisu itace dan silar komi, kasan mezan yi inhar baka bani
Bilkisu ba" tai wani irin murmushi mai kara kafin tai shiru tace "kadaisan nasan gidan su Bilkisu
ko, saina sa ankashemin kowa nagidan su, fara daga kan Malam, Mamar ta, kishiyar mamar ta,
kaninta mata biyu Raiyana da Layla, Baaba wacce tazo gidan mu da danta Muji, Ayaan! Rai
daya tal dinan danake nema wato Balkisu inhar baka bani ita ba saina kashe rai bakwai hada
da iyayen ka yakama rai Tara kenan, nabaka awa ashirin da hudu I lokacin ya cika zakaga kira"
ta katse wayar kit.

Jama'a yaya kenan?
In nine Ayaan hakanan zanbada Bilkisu akashe ta gaskiya koya kukace?
♦♦ *SANGARTATTCE* ♦♦




Maman Abd Shakur

85...

Dafe zuciya Ayaan yayi yana wani irin nishi, kirjinshi na zafi sosai yama rasa ina zaisaka kanshi
yaji dadi, kanshi kaman anzubai wuta, da sauri Mike yafita ya dauko mai cold water, CP ne ya
karba ya bude ya samai abaki da kyar ya kurbi kadan ya saukar dawasu tagwayen ajiyar zuciya
kafin ahankali ya dago jajayen idanunshi ya kalli inspector yace "inaso kayi contacting
headquarter police din zaria azuba jami'an tsaro a anguwar su Bilkisu gabaki daya right now
please" yanda yakara she maganan yasa CP yace "calm down" ya kalli babban inspector dake
tareda shi yace "kira officer saminu na zaria ka sanar dashi, Ayaan bamu address din gidan"
ahankali Ayaan yabasu address din shikuma CP yadau waya yakira headquarter dan atura
police suje Amina kano international Airport tayanda bazasuci sa'an ficewa da Abba daga
airport dinba bayan sun iso, sanan ya kalli Ayaan dake dafe da zuciyar shi yace "tashi muje
masallaci daganan muwuce headquarter dan ayi tracking phone number ta" da kyar ya tashi
suka fita daga dakin yana ganin jiri jiri.
Saida sukai salla sanan suka wuce police headquarter number wani police yazo ya karba ana
kokarin tracking shikuma yabi bayan CP zuwa dakin da ake interrogating yaran Big mum din,
CP ya shiga dakin shikuma ya tsaya ta gaban glass din waje yana kallon yanda ake questioning
dinsu, Sosai suke kuka tsabagen azaba daya daga cikin su yace "wlh, wlh, mu bamusan hajiyar
ba ogan mune yasan hajiyan, ogan mu Bala" da sauri Ayaan yakara gyara tsayuwa yana
kallonsu yana maimaita sunan Bala aranshi, "Bala, Bala a ina ma yataba jin ko ganin sunan
nan?" hanunshi ya goya abaya yafara zagaye wajen chak ya tsaya yace "yes! Wanan letter,
awanan letter naga sunan Bala dama number shi" daidai lokacin CP yafito yana gyara hanun
rigarshi daya tattare kafin ma yay magana Ayaan yace "inada number Ogan nasu Bala ta
hanyar wani sako da aka turamata dana karba naga number shi da sunan shi akasa" gyadakai
CP yayi yace "good good" daidai nan suka bude kofar wani daki da ake tracking number Big

Mum, tashi mai tracking number dake gaban wasu computers yayi yasarama CP yace "sir bamu
iya samun location dinta ba is as if ta karya sim dinne" da sauri Ayaan yace "bari naje na dauko
wasikar saina turo muku number ayi tracking Ogan dan duk inda Bala yake nasan yana tareda
Big mum, CP ya wayan da sukaje airport by now yakamata ace Pops sunyi landing" asanyaye
CP ya dafe kafadar shi yana girgiza mai kai yace "team dina sunce har yanzu babu any jet daya
sauka banda haka ma basuga any suspicious person ba, yanzu dai abinda nakeso dakai Ayaan
shine kaje ka boye Bilkisu inda matar nan bazata taba ganota ba, zakuma muhadata da police
da zasu tsare ta, hospital dinka is not safe tanada men dazata iya saka wa suje su daukota,
kaje idan kaje yanzu ka turamin number Bala koma yaya ake ciki zandinga sanar dakai" gyada
mai kai kawai yayi ahankali yajuya yafita daga office din yana kiran sunan Allah aranshi shi
kadai yasan yanda yakeji aranshi ya shiga mota yatada tunani kawai yake ina zai iya boye
Bilkisu dan duk wani gidajen Abba da nashi babu wanda bata saniba, wani zubin sai big mum
tasan wani abu nashi Mami ma bata saniba, lumshe ido yayi wasu irin hawaye masu zafi suka
zubomai ahankali yace "Ya Allah please take care of my Pops and Mami" baida matsala gidan
su Bilkisu dan yasan babu ta yanda zasu iya wuce jami'an tsaron da aka zuba suje dauko wani,
saidai in Big Mum takashe shi dan wlh bazai taba bada matar shi da batada lpy ba, bazai taba
badata bane, yanzu a ina zai iya boyeta, ya killace ta, dan ko kadan brain dinta bayason
damuwa yanda take last stage of recovery dinan Aaman! Zuciyar shi takira, da sauri ya rage
saurin gudun dayake amota gudun karyay hatsari, to wama zai kira dole shine, yakula da ita
bayan ya tsinceta batare dayaci amanar taba gashi ko godiya baimai ba lokacin ashe yanada
rana, to yanzu ina zaima sami number shi? Da sauri yace "Pops log book" kwana yay da sauri
akan titi yadau hanyar dazai kaishi gidansu, ko parking din kirki baiyiba yafito polisawan dake
gadin gidan na gaishe shi baimabi ta kansu ba yay cikin gidan da mugun gudu, dakin Abba yayi
bayan ya bude drawer shi yaje yana fiffito da takardar du da kyar yaga littafin, zama yay anan
kasa yana duddubawa page by page arude, tsaki yayi ya jefar da book din akasa yace "sh*t"
jingina yay da drawer ya dafe kanshi dake wani irin bugawa da karfi ahankali yace "Allahumma
ajirni fi musibati" haka yadinga maimaita wa kusan sau biyar kafin ya dago kanshi ahankali ya
kafe littafin da pages din keta buduwa sabida iska ido, da sauri ya rarrafa ya dauko book din
yadawo ya zauna yana bi page by page yana dubawa yana wani irin nishi tunda yake arayuwan
shi baitaba sanin tashin hankali haka yakeba saiyau, lokacin Bilkisu shi wanan bamaya
hayyacin shine, harzai ijiye littafin idanunshi suka sauka akan sunan Aaman, da sauri yaciro
wayar shi ya kwashi number yay dailing ya kafa a kunne har yagama ringing ba'a dauka ba
yasake dailing akaro nabiyu harya cirerai saiya ga anyi picking da sauri yace "A...Aaman,
Barister Aaman" daga ta dayan bangaren anatse Aaman dake kwance kan doguwar kujeran
mom dinshi yatashi zaune yace "yes nine, waye ke magana" ahankali yace "Dr Ayaan, amm
mijin mijin wacce ka taimaka, mijin wacce ka dawo mana da ita kano u and ur friend" shiru
Aaman yayi baisake cewa komiba dan yagane shi daga explanation din dayayi, shiru shima
Ayaan yayi zuciyar shi nawani irin mai zafi, ya lumshe ido saikuma ya budesu ahankali muryan
shi nadan rawa yace "am sorry Man" dan murmushi Aaman yayi yace "bakomi, why is ur voice
like dat is everything okay?" girgiza kai yayi wasu irin hawaye sun taru a idonshi muryan shi
narawa yace "please taimakon ka nake nema wayanda suka taba kiddaping wife sunyi
kiddaping Pops dina da Mami and my step Mum ce" zumbur Aaman ya mike tsaye yace
"subhanallahi" "and tace abasu Wife in exchange inba hakaba bazata saki su Pops ba and.."

kasa magana yayi sabida kukan da tun dazu yake dannewa yazomai, runtse ido Aaman yayi
sabida radadin da zuciyar shi tahau yi, ahankali ya budesu ya kalli agogo 8:40 nasafe ne yanzu
ahankali yace "Dr be strong man, ina Abj ne, amma yanzu nan zanbi flight nazo kano before 10
I will be there, text me address din inda kake, be strong Man babu abinda zai sami Dad da
Mom da izinin Allah" gyadamai kai Ayaan yayi yama kasa magana ya katse wayar yamai text
din address din hospital sanan ya mike tsaye bayin Pops ya shiga ya wanko fuskarshi ya share
da towel sanan yawuce yafita ya shiga mota yadau hanyar hospital.

Parking yayi a parking space sanan yafito daga motar jiki asanyaye idanunshi sunyi jajir, dark
shade dinshi ya dauka yasaka sanan ya kulle motar yay cikin asibitin, tun daga bakin office
dinshi yakejin kukan Bilkisu da sauri yabude kofar ya shiga ya mayar ya rufe yay cikin bedroom
din bayan ya cire glasses din ya ijiye akan table ya bude kofa ya shiga, ajikin kofa ya tsaya ya
kafeta da ido yanda take zaune akasa ga abinci a gabanta na Mrs Biggs sai uban kuka take
Nurse Sameera da tsabar karfin kukan ta baima barta taji alamun shigowan mutum ba sai
faman lallashin ta take.

Yafi minti biyu kallonta yake wani irin sonta na ratsa kowani jijiya na jikinshi, dan gyaran murya
yayi da sauri daga Nurse Sameera har ita suka dago kai suka kallai da gudu ta mike tana kuka
tafada jikinshi ta kankame shi tsam tsam tana kuka sosai da sauri Nurse Sameera ta mike kanta
akasa tana murmushi tace "tundazu ta tashi takicin abinci nazaci na dakin ne bata so na aika
aka siyo mata a Mr biggs shima takici sai kuka takeyi taki cemin komi kuma, tunda kadawo bari
natafi" dan murmushi yayi yace "thank you so much nurse Sameera" murmushi tayi tace
"bakomi Dr" tabude kofa tafita daga dakin ta rufo musu, sai alokacin yay hugging dinta back
tightly kafin yafara tapping bayanta alamun tai shiru, dago kanta tayi daga jininshi ta kafeshi da
jajayen idonta dake tsiyayar da hawaye, ahankali ya bude ido shima ya kalleta, dukan kirjinshi
tahauyi tana kuka sosai, da kyar ya daga hannu yakama hanunnata yahada da nashi yana
girgiza mata kai yama kasa magana, shigewa jikinshi takara yi sunkai 2min ahaka sanan yaciro
ta daga jikinshi yaja hanunta sukai cikin dakin akan gado ya zauna ya zaunar da ita a gefenshi,
hanun yasa ya share mata hawayen dake zubowa ya girgiza mata kai ahankali yace "am sorry
nabarki nafita ko, stop crying zokici abincin ki" abincin ya dauko ya daura akan jikinshi yadau
spoon ya debo yakai bakinta budemai tayi tana kallon idonshi tanaci haka yadinga bata fuskarta
kadai nasa shi kwanciyar hankali, saida ta koshi ta karbi spoon din daga hanunshi da sauri ta
debo itama ta kaimai baki tana washe mai baki, bude mata yayi ahankali yana kallon fuskar ya
karba yaci dan yasata farin ciki amma ko kadan bayajin dadin abincin abakin shi, da sauri
tasake debowa tana wani irin washe baki tsabagen murna takaimai bakinshi tana kallonshi,
wani irin zuciyar shi keyi, kasa bude baki yayi hakan yasa tasake matsowa tana budemai
bakinta alamun yabude baki tasaka mai, wani irin rawa zuciyar shi tafara na kuka sake tunamai
da Pops datayi dan dayana yaro haka yakemai in yana rashin lafiya yakicin abinci, da sauri ya
ture spoon din ya jawo ta yasaka ta ajikinshi ya fashe da wani irin kuka, da sauri tafara kokarin
fizge jikinta daga nashi jin yana kuka hakan yasa yasaketa ahankali, kallon fuskarshi tayi ganin
yanda yake kuka yasa ta kwaye fuska zatai kuka itama cike da damuwa, da sauri ya girgiza
mata kai yana goge hawayen dayake, da sauri ta zauna akan cinyarshi tasa hannu kaman
yanda yamata dazu ta share mai hawayen duktai wani irin da fuska rungume fuskarshi tayi

hawaye nataru wa a idonta tana shafa kanshi nakusan 1min saikuma tasake shi ta dago kanta
ta kalleshi dan tabbatar daya dena

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login