Showing 87001 words to 90000 words out of 124573 words

Chapter 30 - Sangartacce Book Complete Pdf by Maman AbdulShakur.pdf

M Shakur   

09 Nov 2025

3898

deba a plate, ya dauko remote ya kunna TV yadawo ya zauna yana chanza channel
zuwa news.
Fitowa tayi sanye da hijabin tazo zata wuce shi ta zauna akan kujera hijabin ta ya jawo harsai
da tai yar kara. "wash wai menene kai" tafado kanshi tana turamai baki, matseta yayi ya cire
hijabin ya ijiye akan kujera yana kallon fuskarta, murguda mai baki tayi batare datai magana ba
tana kallon abincin, cikinta ya shafa ahankali yace "zakici?" gyada mai kai tayi, kwanto da kanta
kirjinshi yayi yana shafa soft kumatun ta, da hanun daman shi yasa spoon a abincin ya debo zai
kai bakinta, make mai kafada tayi tace "ni baby ne" bakinshi yakai saitin kunenta yadan lasa
yirrr dataji yasa tadan zabura zata tashi, rikota yayi yana dan murmushi yace "oya haa" hararan
shi tayi sanan ta budemai bakin ya saka mata yana kallon fararen hakoran ta, da sauri ta hadiye
tana kallon teddy ta tajuyo ta kalleshi da sauri ta washe mai baki tace "wait, my teddy is hungry
too" da sauri ta tashi harda dan gudun ta ta dauko teddy ta dake kan dogon kujera tana tsalle,
bin cinyoyin ta daduk intai tsalle rigan ke dagawa yayi, da gudunta tadawo zata zauna akasa
yajawota jikinshi tana girgiza mata kai asanyaye, abincin yakara debowa yakai bakinta ta amsa
tana jijjiga teddy ta, taci sosai dudda hankalin ta nakan teddy ne kafin ta ballamai harara zata
sauka daga jikinshi, girgiza mata kai yayi yakara jawota jikinshi kaman baby ya rungumeta sosai
ta yanda ko motsi ta kasa ahankali yace "please stay here, sabida na iyacin abincin" fizge kanta
tayi tana turomai baki tana hararan shi zata tashi ahankali yasa hanunshi daya ta bayanta ya
riketa da kyau takasa tashi dayan hanun kuma ya debo shinkafar da cokali yafara ci bai wani ci
sosai ba ya ture yasha ruwa ya kalleta sai faman yima teddy ta kitso take, ahankali yakai
hanunshi kan two kitson dake kanta, shafa kitson yayi kafin ya saukar da hanunshi kan ciwon
kannata yana shafawa, dago manyan idanunta tayi ta yatsine fuska tace "stop". Gorunan da
Mami tabashi yajawo yamika mata tsumin tafara karba sabida alamun sanyin da tagani ajiki da
sauri ta bude takai bakinta lumshe ido tayi tana lashe lebe ta kalleshi tace "dadi" takara kafa
sauran abaki ta shanye goran ta mikamai ta mike tsaye daga jikinshi tana kallon TV saikuma
tajuyo tafashe da kuka tace "cartoon zan kalla" dan murmushi yayi yace "zoki zauna anan saina
kunna miki" da sauri tazo ta zauna kusa dashi, daura kanta yay akan kirjinshi sanan yasa mata
Disney junior tana kallon pj mask shikuma ya tattare kwanukan yatura su one side kafin ya kara
gyara mata zama ya sanya hanunshi yana wasa da jelar gashin ta.
Batare data kalleshi ba tasaka hannu ta fizge jelar tana murguda mai baki tana kallon cartoon
dinta, daganan bai kara tabata ba sai uban kallonta dayake yi kaman yau yafara ganin ta,
shikadai yasan yanda yakejin sonta aranshi, to mesa yamata wulakanci da.
Ahankali yadaura kanshi agefen wuyanta yana shakan kamshin fatarta ya kankame ta sosai,
zafin dataji daga jikinshi yana gasata yasa ta juyo da kai da sauri ta kalleshi, kallonta yayi kasa
kasa saikuma ya lumshe ido, da sauri ta daura hanunta akan goshin shi kafin ahankali tace
"sick?" gyada mata kai yayi, da sauri tace "meke ma ciwo" hanunta yakama ya daura akan
heart dinshi batare dayace komiba, kaman zatai kuka ta murguda mai baki tace "kasha magani"
girgiza mata kai yayi, ashagwabe tace "to wani magani kakesha na dauko ma?" ahankali yace

"madara" da sauri ta ijiye teddy akasa ta tashi daga jikinshi tai wurin fridge tunawa da taga
madara dazu data bude fridge, hollandia evaporated milk ta dauko mai harda dan gudunta tazo
ta tsugunna a kusa dashi tabude ta kaimai bakinshi dan bude ido yayi kadan yasa hannu yature
madaran murya chan chan kasa yace "ba wanan ba" dan matsowa kusa dashi tayi dan bataji
meyace ba ta daura hanunta akan kirjinshi tareda kai kunenta saitin bakinshi tace "meka ce?"
ahankali yace "ba wanan madaran ba" zama tayi kan cinyarshi sabida gajiya datayi da
tsugunnawa tace "to wani madara? a ina yake na dauko to" tai maganan tana hararan shi,
murya chan kasa yace "anan" waigawa tayi tana kalle kalle to ina madaran anan, kaman daga
sama taji yaja zip din gefen rigarta yaja rigar kasa, ihu tayi tana neman tashi daga jikinshi ya
kara riketa sosai yana sauke ajiyan zuciya, hanunshi har rawa suke yadaura akan kirjinta. "Kai"
takirashi da karfi cikin kuka, ta daddage ta fizge hannayen ta daya dike, teddyn ta tadauka ta
bugamai akai tana kuka sosai, ture kanshi tayi da duka hannayen ta biyu ta tureshi da karfin ta
tatashi tai wurin kofa zata bude tafita ahaka tsabagen yanda ta rude, da sauri ya mike tsaye
yazo wajen kofa zai riketa a tsorace ta tsugunna tafashe da kuka tace "don't touch me, wurin
sweeth..." da sauri ya dagota yana girgiza mata kai yasa hannu yadaura akan bakinta, da sauri
ya sanya ta ajikinshi ya rungume ahankali muryan shi narawa yace "am sorry" tureshi tayi tana
kokarin jan rigan ta sama, daukarta yayi yay bedroom da ita, ahankali ya kwantar da ita akan
gadon da sauri tai yunkurin mikewa girgiza mata kai yayi ya maida ita yace "please baby".
♦♦ *SANGARTATTCE* ♦♦



Maman Abd Shakur

76 - 77


Kafin ma tai yunkurin yin wani abu yahada bakinshi da nata yana kokarin zame rigar gabaki
daya daga jikinta, wani irin kuka take jikinta duka narawa hanunta tamika ta dauko filo ta
bugamai akai tana ture kanshi da filon jikinta nawani irin rawa tana kuka, yamutsa ta yacigaba
dayi batare daya saki bakinta ba, jin ana kiran sallan la'asar yasa yasaketa ahankali yatashi ya
zauna abakin gado tareda dafe kanshi yana kokarin saita kanshi, filo ta dauka tana bugamai
abaya da duka karfin ta tana kuka sosai tama kasa magana, da kyar ya dago kanshi dasukai
jajir ya kalleta yanda take kuka na sosamai rai shima ba'a son ranshi bane yake mata wani
abuba, filon dake hanunta takara bugamai akai tana ihu kaman mahaukaciya, ahankali yarike
filon tareda saka dayan hanunshi yajawota tana tutturjewa saida yahada ta da jikinshi, ya ijiye
filon, tana kokarin tashi yaki bata daman yin hakan ya matseta tareda daura kanshi ata wuyanta
yana bubbuga bayanta alamun tai shiru dan bazai iya magana ba ayanda yakeji, tun tana mutsu
mutsu har bacci yay gaba da ita. Ahankali yaciro ta daga jikinshi tareda manna mata kiss agoshi
ya kwantar da ita ya rufeta da bargo sanan ya mike tsaye idanunshi sun kada sunyi jajir, bayi ya
shiga yay wanka yafito ya shirya cikin riga da wando yadau car key da waya yafita daga gidan.

Baiwani dade da fitaba tafarka daga baccin tana kwalla, saikuma kukan ya kankama sosai sosai

take kuka tana kiran sweetheart yazo ya dauketa batason gidan nan mutumin nan sai tabata
yakeyi. Da kyar ta mike tsaye taje bayi, wanka tayo shima da sabida jikinta daduk yamata tsami
ne, sanan tai alwala tafito daure da towel din data gani abayin, wani dan gown data gani white
me hanun shimi a wardrobe din tadauko ta saka tana goge kwalla tana harare harare kafin
tadau hijabi daya bata dazu tasaka tai sallan la'asar, tana idarwa ta kwanta akan dadduman
tana birgima tana kuka. "sweetheart where are you? Katafi kabarni, why?" tafashe da kuka.

Aaman tunda suka koma bauchi rashin lafiya yatasa shi agaba bana wasaba, shi kanshi baisan
cewa haka son Ameerah ya shiga ranshi ba, ganin yanda yake yasa Dr Ameenu ya sanya
Ummy kiran Maman su, da kanshi ya sanar da ita komi, aiko washe gari saiga Maman da
baban su aka tattara aka tafi dashi Abuja gabaki daya. Alhamdulillah yadan samu sauki danhar
abinci idan mum tabashi yanaci, yanada wata cousin Usaida datake sonshi nan Abba yahada
auren su aka saka rana wata daya kuma baiwani musu ba dan Usaida yarinya ce mai hakuri
gata yar gayu.

Ayaan na fitowa daga masallaci hospital dinsu yawuce dan sosai yakejin rashin lpy, office din Dr
Ibrahim yawuce bayan yaduba shi ya daga kai yace "dude wai menene matsalar ka, kaifa Dr ne
bazaka guji abinda zai batama raiba wai, well I know u already know zuciyar ka na gab da
buguwa" awahale yaja gajeren tsaki saikuma yamike tsaye yace "thanks lemme get drugs"
fitowa yay daga office din yana tafiyar nan da isa ana gaidashi yana daga kai kawai kaman
bashine me babbakama Bilkisu kuka ba.
Magunguna yasiya da drip da wasu allurai a pharmacy sanan yadawo office dinshi, saida yasha
maganin da kyar dan ya tsani magani kafin ya kalli alluran tsaki yayi yadau wayarshi yakira Dr
Ibrahim, ko minti biyu ba'ayi ba ya shigo office din yace "Boy gani" wani irin mugun kallo Ayaan
ya watsa mai, dariya sosai Ibrahim yayi yace "dan nadan dana sunan da Abba ke kiran ka dalla"
dauke kai yayi ya bude kwalban alluran ya zugo da sirinji ya mikamai kaman ance yay maganan
dole yace "yimin kuma ahankali" karba Ibrahim yayi tareda daukan auduga ya juya yamai,
ahankali yace "aaauchh" bugemai kafada Ibrahim yayi yace "ashe da zafi kake parke different
patients kullum" dan murmushi yayi yace "thanks Man" kwanciya yayi adogon kujeran office din
ya lumshe ido, Ibrahim yabishi da kallo daga ganinshi kasan ciwo na cinshi dakuma tunani dan
alluran nan ma na kwantar da sha'awa ne, drip din daya ajiye akan saman table ya dauka yana
dubawa wanan na ciwon da heart dinshi keyine dakuma magungunan suma haka, ajiye
magungunan yay ya karaso wajen kujeran yana gangaro dogon karfen da ake makala drip ajiki
ya kalli fuskarshi yanda ya lumshe ido ahankali yace "nama fixing drip dinne?" gyadamai kai
yayi, hakan yasa ya tsugunna yakama hanunshi ya makala mai sanan ya gyara ruwan yana
shiga jikinshi, saida yajira na kusan 3mins sanan ya daura hanunshi akan heart dinshi beating
din dayake yi yasoma dawowa normal normal hakan yasa yajuya yay hanyar fita yace "zan zo
anjima" gyara kwanciya yayi tareda sake lumshe ido yana tunanin Bilkisu, ahankali yaciro
wayarshi daga aljihu number Dad Fawaz yakira, Neurologists ne likitan brain, sanan babban
Consultant ne akan any matsala na kwakwalwa, yana kiranshi bayan sun gaisa yasanar dashi
zaizo hospital dinshi gobe wurin shi da matarshi, nan dai yafada mai matsalanta.

Saida taci kukan ta tana kiran sweetheart tagaji sanan ta tashi daga kan dadduman ta cire
hijabin tabude kofa tafito falo, zama tayi akan kujera tadau teddy ta tanama kitso tana kallon
Channel din cartoon din da tasa yasaka mata dazu. Gajiya tayi ta mike tsaye tana dirke dirke
akan kujera tana dariya gabaki daya ta hargitsa falon dan kanta tagaji tadau ruwa tana sha
sanan ta kwanta tana dariya ita kadai, harta fara gyangyadi taji ankira salla da gudu tana tsalle
tai bedroom tadauro alwala tafito tahau kan dadduman dawani irin tsalle kafin tafara sallan.


Wuraren magrib Big Mummy ta shigo gidan akatuwar jeep dinta driver ta shikejan motar,
parking yayi tafito tana sanye cikin jan ashobin biki mai shegen kyau dayaji uban stones,
securities ne sukazo ta nuna musu babbar jakarta tace "awuce dashi shashina" tanunama driver
jakar da abubuwa ke ciki wanda aka raba nabikin tace "biyoni da wanan" tafiya takeyi na isa
kaman wata boss tana danna waya har zuwa Shashin Mami, murmushi lullube akan fuskarta ta
shiga falon Mami na fitowa daga kitchen kenan taga hajiya fadada murmushin kan fuskarta tayi
tace "oyoyo hajiya saukar yaushe" dan tabe fuska big Mummy tayi tana huro hanci wanda idan
da Sabo Mami tasaba, ta karbi jakan dake hanun dreba shikuma yajuya yafita Mami ta karaso
wajen tana mata sannu da zuwa Big Mummy tamika mata jakar tace "gashin nan inji Atine
tunda bakizo ba wai" karba Mami tayi tace "sabida jikin Ayaan ne ai da nazo bikin zinatu, Hajiya
kinkosan wani abin farin ciki da ikon Allah kuwa daya faru kuwa" "saikin fada" Big Mum tafada
agadaran ce, cikin nuna tsananin farin ciki Mami tace "wlh anga Bilkisu, jiya wayansu suka
kawota daga bauchi, inata so nakira ki nagaya miki Alhaji ya hanani wai surprise zamu miki, dan
wajen ki har ya warke anga Bilkisu haji..." baya da Big Mum tayi zata zube yasa Mami tariko ta
da sauri cike da mamaki tace "baki da lafiya ne hajiya?" arude Big Mummy tace "Bilkisu Bilkisun
mu dai matar Boy kikace angani?" gyada mata kai Mami tayi tana kokarin zaunar da ita akan
kujera ganin tarude sabida good news din, kin zama tayi tarike hanun Mami tace "tayaya aka
ganta? Meta ce muku?" "kaman ya metace?" Mami ta tambayeta tana kallon fuskarta, da sauri
Big Mum ta kakalo wani irin murmushin dole tama Mami, ahankali Mami tace "yarinyar da bama
ta yarda damu, tasami shafewan kwakwalwa ne, duk bata ganemu ba, tana ma dakin Ayaan" da
sauri Big Mummy tana share zufan daya keto mata tace "ina boy din nawa nata ya shi murna"
tabe baki Mami tayi tace "yaje Clinic wai" zumbur Big Mum tamike jikinta har rawa yake da kyar
ta saita kanta ta kakalo hawaye tace "Allah Akbar kabiran! Allah mai girma da daukaka, bari
naje nadubo matar Boy dina" Mami tace "gama abincin su chan angama bari nasa Salamatu
takai musu tunda tahada a food flask already" da sauri Big Mummy tace "basai kinsa yan aiki ba
tunda chan zani, ban in wuce musu dashi" bama tajira Mami tamike ba tai dining tadau food
flask da plate da spoon din data gani ta fice daga shashin har tana harde kafa tana maganganu
da kanta tace "Bala yace tamutu, Bala yace tamutu, Bala eh yace tamutu" haka tadinga
sumbatu kaman tababba hartai shashin nasu.

Tana zaune akan hadadden center carpet din falon tajawo ledan daya kawo dazu da rana
chocolate din da tagani na cabry dairy milk tadauka tana fama da budewa takasa, bude kofan
da akayi yasa ta mike tsaye da sauri dan tabama koma waye ya shigo yabude mata, ido da ido
sukai da big Mummy data shigo rike da food flask da warmer tawani irin kafeta da ido tana
kallonta tun daga sama har katsa, itama kafe Big Mummy tayi da ido kanta nadan juyawa,

mayar da kofan Big Mummy tayi tarufe sanan ta tako kafa ahankali tana mata wani irin kallo
tana takowa, tana shigowa tsakiyar falon ta ijiye food flask din akan kujera, sanan ta dago kai ta
kalleta itama har lokacin ita take kallo kanta nadan juyawa fuskar matar nasata jin wani iri iri
data rasa name ba, ahankali Big Mum ke takowa tana dumfaro inda take atsaye tana mata wani
irin kallo, samun kanta tayi dayin baya, baya, takasa janye idanunta daga kan Big Mum kanta
nawani irin juyawa tana ganin fuskar big mum yana kuma bace mata, jinta tayi ajikin bango
kafin tayi yunkurin motsawa Big Mum ta tareta da hannayen ta, ta hanyar sakata a tsakiyar
hannayen ta data daura akan bango tana wani irin zaro mata ido, wani irin yamutse fuska tayi ta
kudundune hancin ta tana zobaro baki kaman Doddannuwa danta tsorata ta, da sauri ta runtse
idonta kanta nawani irin zafi kaman ana ta fasa ruwa, dan harwani kara takeji daga kanta zuwa
kunenta na shuuuuuu, cikin kakausar murya Big Mum tace "bude idonki shegiya yar matsiyata
dake nufina da tsiya, bude nace, bude idonki!" ta dakamata wani irin tsawa tareda buga bangon
datake manne ajiki, afirgice ta bude ido tana wani irin nishi, tsabagen tsorata saitaga fuskar Big
Mum na rikide mata, gawasu irin maganganun datake ji daga kanta dake mugun vibrating,
fincikar hanunta Big Mum tayi kaman zata cire su daga jikinta tsabagen yanda kanta ke juya
mata tana ganin flash din fuskar Big Mum yana kuma bacewa yasa tama kasa ihu, murde duka
hannayen ta Mum tayi tabaya hakan yasa tasaki wani irin kara tace "was..." finciko ta Mum tayi
tana wani irin yimata abu kaman dodo da fuska tace "kalleni da kyau inda ace nasan su Bala
bazasu kashemin ke da wlh ninai da kaina, amma listen to me, dudda kinyi losing memory ban
yarda ba, inhar kika sake kika tonamin asiri wlh saina" hanunta ta daura akan wuyarta ta
zagaye, arude take kallonta jikinta nawani irin rawa, wani irin kallo Big Mum tasake mata tace
"nida nake tsananin farin ciki burina yakusa cika, ko bayan tafiyar ku bansamu ankamomin shi
yamini signing papers din bane sabida kullum ubanshi da uwar shi natare dashi" janye
hannunta tayi daga wuyanta ta fizgo gaban rigarta luuu tataho tana kukkule ido tsabagen yanda
kanta ke juyawa, ganin haka yasa Big Mum tawani irin jijjigata ahankali ta ware idon tadaura
akan Big Mum, dafe kanta tayi dake wani irin juya mata kaman amadubi saita fara ganin kanta
awani bene tana sanye da hijab tana gudu saitai buge da kujera tafadi, saikuma taga fuskar
matar nan data riketa, wani irin zubewa tayi akasa wajen asandare ta suma tsabagen yanda
kanta kemata wani irin juyi. Tsayawa Big Mum tayi tana kallonta yanda ko numfashin kirki bata
fitarwa, da sauri ta juya tabude kofa tafita daga dakin, leka ko ina tayi ganin babu kowa
ashashin yasa ta sauke ajiyar zuciya tadawo dakin ta tsaya akanta tana tunane tunane, yanzu
idan takashe ta ai koda, dat is idan ma za'a tambayan ta kenan, zata iya cewa tana zuwa ta
dubata saita tafi shashin ta sabida taje tahuta itama daga biki take, hakan ma yafi this is the
best chance na aikata barzahu datake dashi before tai running plan dinta, duk wanda zai shigo
tsakanin ta da dukiyoyin nan da kamfanonin Alhaji wlh bazata mai raiba.

Gama zancen zucinta keda wuya tadau daya daga cikin manya manyan filolin jikin hadaddun
kujerun falon tayo kanta, ahankali ta tsugunna ta daura guiwowin ta akasa tadaura filon asaman
fuskarta ta danne da karfin bala'in, rashin samin iskan numfashi cikin Suman datake yasa tafara
shure shure tana shushure kafa tana dukan filon da hannu, Big Mummy takara

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login