Follow us on social media

Showing 51001 words to 54000 words out of 124573 words

Chapter 18 - Sangartacce Book Complete Complete Hausa Novel by M Shakur

M Shakur   

09 Nov 2025

5133

ya hankadeta gefe azuciye yafita
daga ruwa tareda yin kwallo da glasscup din wine dinshi ya shiga cikin gida, wani irin kuka
tafashe dashi tana tari kafin ta lallaba tafita daga pool din tai ciki itama, tundaga kasa takejin
yanda karan music ke tashi daga dakinshi kaman zai fasa gidan, lallavawa tayi tahau stairs tai
dakinta tana shiga tasaka key, bayi tafada tai wanka da ruwa mai zafi sosai kafin ta dauro
alwala tafito tai salla, haka tawuni adaki batare data fitoba tai girkin abinda xataci ba, har bayan
magrib waka ketashi daga dakinshi kenan bai fita yay salla ba, tayaya zata zauna da mutumin
da baya bin Allah, babu abinda ya damu dashi to yanzu ma tayaya zata chanza shi?. Jin shiru
dakuma alamun takunshi yafito daga daki ya sauka kasa, sai chan taji karan fitan mota yasa
tasan yafita daga gidanne, saukowa tai taje kitchen ta dafa Indomie kafin ta dawo dakinta taci
tai sallan Isha tai karatun Al Qur'ani har wuraren goma nadare sanan tai baccin ta.
Ko a cikin bacci ma mafarke mafarke taketa yi har da asuba ta tashi tadauro alwala tazo tai
salla nan kan dadduma ta zauna tana ta addu'o'i har gari yay haske sosai, wuraren 9 tafito babu
kowa agidan hakan yasa ta gyara gidan ta gyara ko ina ta kunna turaren wuta a burner tea
kawai ta iya sha ta zauna tai shiru tanata tunane tunane, kafin ta dauko wayarta ta kunna data
ta shiga goggle ta tai typing ya ake chanza mutumin dabaya bin Allah yakoma yanabin Allah,
nan dai taga amsoshi da dama daga ciki akwai yimai wa'azi, a tunatar dashi mutuwa da sauran
su dai, tabe baki tayi wanan maisa sarkan yanajin wa'azi ne, awani page ne taga sun rubuta
za'a iya tsorata shi hakan zai iya sa ya chanza, bata ma tsaya ta tantance me suke nufi da
tsoratashin ba kawai zuciyar ta yakama maganar sosai, tana ta tunane tunane tsorata shi,
tsorata shi, tayaya zata tsorata shi yabi Allah, sai chan kuma tai dan murmushi da sauri ta bude
contact dinta tunawa da Mami tasa mata number kowa na gidansu awaya, number shi ta shiga
tamai sending message "please i want to go out and buy something very important" yana zaune
a office yana shirin shiga theater yaga sakon ya shigo dogon tsaki yaja yace "ina tasani mtsww"

yaja tsaki ya ijiye wayar garin ijiyewa mistakenly ya danna k, aiko tana ganin k taji dadi da gudu
takoma sama tai wanka, riga da zani tasa na atampa tasaka hijabi tadau kudin da Mami tabata
dayawa tasaka a jaka da wayarta ta dauka tafito, mai gadi tacema tana son ya kira mata keke
napep aiko sai gashi yakira mata, shatan shi tayi har kasuwa tabashi kudi dayawa tace yajirata
zai maidata gida, aiko yadinga murna
Yace xai jirata anan, shiga tai cikin kasuwan saika shagunonin saida yadi, na farkon ta shiga,
farin yadi ta yanka har yadi shidda ta biya kudi mai dinkin wajen tabamawa tasa yay mata
doguwar riga mai shegen fadi da dogon hannu shima mai fadi akai abu abaaya kaman fiffike,
murmushi tai ganin yanda rigar tayi tabiya kudi tafito tanata kalle kalle wurin, shagon wasu arna
masu kitson attach tagani ta tsaya tanata kallon dogon gashin wig din data gani ajikin kan roba
dasuke daurawa, kaman mai tunani kafin ta nisa ta shiga shagon ta tambaya nawane aka
cemata dubu goma hakanan ta biya tafito tasai wani farin hodan yara na pears tabiya tafito
sanan tabi hanyar data shigo kasuwar tafita mai keken ko nanan ta shiga suka koma gida kara
bashi kudi tayi yanata mata godiya itakuma ta shiga gida rai fess, akarkashin gadon dakinta ta
tura duka abubuwan gabanta nafaduwa tai sallan azahar harda rokon Allah yasa ya tsoratan
sosai, sanan ta sauko kasa ta dafa white rice da stew ta dibi iya cinta takoma sama taci ta
kwanta sai bacci, haka dai tawuni tana tunane tunane da neman nasara wurin Allah, wuraren
goma tana shirin kwanciya taji shigowar shi gidan hakan yasa ta sauke ajiyar zuciya tai fixing
alarm awayarta karfe biyun dare kafin ta gyara kwanciya tai addu'an bacci sai bacci.

Karfe biyun dare alarm yafara ringing da kyar ta mike tsaye ta bude ido tana dafe kai, bayi ta
shiga ta kukkuro baki tafito, agaban gadon ta tsugunna ta jawo kayan daga karkashin gado,
doguwar farin rigan ta warware ta daura akan yar figigiyar rigar baccin dake jikinta, rigan ko har
kasa yake jan mata, hannun ma yafi hanunta tsawo gashi da fadi saitai kaman wata fatalwa
fatalwa aciki, hular dogon gashin tasaka da kyar dan bata iyaba, da sauri ta kalli kanta amadubi
yanda tai kaman wata aljana mayya yasa ta ware ido, hodar ta dauka ta zazzaga sosai a
hanunta ta lapta a fuskarta sosai saitai kaman aljanna da gasken, tasa hannu ta barbaza gashin
ta gaban fuskarta sanan takara kallon yanda tai ita karan kanta bama kanta tsoro take ga
kirjinta wani irin dukan biyar biyar yake, ahankali ta bude kofar dakin ta fita tai gaban dakinshi
tadade a tsaye tana addu'a kafin ta tattaro jarumtarta takira sunayen Allah, sanan tabude kofar
dakin ahankali ta shiga babu hanske sosai dakin sai dan dim light daya bari tana iya hango shi
yanda yake baccin shi hankali kwance akan lumtsatsan gadonshi, ya lullube tundaga kafarshi
har zuwa cikin shi yana baccin shi daya karama fuskarshi kyau, karasawa gaban gadon tayi ta
tsaya zuciyar ta kaman zai fashe wani irin ajiyar zuciya ta sauke tana dafe kirjinta kafin ahankali
ta mikar da hannunta tareda girgiza kanta tayanda gashin wig din ya yabazu sosai, dan gyara
murya tayi kafin tai wani irin murya tace "Ay yaaaa nuuuuu, Ay yaaaaaa nuuuuuuu, Ayyyyyy
Yaaaaaaa, Nuuuuuuuuu" dan motsi yay kaman yasan ana kiranshi, wlh takusa fitsari ajiki da
kyar ta daddage ta kirashi da karfi bala'i "Ayyy Yaaaa Nuuuu" firgigit ya bude ido ya daurasu
akanta, takusa sumewa amma bata bari yagane ba saima kara mikar da hannunta da rigar
yaboye tayi tai wata irin murya tace "Ayy yaaa nuuuuu nu" wani irin ihu Ayaan yayi yamatsa
baya da sauri dan sai yanzu idanunshi suka sake clearing, kara matsowa tayi tana wani jujuya
kai dan yahango farin fuskarta da kyau tai wani iri da hannu kaman zata kamoshi ihu yay
"Popsy" yakira atsorace wani irin murya tai tace "am yourrrr spirittt, kai saaakoo aaakkaaa baan

in kaawooomaaa" wlh gabaki dayan jikinshi rawa yake bilhakki ya tsorata yana komawa baya
me wanan waye wanan a tsakiyar daren nan, tana biyoshi tana wani irin jujjuya kai kaman
zombie tace "ance-idan-har-aka-koma ga Allah-ba-zaka gamu da fishin ma'aiki, kadena wasa
da salla, sallan ma ajam'i zaka dinga yi, ka gyara rayuwar ka, kaaa naaatsuuu kaaabi Allah
yakai wanan bawan kanaji na kona maidakai biri" gyada kai yayi da sauri kaman zaiyi kuka
yakasa kallonta saima shishigewa dayakeyi a bangon gado, itama yanda takejin wani irin
tsoranshi na shiganta idan har takara koda minti dayane zai iya kamata hakan yasa tace "kulle
idanun ka zan kooomaaa duniiiyarrr mu" da sauri ya kankame ido ganin haka yasa ta juya sadaf
sadaf ta bude kofar ahankali tafita ta shiga dakin ta da gudu, ta cire rigar ta goge hodar fuskarta
dashi sanan ta cire gashin tahadesu ta dukunkune ta tura karkashin gado tahau gado da gudu
tareda jan bargo tana numfashi sama sama kirjinta ko kaman zai rushe sabida tsoro.
[7/21, 9:27 AM] +234 706 571 7620: ♦♦ *SANGARTATTCE* ♦♦



Maman Abd Shakur

49 - 50

Yay kusan minti biyar idanunshi arufe jikinshi ko ina na rawa bai taba ganin abu hakaba in his
life kafin ya bude idon ahankali yana bin dakin da kallo, ganin kaman tanamai gizo a ido yasa ya
fasa ihu. "Popsy" ya sauka daga gado da gudu yafita daga dakin yay downstairs, tana cikin
bargo taji ihunshi tafashe dawani irin dariya tana taushe bakinta dudda yanda kirjinta ke bugawa
amma bakaramin dariya tayiba. Haka ya zauna a falon ya kalli nan ya kalli chan sai kiran
sunayen Allah daya dade bai kiraba yake dan wlh ya tsorata har ranshi, haka ya zauna a wurin
yana istigifari har aka kira sallan asalatu mikewa yayi da sauri ya shiga bayin falon ya dauro
alwala tsabagen yanda yake tsoron dakinshi yasa yakasa komawa, car key daya bari anan
center table yadauka yafita tsakar gida yabude mota yanada wasu kaya awurin yadauko
jallabiya yadawo daki yasaka sanan yafita shine harda tashi mai gadi su tafi masallacin tare,
akan kunenta yabude kofa yafita aiko bakaramin dadi abin yamata ba harda sujjada tana
godema Allah, ta shiga bayi ta dauro alwala tazo ta tada salla, saida gari yay haske sosai
wuraren 9 sanan ya shigo gidan daga masallaci sama yatafi ahankali saida ya bude dakinshi ya
dade abakin kofa yana kallon dakin kafin ya shiga ya kwaso kayan dazaisa yaje asibiti dasu
sanan ya sauko kasa ya ijiye kan kujera, abayin falo yay wanka ya shirya yafita agurguje dan
yay latti kuma yanada aikin dazaiyi.
Wuraren biyar na yamma yadawo gidan dauke da leda ahannu, bataji dawowan shiba tana
zaune afalo cikin riga da sket na atampa tai nisa cikin karatun novel awayanta taji ana kokarin
bude kofa, tashi tai a tsorace zata gudu dan gani take kaman yana ganin idonta zai gane itane
aiko garin gudu ta bige da kujera, ihu tai ta rike kafarta daidai lokacin ya shigo dakin da sauri ya
karasa gabanta yana kallon fuskarta dan ya dade bai ganta ba, ahankali ya tsugunna yana
duba karfar ganin babu wani ciwo dataji yasa yace "mesa kike gudu" anatse kaman ba shiba,
girgiza mai kai tayi tana hawaye gabanta na faduwa gani take kaman idan suka hada ido zai
gane itace ta tsorata shi jiya, sakinta yayi ganin yanda jikinta ke rawa kafin ya ijiye ledar daya

shigo dashi akan center table ya nuna mata da hannu yace "dauka kitafi dashi" ledan ta kalla
kafin ta kalli fuskarshi saiyanzu ma talura yau babu sarkan babu dan kunen akunenshi ya
kwanta tareda lumshe ido kaman mai tunani, da sauri tadau ledan tai sama da gudu bude ido
yay kadan yabita da kallo kafin ya sauke ajiyar zuciya ahankali. Tana shiga daki ta rufo kofanta ta zauna akasa ta bude ledan, ice cream ne manya manyan
roba gudu uku different flavors, murmushi tayi ta gyara zama ta dauko daya daga cikinsu
coconut flavor tahau sha tana lumlumshe ido, kasa shanye wa tayi ta ijiye agefe tana murmushi,
ana kiran magrib taji yabude kofa yafita hakan yasa ta sauko ta saka ice cream din a freezer
sanan takoma sama tai alwala tai salla ana kiran isha ma tai alwala tai salla tai karatu kafin ta
tashi ta shiga bayi tai wankan dare tazo tasaka rigar baccin ta iya gwuiwa ta kwanta abinta
tareda saka alarm yau biyu da rabi.
Alarm na tashin ta ta jawo kayan ta saka ta malka uban hoda a fuskarta dayama fi najiya tana
dariyan keta dudda yanda kirjinta ke bugawa, fitowa tai Sadaf Sadaf kaman wata mayya ta
bude kofar dakinshi bata ganshi ba hakan yasa ta fito tunawa da dazu a falo taga ya kwanta,
tana hawa stairs ta ganshi ko akan doguwar kujera yana bacci awahale daga ganinshi kasan
bai dade dayin bacci ba, sakkowa tai sadaf sadaf tana tattare rigar dan karya zubar da ita
hartazo gabanshi ta tsaya tana kallonshi kafin takira sunashi. "Ayyyy yaaa nuuu" afirgice ya
farka dan dama bacci baidade da saceshiba dan kasa bacci yayi tun bayan yadawo daga sallan
Isha'i, a tsorace ya mike zaune ya makale jikin kujera yana kallon aljannar mai dogon gashi, ga
gashin ta yakusa kai ciki, kara matso wa tai tana mimmikar da hannu kaman zata kamoshi, ihu
yayi yana kokarin mikewa daga jikin kujera yace "wlh na riga na tuban ma Allah" wlh takusa
dariya amma ta daure kirjinta na dukan uku uku tace "kaaayiii salla yauuuu?" gyada kai yayi
yama kasa magana da sauri tace "in har ka kara aikata wani aiki na zunubi bazamu barka ba,
rufe idonka lokacin bacewata nakoma duniyar mu tayi" ta dakamai tsawa dawani irin murya, da
sauri yarufe ido jikinshi na rawa aiko ta juya da gudun bala'i tai sama batare data bari kafarta
yay karaba, ahankali ta bude kofar dakinta ta shiga ta mayar ta rufe ahankali sabida karyay
kara, ta cire rigan da sauri tana goge hoda fuskarta da ita kafin ta tunbuke gashin ta dukunkune
su tare ta turasu karkashin gado tahau gado da gudu ta ja bargo tarufe tana dariya kasa kasa
tana dafe kirji sabida yanda yake beating fast.
Yafi minti goma kankame da idanu ya rirrike lumtsa lumtsan filon kujera kafin ya bude idon
ahankali yana kalle kallen falon ganin babu aljanar ta bace yasa ya mike tsaye da sauri yay
sama, dakinta ya bude ya shiga arude, abirkice ta yaye bargo tana zazzaro ido da hawaye har
yacika su dan tazaci yagano itane ke tsorata shi, shigowa yayi yana kallon dakin ko ina a gyare
sai kamshin turaren wuta yake maida kofar yayi yarufe yazo yahayo gadon ya kwanta batare
daya cemata kala ba sai ajiyan zuciya yake saukewa, a tsorace ta zabura ganinshi kusada ita
zata sauka daga gadon ya riko hanunta yajawota yasata ajikinshi batare dayace mata kalaba
ya kankameta yana ijiyan zuciya, tana iyajin yanda kirjinshi ke bugawa fatfat, kankametan
dayayi yasama ko kwawkwaran motsi takasa sai hawayen wahala data farayi ahaka bacci yay
gaba da ita, kasa bacci yay saima kara kankametan dayayi yanamai jin natsuwa ya sumbaci
goshin ta yay istigifari akan kura kurenshi da laifuffukan dayama Allah swt.
Ahaka wahalallen bacci yay gaba da shi ana kiran assalatu ya bude ido tatas ya sauke su akan
fuskarta duk ta takure ajikinshi tana bacci yafi minti goma yana kallon fuskar ta kafin ahankali ya
ijiyeta agefe kaman yana ijiye Kwai, bayinta ya sauka ya shiga, ko ina kwalkwal ga kamshin

dayake bayan yagama abinda zaiyi yafito daure da alwala, da bismilla yafita daga dakin yana
Kalle Kalle gani yake kaman witch din zata fito, yay maza yafita daga gidan ya tada mai gadi
atare suka tafi masallacin.
Wuraren 9 ya shigo gidan dauke da kayan dazaisa daya dauko daga mota har bayason kallon
doguwar kujeran da witch din tazomai yanakai jiya, yay sama da sauri ya bude dakinta ya shiga
bata ciki hakan yasa ya ijiye kayan akan gado ya shiga bayi yayo wanka yafito daure da pink
towel dinta yafara shiri yana cikin kulle boturin hannu riga ta bude kofa tana ganinshi ta juya da
sauri batare datama shigo dakinba zata tafi ahankali kaman ba Ayaan din daba yace "dauko
min takalmina adakina" hannu tasa ta taushe bakinta jin dariya yazo mata aranta batare data
juyo sun hada ido aranta tace "ashe akwai abinda zai iya chanza ka mugu" dakinshi ta shiga
tana kalle kalle dan bataga takalmi ba.

Yana gama sa bituran hannun rigar yadau wallet dinshi dake kan bedside drawer yasaka a
aljihun bayan wando, sanan ya mika hannu yadau wayarshi kiran iPhone xmas, mistakenly
wayar yafadi anan kasa gefen gado, dan gajeren tsaki yaja kafin ahankali ya tsugunna dan
daukar wayar dayaga yanakan wani farin yadi dayaga yadan leko daga karkashin gado,
tsugunnawa yayi yadau wayar ya mike tsaye yasa kafa zai tura farin yadin dabemasan nameba
dayadan leko yakoma ciki sai kuma yasake tsugunnawa hakanan yaji zuciyar shi na fizgar shi
daya duba kome, ahankali yasa hannu yajawo farin yadin gabaki daya, yanayin yanda yajawo
da karfi yasa abubuwan suka barbaje babban roban hoda yay tsalle yay gefe saikuma gashin
dokin arna yay gefe daya saikuma ga yadin dayake aduddunkule, da mamaki yake kallon kayan
dama yarinyar nan nasa attachment ne, saikuma ya mika hannu yadau farin yadin ya mike
tsaye ya warware rigan yana tabe baki, rigan yabi dawani irin kallo daidai lokacin ta bude kofar
ta shigo hanunta rike da black cover shoe dinshi, rigar bashi tsoro dataga ya warware yana
wani irin kallo yasa ta zaro ido ta kallai, tsabagen yanda jikinta ke rawa batamasan sanda ta yar
da takalman ba wani irin kallo yamata yasa arude tafara komawa dayaba tana tafiya. "dan
girman Allah ka yakuri, wlh so nake kawai ka gyaru ka dinga salla saisa namaka hak..." da gudu
ta kwasa tai downstairs ganin yanda yayo kanta, shi dayaga rigan yadaiga yay kama dana
aljanna but ko kadan baikawo wani tunani aranshi ba maganan datayi yasa yagane kenan itace
ta tsorata shi, take yaji rashin yana wani irin soyuwa, ganin binta yake yas ta kwasa da gudu
tafita daga gidan mai gadi namata magana kota kanshi bata bi tafita babu hijabi ajikinta daga ita
sai doguwar riga da dan kwalin ta, tana ko fita taci sa'a daidai wani keke napep yay dropping
wata mata wup ta shige duk ta rude tana kallon waje ganin harya fito daga gate shima fuskarshi
babu alamun rahama yasa tace "malam kama Allah mutafi kafin yazo ya kasheni, GRA zamu"
da sauri mai keken ya kunna kafin Ayaan ya iso harsun waske, da sauri yakoma cikin gida ya
shiga mota yabi bayansu dan baisan inda zataba, sune har GRA batadai san sunan layinsu ba
amma tasan gidan, hakan yasa tana ganin gidan tanuna mai yana parking ko tsayawa mai
magana batayi ba ta shiga gidan da gudun bala'i daidai nan Ayaan shima yay wani irin wawan
parking awaje ya biyota a haukace, Mami, big Mummy, da Abba ne afalon, Abba da Big Mummy
na zaune Mami kuma na tsaye daga ta wurin dining tanama wata yar aiki magana, tana shiga
dakin bama ta lura dasu Abba ba ganin Mami yasa ta fasa wani irin ihu tai wurinta ta shiga
bayanta ta kankame ta sosai tana nuna bakin kofa tace "Mami karki bari yadakeni wlh kasheni
zaiyi yau" kafin Mami tama gama gane kan zancen ta shima ya shigo dakin ya dumfaro su

idanunshi dasuka kankance tsabagen bacin rai akanta, yanda ta rirrike Mami tana neman ma
fadir da itama tsabragen tsoro, "Ayaan!" Abba yakira shi da kakkausar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login