Follow us on social media

Showing 42001 words to 45000 words out of 124573 words

Chapter 15 - Sangartacce Book Complete Complete Hausa Novel by M Shakur

M Shakur   

09 Nov 2025

5072

aka kwashe da dariya, shigewa yay
theater abinshi Abba ya kalli Baaba da Mami dake zaune suna yar dariya suma yace "mutafi
gida ki huta ga mijin tanan ai xai kwana da ita" hakanan suka tashi sukaje driver yajasu sai gida

Sabon kayan asibiti ya dauka ya koma dakin ya ijiye kayan akan gadon yana kallonta yanda
fuskar ta yay fayau tsabagen wahala da kuka gakuma santala santalan cinyoyin ta dasuka
bayyana, dan gajeren tsaki yaja yay gaban gadon yadan zauna ta baki bakin kafin yasa hannu
ya dagota ahankali, dan igiyan bayan rigan ya warware yana wani ciccije lebe, sakin igiyan yayi
kafin yakai hanunshi ta gaban rigar yawani ja rigar kasa da sauri ya saketa tafada gadon bam
dudda cikin bacci take saida tadan yatsine, runtse idonshi yayi da karfi kafin yadan mikar da
hannu yana kokarin ya maida mata rigar inyaso yafita yakira Sameera tasamata, neman rigar
yake wacce ya zameta takai kan cikinta, hanunshi dayaji ya sauka akan kirjinta yasa ya matsa
baya da sauri har yana bigewa da kujera yace "f*ck!" fita yay daga dakin da sauri kaman ana
ingiza shi, yay hanyar office dinshi daidai lokacin Nurse Sameera tafito daga dakin wata patent
daure fuska yayi yace "kije ki chanza mata riga" ahankali tace "to Ango" wani mugun kallo
dayamata yasa tabar wajen da sauri tana gimtse dariya, office dinshi yakoma ya shiga ya rufe
kafin ya wuce bedroom din ciki, bayi ya shiga yay wanka abinshi yafito daure da towel fridge din
dakin yabude yadau Vita milk mai sanyi ya bude yakoma kan gado yana sha, agogo ya kalla
yaga har daya nadare yawuce ma tsaki yayi dan bazai iya kiran Meram ba is too risky hakan
yasa ya ijiye bottle din yakoma ya kwanta sai bacci ba zancen salla.

Wuraren 8:30 yatashi da kyar, ya shiga bayi yayo brush yay wanka yay alwala, yadau mai ya
shafa sanan ya shirya cikin dogon black jeans da soft cotton t-shirt maroon bakaramin kyau
yamai ba color, ya shafa man gashin shi dake karasa gashin kanshi kyalli sanan yadau turaren
shi mai kama jiki ya fesa kafin yahau dadduma yay sallan asuban yana idarwa ya mike yana
kallon agogo dan baida lokacin yin azkar, takalmi ya zira sanan yadau lab coat yafita once ya
zagaye ward yaduba patients dinshi da yarinyar chan gida zai tafi ya huta tun jiya baihuta bafa.
Saida yagama duba patients sanan yawuce dakin datake tun kafin ma ya shiga yaji maganan
su Abba, daure fuska yayi ya shiga dakin, Abba dake shirin fita shida Baba Sulaiman ya kalla
yace "Morning Pops, morning Baffa" kanshi Abba yazo zai shafa da sauri ya doje dan bayason
abinda zaisa yarinyar chan ta raina shi, Abba daya bishi da kallon mamaki saikuma yay shiru
shida Baba Sulaiman suka kalli juna sukai murmushi Abba yace "muntafi office, anjima da
yamma zamu dawo" daure fuska yasake yi yace "saikun dawo" murmushi Abba yay suka fita
daga dakin Baba Sulaiman yace "daga zuwan matar shi yasoma girma bayason kana badashi,
shiba yaro bane ba yanzu wayaga su Ayaan da iyali" dariya dukansu sukayi Abba ya gyara
zaman babbar rigarshi yace "ai haka nakeso dama".

Sai alokacin ya kalli Mami da Baaba dake hirarsu, yadan saci kallonta tana zaune cikin riga da
sket na material mai taushi dark blue sai dot din white ajiki, kanta rufe da white hula tazauna
tana jingine da gado idanun nan sunyi jajir alamun bata dade dagama yin kuka ba, ga dan
karamin cup da aka mata tea aciki tana deba da cokali tana sha dan kin yarda Mami tabata tayi,
ahankali take sha bakaramin kyau taiba, dauke kai yasake yi ya kalli Baaba yace "ina kwana"
kafin ta amsa ya kalli Mami da tunda tamai kallo daya bata sake kallonshi ba dan har yanzu
basu shiryaba, yace "Good morning Mami" Baaba ce kawai ta amsa shi tamai ban gajiya da
sannu sanan ta kalli Mami dake magana da Bilkisu kasa kasa tace "suruka nidai zomu zaga
nagaji da zama wuri daya jikin tsufa kafafuna sunyi tsami" dan dariya Mami tayi ta tashi tana
gyara zaman babban gyalen jikinta tabi bayan Baaban harara ta watsa mai dasuka hada ido da
sauri ya dauke kai, saida ya waiga yaga sun fita sanan yawuce gaban drawer dake dakin
yajawo yana kokarin ciro wani drip dake ciki ya juyo da kai ya kalleta fuska adaure ganin daga
fitar su tasoma matsar hawaye yace "ke!" kin kallonshi tayi dan wlh kallonshi kadai tadamata da
hankali yake barin ma dazu data tashi akace operation yamata ga wajen na bala'in mata zafi
ganin su Abba ne yasa ta mugun daurewa. "ke!" yakara daka mata tsawa daidai lokacin ya
matso wajen gadon, arude ta kallai hawaye na gangarowa daga idonta yawani daure fuska
yace "agidan ku ba'a koya miki gaisuwa bane" da kyar ta iya bude baki heart dinta na racing
tace "in ina kwana" tsaki yaja ya kalli cup din tea hanunta ganin ko rabin tea batayi ba yay tsaki
yace "malama finish dis tea nasamu nabaki maganin ki inba hakaba inbar wajen dinkin yay
tsami daga bayama ya rube" yakara she yana wani irin hararan ta kafin yajuya yafita daga
dakin, pharmacy dinsu yaje dakan shi ya faffadi magungunan da xa'a kawomai ya ciro ATM card
dinshi yabiya da POS sanan yadawo dakin, tadan sha tea dudda bata shanye ba, wani cup ya
dauka yadebo ruwa a dispenser dakin na zafi ya sirka dana sanyi ya danyi dalam dalam ya
mika mata yana dauke kai, ahankali hanunta har rawa yake ta karba zatakai baki tsawa yadaka
mata "ke wai nace kisha ne, God she's so so dull" yay tsaki yadauko ledan ya ciro magungunan
dazata sha kusan kala biyar, ya babbalo tablet da capsules din yasaka ahannu ya mika mata,
ahankali ta mika hannu tana goge hawaye da bayan dayan hannunta ya saka mata, sosai take
kuka wanan karan harda kara, tasa dayan hannunta tana kirga uban kwayoyin maganin daya
bata tasha kaman zararra, guda goma shadaya, dago kai tayi ta kallai kafin tasake fashewa
dawani irin mugun kuka mara sauti dan ko nishi mai karfi bata yi sabida ciwon, sai ta kalleshi ta
kalli magungunan tafin hanun nata tafashe da kuka dan har ga Allah bama tasan ta yanda zata
hadiye duka magungunan nan abakin taba ita bama tasaba shan kwayoyin nanba jike jike Baba
kemata, dan murmushin gefen baki yay saikuma ya zauna akan gadon kusa kusa da ita da
sauri ta makale jikin bango, hanunshi yasaka akan hanun nata ya kwashi duka magungunan ya
rike kafin ya ciro biyu ya mikamata, karba tai atsorace takai baki takai ruwa tana bata baki
tasha, sake mika mata biyu yayi tasha, yasake mika mata biyu tahadiye, zai kara bata biyu
tafashe da kuka tana girgiza mai kai, daure fuska yay hakan yasa ta karba ta hadiye da kyar ya
mika mata ukun dasuka rage babu alamun wasa akan fuskar shi da kyar tasha kaman zata
suma ya karbi cup din ruwan ya ijiye yana duba agogon hanunshi kiran Rolex, saida tai exactly
5 minutes sanan ya mike tsaye ya dauke cup din tea data rage ya ijiye akan table ya kalleta
yace "ke kwanta inason na duba inda na fede" ko kallonshi batayi ba saima dauke kai datayi
tana kokarin hadiye hawayen dake shirin zubowa, takowa yayi yadaura hannunshi akan
kafadun ta da sauri ta kallai kirjinta na bugawa ahankali ya kwantar da ita ya daura kanta kan

filo batare daya janye idonshi daga kan fuskarta ba, runtse ido tai da sauri sabida wani irin
azaban dataji, hannun ya cire daga kafadar ta ya dage rigar sama, bugawan da kirjinta yayi
harsaida yagani daga cikinta, wajen dinkin yabi da kallo kusan na 3mnutes kafin ya mike tsaye
ya makala drip din daya dauko akan karfen makalasu yamata fixing drip din yadauko wasu
allurai yay acikin ruwan 8sanan yadawo bakin gadon ya zauna yana kallon wurin aikin kafin yabi
cikin gabaki daya da kallo yanda yay flat ga fatar looking fresh sai glowing yakeyi, ahankali ya
mika hannunshi ya daura akan dan cibiyar ta, da sauri ta bude ido ta kallai atsorace ita shima
yake kallo akasalan ce yace "wat?" shafa cibiyar yacigaba dayi ahankali kafin ya gangara da
yatsar shi zuwa inda yay dinki yana zagaye wurin hanunta ta daura akan nashi tana wani irin
wahalallen kuka, akaro nabiyu yakara kallonta murya kasa kasa yace "wat?" da kyar ta iya bude
bakinta tace "zapi" hanunta data daura akan nashi yabi dawani irin kallo hakan yasa tai yunkurin
janye hannun da sauri ya rike hanun yana kallon fuskar ta kafin ya maida dubanshi ga hannun,
ahankali ya sa hanunshi ya shafa tsakiyar fatar hanun nata yana feeling yanda hanun keda
wani irin taushi kaman hanun jariri, bin jajayen yatsun ta dasuka sha lalli yay da kallo kafin
ahankali yakai yatsar wurin bakinshi yana kallon yanda idanunta ke fitar da hawaye.
[7/20, 12:30 PM] +234 803 238 4602: ♦♦ *SANGARTATTCE* ♦♦



Maman Abd Shakur

41 - 42

Ahankali yasa yatsar cikin bakinshi yana wani irin tsotsar yatsar kaman yasami minti, sosai
takara karfin kukan ta sabida yanda takejin wani iri gashi yaki bata daman fizge hanun,
knocking kofar akayi hakan yasa yacire hanun daga bakinshi ya maida ya ijiye yana kallon
fuskar ta da idanunshi dasuka chanza launi yay hanyar kofar yabude wata Nurse ce Amina dan
Sameera tagama night wanan tai taking over, gaidashi tayi batare daya amsaba yace "ki cema
Dr Ibrahim ya dubata dan i will not be available today" yana fadin haka yasa kai yafice daga
dakin office dinshi yakoma yadau car keys da wayarshi yafita daga office din bayan ya kulle,
wajen parking yaje ya shiga motar shi yabar asibitin gidanshi ya wuce direct yay parking yafito
ya shiga ciki, akan dogon kujera ya kwanta jin kaman ma zazzabi zazzabi na neman rufeshi,
wayarshi ya lalubo daga aljihun wando yay dailing number Meram saida kiran yakusa katsewa
ta dauka tai shiru, dan murmushi yay dan tunda taji labarin yay aure tadau zafi sosai, dan
murmushi yay yace "ina jiran ki agidana now" zatai magana ya katse wayar tareda kara gyara
kwanciya ya sanya hannayenshi abayan kanshi yana kallon POP, tashi yay zaune ya dunkule
hannu ya daki iska angrily, kafin ya dafe kanshi, tashi yayi yawuce bedroom dinshi yafada kan
gado ya lumshe ido. Wajen 30min Meram ta dauka kafin tazo tana sanye cikin wani open neck
white top me spaghetti hand sai strap belt long skinny pant navy blue, braids ne akanta masu
tsawo babu dan kwali tafito daga motar taci uban hill tai cikin gida bayan tai parking rike da yar
jakarta na Louis Vuitton tana taku daidai ta shiga gidan tana tauna cingum ta mugun daure
fuska, ganin baya sitting room yasa tai bedroom dinshi yana kwance idanunshi biyu saidai duk
sun kankance tsayawa tai daga kofa tana kallon shi yanda maroon t-shirt din jikinshi ya mugun

yimai kyau tai kewanshi bakadan ba itama tasani amma maisa zai yi aure aboye bayan yasan
yanda take sonshi, dan juyo dakai yay ya kalleta sabida yanda jikinshi yabashi ana kallonshi,
kafeta shima yay da ido batare dayace mata ta shigo ba, dauke kai tayi daga kallonshi cike da
basarwa tace "why are u calling me? Bani ka yaudara ba kana using dina sanan kaje kai auren
ka, ancemin ma yarinya kaje ka auro, very decent ba irinaba, ni kawai am just ur machine ko, u
use me as u pleases, hmmm har ka gaji dacin amarcin ne ka kirani dama..." "Ke!" ya daka mata
tsawan dayasa tai shiru, tashi yay ya zauna abakin gado da idanunshi dasukai jajir ya nuna
mata kofa yace "out" bude ido tayi tana kallonshi cike da mamaki yasake nuna mata kofa yace
"i said out kema kinsanni bana rokon abu, are u expecting me na lallaba ki dannai aure, dama
chan ni saurayin kine? Okay is over Fita daga nan, i don't need u as well rubbish" yaja tsaki rai
abace, fashe mishi tai da kuka ganin yanda yaci serious tafado jikinshi tana kuka ta kankame
shi tana kissing face dinshi tace "am sorry Ayaan please karka rabu dani, naji na yarda i will be
ur side chick, have me" ta wurgashi kan gado yanda jikinshi yay laushi ne yasa yatafi shima luu,
nan ta shiga aika mishi da sakkonni kafin ya biyemata dan dama yana cikin sananin bukata.


Tunda ga ranan bai kara komawa hospital dinba kiran Abba ma yayi yace "yatafi wani
conference meeting a Abuja" daganan ya kashe wayarshi dukama dan bayason damu. Dr
Ibrahim ke kula da ita bayan 5 days ya sallameta aiko taji dadi dan tagaji da asibitin ga dinkin ya
fara warkewa dan jikinta nada kyau sosai da kanta zataje bayi tai alwala tai wanka kawai dai
bata daukan abu mai nauyi ne kwata kwata, gidan su Abba aka wuce da ita sabida takara
warkewa kafin akaita gidan mijinta idan yadawo.

Yau satin ta daya agidan taji sauki sosai yanda Abba da Mami keji da ita ita abinma har kunya
yake bata.
Tana kwance hadadden adakin ta lullube da bargo ta daura kanta akan cinyar Baaba daketa
fama da Mami ita gaskiya zata koma yau Mami namata dariya, sallama Abba yayi ya shigo
Mami tace "yauwa Alaji kajifa wai tadage tafiya zatayi yau" kaman Baaba zatai kuka tace "to
Alaji taji sauki dan Allah kubari natafi nabar Muji shi kadai agida" itadai lumshe ido tayi kaman
tana bacci dan batason Baaba ta tafi dan ita take gani takejin dadi, Alhaji yace "to to to shikenan
ai, amma ki shirya" ya kalli Mami yace "muje mu kaita taga gidan yarta ko anjima inmun dawo
sai nasa driver ya kaiki zaria" washe hakora Baaba tayi Alhaji yafita yana dariya, tashi tayi tana
kallon fuskar Bilkisu data lumshe ido ta kalli Mami tace "kinga kasar nan ashe bacci tayi ana
hira" dariya Mami tayi tace "yata ba kasa bace kibarta tai baccin ta tunda fita zamuyi" hijabi
Baaba ta dauka suka fita da Mami tare suna hira a down stairs suka hadu da Abba da big Mum
da itama ta shirya duk suka shiga mota Alhaji yajasu suka fita daga gidan. Gidan yarage daga
ita sai yan aiki.

Wani ubansu gida Abba yakai Baaba, sakin baki kawai tayi tana kallo dan gani tayi gidan ma
yafi gidan su Abban kyau, horn Abba yayi gateman yazo yabude suka shiga, babban compound
ne da aka bi bangon da flowers, sai runfan parking motoci sukai parking suka fito, bayan gidan
suka fara zuwa wani ubansu garden ne daga gefe daya kuma wani hadadden swimming pool
ne, ta kofar kitchen dake garden din sukabi suka shiga kitchen Baaba dai kasa rufe baki tayi

yanzu Bilkisu tane zata zauna awanan gida irin gidan shugaban kasa lallai Bilkisu akwai goshi,
fita daga kitchen din sukayi sukai parlor komi white and sky blue harda kujeru, center carpet da
labulayen, ga gefe kuma wani babban fish bowl ne kifaye sai wasa suke aciki yanda Baaba ta
dinga yi yasa suka dinga mata dariya sukai upstairs inda wani parlor ne awurin sai dakuna uku
na farkon suka shiga komi off white ne, sai kuma dayan dakin da akai brown and milk dayan
kuma akai brown zalla, kafin su kara komawa wanda akai brown and milk akwatunan ciki guda
24 Mami da Big Mummy sukahau bude mata shikuma Abba yakoma kasa danyi waya, sai
kallon akwatinan Bilkisu take tana mamaki, Mami tace "dazaran yadawo daga Abujan zasu tare
in sha Allah" nan fa Baaba ta bingile da ciro kaya tana dubawa tasami na bada labari a zaria.

Ahankali tayaye bargon data lullube dashi dan takasa baccin, suna fita taji gidan yamata wani
iri duk ba dadi, mikewa tai tsaye tana sanye da soft jersey drape skirt black sai pink crop top
daya dan saukan mata kasa amma bai rufe cibi ba sabida ma ance tadinga barin wurin dinkin
nashan iska ne yasa Mami ta siyo mata irin kayan yakin, skirt din yabi jikinta sosai ya fito da
shape dinta dudda bai wani kamata ba, rigar kuma tamata chachas ajiki tareda kara bayyana
kyan surarta, dan black hulane akanta wanda yadan zame baya gashinta da aka tsefe aka
gyara mata ya bayyana duk ya kwanta yana shining, wayarta tadauka tasaka bathroom slippers
white daya bayyana fararen dogayen yatsun kafarta tafito tana tafiya ahankali harta sauko down
stairs babu kowa afalon gashi bata iya kunna makeken tv bangon suba, dan tsaki tayi tai hanyar
fita daga dakin tafito tsakar gida sai kalle kalle take ganin babu kowa sai uban motocin dasuke
apake, ahankali take tafiya tana dan yatsine fuska dan rabon ta da tsakar gidan tun randa aka
sallamota daga asibiti, ahankali take ta tafiya tana zagaye gidan harta ganta a garden, bin wurin
tai da kallo yanda flower din wurin sukai kore yirr ga watering can akasa, cigaba da tafiya tayi
tana shafa flowers din tana murmushin dake lobar mata da dimple, karan katca dataji yasa
tadan daga kai ta kalli saitin inda taji karan wani worker gidan ne dake sanye da uniform yana
bama wani dan biri haka dake sanye da kaya ajikinshi jeans da riga ayaba, an daure burin ajikin
bishiyan mango da chain, ware ido tayi cike da mamaki harda dan saurin ta takara so wajen ta
kalli mutumin dayake ta kallonta sanan ta kalli birin dake kallonta shima yanacin banana, ta
nunashi da hannu tace "laaa monkey dama da monkey agidan nan, monkey wayene?"
murmushi mutumin yayi yana barema birin wani ayaban yace "na oga ne wlh, bakiga yanda
yakeson monkey nanba, shima monkey haka yake sonshi kome yace yayi saiyayi" murmushi
tayi batare data matso ba dan tsoron biri take tunda aka taba labari a school wai biri nason
mata yanxu ma dan taga akulle yake da kacah ne saisa tazo tana kallonshi, ganin yanda aka
samai kaya masu kyau harda sarka awuya sai abin yabata dariya ma, mai aikin yacigaba da
kallonta yana bama birin ayaba yace "amma ke

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login