Showing 102001 words to 105000 words out of 124573 words
Chapter 35 - Sangartacce Book Complete Pdf by Maman AbdulShakur.pdf
kukan, murmushi yamata asanyaye, sake washe mai baki
tayi tasake rungume shi saikuma tasake shi ta sauka daga kan jikinshi ta mike atsaye
agabanshi tana kallon fuskarshi shima ita yake kallo a sanyaye, hannayen ta ta daura akan
kafadar shi tana washemai baki ta dugo da kanta ahankali tana kallon kwayar idonshi shima ita
yake kallo kaman yau yafara ganinta, daura lips dinta tayi akan nashi da sauri ya chapke tareda
rungumota jikinshi sosai yana wani irin sauke ajiyar zuciya, daukar ta yayi chak ya kifata a gado
yasa hannu ya zuge mata zip din doguwar rigan ya cire doguwar rigar ya yar shima cire kayan
jikinshi yayi yahayo gadon, da sauri tafada jikinshi ta kankame shi sake hada bakinsu yayi yana
wasanni da ita kafin ya shige ta yana yanda yaga dama da ita.
Wuraren goma ya shigo garin kano, taxi ya dauka ya bashi address din hospital din da Ayaan
yatura mai, goma da kusan 15 minutes taxi yay parking a hospital din, ya shiga yana kalle kalle
ahankali yaciro wayarshi yay dailing number Ayaan amma ba'a dagaba akaro na uku ya dauka
murya chan kasa yace "please kabani 10min am coming" bai kawo komiba Aaman yace "okay
ina reception" , dagata yayi yakaita bayi wanka yamata agurgurje yafito yana tsane gashin
kanta da towel sai kallonshi take, dan murmushi yamata, yamata kiss a kumatu yace "thank
you, Allah miki albarka kin sa nasami natsuwa" hanunta ya daura akan towel din ya dauko mata
wani bakin doguwar rigan Abaya ya shiryata tsaf yasaka mata dogon hijabi daya kai mata guiwa
pink, yasaka mata loafers sai kallonshi take sanan shikuma ya shirya cikin Jean da riga white
yasaka takalmi yadau jakarta da magungunan ta yadawo yarike mata hannu yace "let's go" fita
sukai daga dakin, a reception yaga Aaman zaune yana danna waya, kaman ance ya dago kai
ya gansu suna tahowa hanunta cikin nashi da sauri ya kori abinda kemai yawo a ranshi ya mike
tsaye yana dan murmushi.
Hannu Ayaan yamika mai suka gaisa da ido yamai alamu suje waje, wajen motar shi sukaje,
ahankali Ayaan yace "duk duniyar nan a yanzu kai kadai nai trusting, koda yau na mutu nasan
tana good hand, please ga wife inaso kabar garin nan da ita harsai naci nasaran kubutar da
iyayena bazan tsaya jiran police ba" bai jira mezaice ba yajuyo ya kalli Bilkisu da shi taketa
kallo, cupping face dinta yayi ahankali yace "Baby follow him he's going to take care of you for
me kinji, be a good gurl, I love you so so much wife" lumshe ido yayi da sauri, patting kafadar
shi Aaman yayi ahankali yace "I can stay with you lemme help you Bro, inada wata sister dake
aure a garin nan zamu iya boyeta a gidanta" girgiza kai Ayaan yayi yace "kai nakeso ka
kulanmin da ita, I want her out of kano, I don't want to risk her life in anyway tana last stage na
recovery ne, please please take care of her for me" da sauri yay wurin motar shi baya ya bude
yasaka jakarta ya rufe yadawo yana mata murmushi yakaita gaban mota yace "kibishi zanzo na
daukeki don't cry okay" washe mai baki tayi, ahankali ya sumbaci gaban goshin ta yasaka ta
aciki ya kullo yadawo inda Aaman yake a tsaye sai binshi da kallo yake hanunshi Ayaan ya
kama ya saka key mota da magungunan ta yace "once kakai kabata magungunan nan twice a
day ne bacci yake sata, ga key kayi parking motar a Airport leave d key with security, I will never
forget dis favor" da sauri ya juya zai wuce Aaman ya kama hanunshi, ahankali ya tsaya chak
batare daya juyoba zagayowa ta gabanshi Aaman yayi yay hugging nashi yana buga kafadar
shi yace "all d best, I promise to take care of her, Allah yabaka sa'a, ya kubutar dasu" Ameen
Ayaan yace yana kokarin hana kanshi kallon motar, ahankali Aaman ya sakeshi yajuya ya bude
motar ya shiga, da sauri ya juya baya bayason ya kalleta dan kuka zaiyi, Aaman yaja motar
sukabar asibitin.
♦♦ *SANGARTATTCE*♦♦
Maman Abd Shakur
86 - 87
Har suka shiga titi waige waigen shi take hartazo tadena ganinshi, kuka tafara mara kara ahaka
har sukakai airport yay parking motar yaciro jakanta ya zagayo ta inda take kukan ta ya bude
mata kofar yana kallon ta, ahankali yace "fito" fitowa tayi tana kallen wajen tana kuka saikuma
ta kalleshi tafashe da kuka sosai, girgiza mata kai yayi cikin muryan lallashi yace "stop crying
gashinan zuwa, zomuje, goge hawayen" share hawayen tai da sauri, yabama security key suka
shiga cikin airport din booking yay musu kafin suwuce departure hall dan, in 15minutes time
jirgin su zai daga, zama sukayi yaje yasiyo mata popcorn yakawo mata karba tayi sai jujjyawa
takeyi tana kalle kalle saida aka fara boarding sanan suka wuce suka shiga jirgin, jirgin yadaga
sama.
Sha biyu daidai na rana jirginsu ya sauka a Abuja Ummy ne tazo da Mota daukan su tana ganin
Bilkisu da gudu tazo ta rungumeta tureta tayi tanason tafara kuka ya harari Ummy yace "ke
kirabu da ita batada lpy, ban key" mikamai key motar Ummy tayi bayan ta kama hanun Bilkisu
dahar tafara kuka, karba yayi ya shiga gaban motar Ummy tabude musu baya suka shiga ta
rufo sukai gidansu dake wuse. Hadadden gidane babba sosai koda sukakai baiwani sha
wahalan shawo Kan Mum dinsu ba, bakaramin tausayi Ayaan din ya bata ma tai musu addu'a
sanan ta lallaba Bilkisu da kyar taci wani abu Aaman yakawo maganin ta Mum tabata tasha Sai
kuka take, sanan Ummy takaita dakinta cikin minti biyu bacci yay awon gaba da ita, fitowa
Ummy tayi hakan yasa Aaman yace "where's she" zama tayi kusa da Mum tace "tai bacci" Dan
ajiyan zuciya ya sauke sanan ya kalli agogon hanunshi yatashi ya kalli Mum yace "bari naje,
zan kai Usaida hospital zamuje muyi blood test su genotype and d rest" murmushi Mum tayi
tace "saika dawo son" ficewa yayi daga gidan bayan ya Kira Usaida yace mata ta shirya.
**************
Da saurin shi ya shiga office dinshi yana share kwalla wani irin kewanta da shaukin ta ke
shigan shi sosai, gadonsu ya kurama ido dan gani yake kaman zai ganta, kayan jikinshi yacire
ya shiga bayi yayo wanka yana fitowa ya shirya cikin wani bakin riga bodyhug da bakin wando
bakaramin kyau yayi ba kayan sun fito da hasken fatarshi sosai, sneakers yasaka yadau wallet
da waya yafice daga office din bayan ya kulle, taxi yatare ya shiga.
******************
Babban gidane da ba'a gama ginewa ba, dan Mami bataga hanya ba sabida wani bakin yadi da
big Mum tarufe mata fuska dashi, zaune take akan kujera tun isowan su ahaka take an daure
mata hannayenta tabayan kujera da kafa, an taushe mata baki sanan anrufe fuskarta da bakin
kyalle, muryan big mum kawai takeji dawasu maza, addu'a kawai take aranta Allah ya kareta
daga shairin big Mum sanan ubangiji Allah ya karemata Ayaan da Bilkisu, alamun tafiya mutane
dayawa taji ana shigowa inda take batasan meke faruwa ba tadai ji Big Mum na cewa ku kulle
shi da kyau, saikuma wuf aka yaye bakin abin daya rufe fuskarta, haske ranane bau awajen
ahankali tabi wurin da kallo gini ne babban gaske da ba'ai plasta ba kawai block ne saikuma
katakwayen roofing sama da aka jera kaman ana shirin saka kwano ne saikuma ba'a sakaba,
ahankali ta juyo da kanta ta kalli Big Mum dake zaune kan wata kushin ita da pilot din Abba
tanamai murmushi, kwalalo ido Mami tayi tanason tai magana amma ba halin yi sabida taushe
mata bakin da akayi, wani irin mugun kallo Big Mum ta watsa mata saikuma ta kalli Bala dake
tsaye shida wasu samari guda biyu tace "budemai fuska ya ganni Bala naga ya farka yana
motsi da kafa" da sauri Mami ta kalli gefenta kirjinta na bugawa wakuma aka kamo ko Ayaan
ne, Alhaji! Tafada aranta tana wani irin salati da sallallami tana sanar da ubangiji halin dasuke
ciki, kwalalo ido shima Abba yayi yanaso yay magana ganin yanda aka daddaure Mami amma
ba hali kaman daga sama yaji muryan big Mum tace "Alhaji" da sauri ya juyo dakai ido da ido
sukayi da big Mum da pilot dinshi suna wani irin kallon juna, murmushi Big Mum tayi tawani
lashe baki tace "dan ka yazaci yanada wayau yasa polisawa suncika airport yazaci anan zaku
sauka ne? Hahaha, karkai mamaki fa, bawani abu yasa nai hakaba sai dukiya, dukiyar ka kawai
nake bida, nariga nafada ma danka ya maida duka dukiyoyin ka sunana sanan ya saki yarana
da aka kama na uku kuma yabani Bilkisu na kashe dan itace taja asirina ya tonu haka bazan
taba yafe mata ba, ayanzu dai nabashi awa ishirin da hudu ko my man" tai maganan tana shafa
gemun pilot dake sanye da uniform yana kallonta, girgixa mata kai yayi tareda fuzar da iska
yace "hajjaju ta aganina awa ashirin da hudu sunyi yawa fa, ko Ina neman mu ake Kuma kinsan
atsakiyan filin daji nai parking koda yaushe wani abu kan iya faruwa, ki rage lokacin, shidan
yamma nayi ki kirashi yabamu abinda mukeso muje mu shiga jirgi mubar garin nan. Gyada kai
tayi ta mikama Bala hannu alamun ya bata wayanta, kawo mata wayar yayi Abba duk yanabin
su da kallo da idanunshi dasukai jajir kokarin magana yake amma ba hali, kunna wayan tayi
bayan tasaka wani sabon layi ya sanya mata nashi, number Ayaan tai dailing daidai lokacin
Ayaan da CP sun shiga dakin da ake tracking number, wayar yaciro yana kallon number da
sauri yay picking yasaka a speaker yanama me tracking din alamu da ido, dan hakanan yaji
aranshi big Mum ce, picking yayi yasa a hands free wani irin dariya tayi tace "bazaku taba iya
kamani ba duk sim din dazan kiraka dashi dazaran nagama magana nake ballawa, nakira ne
nafada maka nafasa baka awa ashirin da hudu karfe shidda daidai zan kira nafada maka inda
zakaje ka ijiye Bilkisu" katse wayar tayi da sauri Ayaan yay wurin computer inda CP ke tsaye
akan me tracking number yace "how far" girgixa mai kai CP yayi alamun ba'a samuba tsaki yayi
hankali atashe, fita yayi yawuce masallaci alwala yayi ya shiga yabi jam'i yay azahar yana
fitowa motar shi ya shiga ya zauna yaciro wayar shi number Bala dayariga yay saving yaciro
yay dailing akashe, wani irin ihu yayi ya daki kujeran motar, kunna motar yayi ya wuce MTN
office wani abokin shi ne babba awajen hakan yasa ya wuce upstairs direct knocking yayi ya
shiga abokin shi mai suna Musa na ganin shi yay dariya yace "Dr ana ganin ka dama" dan
murmushi kawai yayi ya zauna Musa yace "why is ur face like this" girgiza Mai kai yayi yace "I
need a favor" wayar shi ya ciro yajawo wata yar memo dake gabanshi da byro ya rubuta Mai
number Big Mum, da number Bala ahankali yace "please track this two numbers for me in
hakan baiyuba inaso kabani any other number da masu layin suke amfani dashi sanan amin
tracking dinsu" yanda yake magana yasa abokin nashi yatashi da sauri ya bude yar fridge din
office dinshi ya dauko bottle water yadawo ta gabanshi ya bude yabashi, kasa karba Ayaan yayi
saima kafe goran dayayi da ido yakasa karba dudda yanajin kishi, hanunshi mutumin ya kama
ya saka goran ruwan aciki ahankali yace "Dan Allah kasha abokina" kafawa abaki Ayaan yayi
yasha kadan sanan ya ijiye, ahankali mutumin yace "tashi muje adubama dudda dai kaki
gayamin mecece matsalar" fita sukayi daga dakin, wani office suka kara shiga, Musa ya
mikama wani dake aiki takardan yace "binciko mini wayan nan numbers din" karba yayi ya
kwafe number yana danne danne a system din sai yace "sunan layi daya Saratu gwanaye
dayan kuma Bala Mubarak, banda wanan layin Bala nada layi biyu kuma daya bude da sunan
nan" da sauri Ayaan yaciro wayar shi yace "kiramin numbers din please" kira mishi akayi ya
kwasa yajuyo yace "please ku gwada min tracking din numbers din konawa ne zan biya please,
zan tafi yanzu once kunyi kutaramin address din tawaya na" yanda yake maganan ne yasa
Musa yace "wats happening Ayaan?" dauke kai yayi sabida hawayen dayake ji ahankali yace
"anyi kidnapping su Abba ne" da sauri yafita daga wurin bakaramin tausayin shi Musa yaji ba
Ayaan mutum Mai kirki tun kafin yasami aikin nan lokacin da matarshi ke labour Ayaan yamata
CS kyauta sabida baida kudi, da sauri ya kalli Yaron yace "don't rest saika samo location dinsu"
yafita daga office din dukya damu.
Ahanya ya tsaya yay la'asar kafin ya wuce gidan su, gashi nan kawai kaman zararre, parking
yayi a compound ya wuce shashin big Mum, hargitsa dakinta ya shiga yi yana neme neme ko
zai sami any clue, daga bayama rigarshi yacire yay hanging akofa yazo ya daga katifar ta ya
daga gado yana dube dube, yakoma wajen drawers din bedside yahau bubbudewa, wardrobe
dinta yakoma yana ciccciro kayanta yana wurgawa kasa kaman zararre, kaman da kayan yake
fada, finciko kayan ya dinga yi yana yarwa dan kara dayaji akasa yasa ya kalli kasan da sauri,
wayansu kayane daya zubar hade dawani file babba, da sauri ya tsugunna ya dauko file din ya
bude takardu ne daban daban, ahankali yakoma gefen gado ya zauna yana duba takardu falle
falle yawancin su takardun gidajen Abba ne da papers din filaye wanda duk yasan da zamansu,
idanunshi ne suka sauka akan wani takardan owernship din gida wanda sunan hajiya Saratu ne
ajiki, da sauri ya cigaba da budewa yana going through d content, rufewa yayi yana dan tunani
yaushe which house is this? Address din gidan ya duba hakan yasa ya saki file din anan kasa
yaja rigarshi daga kofa yasaka yafice harda dan gudun shi, yana shiga mota kiran CP na
shigowa wayarshi da sauri ya dauka yana driving, daga ta dayan bangaren CP yace "Ayaan
kazo headquarter sabida dazaran takira ka mu samu muyi tracking dinta down, this is five thirty
kai sauri all team dinmu damuka zuba babu wani vital information, munje gidan da yaran
damuka kama sukafada mana suna zama suda Bala amma ba'anan suke ba, hurry up karta
kiraka kana hanya".
Yana shiga office din da ake tracking number kira na shigowa wayarshi alamu CP yamai dayay
picking hakan yasa yay picking yasaka a handsfree, cikin kakkausar murya Big Mum tace "am
not going to repeat myself Ayaan ko abar tracking wayar nan kona harbi baban ka, ka ganni nan
gani gashi sai kallona yake yana son yay magana amma na kulle mai baki" tai maganan tana
wani irin zagaye Abba tana goga mai bakin bindiga awuya, juya ido tayi tace "au bakaji ba
kenan, stop tracking my phone, tusss" Big Mum ta harbi Abba akafan haggu tasa hannu ta
tunbuke tsumman da aka kulle bakin Abba dashi, wani irin ihu azaba Abba yayi har cikin
zuciyan Ayaan yaji ihun dafe zuciyar shi yayi ya kalli CP amugun rude yace "stop, I said stop
tracking d Goddamn number zata kashe min Pops" kafa yasa yawani irin tarwatsa laptops din
jikinshi na rawa yana karajin yanda Abba ke ihu, dan kafa Big Mum tasa ta take inda ta harbai
sabida yay ihu da kyau Ayaan yaji, Mami kam sumewa tayi ganin yanda big mum ta harbi Alhaji.
Wani irin dariya big Mum tayi ta mikama Bala dake kusa da ita bindigar ta zauna akan kujera ta
daura kafa daya kan daya tana kallon fuskar Alhaji yanda wahala yau yasa tsufan shi yafito
sosai dan da baka wani gani sabida cin dadi dakuma kudi, maganar Ayaan ne ya katse mata
tunani, sosai muryan shi ke breaking yace "Big Mum please, please don't kill my Pops, andena
tracking din kome kikeso I will do it amma kifara hadani dashi inji muryan shi if he's still alive
shida Mami na sabida nayarda baki kashemin su ba, Pops" ya kwalama Abba kira ta wayan
arude, Abba da kaman ya suma tsabagen azaba jin muryan Ayaan yasa yadan bude ido yana
bin wurin da kallo, wani irin murmushin keta Big Mum tayi ta mikama Bala wayar bayan ta karbi
bindigar tace "sashi awaya" karban wayan Bala yayi yawani finciko kan Abba kaman zai karya
saida Abba yay Kara ya kara wayan a kunen shi da sauri Ayaan yace "Pops are you okay, zan
bata koma me take so am going to save u, Popsy be strong for me okay, Ina mamina, a ina ta
har...harbe..k" yakasa karashe maganan sabida kuka jin yanda Abba ke wani irin nishi, kukan
shi yasa wani jarumta yazoma Abba yay murmushi yace "is okay my Boy am fine, karka sake
kabama makirar nan dukiyata, dakabata dukiyata gwara ka zuba musu petrol ka kona, karka
sake ka bata Bilkisu stay with your wife, don't give her anything, dan koka bata kasheka zatayi,
da abu yasaman min kai Boy gwara in mutu, idan wanan shine saduwar mu takarshe na yafema
kome kamin aduniyar nan, ga Mamin kanan she's unconscious" sosai Ayaan ke kuka ya
kankame wayar a kirji yanajin muryan Abba, CP kuma yadauko wani sabon laptop suna kokarin
tracking, Bala ne yazo zai fizge wayar Big Mum ta hanashi tana murmushi tace "barsu suna
bidding farewell ne shima yasan he's not leaving here alive" wani irin kallon ta Abba yake cike
da tsana saikuma yakara wayan abakin shi da wani irin mugun sauri dakuma karfin bala'i yace
"Boy muna wani uncompleted buildi...." tus tus Big Mum tamai harbi har biyu akafar daman shi
amma dayace ta shige shi, Bala kuma ya zubamai wani irin naushi ahanci dayasa ya sume
warwas.
Tashi tsaye Ayaan yayi kaman mahaukaci yana ihu a wayan "Pops Pops Pooooopsss" yawani
irin ja sunan kaman wanda ya zare, maganar big Mum yaji ta wayan tace "nabaka 15 minutes
take Bilkisu, documents, da yarana zuwa kasuwar kwari wurin yan kaji ka ijiye su anan kajuy.."
Ayaan da