Showing 27001 words to 30000 words out of 124573 words

Chapter 10 - Sangartacce Book Complete Pdf by Maman AbdulShakur.pdf

M Shakur   

09 Nov 2025

3882

mekakeyi da har yanzu baka tafi ba"
ajiye tawadar yayi yadan matso kadan dan da gap sosai a tsakanin su ya gyara tsayuwa da
kyau sanan yace "zanje na siyo fentin da za'ama dakin mune, kinga gidan mu na chan kauye
badai kyau ba, akwai bishiyar mangwaro, kashu, da gwaiba a tsakar gidan mu harda na

agwaluma ma" zaro manyan dara daran idonta tayi tace "da gaske" gyada mata kai yayi hakan
yasa tai murmushi tana dan kare fuskar ta da hijabi ahankali yakira sunanta "Bilkisu" dago kai
tayi tace "na'am" "kauyen mu akwai dadi saima bayan auren mu munje chan zaki gani kinaso
na kaiki rafi?" murmushi tayi tadaga mai kai cike da kunya yay yar dariya yace "shikenan
gimbiyar mata ni natafi sabon gari siyo fentin" murmushi tamai tace "adawo lpy" "insiyo miki ice
cream?" a kunyace ta daga kai dariya yasake yi yace "wanan dan bakin naki ya iya shan ice
cream ko gimbiyar mata" da dan gudunta ta juya zata zata bude kofa ta tsaya chak numfashin
ta na barazanar barin kirjinta ganinshi tsaye rike da waya yana mata wani irin kallo, Allah kadai
yasan tun yaushe ya shigo zauren dan daga ita har Isyaka babu wanda ya lura dashi, wani irin
kallo yamata kafin yama Isyakan dashima ya tsaya turus yana kallon bakon Malam, wani irin
dogon tsaki yaja musu yace "bunch of villagers" yafita daga zauren ya jingina da mota yana
tattaba waya, bude kofa tayi jiki asanyaye ta shiga cikin gidan nasu batare da tama sake
waigawa bayaba, dakin Umma ta shiga ta zauna agefen Raiyana dake tsince shinkafa tana
maida numfashi ganin zuciyarta nata bugawa.

Yakai kusan 20mins awaje yaga su Malam sun rako su Baba, idanunshi ya sauke akan Pops
ganin yanda duk jikinshi yay sanyi yakoma kaman mara lpy lpy yasa yaji duk wani iri, lallai
wanan abu ya shiga ran Popsy sosai, sallama su Malam suka musu shikuma ya kalli Abba
dayay wani iri ahankali yace "Pops kutafi ni anjima zan dawo sabida anyi inviting dina zuwa
wani induction ceremony anan shika" asanyaya Abba yace "to saika dawo" yabude mota ya
shiga su Baba Suleman man ma suka shiga driver yajasu suka bar wajen bin motar yay da kallo
kafin ya bude dayar motar ya shiga yabar anguwan.

Wuraren la'asar Isyaka yadawo bayan ya sauka daga bus yafara dandarowa layinsu, tunda
yake tafiya yaketa kallon wata bakar van dake pake agaban wani gida anan anguwan tasu,
gadaishi gilashin motan bakake dan haka baya ganin naciki, tafiya yaciga ba dayi anatse kaman
daga sama yaga wasu samari uku sun sha gabanshi, kafin yay tunani ko yama kawo wani abu
aranshi yaga sun fesamai wani abu kaman turare a fuska daga nan kuma bai sake sanin inda
kanshi yakeba.

Da sassafe wanan bakar Van dinan tai parking abakin layinsu aka bude yafito, yana fitowa Van
din yatafi, ahankali yadinga tafiya harya karaso gidansu su da Malam yaci karo akofar gida yace
"ina ka kwana Isyaka?" murmushi ya kakalo yace "Allah taimaki malam naje nai fentin gidan ne"
kallo malam ya bishi dashi kafin chan yace "maiya faru to duk na ganka wani iri?" murmushi yay
yace "Allah taimaki malam bansami bacci bane, gabaki daya aiki na dinga yima gidan jiya"
Malam yay murmushi yace "ayyo to jeka huta Allah maka albarka" da Ameen ya amsa kafin
yawuce ciki.

Wasa wasa fa biki ya kankama Amarya gyra take sha ba kadan ba, Mama nayi Umma nayi
Baaba nayi, tai wani irin fresh tai bulbul fatarta dakeda mugun taushi yakara wani extra taushin,
Walawa ma datagan ta tace abubuwa sun kara manya Isyaka yasamu na sakawa abaki yay
bacci aiko tabuga mata dundu.

*kano*
Cikin bacci yaji Abba na bugamai kafa bude ido yayi yaga Abba ya shirya cikin hadaddiyar
gizna shadda ga uban malum malum yace "jekai wanka harda kai zamu zaria bikin Bilkisu,
kawani kwanta kana bacci kasan karfe nawa?" turo baki yayi Abba ya tallabemai keya ahankali
yamike ya shiga bathroom. Fridge harda su washing machine Abba yasai ma Bilkisu zai bada as gift su Mami dakuma big
Mummy dasuma zasu zaria suka hada mata atampopin da lace harda turarurruka duk sunci
gayu sunyi kyau. kusan 20 minute sanan yafito fuskar nan adaure, ya sanya sky blue shadda
dake kyalli tsabagen kyau ya kafa wata hadaddiyar hula aka yana tafiya daidai sai uban kamshi
yake. gaban mota ya shiga driver yajasu sai zaria, matayen suka fara kaiwa gida Malam ya kira
Mama tamusu jagora ciki sanan Malam yama mazan jagora zuwa massallacin jumma'an dake
anguwan su, bayan anyi sallan jummu'a duk aka natsu a massallaci wanda malamai da dama
abokanen malam sun halarta, saikuma Isyakan dayay kyau yasha yar farar shaddar shi ta
daidai kudi da mutanen shi danhar baban shi yazo daga sokoto, gakuma daliban malam gasu
Abba agefe kusa da malam sai murmushi yake dudda har cikin ranshi yaso ace Bilkisu rabon
danshine. 🎤 limami ya rike ya kalli Baba yace "ina angon da iyayen shi ku matso sabida
adaura" tashi Isyaka dake sahu nabiyu yayi yazo gaba shidai Ayaan sai binshi yake da kallo
yana wani irin tabe baki, microphone din Isyaka ya karba daga hannun limamin yay murmushi
yace "inada wata yar sanarwa ne" mikamai limamu yayi ya e bismilla, karba Isyaka yayi sanan
ya gyara tsayuwa ya kalli Malam da yayan shi dama duka mutanen dasuka cika masallacin
makil, yay gyaran murya sanan yasake kallon malam da murmushi kekan fuskar shi yace "Allah
gafarta malam gaskiya nidai nafasa auren, banison yarka Bilkisu, kayakuri bawai cin mutunci
bane amma bani sonta ko kadan nafasa auren, na fasa" ya ijiye microphone din yafita daga
masallacin ta kofar inda liman kejan sahu, nan fa masallaci ya kacame da surutu baban isyaka
yatashi yabi yaron da sauri amma harya hau mashin yabar wajen.
Wani irin matsiyacin murmushi Ayaan yayi ya kalli fuskar malam dahar wani zufa ke ketomai,
dawowa yay kaman mara lpy ma su Abba se baki suke bashi, hanun Baba Suleman yaja hakan
yasa Baba Suleman dake magana dago kai ya kallai, kara janshi yayi hakan yasa yamike ya
bishi abaya suka fita waje Baba Suleman yace "wai wani irin iskanci ne wanan kana ganin
babanta baida lpy ne kake jawoni waje, ba yanzu zamu tafi ba leave me" Baba Suleman yay
maganan cikin fushi, kaman zai mutu dan bakin ciki yadai saita kanshi yace "Baffa nizan aureta
kafada ma Pops adaura auren dani dama saisa nakira ka waje nafada ma" da mugun mamaki
Baba sule ke kallonshi yace "kace me?" murmushin yake yay yace "adaura dani" da gudu Baba
sule ya juya yay cikin masallacin shikuma ya dunkule hannu ya daki iska. "f*ck wlh zakici ubanki
ne ahannuna" azuciye ya shiga masallacin ya hango Baba sule nama Abba magana akunne
tashi Abba yay tsaye yazo inda yake tsaye yace "son are u serious?" murmushi yama Abban ya
gyada kai, kamashi Abba yayi yamai peck a goshi tsabagen farin ciki, kafin yajuya da sauri
yakoma gaban masallacin yadau mike ya tsaya yace "asaurara jama'a, asaurara" shiru akayi
duk aka maida hankali kan Abba, yay murmushi ya kalli Baba yace "dama muntaba zuwa
neman ma dana auren Bilkisu amma munyi latti lokacin, to gashi dannawa har yanzu yace yana
ciki fa, alfarma muke nema ataimaka mana abamu malam" "Allahu Akbar" kawai aketayi a
masallacin malamai nata kabbara suna cema malam "Allah ya fitar dakai kunya" wan Baba ya

kalli Malam dayay shiru yace "kabasu Bilkisu tunda danshi na sonta kaga munfita kunya"
murmushi Baba yay ka kalli Abba yace "na amince kuma nabaku ubangiji Allah ya sanya
albarka" zokaga murna wajen Abba da Baba Suleman kamoshi Abba yayi ya zaunar dashi kusa
dashi nan fa aka gyara zama liman ya daura aure tsakanin AYAAN ABDULRASHEED DA
BILKISU ABDULBASY akan sadaki dubu dari da hamsin.
[7/15, 12:21 PM] Ummi Tandama: ♦♦ *SANGARTATTCE* ♦♦


Maman Abd Shakur

25 - 26

*idan baka biyaba karka kar karanta, for sell*

Kasa bacci Abba yay ranan gabaki daya danji yayi maganar takara natsun mai azuciya sai
tunane tunane yake.

Bayan kwana biyu.
Wuraren 8 ya shigo falon Abban sanye da black trouser yau normal wando yasa saidai ya dame
wandon, yasa white long sleeve shirt da kake iya hango chain din dake kyalli a wuyar shi yay
tucking yakawo belt mai kyau yasa, yasa black cover shoe dake shining na zuwa aiki ya shigo
dakin yana kokarin gyara tie din wuyarshi hanunshi daya kuma rike da white ironed lab coat
dinshi sai kamshi yake looking cooperate, fatarshi har wani glowing yake sabida hutu, gashin
kanshi da sajen shi sun kwanta lub lub, Abba ne kadai adakin zaune akan carpet ga abinci nan
agabanshi anjera kala kala. "Morning Pops" ya gaida Abba da tunda ya shigo yake kallonshi,
tsugunnawa yayi yadau cup din coffee dake gaban Abba sanin ba sugar aciki yasa yadau two
cube of sugar yasaka yakoma kan kujera ya ijiye labcot din kafin yakoma gaban Tv rike da cup
din coffee ya dauko remote yadawo ya zauna yana kokarin chanza channel daidai lokacin Mami
ta shigo dakin da sallama rike da tray da blow din dake dauke da koko daketa kamshin su citta
akai, ajiyewa tai agaban Abba dataga hankalin shi nakan Ayaan daya daura kafa daya kan daya
yana kallon tashar kwallo, zama Mami tai gefenshi tace "ga kokon dakace na ma" dan juyowa
yay ya kalleta yay murmushi yace "nagode" sanan ya juya ya kalli Ayaan daya natsu yana
kallon Ball yana sipping coffee, ahankali yace "Boy inaso muyi wata magana dakai" juyo dakai
yay ya kalli mahaifin nashi yay murmushi dake karama fuskarshi kyau yace "okay Popsy" tashi
Abba yay yakoma kan kujeran dayake zaune Mami dai ta tabe baki kawai tadau cup tana
kokarin hadama kanta tea, Abba yadan dafa kafadar Ayaan dake kallonshi yace "Boy I've been
thinking alot lately" Ayaan yay sipping coffee yace "yea I've noticed dat, wats d matter Pops"
Abba yace "I've been thinking alot nai addu'a akai, nakuma samu natsuwa saisa nazo maka da
zancen" ya danyi shiru yasake kallon Ayaan din daya natsu yana kallonshi yana kokarin kai cup
din Coffee bakinshi, Abba yace "ina so ka auri yarinyar data taimake ka, wat i mean to say is
inaso ka auri Bilkisu" wani irin mugun choking dinshi coffee dake bakinshi yayi hakan yasa
yafara wani irin mugun tari, da sauri ya mike tsaye yana buga kirjinshi dayan hanunshi kuma
akan bakinshi yana tari sosai yana kallon Abba daya kafeshi da ido, idonshi har ja yayi

tsabagen kwarewan dayayi, da kyar tarin ya tsaya hakan yasa ya kalli Abba yace "Pops bakaine
kai maganan dakayi yanzun nan bako? I refuse to believe u are d one" tashi shima Abba
yakamo hanunshi ya zaunar dashi kan kujeran, kaman wawa ya zauna baki bude yana kallon
fuskar mahaifin nashi, kwantar da murya Abba yayi irin yanda ake lallashin yara yace "akwai
alkairi a auren ku, son ina maka kwadayin yarinyar she's way too good, saisa nakeso ka aure
ta, i want you to marry Bilkisu" fizge hanunshi yay da karfi daga na Abba ya mike tsaye yace
"wah! Pops, like, kaiii, for real?" yay maganan sounding so confuse shi mamaki ma maganan
yabashi kodai Pops baida lpy ne, yasake kallon Abban yace "are you really saying dis, ni Popsy,
ni fa, ni Ayaan na auri that gurl wats her name ma?" ya tsaya yana kokarin tuno sunan. "ehen
Bilkisu, Popsy how old i am dama zanyi aure, and auren ma she!" yawani ja she din arrogantly
yace "wanan yarinyar mara natsuwa mai rawan kai yar kauyen nan gata ma.." tsawan da Abba
ya dakamai yasa ya tsaya galala yana kallonshi. "shut up Ayaan! One more bad word against
that poor innocent girl wlh saina mareka, bazadai ka aure ta bako is fine with me, am not going
to force u, but karka kara fadin any bad thing akanta" surprisingly yake kallon Abba da
idanunshi dasukai ja tunda yake zai iya cewa tunda yay wayau Popsy bai tabamai ihu ko tsawa
ba this is the first time and all akan dat lousy being Bilkisu, hakan ko ba karamin bakanta mai rai
yayi ba yace "but Pops.." kofa Abba ya nunamai alamun yafita hakan yasa yasake kallon fuskar
Abban yama kasa koda kwakkwaran motsi sabida mamaki, baki yabude zaiyi magana Abba ya
dakamai tsawa da har Mami saida ta runtse ido sabida yanda ya shiga kunenta. "i said out"
Abba ya nunamai kofa daukar labcoat dinshi yayi azuciye saikace dashi suke fada yafita daga
dakin ranshi abace, da yan aiki yaci karo a falo yawani daka musu tsawa. "u all are fired out of
this out right this minute" ya nuna musu kofa ganin yanayin fuskarshi yasa duk suka fiffita harda
gudu yafita kaman zaki, Big Mummy da fitowar ta kenan tana kiranshi "Boy Boy" ko jinta baiyiba
tsabagen bacin rai ya shiga mota, tsabagen yanda ranshi yabaci yasa yaja motar dawani irin
gudu kaman mental sai hospital dinsu wanda na abokin Popsy ne yana aiki a wurin, duk uban
nurses din dake gaisheshi ko amsasu bayayi, yawuce office dinshi wata receptionist ta biyoshi
har office din bayan ya zauna ta gaida shi. "good morning sir, karfe goma ne zaku shiga theater
din" wani irin kallo daya mata da idanunshi dasukai jajir yasa jikinta yafara rawa da kyar ya isa
saita kanshi ya kalleta yace "the next senior doctor should do it, banajin dadi yau" jikinta har
rawa yake tajuya ta fita tana memai fatan samun lpy.
Rasa inda zaisa kanshi sabida yanda ranshi ke tafarfasa yasa ya mike tsaye yafara zagaye
office din kafin ya dunkule hannu ya daki iska. "f*ck! Wah sh**t is dis, f*ck!" komawa kan kujeran
yay ya dafe kanshi ga kirjinshi dake tafarfasa kaman zai kone. Tashi yayi yadau car keys din
dayayar akan table yafita daga office din kaman zai fasa kasa yanda yake tafiya, mota ya shiga
ya kunna yabar hospital din kafin yadau waya yay dailing number meram ko ringing daya
baigama yiba ta dauka, da kyar ya iya tattaro kalaman bakinshi ya hada tsabagen bakin cikin
dayake ciki yace "meet me at my house" baima jira mezata ceba ya buga wayan akan dayan sit
din yacigaba da tuki haryakai gidan akofar gidan suka hadu itama tataho da tata motar kallo
daya yamata ya dauke kai yay horn mai gadi ya budemai ya shiga itama tabiyoshi abaya kafin
tai parking harya fito yay cikin gida binshi. Tabishi da kallo tana murmushi. "wakuma yabata
Ayaan dina rai" dariya tai bayan tagama parking kafin ta dauko jakarta tabude taciro hoda
takara shafawa, ta ciro mouth fresh ta feffesa dan tasan Ayaan ya tsani baki na wari fitowa tayi
daga motar tayi cikin gidan, baya sitting room din saidai kamshin shi daya cika ko'ina hakan

yasa ta wuce bedroom din yana kwance kan gado yay rubda ciki ya dafe kanshi, tsugunnawa
tai akasa takai hannu tana shafa mai kunne ahankali tace "waya batama rai baby" bude idanun
dasukai jajir yayi ya daura akanta hakan yasa ta mike tsaye tafara cire kayan jikinta, tass tacire
kafin tahau kanshi tafara kissing dinshi tako ina, tadade tanayi ta shafa nan ta shafa chan sanan
yajuyo yakamota, da kanta tacire mai kaya nan fa yafara maida mata da martani dan gabaki
daya fushin dayayi saida ya saukeshi akanta, tsabagen wuya harda kukan ta sosai, sai
wuraren biyu ya kyaleta ya juyo da kalleta yanda take saukar da ajiyar zuciya yace "jeki dafamin
abinci am starving" ware ido tai ta kalleshi saikuma takasa magana hakanan ta mike tafita daga
dakin kitchen ta shiga ta soya kwai dan abinda kadai ta iya dafawa kenen ta hada tea ta hado a
tray takawo mai kallon abincin yayi ya ture yace "ke kici i cant eat dis" yadau wayarshi yamusu
order food online.
Haka suka wuni ranan suna abu daya ko sallan azahar baiyiba bare na la'asar.
Around 1 nadare yafarka daga baccin dayay gaba dashi, kallon agogo yayi yaga daya nadare,
da sauri ya tashi yana saka kaya duk iskancin shi baya kwana awaje dan yasan Abba na zuwa
dakinshi duk asuba yatada shi suje masallaci, yana gama sa kaya ko tsayawa saka boturin
wandon da daure belt baiyiba yadau wallet dinshi dake kan drawer gefen bed yadau car key
dinshi yafita da sauri ya shiga mota yay horn gate man dake bacci yafito ya budemai gate yafita,
within 15 minutes yakai gidansu ya shiga yay parking. side dinshi yayi yabude ya shiga yana
kokarin maida kofar yarufe ne Mami ta turo kofar ta shigo tana mai wani irin kallo, dan dukar
dakai yayi yaki bari su hada ido ta maida kofar tarufe shikuma ya matsa jikin doguwar kujeran
dakin ya tsaya ahankali yace "sannu Mami" "daga ina kake at dis late?" ta jehomai tambaya,
baki yabude zaiyi magana ta tari numfashin shi rai abace tace "don't tell me daga clinic kake
because u are not from dere tun around 8 muka kira aka cemana u left dere since morning"
kasa magana yayi kanshi akasa, takowa tayi ta matso kusa dashi ta kama habarshi hakan yasa
ya daga kai suka hada ido ta daure fuska tace "open ur mouth kafara shaye shaye ne?" sai a
lokacin yadan sami karfin magana ahankali yace "Mami am a Dr. Kuma saina dinga shaye
shaye bayan nasan illar hakan" bakinshi tabi da kallo jin bataji warin giyaba kam, tabi jikinshi da
kallon tuhuma dan bata yarda dashiba idanunta ne suka sauka kan red lipstick din dake jikin
farar rigar shi almost on every corner alamun kiss din bakin mace, ranta yawani irin mugun baci
gawani irin zafi dataji zuciyar ta nayi ta kama kwalar rigar shi ta rike da kakkausar murya tace
"wayan nan abun dake jikin riganka explain" kasa magana yayi kanshi akasa yaki bari su hada
ido dan tunda yaga tana kallon rigarshi shima ya kalli abinda take kallon, shirun daya mata ya
mugun bata mata rai hakan yasa ta kara kama kwallan rigar shi ta jijjiga shi da duka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login