Follow us on social media
Showing 84001 words to 87000 words out of 124573 words
Chapter 29 - Sangartacce Book Complete Complete Hausa Novel by M Shakur
kunu ba, bude kofan bayin datayi yasa ya daga kai ya
kalleta, Kalle kallen dakin ta shiga yi kafin ta karaso cikin dakin tana neme neme duk inda tayi
idanunshi na kanta bai cemata komiba zuwa tayi gabanshi batare data kalleshi ba tasaki wani
irin kuka shagwaba tana dire dire. "my teddy bear ina yake" kafeta da ido yayi yanda take mai
tsalle tsalle da sauri ya ijiye cup din hanunshi ganin yana neman barar da tea a jikinshi sanan
ya kalleta saikuma ya kauda kai yadau plate da fork ya bude food flask zai dibi abinci saikuma
yadan lumshe ido ya budesu yadan juyo dakai, kadan ya kalleta yace "na hada da teddy bear
da akwatin kayanki nabama securities su kyautar bazaki dinga amfani da abunda wani Kato ya
sai miki agidana ba, suma kayan chan dakika cire once sun bushe they're leaving this house
straight up" ihu tayi tafashe da kuka ta tsugunna awurin ta cusa kanta a kafafun ta. "My teddy
bearrrr wlh saika biyani abuna aiba naka bane" saikuma tamike tsaye tana bubbuga kafa tana
kuka tana hararan shi da murguda mai baki, ahankali ya ijiye plate din da fork ya mike tsaye
yana kallonta, murguda mai baki take sosai tana share munafukan hawayen dake zubowa,
hanunta yaja ya zauna kan gado ya daurata akan jikinshi make mai kafada tayi ta murguda baki
dan murmushi yayi yace "okay okay am sorry baby, mesa kike kuka" da hannu ta nuna shi tace
"bakaine ba ina teddy na" takara murguda mai baki tana goge kwalla, dagata yayi daga jikinshi
yace "okay to stop crying bari naje nasiyo miki wani" washemai baki tayi sosai tana kallon
fuskarshi, kusan sumewa yayi wanan ne first smile datake bashi tunda tazo, mikewa tsaye tayi
daga jikinshi da kyar shima yatashi ya nuna mata rigan daya ciro mata yace "wear dis, ga abinci
kici am coming" ko kallonshi batayi ba tadau rigan tana warware wa, daukan car key yayi da
wallet dinshi yafita daga dakin abincin dabaici ba kenan yabar gidan.
Tsaki tayi tasa rigan tana maganganun ita kadai, tazo gaban madubi man data gani ta shafa
sanan takoma wurin abincin kunun tasha sosai taci ships da egg sanan ta tashi tana kalle kalle
dakin zama tayi akasa tunawa da sweetheart tafashe da kuka sosai. "sweetheart ina kake?
Inane nan daka kawoni wurin mutanen nan da mutumin nan, please come back, wayyo Allah na
Anty Ummy" kuka tasha sosai dan kanta tagaji ta share fuska saikuma tafara tsalle tsalle har
falo, wurin TV tai dan kunna ta kalli cartoon amma tayi tayi tayi ta kunna TV takasa hakan yasa
ta cigaba da tsalle tsalle tahau wanan kujeran ta dirko tahau wanan saikuma tai hanyar kofa
dazai fitar da ita daga dakin dayar fingilar rigar jikinta mara hannu gashi iya guiwa ta tsaya mata
kanta babu dan kwali sai kitson nan guda biyu bude kofa tayi tafita tana tsalle tsalle, workers
biyu ne kawai maza a part dinshi dake watering flowers daya kuma na rage tsawon su da
almakashi. Sai guje guje take abinta tana on ur mat get set ready go, taje ta taba wanan bangon
sanan tadawo wanan bangon, gashi tasa over size slippers dinshi a kafarta daya mata yawa
sosai. Workers din kuwa hankalin su nakan aikin su sunayi suna hira sama sama.
Tana cikin gudun ta timm tafadi guiwan ta daya ya gurje wani irin ihu datayi yasa ma'aikatan
suka fito da gudu sukayo kanta ta baje akasa ta dago kafarta daya tana duba guiwar tana kuka
tana yarfe hannu dan gurjewa ma tayi kadan amma take uban ihun nan, daya daga cikin sune
yace "sannu tashi ki shiga ciki" hararan su tayi ta make musu kafada, dayan kuma yabita da
wani irin kallon maita ga rigarta tadanja kasa dan kana ganin cleavage dinta, wanda yay
maganan ya kalli dayan dayake kallonta yace "wuce mutafi Musa" da sauri Musan ya tsugunna
ya mika hannu zai taba kafar yace "mugan kafar" daidai lokacin Ayaan yashigo part din
hanunshi daya rike da babban teddy bear red me gashi dayan hanun kuma white leda ne dake
dauke da different snacks, tsayawa yay chak yana kallonsu yanda suke kallon mai mata
barinma na tsugunnen. Washe baki Musa yayi yace "haba mana kibari naduba miki ciwon kefa
me kyau ce" make mai kafada tayi tana kuka ta matsawa baya tana hararan shi, dayan yace
"Allah baka sa'a nidai kaga tafiya ta" yajuya zai koma wajen plant Ayaan daya gani a tsaye yana
musu wani irin kallo da idanunshi dayay jajur yasa bakinshi yafara rawa yanason yakira sunan
Musa amma yakasa, wani irin watsar da kayan hanunshi dayayi sukai kara shi yasa daga Musa
har ita suka dago kai, arude Musa ya mike tsaye ya kalli dayan da shima jikinshi ke rawa yake
yace "kai nafasa aikin, nabar aikin, natafi" da sauri yajuya yazo ta gefen Ayaan zai wuce da
gudunshi, wani irin fizgo shi da Ayaan yayi saida rigar jikinshi ta yage, bugashi yayi da bango
bamm, yawani irin shake shi, dayan na ganin haka da mugun gudu yazo yabi tabayan su yafice,
yanda taga Ayaan ya shake shi mutumin na neman mutuwa yasa ta mike tsaye tana zazzaro
ido jikinta ko ina na rawa, wani irin duka Ayaan yarufe shi dashi a zuciye yana buga bayan shi
da bango. "uban wayace ka kallan min matata? Uban wayace ka kalla min mata ta har kasan ita
mai kyau ce ko dan ubanka, yausaina tsiya yar da idon daka kalleta dasu" kamo wuyar shi yayi
yana neman kai hanunshi cikin idanunshi, idan kaga Ayaan zaka rantse mahaukaci ne, fashewa
tayi da kuka sosai tsabagen yanda ta tsorata tazo wurin ganin kokarin budemai ido da mutumin
ya runtse gam yake, tabaya ta rungume shi sosai jikinta na wani irin rawa tafashe da kuka tace
"please stop am scared" yanda ta daura hanunta akan kirjinshi yasa wani irin shocking ya shiga
jikinshi, da sauri jikinshi ya saki hakan yabama Musa dayaji jiki a hanunshi ya fizge kanshi ya
gudu da kyar, yunkurin binshi yayi tai baya zata fadi da sauri ya fizgota azuciye, kankame
idanunta tayi a tsorace, ya tsugunna yadau teddy ta da ledan ya fizgo hanunta yabude daki ya
shiga da ita.
Wani irin jefata yay akan kujera da idanunshi dasukai kaman banashi ba yace "uban wayace
kifita ahaka, kinja wasu maza sun kallan min ke eh, bakisan da aurena akan kiba, u are my wife,
my property, am ur husband" make mai kafada tayi tana kallon dan gurjewan datayi tace "ni
banda husband, kuma ni sweetheart zan aura dankaji, nasan yau zaizo ya dauke ni mubar
muku gidan ku, ni banason nan gidan ma nafison gidan sweetheart dina, farm house dankaji
infad..." wani irin tari dataji yanayi yasa ta daga kai ta kalleshi, dafe kirjinshi yayi numfashin shi
na neman barin kirjinshi yana kokarin saita kanshi yana tari kaman mai asma, arude ta mike
tsaye tana kalle kalle, ruwan data hango kan fridge ta dauka da sauri ta juyo kafin ta karaso ta
bashi har ya zube a wurin asume".
♦♦ *SANGARTATTCE* ♦♦
Maman Abd Shakur
73...
*dake nake, kedai wanan rubabbiyar me hanun tantabara dazata marking ta fitar dashi waje, da
idanun kaman na agwagwa, maicin amana dai yay asara, yar air mekama da macen bera,
yama sunan macen bera ?? Beratu kawai*
Tsugunnawa tayi ta kwalalo ido waje tana kallonshi ganin ko numfashi bayayi, arude ta daura
hannayen ta akan kirjinshi tana dukanshi. "kai, kai, wai bazaka tashi ba, bude idanun ka" girgiza
shi take sosai amma ko motsi bayayi, fashewa tayi da kuka ta mike tsaye tana kalle kallen dakin
tarasa abinyi, bottle water data dauko ta ijiye kusa dashi ne tagani hakan yasa ta tsugunna da
gudu tana kuka tadau ruwan ta bude takai bakinshi cikin kuka tace "dan Allah kasha to katashi
kaji, to bazan kara fitan ba, amsa" jijigashi takeyi ruwan akan bakinshi amma baiko motsa,
mistakenly garin jijigashi yasa ruwan ya bare mai a fuska daga hanunta, wani irin ajiyan zuciya
ya sauke batare daya bude idanunshi ba hakan yasa tafashe da mugun kuka tace "kai kabude
ido nace, yakuri to" labban shi dataga yabude yanason yay magana yasa takai kunenta saitin
bakinshi da sauri, murya chan chan ciki yace "press my heart" da sauri ta daga kanta ta daura
hannuwanta ata saitin zuciyan shi wanda baya bugu da kyau ta daura ta danne da duka karfin
ta tana kallon fuskarshi, ganin har lokacin babu wani chanji yasa tasake danne zuciyar, jin still
batajin bugun zuciyan sosai yasa ta daddage tai nai uku tana kallonshi, ajiyar zuciya ya sauke
sosai tareda bude idanunshi kadan ya kalleta, fadawa tayi kanshi tafashe da kuka tace "kai
bazan karaba" saikuma ta dago kanta ta kallai Ita yake kallo asanyaye da idanunshi dasuka
kankance tace "u are sick ina maganin ka na dauko ma" shiru yayi yana kallonta, share kwallan
daya zubo mata tayi tace "ina maganin ka" shiru yayi yana kallonta da idanun nan dasuka
kankance suka chanza kala, matsawa tayi ta jingina da kujeran ta cusa kanta akan guiwowinta
tafashe da kuka sosai tace "ni nagaji da gidan nan, anata dukana, anata dambe da mutane har
ana kwakule ido ma, tunda nazo tashin hankali nake gani, am tired, Sweetheart kazo ka tafi
dani, where are you sweethea..." kasa karashe maganan datake yi tayi sabida yanda Ayaan
yataso ya daura kanshi shima akan guiwanta duk yanda yaso ya daure yakasa wani irin nishi
yake bakinshi na rawa yace "dan Allah, dan Allah Baby, I know you are not well but pl..."
saikuma yay shiru jin yana neman yakara sumewa sabida yanda zuciyarshi ke wani irin gudu,
arude ta dafa kanshi tace "kai wai me haka mutuwa zakayi? Na shiga uku Sweet..." fadawa yayi
jikinta ya kankame ta sosai yanason yay magana amma yakasa ajiyan zuciya kawai yakeyi,
yanda taji zuciyarshi na wani irin beating ba kakkautawa yasa tace "u heart is sick" saikuma tai
shiru tana sauraron yanda jikinshi ma yadau rawa kodai ba mutum bane dama gashi fari kaman
aljanin zabiya da Anty Ummy tabata labari, ahankali ta shiga tureshi daga jikinta muryan ta
narawa tace "sas..sa..sakeni inje induba ko sweetheart yazo mutafi" wani irin matseta yayi
ajikinshi yanajan numfashi ya chusa kanshi awuyan ta kirjinshi nawani irin bugu yafashe da
kuka sosai yama kasa maganan, itama arude tafashe da kuka so kawai take ta kwaci kanta
daga wanan kwakumetan dayayi, cikin kuka tace "sakeni inje in duba swe..." kara fashewa da
kukan da yana ganin rabonshi da yin irinshi tun yana yaro, shi karan kanshi baze iya explaining
yanda yakeji aranshi inda takira katon nanba, zata sake magana ya daga hanunshi ya kyar ya
daura akan bakinta ya shiga rera mata wani irin kuka mai tsinkar da zuciyar mutum, da kyar ya
iya controlling yanda zuciyarshi ke bugawa ya bude baki cikin kuka yace "p..pl...lz..stop calling
dat name wlh zan iya mutuwa, am begging yhu baby dan Allah ki tausaya min, am suf...fering"
shi kanshi baisan meke damun shi ba, yanda yake reramata wani irin kuka irin na sangartattun
yaran nan mara kara awuya, hawayenshi har gangarawa suke yi daga wuyanta zuwa kirjinta, da
sauri ta hadiye nata kukan taji yawani irin mugun bata tausayi duddu bata gane takamai men
meke sakashi kukan ba, amma saitaji tana wani irin jin tausayin shi ahankali tace "to nadena
amma nadinga cemai uncle to" runtse idonshi yya da mugun karfi wasu hawayen sharr nazubo
wa shi gabaki daya bama yaso yaji tana maganan wani namiji ne aduniyan nan, shiru itama tayi
jin yanda hawaye ke gangarawa jikinta, ahankali ta sakala hannayen ta ta daura asaman kanshi
ta shafa mai alamun lallashi, wani irin ajiyan zuciya ya sauke yakara kankame ta da kyau ya
lumshe ido, tun tana sauraron yanda heart dinshi ke beating da mugun fast har tazo tajishi
yasoma komawa dai dai ahaka itama wani wahalallen bacci yay gaba da ita.
♦♦ *SANGARTATTCE* ♦♦
Maman Abd Shakur
74 - 75
Wuraren sha biyu na rana Baba ya shirya zai tafi Abba sai kiran Ayaan yake amma wayan shi
bata shiga dan yakawo ta suyi sallama da mahaifin ta hakan yasa ya kalli Mami yace "jeki kira
Ayaan firdausi" tom tace tafita daga dakin sanye da babban lullibin dake jikinta. Akofar dakin tai
sallama tai sallama taji shiru hakan yasa ta bude kofan yanda taga Ayaan da Bilkisu ne yasa tai
maza ta rufo musu kofa tana girgiza kai, komawa tayi lokacin har Baba da Abba sun fito
compound Abba yace "ina suke" dan murmushi tayi tace "inaga kaman yakaita asibiti ne" Baba
yace "dama banaso taga tafiya ta dan shirmen zata cigaba da muku ga wanan adinga bata
addu'o'i ne nayi a ruwan in sha Allah zata dawo hayyacin ta" karban goran ruwan Mami tayi
shikuma Baba ya shiga motan suna mai Allah kiyaye driver yajashi suka fita daga gidan, kamo
hanunta Abba yayi yace "come here meyafaru baga motar boy nan ba aparke" dariya kawai tayi
tace "wlh bacci suke nashe nashe afalo abinsu" wani irin washe baki Abba yayi yace "masha
Allah, Allah sarki my Baby Boy yaushe rabon yay Bacci nashe nashe haka kullum ciwo yake,
Allhamdulillah, Allah nagode maka daka dawomai da farin cikinshi, da abu yataba min yaron
nan Firdausi wlh gwara ni yataba ni sau dubu" tabe baki Mami tayi tace "oh har yanzu hajiya
bari naje na kirata" waya yaciro daga aljihun gaban rigar shi jin ana kiranshi yace "takirani tace
koda daddare yau kokuma gobe zata dawo wai sai yau suka kai Amaryan kuma zasu tsaya
mata jere, insun gama dawuri zamu ganta" gyadamai qkai Mami tayi, Abba yace "dan Allah je
adaura musu abincin rana abinci merai da lafiya, kar wanda yadame su fa, kuma harda ke karki
daman min yarana, idan kin gama ki aika musu da abincin su part dinsu" baki Mami tasaki tana
kallonshi cikeda mamaki, murmushi yamata yajawo ta suka shiga ciki yana yar dariyan manya.
Wajajen azahar ya farka sabida kiran sallan da akayi yana dafe kanshi sabida yanda kan kemai
mugun ciwo, juyo da kanshi yayi ya kalleta yanda take baccinta awahale, dan murmushi yayi ya
kalli dan gurjewan datayi akafa, ahankali ya mike tsaye ya dauketa batare daya tada taba ya
shigar da ita bedroom akan gado ya kwantar da ita ya ja bargo ya lullube mata kafa sabida
sanyi sanan ya shiga bayi wanka yayi dan yadanji dadin jikinshi ya dauro alwala ya fito yasaka
soft dark blue yadi simple jumper akamai turare ya fesa yafita daga dakin da sauri dan bayaso
yana missing jam'i, saida aka idar yadawo gidan shashin Mami yayi, dining ya tsaya ya dauki
apple sabida yunwar daya keji yayi sama, sallama yayi ya shiga dakin Mami bayi take kokarin
shiga ganinshi saiya sa ta tsaya murmushi yamata yace "Mami na" "har an tashi daga baccin"
da sauri ya kalli Mamin da idanunshi masu kama dana mejin bacci, dan dariya yayi ya gutsiri
apple batare dayace komiba, fridge Mami tabude ta dauko wani tsumi a gora dayay sanyi ta
bashi ya karba yana kallon goran tace "gashi ka kaimata ta shanye" da sauri yace "meshi
Mami?" hararan shi tayi ta dauko goran da Baba yabata na ruwan addu'a tace "wanan kuma
kadinga bata kullum ruwan addu'a ne Baba yamata kafin yatafi" karba shima yayi ashagwabe
yace "Mami am hungry fa" girgiza kai tayi tace "kadai ajiye iyali yanzu kake abu har yanzu
kaman yaro, anyway abincin ku na shashin ku" tashi yayi rike da gorunan yace "bari naje naci
inmun gama zamu je hospital" anatse Mami tace "daka bari gobe kuje wat if yanzu kun fita taita
cewa ka kaita chan wajen wayanda suka kawota, kabari tadan manta tukun gobe koda da
yamma ne basai kujeba" shiru yadanyi saikuma yace "to Mami" fita yay daga dakin yana
gutsuran apple din hanunshi, tun daga barrander yakejin dirke dirke da karan kujera, bude kofa
yayi ya shiga tana tsaye akan kujera rike da teddy daya siyo mata, wurga teddy tayi sama saitai
wani irin ihun dadi ta dirko kasa ta chabe, akan daya daga cikin kujeru falon ya zauna yana
kallonta yanda take wasan hankali kwance saibin kafafun ta da kallo yake, juyowa tayi ta
kalleshi suka hada ido ya lumshe ido sabida yanda idanunta suka mai wani yarr, da sauri ta
dirko daga kan kujeran tayo inda yake tana washe baki tace "kaima zakayi in arama teddy na?"
batare daya bude idoba yasa kafanshi ya tadiyota jikinshi dan kara tayi tace "wayyo teddy na,
na danneta tana kuka" dan murmushin gefen baki yayi yadan dagata yasa hannu ya zaro teddy
din ya ijiye akan kujeran next to him, bin teddy tayi da kallo ta makemai kafada tace "kai kabani
teddy na, kakusa sa na kasheta" ware idonshi yayi ya sauke su akan bakin datake turomai wani
irin miyau me daci ya hadiye kafin ya mayar da idon ya lumshe su ahankali yace "kinyi salla?"
turomai baki tayi ta balla mai harara tace "banai alwala ba natuna hijabi na nachan gidan mu,
farm..." da sauri ya mike tsaye ya dauke ta harsaida tadan firgita ta rirrike shi, bedroom yay da
ita yaje gaban wardrobe dinshi da ita ya sauketa ya bude, kayane da yawa na mata a kusa da
nashi hannu yasa ya zaro hijabi yabata yace "pray kizo muci abinci" turomai baki tayi, ahankali
yasa yatsa ya shafa lips din yana mata wani irin kallo da lazy eyes dinshi, da sauri ta tureshi
tana hararan shi ta mikamai gogeggen hijabin ashagwabe tace "bude min ni" karba yayi batare
daya janye idanunshi daga kan fuskarta ba ya warware yasaka mata ya gyara wuyan,
bakaramin kyau hijab din yamata ba, mutuwar tsaye yayi yakasa daina kallonta, juyawa tayi
batare data damu da yanda yake kallonta ba tahau kan dadduma tafara salla yafi 2min a tsaye
a wurin kafin yaje palour, abincin ya bude a warmer, fried rice dayaji veggies ne da roasted
turkey ya