Follow us on social media

Showing 72001 words to 75000 words out of 124573 words

Chapter 25 - Sangartacce Book Complete Complete Hausa Novel by M Shakur

M Shakur   

09 Nov 2025

5125


ciwon dake kanta ke lilo tana kusa dashi takara washemai baki da sauri ya dauke kai ya kalli Dr
yace "ina zamu samu hijabi" shiru Dr yayi kaman mai tunani sai chan yace "i think inada hijabin
Maryam a office dina bari na dubo na kawo muku" da sauri yafita hakan yasa tawani irin juyar
dakai ta harari kofar tana turo baki ta gefen ido ya kalleta abinma mamaki ya bashi, zama yayi
akan gadon yaciro wayarshi yana daddana wa, da sauri ta zauna tana kallon wayar, hannu tasa
ta fizge wayar da sauri ya dago kai ya kalleta nunamai wayar tayi saita boye abaya tana
makemai kafada, abinma dariya yadan so bashi hakan yasa yay mata murmushi 4 d first time,
ware ido tayi saikuma ta ijiye wayan akan gado ta mike tsaye tana tafa hannu sosai tace
"yeeeeee" dan girgiza kai yayi kawai yace "funny" yadau wayar ya maida aljihu, ana bude kofa
ta dawo kusa dashi ta zauna da gudu, Dr ne ya shigo dakin rike da maroon hijab ya mikama
Aaman ganin yanda taketa murguda mai baki, karban hijabin yayi yace "thank u" ya mika mata
hijabin da sauri ta karba tana jijjiga hijabin tana dariya kaman taga kayan wasa, ganin batama
san meba yasa ya fizge ya warware ya saka mata kallon kanta ta dingayi tana jajjjan hijabin
tana kokarin cirewa hakan yasa ya girgiza mata kai yace "No karki cire" da sauri takara
tambayar shi "karna cire?" gyada mata kai yayi itama da sauri ta gyadamai kai, slippers yabata
tasaka sanan yay hanyar fita Dr nagaba, da sauri tabishi suka fita a pharmacy ya tsaya ya
saimata maganin duk tana kusa dashi tana kallon fuskarshi sanan suka wuce har wurin mota ya
bude mata ya nuna mata ta shiga, ta shiga ya rufe ya zagaya duk tana binshi da ido sanan ya
ahigo ya tada motar sukabar asibitin.

Cikinta ta rike ta hijabi tana shafawa tana tabe baki kaman mai shirin kuka tana kallonshi, ganin
hankalinshi nakan tuki yasa ta kece dawani irin shegen kuka da sauri ya juyo ya kalleta yace
"menene?" wani sabon kukan takara kecewa dashi tace "yunwaaa" da sauri yace "okay okay
dena kukan, zakici apple?" gyadamai kai tayi hakan yasa yay parking abakin hanya daidai
wajen masu saida fruits yasai mata apples dayasa aka wanke mata ya biya ya mika mata
karban ledan duka tayi da sauri ta ciro daya tafara ci tana murmushi, kallonta yayi da sauri ta
dago dara daran idanunta ta kallai washe mai baki tayi tasa hannu taciro katoton data balla

yake cikin bakinta taciro ta mikamai da sauri ya girgiza kai yace "no bazan ciba" wani irin ihu
tayi, ta kece dawani irin kuka da sauri ya mika mata hannu yace "okay okay, sorry karki yi kuka
bani to" sakamai tayi ahannu tana washe baki kaman ba ita take ihu da kuka yanzun nan ba, ya
karba yana dan murmushi kafeshi tai da ido tana jiran yaci tareda shagwabe fuska ahankali
tace "ci" kallon Apple din yayi yanda yay dama dama da miyau sanan ya kalleta yanda ta
tsareshi da ido, dan murmushi dole yasake yimata yay yunkurin kulle hannun, wani irin ihu
datayi wlh saida ya firgitashi dan mutum ne shi marason hayaniya tawani irin fashe da kuka
tace "ci" baisan lokacin daya hadiye apple dinma, tafashe da dariya tana kallonshi tacigaba
dacin apple dinta shikuma ya kunna motar ya cigaba da tafiya har gidan gona, bishiyoyi kala
kala da shuka ne daban daban, ta gefe kuma wani flat ne kwara daya babba sosai, parking yayi
yafito ya zagayo ya bude mata da sauri tafito tana waige waige rike da apple dinta ahannu,
gaba yayi hakan yasa tabishi da sauri ya bude kofa ya shiga, babban palour ne dayasha kujeru
sai tv bango akan dogon kujera ya zauna hakan yasa itama ta zauna kusa dashi da sauri tana
kallon fuskarshi, shima ita yake kallo saikuma yaciro wayarshi yay dailing number wani mai kula
da kajinsu ahankali yace "Umar dan Allah turomin Zainab" katse wayar yayi ya ijiye ya tashi, da
sauri itama ta tashi dan juyowa yay ya kalleta saikuma yay Jim yacigaba da tafiya abinshi,
kitchen ya shiga tana biye dashi tea yahada mata mai kauri a cup yadau slice bread ya shafa
mata butter ya daura mata akan plate ya dauko ya juyo ya kalleta ganin yanda take kallonshi
tana kallon abincin yasa yace "zaki ci?" da sauri ta gyadamai kai yace "okay to muje kici" yajuya
yafita daga kitchen din da gudu tabiyoshi falo suka shiga ya ijiye mata cup din tea da plate din
akasa da sauri ta zauna tana kokarin cire hijabin takasa saita dago kai ta kalleshi ganin ita yake
kallo yasa ta kwaye fuska tace "yaki fita" daidai lokacin wata yarinyar yar budurwa haka doguwa
sanye da hijabin ta ta shigo bakinta dauke da sallama tace "gani Uncle" murmushi yamata yace
"yauwa Zainab dan tayani cire mata hijabin nan" murmushi tayi ta shigo dakin tace "Uncle
bakuwa kayi" kwanciya yay akan kujera yace "yeah bamata da lpy ne" daidai lokacin zainab
takaraso gabanta da sauri takoma baya ta make ajikin kujeran dayake kai tanason tai kuka,
ahankali yace "hijabin xata cire miki karki damu she's my sister" kallonshi tayi idanunta sun ciko
da kwalla ya gyada mata kai tareda nuna idonta ahankali yace "don't cry, bari tacire miki" ya kalli
Zainab yamata alamun datazo, zuwa tayi da kyar ya samu tabari zainab tacire mata hijabin
sanan ya dauko mata tea ta tacigaba da sha, saida tagama sha, nan ma bakaramin daru yasha
da itaba kafin ta bari zainab ta kaita ciki dantai wanka da kyar yasamu ta yarda suka shiga
bedroom, suna shiga yadau key yafita dan zuwa yasiyo mata kaya sanan yayo take away
danshi bai iya girki ba.

Ko minti talatin baiyi ba ya dawo ya paka motar shi a tsakar gidan, tun daga waje yakejin kukan
ta girgiza kai kawai yayi ya bude bayan motan ya dauko katoton babban leda daya siyo mata
kayan sawa na mata, sai kuma ledan take away ya dauko yay hanyar cikin gida dashi da
sallama ya bude kofan ya shigo falon da gudun ta tafito daga uwardakan tana sanye da
doguwar rigar atampa ja daga gani zainab ce ta bata kayanta, tazo da sauri tana kuka ganin
shirin fadawa jikinshi take yasa ya juya da sauri yay facing kujera yana daura ledokin akan
kujera hakan yasa ta tsaya abayanshi tana goge kwalla, ahankali ya juyo ya sauke idanunshi
akan fuskarta yanda hawaye ke gangarowa yanabin kuncinta, anatse yace "mesa kike kuka"
hanyar uwardaka ta nunamai daidai lokacin Zainab tafito tana kokarin saka hijabi kayan jikinta

duk sun jike, yace "ita ta jikaki haka zainab?" dariya zainab tayi tazo wajen tace "ihu tadinga yi
wai bazata yi wankan ba dana hada mata ruwa shine ta dinga zubamin da kyar dai tayi, Uncle
wlh tanada kyau bakuwar nan naka ya sunanta?" da sauri itama Bilkisu ta kallai tanuna kanta
tace "ya sunana uncle?" dauke kai yayi dan idanunta namai wani irin ya zauna akan kujeran
yadau leda daya na take away ya mikama zainab a kunyace ta karba tana godiya, da sauri ta
zauna kusa dashi harda leka fuskarshi dago kai yayi ya kalleta hakan yasa ta washemai fararen
hakoran ta, dan murmushi yamata yana mamakin ta, tuntsirewa tayi da dariya takara matsowa
kusa dashi tace "ya sunana?" Ahankali yace "kinaso na baki suna?" da sauri ta gyadamai kai
tana washe baki lumshe ido yayi kafin ya budesu yakara daurasu akanta yace "okay dagayau
sunanki Ameerah" da gudu ta mike tsaye tana tsalle "yeeeee Ameerah, Ameerah" ta kalli
Zainab data tsaya tana kallon ta tana yaba kyanta aranta ta murguda mata baki tare da hararan
ta turo baki tace "sunana Ameerah ko Uncle" daga mata kai yayi Zainab tace "Uncle natafi" kudi
yabata taki karba tafita da sauri.
Ahankali yabude dayan ledan dayan take away yaciro jellof rice ya kalleta inda take tsaye
tanata kiran kanta da Ameerah tana juyi ahankali yace "Ameerah" da sauri ta dago kai ta
kalleshi tareda washemai baki abincin ya nuna mata hakan yasa tazo ta zauna kusa dashi yasa
mata spoon yabata tafara ci saida taci kusan rabi ta ture tana yatsine fuska, maganin ta yabata
da ruwa tasha da kyar tasha sanan tadau abincin tanaci tana wasa dashi shikuma chatting yake
a watsapp da Dr Ameenu, kanta dayaji ya kwanto akan kafadar shi yasa ya dago kai ya kalleta
tai bacci ga takeaway akan cinyarta shinkafan dukya zuzzuba akan rigarta yakai kusan 5
minutes yana kallon fuskarta kafin ahankali ya janye kafadar shi ya gyara mata kwanciya akan
kujeran tareda karbe take away ya kakkabe shinkafar jikinta acikin roban yawuce yakai kitchen
sanan yadawo ya zauna kujeran nesa da ita yana kallon fuskar ta, addu'a kawai yake ko ina
iyayen ta suke Allah ya bayyana su.




*kano*

Ahankali Abba yay sallama ya turo kofar dakin Bilkisu wanda Ayaan ya mayar nashi, abu
dayane ke fitar dashi daga dakin shine salla ko wani irin zazzabi yake saiya tashi yana dafe
bango yatafi masallaci. Mami itama ta tare gidan dan kula dashi, Big Mummy kuma takoma gida
sabida bakuwar ta Munari wacce yanzu take neman kusan sati hudu da zuwa kenan amma dai
kullum saitazo ta duba Ayaan. Shigowar Abba kenan bayan ya raka Dr Ibrahim dayazo dubashi
dan anyi anyi dashi yaje asibiti yaki.
Ahankali Abba ya zauna kusa dashi akan gadon hanunshi rike da tray na abinci dan yau
throughout yakicin komi, dafa goshin shi Abba yayi hakan yasa yadan bude idanunshi da sukai
jajir, gashin shi da gemunshi sunyi busu busu, hannu Abba yasa ya taimaka mai ya tashi zaune
ya jingina da gado, Abba yace "zoka ci abinci Boy so kake ka kashe kanka wai, dare da rana
police nakan case dinan, nasa amana rokon Allah, in sha Allah, Allah zai bayyana mana
gaskiya, da kansu zasu dawo da ita" Abba yay maganan yana mika mishi bowl din pepper soup,
ture bowl din yayi da hannu ya dau pillow ya rike muryan na rawa yace "bazan iyaci ba, tana

chan hala ma basu bata abinci ba halama sunata dukan tane yanzu haka, kullum da tunanin ta
nake wuni na tashi Pops..." yanda muryan shi ke rawa yasa Abba ya jawoshi jikinshi yana
bubbuga bayanshi kafin ahankali ya ciroshu yama forehead dinshi peck yace "za'a ganta da
izinin Allah yanzu dai ko 3 spoon ne kasha kaga zaria zani inaso naje nasami mahaifin Bilkisu,
yakamata susan wats going on, idan bamu fada musu ba bamuyi adalci ba" dafe kanshi
dayakeji kaman zai fashemai yayi Abba kaman zaimai kuka yace "sannu Boy oya sha sha saika
sha magani" da kyar ya bude ido ya karbi coffee da Mami tasamai madara, saida yasha sanan
Abba ya lullube shi da bargo yafita baitaba sanin haka Boy keson Bilkisu ba, driver yajashi sai
zaria.

Kiran sallan la'asar ya farkar dashi daga baccin wahalar daya dauke shi da kyar ya sauko daga
gado ya shiga bayi yaje ya dauro alwala yafita daga dakin a stairs ya hadu da Mami ta hado
abinci a tray zata kawo mai da sauri ta ijiye tray akasa ta rikeshi ganin kaman zai fadi, kaman
zatai kuka tace "ina zaka ahaka Ayaan kana layi?" da kyar ya ware idonshi ya kalleta yace
"masallaci zani Mami" girgiza mai kai tayi tace "Ayaan no mukoma daki kayi achan u don't look
good, baxaka iya zuwa masallaci ba" ahankali yace "zan iya Mami please ki barni nasan nama
Allah laifuffuka da yawa, cikinsu harda rashin sonyin salla, amma yanzu in sha Allah ba ciwo ba
koma me saina je masallaci" ahankali ya zame hanun daga nata yana tattaba karfen stairs ya
sauka kasa Mami tabishi da kallo da sauri ta share hawayen daya zubomata suna ganin
jarabawa.

Koda aka idar da salla yafi minti talatin azaune shi kadai amsallacin dan duk an watse sai shi
baima da karfin tashi, dafashi dayaji anyi yasa ya dago kai limamin masallacin ne daya shigo
daukar wayan shi daya manta dashi yace "baka da lafiya ne na taimaka maka na kaika gida"
dago kai yayi ya kalli Imam kafin ahankali yace "tambaya nakeda shi" yanda yay maganan
kaman zararre yasa lmam ya zauna ya lankwshe kafa, jingina kanshi dayamai nauyi yayi ya
kalli Imam da idanunshi dasuka kankance ahankali yace "a Austria na girma, achan nai
secondary school har nazama likita, am a very bad boy, idan nace bad i mean bad baddest, d
only thing danasan banayi shine shaye shaye but zuwa clubbing, daukan mata, saka sarka, dan
kunne, rashin salla duk nine, bayan nakare karatu na tattas na dawo harna fara aiki a asibitin
abokin Pops dina inanan da halina even though Mami na da Abba suna kokarin su barinma
Mami suga na dena amma naki, bansan meya sameni ba sai akace na haukace, ranan dai
dana farka na ganni cikin kaya masu datti, awaje mai datti da bola ga wari, sanan gani kusa
dawata yarinya wacce ita ta taimakeni da ina hauka hawaye duk sun bushe a idonta, ba
karamin wulakanci namata ba har ina marinta a fuska amma kasan wani abu Imam?" yatambayi
limamin yana bude ido kadan dan idanunshi a lumshe suke Imam yace "ina jinka" cije leben shi
yayi cikin jin azaban da kanshi kemai yace "bayan na koma gida dudda fuskar yarinyar data
taimaken nata bijiromin koda kulle ido kuwa nayi amma nai shiru naki fadinma babana harsai
randa babana ya tamabye ni ya akayi na warke, na fadanmai, shine muka shirya mukaje zaria
neman gidansu, bazan taba manta ranan" ya dafe kanshi yana wani irin murmushi yace "kafarta
nafara gani da dogayen yatsun kafar dan batasa takalmi ba, kafarta na cikin jan lalle dayay wani
irin kyau ta shigo dakin baban nasu da muke ciki tana sanye cikin pink hijabi mai hula, yanayin
yanda take magana da komi nata sainaji ta shiga raina sosai, bantaba son wata mace aduniyar

nan ba, banma san ya ake so ba amma saina ji ita ta tsayamin arai sosai, kome nakeyi saita
fado zuciya ta, bantaba nunama kowaba saidai duk lokacin dazan hadu da ita saina mata
wulakanci, naci xalin ta, nasata kuka, ranan da mahaifiya ya bijiromin da zancen aureta ranan
banyi barci ba sabida farin ciki amma ban nunama kowaba saima kekashe ido danayi nace
banison ta, ni mamakin kaina nake nine keson karaman yarinya haka yar talakawa, aranan da
mukaje gidansu mahaifin ta yace mana ansa mata rana bikinta saura sati daya zuciyata takusa
bugawa, da gangan nai karyan waya nake nafito ko zan ga wani almajiri ya nunamin waye
isyakan da akace zata aura, ina fitowa naganta tana hira da shi jinai kaman na kashe isyakan
wlh Imam, luckily sainaji yana fada mata inda zashi koda muka tashi tafiya saiban bisu
munkoma kanon ba, adayake nai wayau nadau hoton isyakan saina turama wayan su kanin
abokina dake zaria yana karatu a ABU da abokanshi hoton Isyakan nafada musu inda naji yace
zaije, haka suka je basu ganshi ba suka fadamin saina cemusu to suzo layin su yarinyar su
jirashi, suna zuwa suka kamomin shi aka kaishi hotel din dana sauka, kaga dukan danami kuwa
wlh nakusa harbeshi sabida tsananin kishin yanda na gansu tare suna hira harda wani wai
yasiyo mata ice cream, to saikuma na kwabi kaina akan kissan kai ba halin da musulmi yakama
ta yanayi bane, saina bijiro mishi da ranan biki awajen daurin aure yace yafasa aurenta sanan
namai kyauta sosai namai warning daya tsorata yaron ainun, shekaran jiya saida nakira shi na
rokeshi ya yafemin bansan ko harda alhakin shi yake binaba yanzu ba, yace ya yafemin yanzu
ma yay aure sanan ya bude shago dakuma makaranta da kudin dana bashi" sai yay shiru Imam
yace "ina jinka" ahankali yace "Imam inason Bilkisu sama da yanda kake tunani amma inhar
zan hadu da ita sau dari saina sakata kuka sau dari da hamsin, inci zalinta in gaya mata bakar
magana, har muka tare agidan mu, yanzu haka yan kidnappers sunzo har gida sun dauke min
ita, i think Allah na hukunta nine akan laifuffukan dana mishi" hawayen daya zubomai ne ya
share da sauri yana sauke ajiyan zuciya ahankali yace "na tuba Imam, bazan kara koma ma
aikin alfahasha ba, dan Allah katayani rokon Allah yadawo min da farin cikina Bilkis, ya tsaremin
ita duk inda take, yadawo min da ita cikin koshin lpy, wlh na tuba, na tuba, na tuba, nai
nadaman duk abubuwan danai ada, I love my wife more than life itself, Imam mezanyi Allah ya
yafemin yadawo min da Bilkis?".
♦♦ *SANGARTATTCE* ♦♦




65 - 66


Sassanyar murmushi Imam yamai yace "Allah gafurur Raheem ne, kadage da addu'a kadinga
tashi cikin dare kana rokon Allah, kana gayama Allah bukatun ka, matar ka zata dawo, da izinin
Allah zan tayaka da addu'a banda hakama duk inda take Allah ya tsare maka ita ya kare maka
ita" ahankali yace "Ameen" Imam ya mike ya mikamai hannu yace "tashi na taimaka ma katafi
gida" ahankali yamika ma Imam hannu da taimakon shi ya mike tsaye suka fita daga masallacin
daidai wajen masallacin suka hadu da securities din da Mami ta turo azo adubo mata shi dan
tajishi shiru, mika musu shi Imam yayi suka tafi dashi gida.

Suna shiga cikin gidan idanunshi suka sauka akan motar shi dake parking lot, wajen motar yayi
da taimakon su ya bude, idanunshi ne suka sauka akan jakar Bilkisu daya karba ranan dazata
bata hakan yasa ya mika hannu ya dauko, ahankali ya rungume jakar sosai ajiki yay cikin gida
rike da ita, a parlor ya zauna yana zazzage jakar babu komi ciki sai wayarta da lace dinta da
sauri yadau wayarta yana duddubawa amma akashe take ba chaji, da kyar ya mike yay sama
ya shiga dakin ya makala wayar achaji, tana dan yi 10% ya kunna da sauri, gallery ya shiga da
saurin bala'i kaman mahaukaci nanko yaci karo da hoton ta guda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login