Showing 108001 words to 111000 words out of 124573 words

Chapter 37 - Sangartacce Book Complete Pdf by Maman AbdulShakur.pdf

M Shakur   

09 Nov 2025

3896

numfashi da kyau" karban shi akai daga hanun Abba, polisawan na
murna suna "ashe doguwar suma ce" aka fita dashi shima Abba da bakin shi yakasa shiru sai
"Alhamdulillah, Alhamdulillah yake" aka kinkime shi akai waje dashi, Mami ma haka, sanan
kuma Big Mum mayya mai taurin rai harbi biyu gareta a hannu, biyu akafa, daya a kafadar
haggun, dagata wasu polisawan sukayi suka sakata a motar su itada su Bala da Ayaan ya
raunatar sukai asibitin polisawa da ita.
♦♦ *SANGARTATTCE* ♦♦

Maman Abd Shakur

90 - 91

*Momma!! You're Special!! I love the you in you!! I admire your courage!! Remember Allah is
with you, u are not alone in dis journey, so let's keep fighting and pushing, you u will definitely
reach dat spot dat I picture you to be. All it takes is patient u will overcome this phase of life my
Momma*.




Bayan 2 weeks.

Babban dakine acikin asibitin, yana kwance akan gado sanye da white singlet da aka nannade
sama kadan sabida bandejin dake cikin shi daidai inda aka ciro bullet din, saikuma dogon
wandon jeans, Abba ne zaune kusa dashi da sandar dayake dogarawa yay tafiya dan tunda aka
ciremai bullet din baya iya tafiya saida taimakon Sanda, saikuma Malam wanda yazo duba
Ayaan yauda safe shida Raiyana dan kuka tadinga yi zata bishi ta dubo Bilkisu zuwan suma
saisuka tarar da sabon labari, saikuma Baba Suleman dake zaune akan doguwar kujeran dakin,
gabaki dayan su barin ma Abba yafi ramewa sosai sabida rashin lafiyan Ayaan, bugawa zuciyan
shi yayi abinda ma yahana shi tashi har yanzu kenan dan sosai zuciyar shi tabugu sabida tashin
hankalin daya shiga, inda akamai aiki kuwa harya soma warkewa wanda yauko gobe ma za'a
cire bandejin gabaki daya.

Hankalin Abba sosai yake atashe dan basuga Bilkisu ba kuma duk wani gidajen su saida yasa
aka duba koya boyeta awurinne amma babu ita, saisa addu'a kawai sukeyi Allah ya tashi
kafadar shi yafada musu inda Bilkisu take.

Big Mum kuwa bayan ancire mata bullets din datasha, hanunta da Ayaan yataka yamata wasu
irin karairaya ne da aka kasa gyarawa saidai aka guntule hanun gabaki daya, bayan kwana biyu
aka shigar da case din kotu bayan all d evidence da lawyer dake kare Abba ya gabatar a kotu
nan Alkali yay sentencing life in prison na yunkurin kinsan kai, kidnapping dakuma sauran crime
dinta, taci kuka kaman idanunta su fito da guntulallen hanunta, lawyer Abba ya mikamata
takardan sakin da Abba yabashi ya bata saki uku takara rushewa dawani kukan, suma su Bala
duk prison din aka kaisu sai tsine ma Big Mum suke Wai ita tasasu awanan wahalan shiko pilot
kuka wiwi, yanada aikin shi gashi alhaji na kyautata mai yabiye ma big mum gashinan abinda
tajamai, kuka kam ya Shahi haka aka tattara su akai gidan yari dasu.

***********************



A Abuja kuwa Bilkisu ta tasasu agaba kuka badare ba rana d only maganan da take yi shine ina
yake ina yake, Aaman kaman zai haukace yanda kukan ta ke tadamai da hankali tun yana kiran
number Ayaan ya shiga har yazo yadena shiga gabaki daya, hankalin shi dukya tashi maiya
sami Ayaan? So yake yaje Abujan amma yakasa dan inhar bashi yazo ya lallabata yace mata
gashinan zuwa yana hanya ba batacin abinci, yaudai ya yanke shawara zai tafi Kanon yaje
yadubo meke faruwa sati biyu bawasa ba gashi wani irin mugun zazzabi ta tashi dashi yau, da
kyar Mum ta lallabota tai wanka tafito tana rawan sanyi, kaya tabata tasaka, tabata tea mai zafi
tana karban tea ta ijiye tana girgiza kai tana yatsine fuska, ahankali Mum ta rungumota jikinta
tace "yakuri kisha kinji daughter yauwa yar albarka sha nabaki magani" Mum tai maganan tana
kai tea din bakinta yatsine fuska tayi ta kurbi kadan, ture tea tayi da sauri tana kokarin yin amai
da sauri Mum ta ijiye tea tanason ta dagata amma harta kwaro aman anan kan gado.
"subhannallah sannu yar nan" dagata Mum tayi da taimakon ta tai bayi da ita ta wanke mata
fuska da wuyan data bata sai uban kuka take, jikinta yay mugun zafi hanunta Mum tarike tafito
ta ita tai dakinta da ita kasancewar tariga tabata gadon, abakin kofar dakin sukaci karo da
Aaman duk yay wani irin yana kallon fuskar Bilkisu dake kuka awahale, kallo daya Mum tamai
ta shige da ita dakinta kwantar da ita tayi akan gadonta ta lulllubeta ganin sanyi takeji ta kashe
AC tadawo kusa da ita tana share mata hawaye tana bubbuga bayan ta tana girgiza mata kai
tace "stop crying yar albarka sleep" haka tadinga mata har wani wahalallen bacci yay gaba da
ita tamike tafito daga dakin har lokacin Aaman na inda ta barshi tsaye ya daura kai abango.
"Aaman" takira sunan shi anatse, bude ido yayi ya kalleta kasancewar Mum nurse ce yasa da
sauri yace "Mum meke damunta wani magani zan siyomata?" girgiza kai tayi tace "don't worry"
saikuma ta matso kusa dashi ahankali tace "Aaman ka shirya kaje kano kanemo Ayaan musan
halin dayake ciki, matarshi is pregnant" da sauri Aaman ya kalleta, gyadamai kai tayi tace "yes
she is, please go and find out meke faruwa, kaga magungunan brain dinta sun kare by now ya
kamata tana shan wasu ne dan stage by stage medications ake baka, yanzu kusan 4 days
batasha any ba, please get ready and leave for kano" gyada mata kai yayi ya wuce jikinshi yay
wani irin mugun sanyi da sauri ya share hawayen dasuka dan leko daga idanunshi yay part
dinshi wanka yayi ya shirya cikin white shadda yafito yazo yama Mum sallama sanan yatafi.


*Kano*
Ahankali idanunshi ke motsi yana kokarin budesu da sauri Abba yakama hanunshi yace "Boy,
Boy gani nan anan open ur eyes am with you mah Boy" da sauri Baba da Baba Suleman ma
suka taso suka tsaya akanshi Baba sai tofamai addu'a yake, ahankali yabude idanun dasukai ja
sosai ya daura shi akan fuskar Abba yana kallon su gabaki daya asanyaye, Abba kaman zaiyi
hawaye ya shafa gefen fuskarshi yana murmushi yace "ya kakeji yanzu Boy mekema ciwo?
Sulemanu kira Ibrahim yadubamin shi" bakaramin nauyi zuciyar shi kemai ba kaman an daura
dutse akai shikadai ne abinda kemai ciwo, ahankali yake bude baki ganin haka yasa Abba ya
matsa kusa dashi sosai yakai fuskar shi saitin fuskar shi yace "talk to me mekake so?" murya

chan kasa da kyar yace "wife" sake kallonshi Abba yayi saikuma yakamo hanunshi Wanda ba
karin ruwa ajiki yarike yana kallon fuskar shi anatse yace "Boy bamu ganta ba, dama jira muke
katashi muji ina ka kaita?" shiru yayi idanunshi nadan jujjyawa hakan yasa Abba yahau shafa
goshin shi ganin yana kokarin magana yasa Abba yakai kunenshi saitin bakinshi ahankali yace
"Aaman" da sauri Abba yace "wurin Barrister Aaman?" lumshe ido yayi yabude alamun eh
daidai lokacin kuma Dr Ibrahim ya shigo tareda Baba Suleman.

Taxi daya dauko daga airport bayan ya sauka ne ya sauke shi agaban gidan su Ayaan, fitowa
yayi bayan ya salami driver sai uban kamshi yake farin shaddar jikinshi sai wani wal wal yake,
uban securities din d aka zuba akofar gidanne suka tareshi "wakake nema?" ahankali yace "Dr
Ayaan" jin yakira sunan dan masu gidan yasa suka budemai kofa shikuma ganin basu cemai
komiba yasa yace yana nan Kenan yay cikin gidan, inda aka taba shiga dasu da farkon zuwan
shi yayi a natse, agaban kofa ya tsaya yay sallama batare daya bude kofar ba, Raiyana dake
kitchen da Mami, girki suke yi zasu tafi asibiti Abba yakira wai Ayaan yafarka Sai murna suke.
Kasancewar Mami dukta sallami yan aikin ta yasa ta kalli Raiyana dake sanye da doguwar rigan
atampa ja da dan kwalinta tace "jeki bude kofa naji ana sallama" akunyace tace "to" tajuya da
gudu tafita daga kitchen din tai falo, bude kofar dakin tayi gabaki daya hankalinta nakan TV
dake aiki a falon ana wani film din fada, wani irin dukan uku kirjinshi yayi ganin yarinya mai
kama da Bilkisu exactly bambanci kawai shine wanan tafi Bilkisu tsawo sosai dan doguwa ce,
dan gyaran murya yayi hakan yasa tajuyo da sauri adan rude suka hada ido, dauke kai tayi da
sauri ganin yanda ya tsareta da ido ahankali tace "Mami tace wai ka shigo" juyawa tayi da sauri
ya bita da kallo saida ta shige kitchen sanan ya sauke ajiyar zuciya ya shiga dakin ya zauna
akan daya daga cikin hadaddun kujerun falon.
Ko minti biyu ba'ayi ba Mami tafito daga kitchen din cikin babban mayafin ta tana ganinshi ta
ganeshi murmushi tayi shikuma yadan zamo ya gaidata yace "ina yini Mami, ashe abinda yafaru
kenan Allah kare tsarewa ya kiyaye gaba" Ameen Mami tace "sannu da zuwa Aaman, ya
hanya" murmushi yayi yace "lpy lau Mum, ina Ayaan Mum inata kiranshi baya shiga" nan yabata
labarin komi kaman Mami zatai kuka itama ta sanar dashi abinda yafaru bakaramin tausayi yaji
ba kaman zaiyi kuka ahankali Mami ta mike tace "bari nasa akawo maka lemu muhada abincin
a flask saimu tafi asibitin, mungode sosai da taimakon dakamana" wucewa kitchen tayi ko minti
daya ba'a karaba saiga Raiyana tafito da tray dake dauke da exotic mai sanyi da ruwa da cup
sai dambun nama da cake yanda ya kafeta da ido yasa ta dauke kai jikinta na rawa tazo
gavanshi table taja tadaura akai, ahankali tana kallon kasa tace "Mami tacewai kafara sha
gatanan zuwa" tajuya da sauri zata tafi yace "ke kanwar Bilkisu ce" da sauri ta juyo suka hada
ido ta gyadamai kai tareda sauke idanunta kasa, gyadakai shima yayi saikuma yace "ya
sunanki?" batare data dago kaiba tace "Raiyana" da sauri ta juya tacigaba da tafiya kaman
daga sama taji yace "Raiyanah" dan dago kai tayi suka hada ido da sauri ta juya ta shige
kitchen din kirjinta na bugawa. Ciro wayar shi yayi yay dailing number Mum dinshi dake zaune
adaki kusa da Dad, ringing biyu ta dauka kafin tai magana ma yaji kukan Bilkisu dake kusa
dasu, Mum tace "yaya ka ganshi kuwa" gyada kai yayi saikuma yafada mata anma harbeshi ne
ashe yanzu haka yana asibiti, Abban shi dake wurin yace "bari kawai mutaho da ita kaga shi
kawai taketa tambaya" Mum tace "baban ka yace zamu kawota yanzu" ahankali yace "okay
idan kun sauka za'a zo ataho daku" katse wayar yayi daidai lokacin Mami da Raiyana sun fito

rike da manyan basket dake dauke da kulan abinci da flask, nan yafadan ma Mami su Dad zasu
kawota bakaramin murna tayi ba ta tura driver airport yaje yajurasu sukuma suka wuce hospital.

Ahankali Mami ta tura kofar dakin da aka kwantar da Ayaan ta shiga Aaman da Raiyana biye
da ita kowanen su idanunshi akan Ayaan dake zaune akan gado yay wanka danhar kaya ya
chanza yana sanye da 3quater daya tsayamai a gwuiwa saikuma white t shirt dayasa amma
anannade ta saman cikinshi kadan, bowl din dake dauke da sliced fruits ne a hanunshi yanaci
kadan kadan yana lumshe ido ko kadan bayajin dadin fruits din danma su Abba sun tursasa
shine baiyi niyyan sha ba, da sauri Mami tai kanshi Abba kuma yana ganin Aaman ya washe
baki yace "oyoyo son" shigowa dakin Aaman yayi yana gaida kowa, ahankali Ayaan yadago
kanshi daga kafadar Mami ya kalli Aaman hakan yasa Mami ta tashi takoma kusada Abba
shikuma Aaman yadawo kusa dashi ya zauna zaiyi magana Aaman ya girgiza mai kai yana
murmushi yace "don't worry Mum da Dad dina are on their way zasu kawoma matar ka" dudda
yanda zuciyar shi kemai nauyi saida yay murmushi, dan murmushi Malam yayi Raiyana kuwan
boyewa tayi abayan shi tana dariya itama Allah bata mai sonta haka irin mijin Anty Baby, karfe
uku da minti ishirin wayan Aaman yadau kara dauka yayi da sauri Ayaan dake kwance yafara
kokarin tashi, murmushi kowa na dakin yayi Aaman ya taimaka mai yatashi ya zauna tareda
jingina da pillow, mikewa yayi ya kara wayar a kunne ahankali yace "okay Mum saikun zo" ya
katse wayar yanda Ayaan ke kallonshi yasa yay murmushi yace "gasunan zuwa wai sunga
driver da Mami ta tura" dan lumshe ido yayi, Abba baisan lokacin daya mutsili Mami tariga ba
murya chan kasa yace "look at our handsome Boy" murmushi tayi ta ture hanunshi ta kalli
Raiyana tace "tsabagen doki bakici abinci bafa Raiyana zokici" murmushi tayi akunyace tana
kara labewa abayan Baba dan ita kunyan su takeji barin ma mijin Anty Baby da abokin nan
nashi, ido Ayaan yabude ya kalleta murmushi ya sakar mata kafin ya kara lumshe idon, Baba
yace "badake wai ake magana ba" dan dago kai tayi karaf suka hada ido da Aaman, murguda
mai baki tayi ta kalli Mami tace "Mami banajin yunwa ne yanzu" Abba ne yatashi rike da sandar
shi ya kalli Baba Suleman da Baba yace "kunga muje waje mujira bakin mu, mu shigo dasu"
tashi duk sukayi suka fita dakin yarage daga Ayaan dake zaune jingine da bango ya lumshe ido
sai Aaman dake kusa dashi Mami dakuma Raiyana dake kusada ita tana wasa da yatsun ta.

Ahankali Ayaan ya daura hanunshi akan na Aaman hakan yasa Aaman yadan juyo ya kallai
murmushi yamai murya chan kasa yace "thank yhu" baki Aaman yabude zaiyi magana aka
bude kofar dakin da sauri ya juya Mum dinshi da Dad dinshine suka shigo da fara'a akan
fuskokin su, Mami na ganinsu ta shaida iyayen shine sabida kaman gaisuwa sukai na mutunci
da girmamawa ta gode musu, Raiyana ma ta gaidasu akunyace da kyar Ayaan yakara bude
idanunshi duka yana kallon kofa ganin baiga Wife ba, da kyar ya iya tattara natsuwar shi ya
gaidasu ahankali, amsawa sukayi sunamai sannu da kuma jajen abinda yafaru saiga Dr Ibrahim
ya shigo dakin murmushi kwance kan fuskar shi ya kalli Ayaan da sai kallon kofa yake yace "Dr
we are going for scanning" daure fuska yayi yacigaba da kallon kofan, ko damuwa Dr Ibrahim
baiyi ba ya kwantar dashi ahankali ya gyara gadon su Mami suka mammatsa ya gungura shi ya
fitar dashi daga dakin, su Abba na ganin anfito dashi suka fito daga inda suka labe kaman wasu
yara Abba yawani kashe da Baba Suleman suna dariya, sanan suka shiga dakin gaisuwa sosai
akayi kafin dukansu su dunguma su fito aka shishiga mota sai gida bini bini Raiyana duk inta

dago kai sai sun hada ido da Aaman, tsaki tayi tace "tama godema Allah dama yau zasu tafi
xaria wanan mutumin ya dameta".

Office dinshi dayaga Dr Ibrahim ya bude da key ya shiga dashi yasa ya juyo ya kalleshi, gira
daya ya daga mishi yace "wat? Anan za'ai scanning din to" maida kofar office din yayi yarufe, ya
dawo inda yake da taimakon shi ya sakko daga gadon yana tafiya ahankali yabude bedroom ya
shiga dashi akan gadon da aka gyara fess ya kwantar dashi ya dauko wayar shi da Abba
yabashi ya ijiyemai kusa dashi sanan ya mike yace "am coming bari naje na dauko abinda nake
bukata, I think if ur condition improve zuwa gobe saina sallameka ko patient" dan hararan shi
Ayaan yayi saikuma da sauri murya chan kasa yace "please kiramin Pops awaje where is wife,
jiyaye ranshi yawani irin baci zafin da zuciyar shi tayi yasa da sauri kuma ya saki ranshi karya
illatar da kanshi, Dr Ibrahim daya gama karance reaction dinshi yafita daga dakin yana
murmushi ya tura gadon yafita dashi daga office din, ahankali ya tura kofar office dinshi ya shiga
Bilkisu dake zaune akan kujeran office dinshi Sai hawaye take sharewa da hijabi dan tagaji da
kuka mai karfi yasa takoma hawaye kawai. Shigowa yayi yace "tashi muje na kaiki wurin shi" da
sauri ta kallai, gyada mata kai yayi hakan yasa ta mike da sauri hartana nema tafadi da sauri
yace "easy" yajuya yafita tabishi abaya, ahankali yabude kofar office din Ayaan ya kalleta yanda
take share hawaye sai abinma yaso bashi dariya yace "stop crying go inside yana cikin dakin"
yanuna mata kofar, gyada mai kai tayi ta shiga ya rufo musu kofar yay office dinshi file din
Ayaan din yaduba yana karantawa probably ma gobe zai sallame shi dan heart dinshi ne
matsalan dazaran yarage nauyin zai sallameshi.

Saida tagama kalle kallen office din sanan tabude kofar bedroom din ta shiga idanunshi a
lunshe amma ba bacci yakeba, wani irin bugawa kirjinta keyi tana sanya shi a ido takasa daina
kallonshi, wani irin kuka mai karfi tafashe da shi tana kallonshi da sauri ya ware ido ya kalli
saitin inda yakejin kukan da harya mutu bazai manta kona wayeba, kasa dena kallonta yayi
bakaramin ramewa tayiba duktai zuru zuru, ahankali yabude mata hannu yana kallon kwayar
idonta alamun tazo dawani irin gudu taje tafada kanshi takankameshi tasaki wani irin kuka tana
dukan kirjinshi sosai, hanun nata yarike yana girgiza mata kai yakai hanun saitin bakinshi yama
hanun peck tareda kara gyarata ajikinshi ya kankameta sosai yakasa magana sai ajiyar zuciya
dayake saukewa, sunfi minti goma ahaka da sauri ta sakeshi hango bandeji datayi acikin shi
tazo ta tsugunna agaban gadon tana kallon wurin tana kallonshi, murmushi yayi ya kamo
hanunta da sauri ta mike tana kallon ciwon, hannu yasa ya cire hijabin jikinta ya ijiye agefe ya
tsaya yana kallonta riga da skirt na atampa kore ne ajikinta sai gashinta da aka mata kitso
shuku yan kanana, ta rame saidai kuma ta ciko sosai abaya da kirji, ahankali yajawota ya
zaunar da ita abakin gadon, hanunshi ya daura akan wuyanta jin yanda take running
temperature ganin yanda take kallon ciwon har lokacin yasa ya juyo da kanta goshin shi ya
daura akan nata murya chan kasa yace "you are sick Baby" janye goshinta tayi daga nashi ta
koma ta tsugununna kusa da cikin shi tana kallon bandejin tai raurau da ido zata fara kuka
hanunta ya kamo ya janyota jikinshi yana dan murmushi ya juyo da fuskarta yana kallon kwayar
idonta, fashewa tayi da kuka saikuma ta rungumeshi, murmushi yasake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login