Showing 1 words to 3000 words out of 124573 words
Chapter 1 - Sangartacce Book Complete Pdf by Maman AbdulShakur.pdf

Compiled By Umar Dalha Funtua.
♦♦♦
*SANGARTATTCE*♦♦♦
Maman Abd Shakur
1...
Free page
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai.
"wayyo Allah na Baba mutuwa zanyi, wayyo Mama huramin cikin" mata biyune suka zagayeta
akan tabarman dawasu yara mata guda biyu dake tsakar gidan dayasha simenti kal kal dashi
duk sunyi zuru zuru, kana ganinsu kaga tashin hankali kwance akan fuskarsu, chan ta gefen
tabarman kuma wajajen inda kafanta yake wani dan tsohone haka dake sanye da babbar riga
dakuma yar hula daya zagayeta da rawani irin na malamai dinan ya rike kofin silver yakara
abaki yanata addu'o'i aciki anatse, ihu takara yi ta dage rigarta sama tabude daidai cikinta dake
nan kaman bata tabacin abinci ba, ta gefen haggun cikin ya dan kumbura idan kaga wajen
saika rantse wani irin babban kurjine yafito ya kumbura haka yay ruwa zai fashe, ihu tasake yi
tariko hannayen matan dake kanta tace "wayyo Allah Mamammu na shiga uku, azaba Mama
wayyo, azaba yakemin" tasaki hanunsu tana ihu "Baba Baba baba kiranka nakefa, wayyyo Allah
na ba banu ni" wani irin ihu take ta rirrike hannayansu gam tana nishi, wajen ciwon cikin kuwa
sai balbal yake yanda kasan halita mai rai ne acikin wurin, duk ihun ta yacika gidan, tsabagen
takaici ma daya daga cikin matayen wacce itace mahaifiyarta taja tsaki, hakan yasa dayar ta
goge zufan datake yi agoshi, takamo fuskarta da hanunta tarike tace "haba Balkisu, iye mai
gadon zinare, ki daure mana baga baban kinan namiki addu'a aruwaba, kefa mai dauriya ce,
jaruma, kinga Layla da Raiyana zasuce ke raguwa cefa gashima sai kallonki suke" girgiza kai
tayi tawani irin kece da kuka da ihu harda shesheka tace "ni kukiramin Baaba wlh, Baaba tazo,
Baaba kizo ki taimakeni" tafara shure kafa idanun nan sunyi jajir tace "Baba, Baba, Muji, wayyo
Allah na Mujittapa kuzo kutaimake ni, Shato kuzu dan Allah na shiga uku, wayyo Mama
dubamin kiga kodai barkewa cikin yakeyi ne?" tawani irin buga ihu hakan yasa mahaifiyarta
dake kanta ta buge bakinta da karfi tace "kewai baki iya kiran sunan Allah bane banziya kawai"
daidai lokacin Baba ya cire cup daga bakinshi ya kalli Uwargidan yace "dagomin ita Zainaba"
dagota tayi ahankali sai wani uban nishi take tana cije baki tace "tsaya tsaya uhmm" tsayawa
tayi tana kallonta cike da tausayi, hannu budurwan tasa akan kafadar matar tareda runtse ido
da karfi tana nishi tace "tona shirya" har Mama saida tasa hannu suka dagota zaune ahankali
wani irin ihu tayi kaman zata mutu "ya isa, ya isa, yayi" suka jinginar da ita ajikin bango,
kafamata kofin Baba yay abaki ta kurbi ruwan sosai tasha tana kara dage rigar atampan jikin ta
sama, ragowan ruwan Baba ya debo yay addu'a zai shafamata akan kullutun da sauri tarike
hanunshi tana ihu tana kuka tace "Baba wlh azaba yakemin, in kanama Allah karka tabamin,
kaji dan yarasulullahi" hanunta Mama dake kanta ta buge tana wurga mata wani mugun kallo,
hakan yasa Baba ya girgiza kai ya shafamata ruwan awajen tana wani irin shegen ihu da duk
yacika musu kunne, tashi Baba yay ya kalli mahaifiyarta ya mika mata cup din yace "bayan awa
daya kikara bata Amina, bari nakoma zaure wajen dalibai" jiki asanyaye ta karba tace "to
malam" juyawa yayi yay hanyar zaure bude kofa yayi sanan ya daga asabari dazai sadashi da
zauren yafita, almajirai ne cike a zauren sunata karatu da alo, ga wasu manya akansu dake rike
da bulala suna lura dasu, bangon zauren duk jakunkunan almajiran ne dakuma taburmai
dasuke kwana akai dan zauren nada girma sosai, daliban na ganinshi suka kara karfin karatun
dasuke, fita yayi daga zauren zuwa kofar gida nan ma wasu almajiran ne akan simentin kofar
gidan dayawa sunata karatu da alo, anyi babbar runfa daya kare kofar gidan sabida koda ana
ruwan sama dan wasu almajiran anan waje suke kwana, ga robobin almajiran cike akan dankali
dan dazaran karfe biyu tayi zasu tsaya sai ayi salla kowa yatafi bara, daga chan gefen kofar
gidan kuma lungu ne dayasa suka gineshi dajar kasa aka zagaye suka maida bayi, anan
almajiran suke wanka suke dai komi nasu sanan a kofar gidan akwai rijiya da guga dasuke
diban ruwa, zama yayi akan tabarma da aka wareshi musamman tashi ce dan akwai yar
dadduma mai taushi akai ya zauna tareda yin bismilla yanajan chasbaha, yana bin kowani
dalibin dake wurin yana karatu da kallo, wani dalibi babba dan yana daga cikin wayanda ke kula
da sauran almajiran ne yazo kusa da malam ya zauna tareda tankawshe kafa yadan dukar
dakai yace "Allah taimaki Malam, Allah gafarta ma Malam, Allah kare mana Malam" ahankali
Baba ya ijiye charbin ya kalli yaron yace "sun biya karatun da kyau Isyaka?" "i sunbiya Malam,
na muhammadu ne kawai bai kawo da kyau ba amma nakara maimaita mai" murmushi Malam
yayi tareda kishingida da bango yace "masha Allah to, daukomin Al Qur'ani na nabarshi a zaure
saika biyamin naka inji" dan kallonshi matashin yayi saikuma ya sunkuyar da kai yace "Malam
ya jikin Balkisun?" ajiyar zuciya Malam ya sauke yace "da sauki namata addu'a zata sami lpy
nan bada jimawaba" cike da damuwa Isyaka yatashi yabar wajen zuwa zauren dan dauko
abinda Malam ya aikeshi.
Gyangyadi tafara yi anan wajen a zaune, hakan yasa duk suka sauke ijiyar zuciya, Uwargidan
dasuke kira da Umma tamike ta kalli Maman Bilkisun tace "sha biyu tayi bari na daura girki
Amina" kallon yaran daduk sai kallon Bilkisu dake nan zaune tana gyangyadi suke tace "ai sai
atashi aje ataya Umma aiki ko" hijabi Raiyana ta cire wacce ita kebin Bilkisu shekaran ta 15
tamikama Layla hijabin wacce take auta shekaran ta 8 tace "ungo kaimin daki" karba Layla tayi
ta wuce dakin su ta ijiye tafito suka karasa kitchen din jajjage Umma tasa Raiyana itakuma
Layla Umma tace "tahura mata wutar ta kama" tafice daga kitchen din zuwa tsakar gida dan
tankaden tuwo.
Layla dake fifita wuta ne ta juyo ta kalli Raiyana dake jajjage, ajiye maficin tayi tazo kusa da
Raiyana ta tsaya kaman zatai kuka tace "Anty Raiyana maisa Baba bazai kai Anty Baby asibiti
ba, kinga ko koyau a makarantar mu anmana primary science fa, ance idan abu yafito acikin ka
yay babba har yana motsi operation akeyi, Allah kuwa, Baba kuma yanata mata karatu tanasha
da dafa mata ganye maisa bazaice aje asibiti ba" tunda take maganan Raiyana ta tsayar da
jajjagen tana kallonta, Umma ne ta shigo kitchen din ta kallesu tace "surutun me kukeyi ba aiki
nasaku ba?" baki Layla tabude zatai magana Raiyana ta girgiza mata kai hakan yasa tai shiru
takoma gaban murhun tacigaba da fifita, abinda Umma ta shigo dauka ta dauka tafice daga
kitchen din, hakan yasa Raiyana tadawo wajen murhun ta tsugunna tace "karki kara fadin
maganan nan, Baba bai yarda da maganin asibiti ba kuma idan yajiki kinsan sauran, karki
karayin maganan kinji" ahankali Layla ta gyada mata kai kowaccen su tacigaba da aikin da aka
sakata.
Wuraren sha biyu da rabi ta farka azabure ta mike Mama dake zaune gefenta tana dama ma
malam fura ta kalleta tace "ya cikin" hanyar dakinsu tayi ta daga labule ta kalli agogo sanan ta
kalli Mama tace "Mama nakusa lattin makaranta shine baku tasheni ba" turo baki tayi tai gaban
rijiya tadau botiki zataja ruwa, tabe baki Mama tayi tacigaba da dama furan ta, agurguje taje
tayo wanka tafito daure da zani a kirji tashiga daki da gudu, uwar dakan su ta shiga dake nan
agyare ko ina dan gado ne madaidaici sai ledan daki da aka shimfide, tsugunnawa tayi tajawo
ganamasgo daga karkashin gado ta bude taciro kayan makarantar ta dake nan agoge, purple
dogon wandon tafara sawa sanan tasaka rigar dayakai har gwuiwa fara tana dan bata fuska
sabida yanda cikin ke mata ciwo kadan kadan yanzu ba kaman dazu ga, gaban madubi taje ta
shafa farar hoda tasaka kwali, basilin ta lakato ta shafa akan pink and black lips dinta, dan lips
dinta daga tsakiyar su pink ne sosai sai kasan kuma baki kaman ta shafa janbaki haka suke
gashi sunwani irin tattare gwanin kyau and sexy, idan ka kalla kaman nama, komawa gadon tayi
tasanya farin hijabin daya wuce gwuiwa, ta maida ganamasgo karkashin gadon tadau yar
jakarta da litattafan ta keciki tafito ta zauna adakalin bakin kofa tana kokarin saka safa da
takalmin makaranta Umma da fitowar ta daga kitchen kenan tace "Baby yaushe kika warke
dahar zaki tafi makarantar allazi boko?" dan murmushi tayi daya bayyanar da beauty point dinta
tace "Umma yafa dena fa wlh, kuma kinga nice monitor aji chalk natare dani dole nakai" baki
Umma ta kama tace "su manito manya" dariya Balkisu tasaki harda fadawa jikin Mama dake
kan tabarma tace "ana monito kina manito Umma" tacigaba da dariya kaman ba ita ke ihu
dazuba, rankwashi Mama tasakin mata akai tace "tashi min akan jiki kafin na juye miki furan
nan akan kayan makarantar nan" ahankali ta tashi kaman zatai kuka ta zauna kusa da ita
Umma ta bude kullin zani taciro naira hamsin ta mikamata tace "gashi kihau mota, daga fillin
mallawa zuwa dogon bauchi da shegen nisa keda baki da lpy" karba tayi cike da murna tace
"nagode Umma na Allah barmin ke" komawa tayi kusa da Mama tana kallon furan, kaman zatai
kuka tace "Mama dan sammin kinga ba'a gama abincin rana ba karnaje makaranta haka da
yunwa" hararan ta Mama tayi tace "kwadayayya" dariya tayi tace "eh naji Mama kidan ban" da
sauri ta shiga daki ta dauko karamin kofin roba Maman ta tsiya mata dan daidai ta shanye
harda saka yatsa tana kakkale kofin ta lashe tass sanan ta ijiye kofin tana goge baki tace
"nagode Mama natafi" da sauri tadau jakarta ta leka kitchen taga su Raiyana na kwasan tuwo
tace "natafi" atare suka mata addu'a, Mama tace "salla fa?" "a school zanyi Mama" tabude kofa
sanan ta daga asabari tafita.
[7/15, 12:17 PM] Ummi Tandama: ♦♦♦ *SANGARTATTCE*♦♦♦
Maman Abd Shakur
2 - 3
Free page
Zaure tawuce tana bin almajiran wajen da kallo kafin ta fita kofar gida tai wajen Baba da tunda
tafito ita yake kallo, tsugunnawa tai agabanshi tawani kwaye fuska kaman zatai kuka ahankali
tace "Baba natafi makaranta amma ni banci komiba ba'a gama abincin ranaba" girgiza kai
kawai Malam yayi sanin halin yar tashi, hakan yasa ya saka hannu cikin aljihun babbar rigar
dake jikinshi yaciro dari yabata da sauri ta karba tana murmushi tace "nagode Babana, Allah
biyaka natafi" "ya cikin?" ya tambayeta anatse, tashi tayi tana kokarin saka kudin ajaka sanan
tace "yadena Baba tundazu, natafi" "adawo lpy" tajuya ta fita tana waige waigen zauren, fitowa
tayi tafara tafiya a layinsu daya yawaitu da bishiyoyin dogon yaro, dadan sauri take tafiya
sabida takai bakin titi tahau boss dazai kaita school, wani gida dan madaidaici dake nan cikin
layinsu ta shiga harda dan gudan ta dan sauri take wata matace yar dattijuwa haka, tana zaune
tana tuyan waina anan tsakar gidan ahankali kaman wacce kwai ya fashewa aciki ta karasa
kusa da matar wacce batama lura da itaba saidai kawai taji mutum akanta, fashewa tayi da
kuka kaman wacce aka doka hakan yasa matar ta rike baki tace "mekuma aka miki iya
shagwaba iya sonjiki Bilkisu" kara fashewa tai da kuka tana buga kafa akasa cikin kukan tace
"tun safe banda lpy kokizo ki dubani kinata wainar saidawa abinki ko Baaba" arude matar tace
"ni? Haba tagidana ai kema kinsan inda nasan bakida lpy tuni xan ijiye wainar nan nazo, dena
kukan keko, halan cikin ne yatashi?" gyada kai tayi tana share hawayen Baaba tace "shiga daki
ki dauko kular ki nasaka miki wainar ki kitafi kinga yau kinyi latti" da sauri tashiga dakin Baaba
tana kokarin daukar kulan tace "Baaba ina Muji?" daga tachan waje Baaba tace "yafita da Keke
napep waiko zai sami fasinja, saiyau ya daukota daga gareji" daidai nan tafito tamika ma Baaba
kular, karba tayi tazuba mata wainar dayawa sanan ta baza mata kuli dayawa akai ta rufe kulan
tabata tareda ciro hamsin tace "gashi adawo lpy" karba kulan tayi tace "kibar kudin Baba
yabani, natafi Baaba saina dawo" "adawo lpy yar albarka banda wasa a aji kinji yar gidana" fita
tayi tana murmushi tana mugun son Baaba, yayar mamanta ne haka suke kiranta, bayan tai
aure data haifi Mujittapa (Mustapha) danta na farko shine Maman su lokacin kafin tai aure tazo
tayata raino aiko malam yana ganin Maman su ya like mata ya nace yanaso, bayan wani dan
lokaci fa suka tafi kauyen su dake chan hanyar gombe kauyen bojude lokacin tun kafin iyayensu
su rasu akai bikin aka kawota gidan malam, Umma bata da matsala hakan yasa malam ya hade
kansu suna zaman lpy, yayan malam 8, Umma yaranta 5 duka maza wanda duk malam yatura
su nijar wajen wani babban abokin shi malami yin karatun addini awani babbar makarantar shi,
yanzu ma watan su daya da tafiya kenan sai bayan shekara biyar zasu dawo dan makarantar
har certificate ake badawa inka gama, sai kuma maman su data haifi su uku Balkisu, Raiyana
da Layla, dukan su malam yasasu a government girls secondary school ne Raiyana da Layla na
safe suke zuwa, itakuma dayake SS ne rana ne nata.
Karasowa bakin titi tayi ta tsaya tana jiran Bus wata makauniya tagani ita da yarta suna ta bara
a shagunonin kan hanya wai tun safe basuci abinci ba, ba karamin tausayi suka bataba, tana
kallonsu suka koma kan dakali suka zauna yarinyar nata kuka, jakarta ta laluba taciro naira
darin da Baba yabata ta karasa kan dakalin dataga sun zauna, yarinyar nata kuka wai yunwa
takeji maman na lallashin ta, ahankali ta duka darin ta mikama yarinyar tareda mata murmushi
tace "dena kuka gashi" karba yarinyar tayi tana fadama maman ta bakaramin dadi matar tajiba
tace "mungode yar nan, ubangiji Allah ya miki albarka ya raya miki yaranki" dariya Bilkisu tayi
sosai tace "Ameen amma nibanyi aure ba mama" washe baki makauniyar tayi tace "to ubangiji
Allah ya baki miji nagari wanda zai saki farin ciki sama da wanan dakika samu" ahankali tace
"Ameen nagode" ta dagama karamar yarinyar hannu sanan tajuya ta tare bus din dake zuwa ta
shiga har lokacin yarinyar nata dagamata hannu itama daga mata hannun tayi har bus yawuce
ta daina hangosu.
Allah yasota koda ta shiga school ana gab dafara taran latti, da sauri tafara yin masallaci tai
salla sanan tafito tai aji lokacin duk yan aji sun zauna ana ganinta akai tsit kowa nata kallonta
hakan yasa tasha jinin jikinta, kujeran layi nabiyu ta wuce ta tsaya agaban sit din ganin duk su
Aisha Shehu sun cike Walawa ta zauna awurinta, daure fuska tayi ta kalli Walawa tace "wlh
kitashin min daga wuri ai chan ne sit dinki" tanuna kujeran bayan nasu, hararan ta Walawa tayi
ta cigaba da zanen flower datake yi a paper, su Aisha Shehu dai sai dariya suke kasa kasa dan
dama dagangan Walawa tazauna neman tsokana ne, ganin ko kulata Walawa batayi ba yasa
taji abin ya mugun bata mata rai hakan yasa ta fizge byron hanun Walawa afadace tace
"badake nake magana ba, kinga kitashi" kaman jira Walawa takeyi ta mike tsaye fuska a daure
ta kalli su Fateema da Fa'za dake kusa da ita suma duk suna dariya kasa kasa tace "ku
matsamin na fitan ma almasifatu daga wuri" gyaggyara kafa sukayi Walawa tafara tafiya hakan
yasa Bilkisu tazo daidai bakin sit din tana jiran Walawa tafito itakuma ta shiga fuskar nan nata
adaure fitowa Walawa tayi, saida tazo gab da Bilkisu tasa hannu ta taba mata nono, atsorace
Bilkisu ta tsugunna a wurin tareda fasa ihu "wayyo Allah" ta kankame jikinta, aiko duka ajin
sukahau ihu da dariya, su Aisha Shehu dasu Fa'iza harda buga benci suna dariya, Walawa ko
hanyar kofa tayi ta tsugunna tana dariya harda rike ciki, gabaki daya ajin dariya ake Aisha
Shehu tace "babu wacce ba'a tabama nono a ajinan ba, kece kullum kiki yarda yar malam,
yaudai an taba dama gasu manya manya" aikuwa kowa dariya suna bubbuga benci irin abun
yay musu mugun sugar dinan, saida ta goge hawayen datake yi sanan ta mike tazo gaban
Aisha Shehu tace "eh aini kinsan ba yar iska bace irinku ba masu wasan taba nono a school"
tana fadin haka tai hanyar kofa wurin Walawa, Aisha Shehu tabita da harara tace "to uban waye
yan iskan, ba wasa bane kowa ajin nan an taba nashi saike, koba hakabane?" ta tambayi su
Fa'iza da Fateema suma duk dariyan suke harda kama ciki danba karamin dadi abun yamusu
ba yau yanda aka kama na Bilkisu yar malam yau, dan ita kadaice bata yarda amata wanan
iskancin a aji gashi yau an shammaceta anyi kowa dadi yakeji. Kan Walawa Bilkisu tayi wacce
tun kafin tazo kanta tahade hannu tana dariya tace "haba Billy yar malam, yakuri mana kawas ai
bankama ba tabawa kawai nayifa dan nasan bakiso wlh bazan karaba, yakuri" kamota Bilkisu
tayi ta durma mata duddu abaya daidai lokacin wata malamar english dinsu ta shigo aji hakan
yasa duk suka koma wajen zamansu kowa ya natsu.
(oya name abunda kukayi zamanin secondary school?? Barinma wayanda sukayi girls school
kadaií ½í¸‚)
Wuraren 4 suka fito break da salla, bayan sunyi salla duk tare suka tayata cin wainar dan dama
sune kawayen nata Aisha Shehu Walawa da Fa'ixa saikuma Fateema, bayan sungama
ciyeciyen su sanan suka koma class, sai wuraren biyar da rabi aka tashe su duk suka fito suna
tafiya har suka gangaro bakin titi suka shiga bus kowacce tai gidansu.
Gidan Umma tafara biyawa ta ijiye kulan sanan tafito akofar gidansu tahadu da Isyaka yana
alwalan sallan magriba, murmushi tamai hakan shima yamata murmushi da sauri ta shiga gida
ta gaida Baba sanan tawuce cikin gida. Babu kowa a tsakar gidan duk sun shiga daki hakan
yasa taja ruwa tazuba a buta tai bayin su bayan tafito