Follow us on social media
Showing 3001 words to 6000 words out of 29865 words
Chapter 2 - SO MAKAHO NE Rikicin Zukata by Qwinn minerhly
ki kwanta ko my baby?" Sai gimbiya ta ɗaga mata kai alamar "eh'
To nan fa ta nufi dinning area ta zauna ta buɗe womers ɗin ta zuba farfesun kayan ciki ta dan ci kaɗan ta kora da hot coffee ta miƙe taje tayiwa mum sallama ta tafi part ɗinta.
To kafin gimbiya ta kwanta sai ta nufi dressing mirror ɗinta dake cikin bedroom ɗin ɗakinta, ta zauna tana duba leɓenta daya mata nauyi ya ku mayi jah sosai, kawai sai naga murmushi akan fuskar ta wanda ita kaɗai ta san manufar sa.
To bayan gimbiya ta kwanta sai bacci ya gagara, sai kalaman wannan kyakyawan mutumin me siffar aljanu ne yake tayi mata yawo a kunnuwan ta.
"" Ke!!! Ke wacece ke dazaki shigo gurin nan? Ehe nace who are u? Daga gani ke ƙaramar mara kunya ce , to bari kiji wlh sainayi maganinki stupid girl"'
Gimbiya ta dada yin wani juyi a katon haɗaɗɗan royal bed ɗinta .
""'' ke becareful danni ba tsaran ki bane da zakizo kina min misbehave anan wlh kinci sa'a yarinya sauri nake yi yau da saikin yabawa aya zaƙinta nonsense girl""'
Firgigit gimbiya ta miƙe zaune ta mari kumatun ta tace cikin tsawa,
"Wai what's going up with me!!! Wlh ba zai yuba,
Ka zageni
Ka buge ni
Kaci min mutunci,
Kuma sannan na dawo gida ka hana ni bacci,
toh wlh saina rama.
Ke zuciyata bazaki cuce ni ba, wlh imporsible don baka daƙi banza ehe.
To anan fa ta kwanta barci, da ƙyar wani bacci me nauyi ya kwashe ta inda tayi ta mafarke mafarke kuma duk akan D.Ashmir.
""Hmm niko nace tofah""
*GIDAN* *DARAUTA*
comments and I will type more for you my fans
✍️✍️✍️✍️
_Taku_
_Qwinn_ _minrerhly_
_Mrs_ _Yusuf_
❤️❤️❤️❤️
[8/26, 11:22 PM] Qwinn Minerhly: *SO MAKAHO NE*
(LOVE IS BLIND)
🖤🖤🖤🖤🖤
🖤🖤🖤🖤🖤
🖤🖤🖤🖤🖤
🖤🖤🖤🖤🖤
__My_ _first_ _novel_ , _inafatan_ _zaya_ _nishadantar_ _daku_ ya ilimantar _da_ _ku_ ,
_Short_ _and_ _romantic__.
*_Writer* ✍️✍️✍️✍️
*Na* *Qwinn* *minerhly*
_Masoyan_ _novel_ _ɗina_ _ina_ _godiya_ _da_ _nuna_ _kaunaku_ _ga_ _wannan_ _book_ _din_ _da_ _kuma_ _addu'oin_ _ku_ ,
_Allah_ _yabar kauna_ .
Part 15_20
*GIDAN* *SARAUTA*
MAI MARTABA Sarki *BELLO MUHAMMAD ll Sarki ne agarin Kano wanda ya gada a gun mahaifin shi, asalin su *FULANI* ne.
sarauta ce tun na iyaye da kakanni.
Mahaifin sa wato *SARKI* *MUHAMMAD* *YUNUS* ya mutu ne shekaru kusan ashirin, wanda bayan mutuwar sa da sati uku aka naɗa ɗansa kuma magajin sa wato Sarki Bello Muhammad ll, Wanda alokacin yanada mata ɗaya, wato *Hajiya* *Kilishi* da kuma ɗa guda ɗaya, wato *Adnan* wanda alokacin bai fi 8yrs ba.
Hajiya Maryam wato (Kilishi) dai ƙanwa ce agun *Sarkin* *Karaye* , bafulatana ce ta usuli, kyakkyawa ce ba laifi.
Tunda akayi auran, ta samu cikin yarima wato (Adnan) bayan ta haife shi, bata ƙara samun wani cikin ba.
Sai da tayi shekara biyar da haihuwar yarima tukun ta samu wani cikin,
Inda ta haifi ya mace saide ta fito babu rai, to tun daga nan bata ƙara samun wani cikin ba.
Wanda alokacin ne aka fara bawa yarima wani irin gata wanda har ya so yayi yawa musamman agun mahaifiyar sa, wanda take ganin babu ya ita tunda ta haifi ɗa namiji kuma Magaji, wanda haka ne yayi sanadiyar tasowar yarima cikin rashin tarbiyya da ɗaha.
Wannan kenan...
Bayan shekara kamar huɗu mai martaba ya kara aure inda ya auro yar *Sarkin* *Borno* Hajiya Turai wato (Fulani).
Asalin ta shuwa'arab ne,
( "Kar ku ji na kirata da fulani kuma tana shuwa, to kunsan gidan sarauta yana da tsari, saboda suna da al'ada, musamman matan sarki akwai sunayen da a ke kiran su dashi wanda bana yanka ba indai a gidan sarauta suke aure, to a taƙaice dai sunayen matan sarki ne kilishi da fulani").
Hajiya Turai dai Arab ce wanda take da wani irin kyan gaske harta doke uwar gida, wanda hakan ne yayi sanadin haddasa wata iriyar tsana, tsakanin ta da hajiya kilishi.
A gaskiya kilishi ta tsani fulani, a cewar ta wai "gata da kyau kuma mai martaba yana mugun son ta" to wannan ne silar rashin jituwar su.
To bayan auran mai martaba da fulani ne da shekara biyu ta haifi kyakkyawar yarta mai kama daita wato *Gimbiya* *Nihal*
Wacce ta taso cikin gatan uwa da uba domin mai martaba yana son ya mace sosai, ga kuma soyayyar mahaifiyar ta.
To princess nihal dai yarinya ce wacce ta taso cikin gata da kuma kulawa, shi yasa ta taso bata fiya son jama'a ba, sai iyayenta, To tunda tayi primary, tagama tayi secondary a Abuja na yayan shuwa'gabanni zallah, me suna (INTERNATIONAL DAILY CARE). wanda a yanzu tana University ne, a kasar Wow Russia under American.
To tunda gimbiya ta taso bata da wasu ƙawaye wanda har tayi primary nd secondary School, ƙawaye suna ta binta har gidansu wai suna son suyi ƙawance amma gimbiya taƙi basu fuska, kuma suma ya'yan manya ne fa, but ita kawai bata son hayaniya ne da disturbance,
Aduniyar nan ƙawar gimbiya ɗaya ce wacce suka haɗu daita a achan wow Russian, school ɗinsu ɗaya amma course kowa da nashi, sun haɗu daita ne dalilin anfito a makaranta zasu shiga wani restaurant me suna (Special Gift Restaurant) Wanda gimbiya bata taɓa zuwa gun cin abinci ba, wani take zuwa me suna (Small Chops) to sai take jin wasu daga cikin course mate ɗinta suna labarin special gift restaurant, to shine fa a yau ta ce bari taje chan taji ya abincin gun yake.
Shi ne fa yau taje chan har tayi ƙawa achan, me suna *Noor* Wanda saida suka fara faɗa kafin ƙawancen inda gimbiya ce ta fara zuwa gun sai Peter ɗin yazo ya tambaye ta me take so? cikin harshen turanci ta bashi list ya tafi, to sai ga noor ta shigo ciki, to Kasan cewar ta saba da masu gurin kuma sun san abinda take so kawai tana shigowa zasu miƙo mata, to yau ma haka akayi, tana zuwa saita nemi kujera ta zauna kawai sai Peter ya kawo wa noor abinda tafiso a gurin, karaf sai akan idon gimbiya aikam ta miƙe ta taho wajan tana zuwa tafara bala'i da harshen turanci cewar "kai kaisa ni na fara zuwa gun amma sai wata tazo a bata itaɗin wace ce?wlh baku isa ba", nan fa noor ta tanka mata tace "ke din wace ce kema? da baza aji dani ba dan kina gurin"? nan fa faɗa ya ɓarke tsakanin su,
Inda gimbiya tace oh! tambaya ta kike wace ce ni?"to "sunana Princess Nihal, ya ce ga SARKIN KANO MAI MARTABA BELLO MUHAMMAD ll". Nan taga noor ko gizau ba tayi ba saima kwafa da tayi tace to nima kina son sanin wacece ni? "sunana Noor ya ce agun GOVERNOR ABDULKARIM NASIR GAYA". Tofah!
Kowa yana da iko kenan?
Nan fa guri yayi tsit kamar ba mutane dama peters ɗin suna ta basu hakuri tun ɗazu, to amma yanzu kowanne su yayi shock da jin abinda junan su suka faɗa musamman gimbiya, sai fa kallon kallo sukewa juna,inda noor take mamakin irin kyaun da gimbiya take dashi to sai dai a ɓangaran gimbiya kuma sai da tafi noor shock sabida bata taba ganin me irin kyan noor ba.
Niko nace " tofah ya'yan masu kyau an haɗu gu ɗaya"
to nan dai kowa ya watse sai gimbiya da noor kaɗai suka ragu inda gimbiya ta fasa cin abincin tayi tafiyar ta, ita kuma noor tayi zaman ta taci abinci, tukun tayi tafiyar ta.
To washe gari ma hakan ce ta faru sun kuma haɗuwa a gunrin cin abincin, To anan ne gimbiya ta zo har inda noor take tayi mata sallama itama noor ta amsa da fara'a, dama noor ba baƙuwar zafi bace ita, nan suka zauna fira ta ɓarke tsakanin su dama noor gwanace a surutu,
To silar ƙawancen gimbiya da noor kenan.
Inda sukayi wata irin shaƙuwa a tsakaninsu idan ɗaya bai ga ɗaya ba, ba sukuni.
To yanzu ma hutu suka yi, suka dawo Nigeria shi ne har gimbiya ta haɗu da ashmir a palace.
Wannan kenan
To anan muka kawo karshen labarin gidan mai martaba wato gidansu nihal.
*GOVERNMENT* *HOUSE* .....
To zamuje muji a wani hali ashmir yake ciki......
More comments more typing✍️✍️✍️✍️
_Taku_
_Qwinn_ _minerhly_
_Mrs_ _Yusuf_
❤️❤️❤️❤️
[8/26, 11:22 PM] Qwinn Minerhly: *SO MAKAHO NE*
(LOVE IS BLIND)
🖤🖤🖤🖤🖤
🖤🖤🖤🖤🖤
🖤🖤🖤🖤🖤
🖤🖤🖤🖤🖤
*ELEGANT ONLINE WRITER'S*📖
*Writer*✍️✍️✍️✍️
*Na Qwinn minerhly*
Masoyan so makaho ne, jinjina gareku fans Allah ya bar kauna❤️❤️❤️
Page 25_30
______ to bayan mahaifiyar hajiya nuhaira ta amince da zancen auran su, sai Alh Abdulkarim ya dawo Nigeria ya sanar da iyayensa cewar, "shifa ya samu mata a Sudan don haka aure zai yi," ba tare da ɓata lokaci ba akaje aka tambayo masa auran ta, iyayen ta suka amince aka ɗauro aure aka taho da amarya.
To bayan haka...
Abdulkarim da nuhaira soyayyar su suke zubawa son ransu, domin kuwa suna matuƙar son junan su, tana masa biyayya sosai, yayin da shi kuma yake kyautata mata.
To ana cikin haka Hajiya nuhaira ta samu ciki, farin ciki agurun su babu magana, aikuwa ta haifo ɗanta kyakkyawan gaske me kama da ita kamar tayi kaƙi, aka saka mishi sunan mahaifinta daya rasu wato (Ashmir)
Aikuwa ɗan nan yaga gata, gurin iyaye da kakanni, kowa kamar ya lashe shi don so, to bayan shekaru biyar da haihuwar ashmir, sai nuhaira ta samu wani cikin, shima sunyi murna sosai, don ta samu jinkiri sosai, aikuwa after 9months ta haifo kyakyawan ɗan ta me kama da ubansa wato Abdulkarim, yaci sunan Alh Nasir me naira, wato mahaifin Abdulkarim, aikuwa shima ya samu gata, saide kunsan gatan da ɗan fari yake samu, babu ya shi, domin ashmir ya samu gata sosai, kuma both ta kowane fanni, don mahaifiyar hajiya nuhaira lokacin da aka haifi ashmir sai da tazo taga ɗan jikanta, a cewar ta wai "dama su bata shi, ta tafi da shi Sudan ɗin ya rayu a chan gurin ta.
To ana haka kwatsam wata ranar Alhamis aka tashi da wata rasuwa, wato mahaifin Abdulkarim ya rasu bayan gajeran jinyar da yayi ta kwana biyu, Allah sarki Alh Nasir me Naira, (kulli nafsin zaikatul maut) mutum na gari me taimakon al'ummar sa ga hakuri da kawaici, To saide muce Allah yaji kansa da rahama, Ameen, sunji mutuwar sa sosai, don kuwa Abdulkarim har zazzaɓi saida yayi, to bayan arba'in, sai al'amura suka ɗan daidaitu, aka fara sabawa da rashin Alh Nasir, inda Alh Abdulkarim yayi yayi mahaifiyar sa ta dawo cikin gidan sa ita kuma taƙi, a cewar ta yabarta achan gidan tafi sabawa da shi.
To wannan kenan
Alokacin shekaran Nasir goma sha ɗaya, kawai Hajiya nuhaira tafara laulayi, ita wlh harta hakura da haihuwar, sun cira rai gaba ɗaya da haihuwar, sai ga shi ta samu cikin noor, bayan wata tara, ta haifi yarta me kama daita sak, kamar su ɗaya da ashmir.
Wow abunka da ya mace nan kuwa aka dinga nan nan da ita, haka ta taso cikin shagwaɓa,
To kasan cewar Mum tafi ji da ashmir acikin ƴaƴanta, wai acewar ta, "me sunan mahaifin ta ne, kuma gashi me kama da ita sosai, shi yasa take mugun son sa, shi kuma dad yace to ayi raba dai-dai, shima yafi ji da Nasir wai acewar sa me sunan baban sa ne, kuma gashi yana mugun kama da shi, niko nace"tofah! Ita kuma noor waya fi son ta?
... Ita kuma noor gaba ɗayan su suka haɗu suke nuna mata soyayya a cewar su wai basu da y'a mace sai ita, shiyasa ta taso cikin soyayyar iyaye da yan'uwa da kuma kakanni ta.
Shi kuma Alh kabeer wato kanin Alh Abdulkarim yazama babban ɗan kasuwa, ya gaji mahaifin su, yanada mata biyu, Hajiya Hafsah, da Hajiya Binta, wato dai Hajiya Hafsah itace uwar gida, kuma tanada ya, me suna (Amira),
ita kuma Hajiya Binta itace amarya, sannan itama tanada ya, me suna (Islam).
basa zaman lafiya kwata kwata ga kishin tsiya, kowacce yarta ɗaya, ya'ya mata suke da shi, kuma kowacce na son ta haifi ɗa namiji amma bata samu ba, shi kuma yafi ji da amaryar sa, shiyasa uwar gidan ta tsani amaryar, kuma gashi da Amira da Islam, kowacce tana masifar son ashmir. To fah!
Wannan kenan
To alokacin ashmir ya kammala karatunsa na likitoci a jermany inda ya karanci,
DERMARTOLOGIST and CARDIOLOGIST,
To ayanzu dai,
D. Ashmir dai kwararre kuma shahararren babban likita ne a ɓangaren,
FATA(DERMARTOLOGIST)
ZUCIYA (CARDIOLOGIST).
Inda suka rike shi achan, cewar su wai shi ɗin na daban ne, gashi da baiwa kuma ya san aikin shi sosai, shi yasa ba sa son ya ƙubce masu.
To shi kuma D. Ashmir, anasa ɓangaren, cewa yayi " zai yi masu aiki na ɗan wani lokaci ne, bayan ya kammala zai dawo ya bautawa ƙasar sa, domin shi ɗin me kishin ƙasar sa ne.
To bayan haka, shi kuma Nasir ya kammala karatunsa a ƙasar Sudan, wato ƙasar mahaifiyarsa, inda shi ɗinma kwararran likita ne Yanzu me matsayin,
MEDICAL OFFICER DOCTOR.
To ayanzu dai nasir yana aiki ne a Nigeria acikin tangamemen asibitin da Alh Abdulkarim ya bude masu shida ashmir, me suna ANN MEDICAL HOSPITAL (ASHMIR NASIR NOOR MEDICAL HOSPITAL), acikin babban unguwar nan me suna Nassarawa GRA.
Ita kuma noor tana chan ƙasar Wow Russian, tana karanta (Mass communication ) ita burinta ace yau tazama babbar yar jarida wato (Journalist) noor kenan.
To abubuwa da dama sun shuɗe a wannan lokacin.
Bayan Alh Abdulkarim ya taka manyan matakai na mulki a ɓangaren siyasa, har ta kai iyanzu yana takarar gwamna, inda kuwa Allah ya bashi nasara ya lashe wannan zaɓen, domin jama'ar gari suna son shi sosai, a cewar su wai ya cika kuma shi ɗin ɗan halak ne.
Shi ne yanzu fa ya zama governor Abdulkarim Nasir Gaya.
(namanta ban faɗa maku asalin ƙauyan su abaya ba, gaya ne.)
To mundawo daga labarin su ashmir, yanzu labari zai ɗora...
____________________ to bayan Mum ta tafi part ɗin His Excelency, sai ta same shi ya zauna a resting chair ɗin ɗakin, yana kallon tashar zeeworld, inda suke hasko wannan Film ɗin me suna, Jodha Akbar, aikuwa dad ya natsu yana kallo domin Film ɗin ya tafi da shi, mum ta shigo da sallama, dad ya ɗago ya amsa mata sallama, ta ƙaraso haɗe da cewa Barka da hutawa ranka ya dade, dad yace yauwa firstlady sannun ki da shigowa, Mum ta matso kusa da dad, ta dafa shi tace "zaujih! Dad ya amsa mata da "na'am, mum tace "pls ur Excellency inason mu natsu gaba ɗayan mu, bcaus bana so ɗan mu yaje yayi zaɓen tumun dare, garin nemen gira a rasa ido, kaga wa gari ya waya"? Dad ya ɗago kanshi yace "kamar ya kenan Hajiya"? Mum tace "abunda nake nufi shi ne idan muka matsa masa ya nemo matar aure yanzu, kaga zai iya zaɓo mana ɓata gari, wacce bata da halaiya me kyau, kuma kasan duk nagartar ɗa namiji, to idan fa bai samu mace ta gari ba, to dole zata sauya shi kota halin ƙaƙa, to shi yasa nake so mubi abun a sannu, so that mu samu results me kyau, bana son a gurɓata min tarbiyyar ɗana, duk shekarun da muka ɗiba muna bashi tarbiyya kawai rana ɗaya mace ta ruguza mana shi, ka gane ko zaujih"?
Nan fa jikin dad yayi sanyi, sosai, sabida duk Abinda Hajiya tafaɗa gaskiya ne, to amma yasan da cewa ya'yan kanin shi wato kabeer suna son ashmir ɗin, to ashmir ya zaɓi ɗaya mana acikin su, sabida kada kanin sa yayi zargin wani abu.
To ganin ganin his excelency ya tafi tunani ne, shi yasa Mum ta dafa shi, tace "meya faru ne zaujih ko dai da matsala ne"? Nan dad ya ɗago kanshi, yace "ahm Hajiya na gamsu da kalaman ki, but amma wani hanzari ba gudu ba, bakya ganin cewa Alh kabeer zai yi zargin wani abu, musamman idan ashmir bai amshi tayin soyayyar yar sa ɗaya ba? Kinsan da cewa kabeer ya taɓa tuntuɓa ta akan wannan zancen cewa, ashmir yaje gidan sa ya zaɓi ɗaya cikin ya'yan sa ko Amira ko islam, ya zaɓi duk wacce tayi masa, kinsan da haka ko? To bana son wannan zancen ya shafi zumuncin mu, domin na fahimci Yaron nan baya ra'ayin yaran nan, shi kuma kabeer yana ganin kamar mune ba ma son abun, domin shi a tunanin sa zamu iya tursasa ashmir akan hakan".
Itako mum ta tafi tunani domin ita a gaskiya bata son ɗan ta ya auri ɗaya daga cikin su amira, Dalili kuwa gidan Alh kabeer babu isasshen tarbiyya, daga iyayen mata har ya'yan, sabida idan iyayen mata suna faɗa har ya'yan shiga suke, kowacce ta shigar wa uwarta, to saboda haka ita bata so gaskiya, amma matsalar shine ba zata iya fitowa ƙiri ƙiri ta faɗa wa his Excellency ba sabida ko ba komai ya'yan ɗan uwansa ne, ba zaiji daɗi ba idan ta kushe abun, to amma tasan yanda zata biyo wa lamarin, sabida bazai yuba, ai itama akwai wata yarinya a Sudan me suna LIARAH, yar kanin baban ta ne kuma yarinya tun da taga ashmir, take mugun son shi, amma shi yace baya so, kuma gata balarabiya sak, amma ashmir yace ba yaso, ita kuma mum a tsarinta babu dole idan ɗanta yace bayaso to shike nan.
Nan his Excellency yayi gyaran murya yace, "ya dai Hajiya nuhaira", Mum tayi firgigit tace "no ba komai, amma inaso kasani Alh, yanzu ba'a auran dole, kai da kanka kasan irin illar da hakan ke haifar wa ko? Kuma kasan muddin ashmir ya zaɓi ɗaya daga cikin su Amira to babu zaman lafiya saboda kasan bawani jituwa tsakanin su ko, to ya lafiyar kura dama? kuma ina so kasan cewa ɗan ka me tsatsauran ra'ayi ne, baya son dole, kasan da cewa liarah yar kanin babana tana son sa amma fafir yaƙi, kuma bazan masa dole ba tunda namiji ne shi, kawai mu hakura har nanda 3months ɗin muga abinda Allah zai yi",
Nan dad ya numfasa
Domin shi bai taɓa sanin cewar ma iyalan kabeer basa zaman lafiya ba, yace, "to shikenan Hajiya mujira nanda 3months ɗin muga abinda Allah zai yi, amma lallai ashmir nan da 3months yayi ƙoƙarin samun matar aure", mum ta numfasa tace insha Allahu zaujih.
GIDAN ALHAJI KABEER
Amira ce sanye da abaya red tayi rolling da ɗan