Follow us on social media

Showing 12001 words to 15000 words out of 29865 words

Chapter 5 - SO MAKAHO NE Rikicin Zukata by Qwinn minerhly

na kyale ku kar na takura maku ko?"


Chan noor ta ce "mummy bari nazo na tafi kinsan yau ne zamuje saloon da besty ko?"

Mummy tace "alright sai kun dawo"

Noor tayi hugging din islam tace "kina nan dai ko har na dawo koma dai ya kamata ki kwana mana a nan",

Islam tace "wlh anjima da yamma zan koma ba kwana zanyi ba."


Nan noor tasa kai tana cewa "alright sai na dawo mummy da yaya nasir"

Suka amsa da a dawo lafya.




Can mummy ta tashi tace "bari na shiga ciki islam,"
Islam tace "to mummy sai na shigo bangaren naki."

Islam ta dubi yaya nasir tace "babban yaya yana ina?" Yace mata "yana part din shi',
Tace to bari na leka sa

Tana zuwa part din babban yaya ta hau nocking....



Ita kuma noor ta tafi sun hade da neehal a can wani katafaren saloon me suna PRINCESS GLAMOUR'S SALOON mallakin neehal ne, babban saloon ne babu abinda ba sayi anan akwai bangaren maza akwai na mata.


Sun hadu anan parking space din gurin suka shiga gun tare suna hiran yaushe gamo.

Sunje anyi musu gyaran gashi, gyaran fuska, da kuma wankin kafa.


Bayan sun fito ne zasu tafi boutique sun nufi parking space din gurin sai wani hadaddan guy ya fito daga cikin saloon din bangaren maza, sai hango su, aikuwa yayi maza ya nufe su yace da su "hy guys ya kuke?"

Dukan su suka kauda fuska wai a cewar basu ma san yana yi ba.

Aikuwa yace "pls yan mata ku taimaka wa rayuwa na ku saurare ni,"

Nan ya shiga rattafo zance shi wai yana son gimbiya kuma don Allah ta bashi number ta.


Noor tace "kayi hakuri an bada ita"

Neehal da tuni ta bude murfin mota zata shiga ya maza ya riko murfin, ya durkusa har kasa, kuma gashi haddaden gaye, gashi da ga gani yana ji da kansa.

Kawai sai gimbiya tace "mike ya zaka duka kasa a kan wannan abun?"

Aikuwa gayan yace "wlh ko cewa kikayi na yi tsallan kwado yi zanyi?"


Gimbiya tace "zan baka number ta amma da sharadi"

Yace eh "na yarda ko mene ne sharadin"


Tace "bana son yawan kira, zaka ga ka kira ba lallai na daga ba kuma bana son dogon zance a waya kaji ni"?

Da gudu yace mata "eh eh naji Madam wlh haka za'a yi"

Ta sa masa number ta, ta cewa noor "ki shiga naki motar mu tafi"


Aikuwa nan kowa yaja motor sa suka bar gun.



Bayan sun shiga boutique sun gama siyyaya sai suka tafi gun biyan kudi, suna zuwa aka ce wai an biya masu kudin su, neehal tace "wane ne shi din?" Ai suma suna da kudin biya ko sunyi masu kama da wadan da baza su iya biya bane," shidai accountant sai basu hakuri yake, yana cewa wlh me girma chirman ne yazo yanzu da ya ganku kuna siyyaya sai yace "kada a bari ku biya kudi shi zai biya maku, kuma dama shi ne me boutique din."

Noor tace "shut up malan ai bamu tambaye ka ka fada mana ko shi waye ba".

Da kyar ya samu ya basu hakuri suka hakura.

Suna fito wa, suka hange shi a wani dan table a kusa da wani office.

Yana hango su ya taso da sauri sauri.
Assalamu alaikum
Barkan ku da wannan lokacin yan mata,
Aciki ciki suka amsa sallama.
Yace "suna na Alh Adamu, dan Allah ko zaku bani dama na gabatar maku da kaina?"
Neehal ta kawar da kai,
Noor tace "malam dan Allah kayi hakuri wlh sauri muke mu koma gida."

Yace "dama da ke nake son nagana dan Allah ko zaki bani dama?"
Noor ta juyar da kanta can gefe.
Ita kuma nihal tace "to Alh adam kayi hakuri ba zaka samu shiga ba,"
Yace haba dan Allah kuyi hakuri mana yan mata kuyi min alfarma, ai nasa ni, daga ganin ku, ku ba irin wadan nan yan matan bane mara sa kamun kai."

Nihal tace "to shikenan tunda kace Allah ai angama magana, kawo wayar ka nasa maka number ta."
Da sauri ya bata wayar, tasa ka mashi number, ita kuma noor sai wurgo wa nihal harara take.

Nihal tayi kamar bata ganta ba, shi ko Alh Adamu sai godiya yake zabgawa nihal.

Kowa ya nufi tashi motar, nihal tace wa noor "pls besty karki wulakanta shi, ki saurare shi pls kinji kawata?"

Noor tace "alright naji, kuma kema ki shirya domin yau zan bawa yaya fayal number ki, domin ya dame ni, dama cewa nayi sai mun hadu zan maki bayani kinji kawata? ki kular min da kanki pls n pls ki gaida mummy kinji?"

Nihal tayi murmushi sannan tace "to ya zan dake tunda haka kika yi besty, kar ki damu zan kula da kaina kuma zan isar da sakon ki, sai anijima, my regard to mum."

Nan dai kowa ya tada motar shi yaja, suka bar gurin gaba daya.

Duk wannan abun Alh Adamu yana kallon su cike da birgewa domin wlh sun birgeshi sosai gasu kyawawa da su, bai san lokacin da wani murmushi ya subuce masa ba.


Mrs Yusuf
❤️❤️❤️
[8/26, 11:22 PM] Qwinn Minerhly: *SO MAKAHO NE*
(LOVE IS BLIND)
🖤🖤🖤🖤🖤
🖤🖤🖤🖤🖤
🖤🖤🖤🖤🖤
🖤🖤🖤🖤🖤






*ELEGANT ONLINE WRITER'S*📖










*Writer*✍️✍️✍️✍️
*Na Qwinn minerhly*







_ina_ _fatan_ _xaya_ _nishaɗantar_ , _daku_ _haɗi_ _da_ _ilmantarwa_ ,
_Short_ _and_ _romantic_ _story_ .






Page 35_40


"A hankali ta dinga hango bayan shi,domin suna da nisa a tsakanin su, sabida sune a gaba, kawai sai taji gaban ta ya faɗi."




Oh my God, "cewar fayal"

What happened? "Cewar ashmir."


Ashmir am coming rights now, na manta waya na beside bed. "Cewar fayal"



Okay, saika dawo kuma kayi sauri. "Cewar ashmir"





Tafiya yake, kawai ya hango wata kyakkyawar yarinya tana tahowa, "innallilahi wace ce wannan? Gaskia ina son ta wlh I love her, kawai sai ya doshe su domin ya ganta da noor, kuma ya tabbatar ƙawar ta ce.


Nan fa fayal ya nufu su, yana zuwa noor tace "lahhh yaya fayal kaine?" Fayal yayi wani murnushi me sauti haɗi da cewa "yeah lil sis ni ne."


Noor tace "yaya fayal ina yaya ash... Ai kafin ta ƙarasa fayal yace "lil sis is she ur friend? Haɗe da pointing ɗin nihal.

Noor tace "eh yaya fayal nihal ce, ƙawa ta ce kuma aminiya ta ce."



Sai a sannan nihal ta ɗago ta kalli fayal, eh lallai dai kam ba laifi yana da kyau, amma ko kadan bai birge ta ba.
Sai taga kamar bai dace ba ace bata gaishe shi ba, sabida ita a tunanin ta ma shi ne babban yaya da taji noor na yawan faɗa. Saida ta ɗan yi jim sannan tace "ina wuni"

Fayal daya daskare a gun tun lokacin da gimbiya ta ɗago tana kallon shi, sabida bai gama ganin kyan ta ba saida ta ɗago.

Yace "lafiya lau gimbiyar mata, da fatan kina lafiya?

Gimbiya tace "lafiya a gajarce".


Fayal yace "very nice"


Gimbiya tace "ahm besty nayi gaba zan je na tada motor kafin ki ƙara so."


Noor tace "okay besty"

Ai kanfin ta ƙarasa gimbiya tayi gaba, sabida ta gaji da kallon da fayal yake mata.


Noor tace "yaya fayal ina yaya ashmir?

Fayal yace "yana can cikin motar zamu fita ne da shi, sai kuma nayi mantuwa, shi ne na dawo zan je na ɗauko sai na hango ki keda ƙawar ki, pls noor help me wlh I fall in love with her, wlh ta haɗu sosai, she is very nice." noor tayi haɗiyar zuciya haɗi da cewa "yaya fayal gimbiya tana da tsari amma nayi maka alƙawarin shawo maka kanta, dama a da naso ta da yaya ashmir, shi kuma yaƙi saurara ta, kasan halin shi, to amma tunda kana son ta inshallah I will try my best yaya fayal."



Nan ya riƙo hannun noor yana cewa "thanks my sister idan kika yi min haka kin gama min komai, nagode."


Noor ta yi murmushi tace "babu komai yaya fayal, let me go to her tana jirana."


Fayal yace "is okay sai an jima lil sis thanks."

Noor tayi gaba tana saƙe saƙe a cikin ranta.

Shi kuma fayal har ya nufi part din ashmir sai ya shafa aljihun shi yaji wayar tasa a ciki, murmushi yayi yace "awesome dama ina tare da waya na shi ne na dawo ɗaukar ta, wow to rabon na haɗu da baby luv ɗita ce, i love that.



Acan ɓangaren ashmir ya gaji da jiran sa, ya shige mota yana zaune yana researching wani abu a wayar sa, to shi ne ya dauke masa hankali har bai damu ba sosai.


Sai ga fayal ya dawo, ya buɗe motar ya shiga, ashmir ya haɗe rai sosai haɗe da cewa "aina ka tsaya? Kuma sai ka barni a mota ina jiran ka sai kace wani drivern ka?"


Murmushi fayal yayi sabida ya san za'a rina, sannan yace "sorry friend baza'a kuma, kasan me ya faru kuwa a wannan fitar ta wa?


Ashmir yace "ina zan sani nida ka barni a anan, sai ka faɗa."

Fayal yayi murmushi yace "freind yau nayi wani babban kamo wlh a gidan nan, wata ƙawar noor ce tazo, ashmir ta haɗu to the extent, wlh bayan yan gidan nan ban taba ganin kyakkyawa irin ta ba, aboki na kasan ku ɗin na daban ne sabida idan akace maka Balarabe an gama Magana, but ina matukar son ta wlh yana faɗa yana murnushi."


Ɗan ƙaramin tsaki ashmir yaja sannan yace "kullum kai a haka kake, yau kaga wannnan gobe kaga wancan, pls freind kar ka zubar min da girma a idon su noor, sabida kaje yau kuma ka jajiɓo mana wata ƙaramar yarinya, wai ita ƙawar noor, banda yarinta mai za'ayi anan?


Pls cool down mana aboki na, suwa da suwa kake magana akai? Daga maryam da raiha sai kuma zee to har wani yawa ne dasu kuma su ɗin ma duk sune suke bi na, zee ce kawai na san ina sonta, kuma itama yau na haɗu da wacce nafi so a duniya sai dai tayi hakuri."


Taɓe baki ashmir yayi yace "nidai na faɗa maka kar je ka rage mana ƙima a idon yara."


Murmushi fayal yayi, bai yi magana ba, drivern ashmir ne ya jasu suka tafi.




Noor tana ƙara sawa taga nihal jingeni da motar ta, noor tace "sory habbibty na barki na tsaya na ɗan sallami yaya fayal ne shi yasa na ɗan jima."



Hararar ta nihal tayi, noor ta matso kusa da ita tace "sorry ko habibty."

Nihal tace "shike nan ya wuce zan tafi besty, ga saƙon da mum tace a baki, ta faɗa haɗe da miƙa mata jakar.


Noor ta ƙarba ta buɗe jakar taga wani haɗaddan alkyabba, tayi hugging ɗin nihal tace wow ina godiya kiyiwa mum godiya, wlh yayi kyau sosai."


Nihal tace "yayi kyau, haɗe da shige wa cikin motar sannan tace gobe ki shirya around 12:00pm sai mu tafi saloon ɗin okay?"


Noor tace babu danuwa, Allah ya kaimu, kema ga saƙon da mum ta baki nan, ta ajiye mata a sit ɗin baya.

Nihal tace "godiya nake sosai freind I will miss u."


Me too I will miss u alot, take care of ur self, drive safe. "Cewar Noor haɗe da ɗaga mata hannu tana mata bye."


Nihal ta fice da gudu haɗe da murmushi a kan fukarta.


Wannan kenan

Taku
Qwinn minerhly
Mr Yusuf
❤️❤️❤️
[8/26, 11:22 PM] Qwinn Minerhly: *SO MAKAHO NE*
(LOVE IS BLIND)
🖤🖤🖤🖤🖤
🖤🖤🖤🖤🖤
🖤🖤🖤🖤🖤
🖤🖤🖤🖤🖤







*ELEGANT ONLINE WRITER'S*📖


*Writer*✍️✍️✍️✍️
*Na Qwinn minerhly*


Assalamu alaikum, masoyan book din nan ina godiya, Allah ya bar zumunci Amin, sannan ina barar addu'ar ku, ga yayata, Allah Ubangiji yayi mata rahama, Allah ya kai haske kabarin ta, Amin thumma Amin👏👏👏👏👏👏


_Short_ _and_ _romantic_ _story_ .


Page 55_60


Sai nanata Innalillahi waiinna ilaihi rajiun yake.....


Amma duk wannan maganar acikin zuciyarsa yake yi,
Fayal yace "ya dai naga kamar ka tafi tunani ko ka santa ne?"

Da sauri ashmir ya gyada kansa yana cewa "no ban santa ba, kawai dai tayi min kama da wata ce."

Ajiyar zuciya fayal yayi "yana cewa Alhmdlhi kar ka ballo min ruwa."

Nan suka ci gaba da hiran su, inda gaba daya hankalin ashmir yayi can wani gurin.



Alh adamu ne a cikin office dinsa yana kallon hotunan su noor da ta saka a status dinta na gefen sweeming pool a school dinsu, sai doka murmushi yake tayi yana cewa "kinyi kyau my princess u look so cute, kamar a sace ki, inda yayi mata comments da kinyi kyau my noor, ya school din?"





Dukan su na hango a gefen pool suna ta nishadi abin su, suna hira, noor ce taga anyi mata message, ta duba sai taga Alh adam ne, tayi mashi reply, suka ci-gaba da hiran su, sai ga wani Baturen saurayi kyakkyawa da shi ya zo gun, Yana yi musu magana, hi guy's, suka ansa mashi da hi, nan ya fara rattafo zance wai shi noor yake so waya mutu waya tashi, aikuwa Minal tace mashi "idan kana so mu ba ka ita sai kayi mana Yaren mu wato hausa, nan fa ya dinga bin bakin su yana jin me suke fada shima yana jagwalgwalawa, su kuma suka dinga kwasan dariya abinsu, tun daga ranar ya zama freind din su, ko'ina yana bin su.





Government house

Bayan rabuwar fayal da ashmir, yaya ashmir ya shiga matsanancin damuwa domin bai san yana son wannan yarinyar ba sai ranan, yanzu ya kara zama so silent, baya son yawan magana da shiga mutane, wai dama haka soyayya take? Shi dai Allah ya sani yana son ta, gashi abokin sa na son ta, kuma ya riga shi furta wa, ya zama dole ya bar masa ita, shi dai ya shiga ukun sa, a haka ya keta tunanin ta kullum.




Amira ta gama kwanakin ta har ta tafi, an hada mata goma ta arziki, ta tafi da shi, don daddy ma sai da ya bata babban kyauta ita da yar uwar ta.
Ta koma gida cike da farin ciki da annashuwa.




Bayan kwana biyu

Mummy ce a cikin dakin ta, tana tasbihi, amma hankalinta yana can gun son, ta daina ganin sa, ya daina zuwa ayi breakfast dashi, ya daina zuwa lunch, ya daina zuwa dinner, ya daina zuwa hira daita a part dinta, to bari ita ta je ta gano shi ko lfya, gashi ya kusa koma wa jermany aikin sa.




Mum ce a dakin yaya ashmir a kusa da gadon sa, tana cewa "son meya same ka, baka da lafiya ne shi ne baka fada wa kowa ba, ta taɓa jikin sa taji da zafi rau, son me kake so ka fada min, pls son tell me, what's going on son?"

Ashmir ne ya samu da kyar ya buɗe bakin sa, yana cewa mummy, "mummy bani da lafiya ne, sannan kuma akwai wata yarinya da nake yawan dreaming dinta, wlh mummy son ta nake yi, ban taba tunanin zan so wata y'a a duniya ba sai yau, mummy sai de kash da matsala."

Cikin ruɗe wa mummy take tambayar shi mece ce matsalar?

Jimm yayi yana tunani, kawai gwara kar ya cewa mummy itace kawar noor, gwara yace mata bai san inda take ba, sabida itace zabin abokin sa, mum matsalar itace, ban san inda take ba, so daya na taba ganin ta, kuma ban sake ganin ta ba sai a mafarki."

Nauyayyan ajiyar zuciya Mum ta sauke tana cewa "son soyayya ce ta mai da kai haka, son tunda nake da kai baka taɓa ce min kana son wata ba sai yau, lallai dole nasan abun yi, dole na nemo maka ita son insha Allahu."


Nan tayi wa family doctor su waya take sanar da shi yazo ya duba ashmir.


Doctor suraj, ne akan ashmir yana duba sa, inda ya gano cewa damuwa da tunani ce kawai ta haifar masa da ciwo, kuma idan bai rage ba zai iya haddasa masa ciwon zuciya.



To bayan doctor Suraj ya gama masa treatment, har ya samu bacci, bayan nan doctor ya tafi.



Bayan kwana biyu ashmir ne da doctor suraj, yana ɗan dada masa wasu gwaje gwaje, inda ya gano ashmir ya warware sosai sai abinda baza a rasa ba.


Doctor ne yake cewa ashmir "haba dr ashmir sai kace ba CARDIOLOGIST BA (LIKITAN ZUCIYA) gaba daya ka sawa zuciyar ka damuwa to dan Allah a bi a hankali, kune fa masu taimakawa mutane, to kuma idan kuma kuka rafke wa zai duba su, so pls doctor take it easy, nd ko da ban san abinda kake so ba nasan insha Allahu bazai fi karfin ka."

Nan ashmir ya shiga masa godiya yana masa sallama.


Yau ne hutun ashmir ya ƙare, zai koma jermany, jiki yayi kyau sosai, yana yi wa mutan gidan sallama, nasir kuma zai raka sa har airport.



Nihal ce take waya da fayal, yana ta ce mata shi yayi missing din ta wlh zai biyo ta america har school, nihal ta rike baki tana cewa "rufa min asiri, ka dai yi hakuri mun kusa karɓar excuse, zamu dawo sai ka ganni."

Noor kuma suna can gefe ita da minal da wannan baturan mai suna lucky, suna ta hira suna shan ice cream abin su.





After 1 months da dawowarsa jermany, yana hakince a kan wani hadaddan kujera, yana ta lilo da shi, da wani soft drink a hannun sa, idon sa alumshe kamar mai bacci, amma ba bacci yake ba, kawai dai yana enjoying moment din ne.
Wayar sa ce tayi ruri, sai da ta kusan katsewa tukun ya ɗauka, yana duba sunan ya maza ya daga. Muryar sa a sarke yake cewa "hlo lil sis, y school?
Sai da noor ta shagwabe fuska tukun tace "wlh brother baka so na, ka manta dani kwakwata, baka nema na, sai idan ni ce na neme ka."

Sai da ta gama tukun ya shiga rarrashin ta, yana cewa sorry lil sis, wlh kina rai na, kawai dai aiki ne ya min yawa shiya sa ba kya jina amma yanzu zan dinga neman ki kinji ko?"

Nan ta gyada kai tana cewa "to yaya, yanzu yaushe zaka kawo min visiting?

Sai da yayi jimm sannan yace "on Sunday insha Allah zaki ganni kinji ko?

Nan ta shiga murna tana cewa "Allah ya kawo ka lafiya big bross."

Yayi hanging din wayar yana jinjina rigimar lil sis, mumushi yayi da shi kadai ya baiwa kan shi sani.



Bayan 2 days, ashmir ne a school din su noor, yanzu yayi parking, da ya ke ya hana mabiyan sa bin sa, suma anan sun bashi masu tsaro sabida kasancewar sa babban ma'aikaci a wannan babban asibiti, to amma yau shi kadai ya fito.

Da gudun ta ta fito tana ihun yaya ashmir!!! Oyo yo, ta yi hugging dinsa, da gudun ta, tana cewa "nayi missing dinka yaya ashmir,"
Lil sis zaki kada ni fa, ke ba kya girma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login