Follow us on social media
Showing 24001 words to 27000 words out of 29865 words
Chapter 9 - SO MAKAHO NE Rikicin Zukata by Qwinn minerhly
wife, a hankali ta gyada masa kanta....
Bayan sati biyu da bikin su ashmir, nihal ce a gefen swimming pool ɗin gidan tana zaune a bakin ruwa ƙafafuwan ta suna cikin ruwan, waya ce rike a hannun ta, ta kai shi kunnen ta, tana cewa "besty ykk ya yaya na, a can ɓangaren kuma noor ce take ce mata "wlh komai Alhmdlh, yayan ki ya na nan, yanzu ya shiga wanka, nihal tace "to dai a kular min da brother na, komai yace yana so a ba shi pls" noor tace "hmm abinda zan fada shi kika rigani faɗa, to dai nima a kular min da yaya na pls, a tarairaye shi kamar kwai a cikin miya," nihal tace "kaji ta to sannu mai yaya, yayan naki da duk ya bi ya takura min, kullum abu ɗaya, ko office ya kasa zuwa wlh kullum yana gida"
Hmm to nima fa hakan take "wannan yayan naki ya fiya naci, kamar cingum, ni duk na ƙosa ya fara fita ma. Cewar noor
Oh abin harda su cin mutunci, to ai shike nan, cewar nihal
Ga minal na ƙira na, bari na haɗa conference mu sha hiran mu na yaushe gamo, cewar nihal
Nan suka haɗa junansu a waya suna ta hira harda kyakyatawa.
Washe gari
Nihal ce take ta shiri, wani haɗadd'en less ta sa kalar purple mai ratsin peach, ta sha kyau ta yafa peach din mayafi da jaka da takalmi ma duk peach ne, tasa wani diamond dankuni da sarka da abin hannu, wow tayi matuƙar kyau gaskiya, hugging ɗin ta taji anyi ta baya ana lashe mata wuyan ta, wow kinyi kyau mata ta, duban shi tayi tun daga sama har kasa sai taga yayi mata wani kyau, ya sha wani yadi mai tsada peach color, kai ma kayi kyau miji na ta fada tana lumshe idon ta.
Nihal na hango a palon mummy, sai jan ta take da hira ita kuma nihal kunya ya hana ta sake wa, mummy ce ta juya gefen ta tana cewa "son fita ka bamu guri da ɗiya ta, duk ka hana ta sake wa, yaya ashmir kuwa sosa kan yake yana cewa "yanzu mum ƙora ta kike yi, naga alamar kin ma daina ji da ni mum, yanzu ba kya tani" eh ɗin bana ta kai ta ɗiya ta nake, murmushi ashmir yayi sannan ya fice yana sosa ƙeya, sosai nihal ta saki jiki da mum suna ta hira.
Sai da suka yini a gidan sannan suka koma gidan su.
Washe gari
Noor ce ta buga sammako a gidan yaya ashmir, aikuwa nihal tayi murna, nan suka ƙaraso ita da mijin ta, wato yarima adnan, dama shi ya kawo ta, nan nihal tayi masu iso sannan tace "bari taje ta ƙira wo yaya ashmir su gaisa, nan kuwa ta tafi ɗaki, tana zuwa ta shige cikin bargon sa, nan ya cakumo ta, yana cewa "wa na kama? Wato dan kin yi baƙi, shine kika tafi kika kyaleni ko? To yanzu wa na kama, kuma sai na rama." Lah wlh yaya ashmir baƙi ne damu kuma yanzu ma suna parlon kasa suna jiran mu... Ai kan ta ƙarasa ya caɓe baƙin ta yana kissing kamar ya samu lollipop.......
Mr Yusuf
❤️❤️❤️
[8/26, 11:22 PM] Qwinn Minerhly: *SO MAKAHO NE*
(LOVE IS BLIND)
🖤🖤🖤🖤🖤
🖤🖤🖤🖤🖤
🖤🖤🖤🖤🖤
🖤🖤🖤🖤🖤
*ELEGANT ONLINE WRITER'S*📖
*Writer*✍️✍️✍️✍️
*Na Qwinn minerhly*
_Short_ _and_ _romantic_ _story_ .
I dedicated this page to my besty, Allah ya bar mu tare, much luv.
Page 60_65
Ɗa gowan da zai yi, sai ya hango bayan wata, a gaban su noor, kawai sai ya ja motar sa ya fice da gudu, yana tunanin ta a zuciyar sa, ya so ya gan ta ko so ɗaya ne.
Noor kuwa har ta buɗe bakin ta, zata kira shi, kawai sai ta ga ya fice da gudu.
Nihal kuwa motar sa na tashi ta kalli gurin a guje, sai de kash bayan motar kawai ta iya hango wa.
Minal kuwa tana ganin yaya ashmir ya tafi ta fara zuba wai "wow noor dama haka yayan ki ya ke da kyau, wlh ya hadu, wlh duk kyan ki, ya fi ki kyau yarinya."
Noor ta taɓe baki sannan tace "bawa ni nan, bai fini kyau ba, kai amma dai wlh besty yau kin ban haushi, ina ta neman ki, ku gaisa da yaya na, shi ne zaki wani tafi wani gun. Ta kare maganar tana ɓata fuska."
Nihal kuwa cewa tayi "oh sorry my dear friend, wlh bansan zai zo ba, da ban je ko'ina ba, ai kece da lefi baki gaya mana ba, why?"
Noor tace "wlh I just want to surprise you guy's ne kawai amma ba komai wataran a hadu, ga tsara bar mu nan daya kawo mana."
Nan nihal ta shiga duba wa sosai yayi masu tsara ba irin su chocolate, cake, ice cream, snacks, sweet, cingum, da abubuwan kwamulashe, kala kala, don sai da ya ciko masu manyan ledoji biyu. Nihal tace "wow amma Allah ya shi ma yaya ashmir din nan Albarka, kuce yau ni babu ruwa na da abinci."
Nan suka fara cin wannan kayan kwalam din, nihal tana ba su labarin abinda yasa basu ganta ba, wai wani lecturer su ne, ya kira ta wai yana son ta, kuma da wai da aure, ga shi ba musulmi ba ne, kuma bature ne. Aikuwa suka kwashe da dariya, harda tafa wa, noor tace "sayi su gama wlh ai nan da 6months zamu yi graduate, naga ta tsiya"
Ashmir ne a katon gadon sa, bayan dawowarsa gida, da yake direct gida ya wuce, idon sa alumshe yana tunano zancen sa da mummy a kan yarinyar da yace yana so.
Bayan wata biyu da sati uku
Gidan sarauta
Mai martaba ne ake ta hada hada a cikin masarautar sa, dalilin yau suna da Babban bako wato His Excellent, governor Abdulkarim Nasir Gaya, shi ne yau zai zo gun mai martaba sabida bikin buɗe companies din da suka yi haɗa ka, wajan gina su, ya kammala, kuma ga wata muhimmiyar magana da ke tafe da shi.
Fada yau a cike take da dimbin al'umma, sabida baƙi na musamman da aka yi, nan na hango mai martaba da his excellent, suna tattaunawa, a tsakanin su, inda bayan sun kammala tattaunawar su ne, na bikin bude companies din, sai his excellent yace da mai martaba, "ni kuwa akwai wani abin ya ke damu na, game da yaron nan, ashmir, yaki ya kawo mana wacce yake so, sannan akwai ya'yan kani na, Alh kabeer nace masa yaje ya zaɓa a can, nan ma yaƙi, to amma nan ɗin ban ji rashin dadi ba, dalili kuwa ance duk yaran biyu suna son shi, to kaga idan har ya zaɓi ɗaya acikin su, zai yi san kai, to gwara a hakura, Allah ya fito masu da mafi Alkhairi, to shi ne nace bari na kawo zancen nan ko zamu samu mafita."
Mai martabar sai da yayi ajiyar zuciya sannan yace "to ai ur excellent wannan ba wani abun damuwa bane, kawai ayi tuwo na mai na."
Sai da his excellent ya kuma tambaya yana cewa "ban fahimce ka ba."
Mai martaba yace "Abinda na ke nufi shi ne, mu hada su aure da yata nihal."
Nan fa his excellent ya washe baki yana cewa "kai masha Allah, wannan abu yayi dadi, sosai, Allah ya saka da Alkhairi.
Nan suka amsa da Amin
Sai mai martaba yace "sai a bari ranar bikin buɗe companies, kawai sai a sanar a ranar, ayi walimar saka ranar aure."
His excellent yace hakan ma yayi kyau sosai, nan aka bawa malamai dama suka rufe taro da addu'a.
Bayan nan a kaje aka yi lunch kowa ya watse.
After 1 week
Wani katafaren babban wajan taron manya na hango, cike da al'umma.
Wajan zama daki daki kowa da wajan sa
Kowa da inda aka tanadar masa ya zauna
Akwai kujerun masu taron,
Akwai na masu gabatar da taro,
Akwai na yayan masu taron, da matan su,
Akwai na yan gayyyata,
Akwai na masu tsara taron yadda ya kamata.
Can na hango kujera ta musamman
Ga his excellent, ga mai martaba, ga gwamnan bauchi ma ya zo, gana jigawa ma yazo dana kaduna. Ga hadimai da wazirai da turakai.
Can na hango wasu kujeru na musamman na matan gwamnoni da matan sarakai.
Can na hango wasu high tables kujeru, dana maza dana mata.
Anan na hango ɓangaren yayan gwamnoni, da ya'yan sarakai, dana wasu manyan, iya maza.
Ana can ma haka na hango na ya'yan gwamnoni da yayan sarakai, da dai sauran su.
Taro yayi taro ya hadu iya haduwa, da kyar na samu na hango doctor ashmir ya sha wani suit silver color, fuskarsa ta sha gyara, gashin kansa ya sha gyara ya kwanta luf luf, yayi matuƙar kyau a kayan, kamar balarabe ko daya ke dama balaraben ne.
Gasu yaya nasir shima an sha kyau a cikin wani bakin suit, yayi kyau sosai.
Ga adnan, wato yarima mai jiran gado, shima yayi kyau matuka, ya sha wani White nd black suit, dama shima kyakkyawa ne, kasan cewar shi black beauty, ga shi dogo, ga hanci ga zara zaran idanuwa ga karamin baki, gashin kansa shima ya sha gyara luf luf.
Ga sauran ya'yan manya a gun kowa naji da kansa.
Nan na hango nihal ta sha kwalliya a cikin wata haddan wedding gown, silver nd white color, ta sha kyau, gashin kanta ya sha gyara an rufe sa da wata yar mayafi shara shara silver.
Itama noor irin shigar su ɗaya da nihal, sai de nata calon Black nd white ne itama ta sha kyau.
Minal ma wata hadaddiyar less ta saka maroon color, Kasancewar dad dinta da yan gidan su sun zo taron, itama tayi matukar kyau abin ta.
Amira kuwa ta sha kwalliya da wani atamfa super wax red nd yellow, tayi kyau sosai itama.
Islam kuwa wata hadadd'iyar abaya ta saka, black nd orange color, tayi kyau sosai itama.
Taro yayi taro ana ta gabatar da abinda ya haɗa mutane, komai cikin tsari a keyi, ga lafiyayyun abinci kala kala, irin su fried rice, jellof rice, fried supagetti, fried cous cous, chips nd kaji, tsire, snaks, drinks, dambun kaza dana nama etc. Sai drinks kala kala.
Nan aka gama gabatar da abinda ake yi, sannan a kazo ana sanar da an haɗa dr ashmir aure da gimbiya nihal, inda aka umarce su da su fito a gan su da kyau, domin a shaida su.
Kirjin nihal da na ashmir a tare suka buga lokaci guda.
Da taimakon Noor nihal ta samu ta fito, shi ko ashmir ya dade da fito wa.
Nan masu camera da video suka dinga watsa masu camera, amm sun dace kowa yake cewa, dama an bawa, ashmir zobe kafin ya fito wanda iyayen ne suka tana da, domin ya sawa nihal itama an bawa noor ta bawa nihal, ita kuwa nihal sai da noor ta ja mata kunne akan dan Allah kar ta bada su, domin akwai yan jarida a gun.
Nan nihal ta taho, tana tafiya a hankali, rigar ta sai jan kasa yake yi, duk ta firgice wai wannan mutumin ne za'a hada su aure, Ita dai kashin ta ya bushe.
Nan ashmir ya taho shima da karfin sa, domin Allah ne kadai yasan irin farin cikin daya ke ciki, amma abinka da miskili daya matso kusa da ita sai ya sha mur.
Nan ashmir ya duka har kasa ya riko hannun ta yana daukar alkwaririka, cikin harshen turanci yake maganar, ana ta tafi domin sun ƙayata gurin kamar a indian film, sannan ya saka mata zoben, itama ta saka ma shi, nan aka din ga watsa masu kudi ana tafi ana video da camera. Wayyo ku hasko kuga irin burgewar da suka yi a gun. Bayan nan kowa yaje ya zauna a gun zaman sa, inda wani babba ya tashi ya na sanar da mutane cewa an tsayar da biki nan da 3 months. Fatan Alkhairi.
Nan fa a kaci aka sha, taro ya fara watsewa.
Islam ce ta fashe da kuka ganin yaya ashmir ba ita zai aura ba, sai lallashin ta ake.
Amira kuwa gigicewa tayi ganin wai yaya ashmir wata zai aura, su ko oho.
Minal kuwa itama kamar tayi kuka, don Allah ya sani tun ranar da ta fara ganin ashmir taji ta fara san sa, amma ya zata yi, kuma ko ba komai ai nihal ƙawar ta ce, sai de tayi masu fatan Alkhairi.
Fayal kuwa ruɗewa yayi ganin abinda ya faru amma kuma ya san cewa, abokin sa bashi da lefi ko kaɗan. Dan haka yana masu fatan Alkhairi.
To daya ke manyan taron sun watse saura matasan, su gwamnoni da su manyan yan siyasa da sarakai da hadimai an tafi da su government house, wai za'a danyi wani meeting daga nan kowa ya watse ya tafi gida.
Ashmir ne a zaune kusa da nihal wacce noor ta kawo masa ita, ya sha mur kamar ba shi ba, itama nihal sai wani harare harare ta ke yi.
Ke ba ki iya gaisuwa bane, kin wani zauna kamar an jefo ki.
Eh ban iya ba, ka koya min mana, to cewa nayi ina son ka da zaka yi min wulakanci.
Ashmir baki sake yake kallon ta, hmm yarinya zaki shigo hannu ne, za kiyi bayani, nima ai ba cewa nayi ina son ki ba, karamar mara kunya.
Murguɗa masa baƙi tayi, ta tashi zata bar gurin ai kawai rigar ta ya naɗe a takalmin ta, tayi kasa gaba ɗaya zata fadi.
Ashmir ne ya riko ta, ya rike ta gam, shi yasa bata karasa faɗuwar ba, tuni ya tallabo ta, ta fado kirjinsa, ya rungume ta, yana sauke nauyayyan ajiyar zuciya.
Tuni gurin ya ɗau tafi ana ta masu hotuna.
Noor ce ta taho a guje, tana kiran sunan nihal....
Mrs yusuf
❤️❤️❤️
[8/26, 11:22 PM] Qwinn Minerhly: *SO MAKAHO NE*
(LOVE IS BLIND)
🖤🖤🖤🖤🖤
🖤🖤🖤🖤🖤
🖤🖤🖤🖤🖤
🖤🖤🖤🖤🖤
*ELEGANT ONLINE WRITER'S*📖
*Writer*✍️✍️✍️✍️
*Na Qwinn minerhly*
_Short_ _and_ _romantic_ _story_ .
Ina kuke masoyan book ɗina, to gani na tawo maku da sabon littafi na mai suna RAYUWAR SALEEMA, wannan littafin yana tattare da abun mamaki, ban al'ajab, ban tausayi tare da ɗaukan darasi, don haka kada ku bari a barku a baya.
Wannan littafin sadaukarwa ne, ga miji na domin da bazar ka nake taka rawa.much love
End
End
End
Page 80_85
Ai kan ta ƙarasa ya caɓe baƙin ta yana kissing kamar ya samu lollipop.....
Da kyar ta samu ta lallaɓa yaya ashmir suka miƙe suna shirya wa, English wears suka sa, iri ɗaya, jan top, a nata an rubuta "my king", a nashi an rubuta "my qween" sai kuma ashe ɗin wando, sai de nata yana da kwalliyar mata, sun yi matuƙar kyau abin su, sai dai nihal ta ɗaura after dress a nata, suka feshe jikin su da turare, tafe suke suna zancen soyayya, hannun ta saƙale a kan kafaɗar shi.
Takun su ne yayi wa noor iso a kunnuwan ta, aikuwa tana ɗago fuskar ta, ta hange su saman step suna takowa a hankali cikin kwanciyar hankali abin su.
Harara kawai noor take wurgawa nihal sabida ta ƙulu da ita, dan gani take ta shanya su, sai de bata san yaya ashmir ya gan ta ba, suna ƙarasowa kuwa noor ta kuma wurgawa nihal wata harara, nihal kuwa murmushi tayi sannan taje tayi hug ɗin noor tana cewa "wlcm my sister, amma fa ki maida wukar, dan wlh bani na kar zoman ba, nima rataya aka bani," ta faɗa tana kallon yaya ashmir, shi kuma ya wani haɗe rai, kamar bai taɓa dariya ba, kamar ba shine suka gama wasa da shi ba yanzu a sama.
Nan ashmir suka gaisa da adnan sannan nihal ma ta gaishe da yaya adnan, sannan noor ma ta gaishe da yaya ashmir, ya amsa mata ba yabo ba fallasa, sannan yaya ashmir yace wa noor " wai meya faru ne kike ta hararar min mata?" Iah yaya ashmir wlh ni fa ba hararar ta nayi ba, "cewar noor" to nayi miki ƙarya, kin bugo mana sammako duk bai ishe ki ba, amma sai kin zo kina hararar ta dan baki da kunya ko? To kar na sake gani, baƙi san ta zama yayar ki ba ko? oya bata haƙuri, "cewar yaya ashmir" da ya faɗa yana wani cin magani, adnan ne ya maza ya ƙarɓi zancen da cewa "yau nake ganin faɗan rashin gaskiya, to dan ta harare ta ai itace da lefi, sannan kuma sai ta wani bata hakuri, aikuwa kina bata hakuri itama zata baƙi hakuri a matsayin ta na ƙanwa ta, sabida har yanzu ban gane wace yaya, wace ƙanwa ba? ya faɗa tare da murmushi akan fuskar shi. Nan kuwa kowa ya sa dariya ban da yaya ashmir da ya murmusa sabida shi kaf ya sha'afa ma wlh, ashe fa su ɗin a da ƙawaye ne, kuma kowacce da ta tashi aure sai ta auri wan yar uwar ta, kaga kuwa kowa ya zama boss.
Ana cikin haka sai ga su minal da yaya nasir sun shigo cikin gidan, nan kuwa nihal da noor suka yi farin cikin ganin su, nan hira ta barƙe a tsakanin su nan ashmir ya ja su, suka koma ɗayan part ɗin, itama nihal ta ja su suka shiga kitchen su ukun suna girki, minal tana jin ƙamshin tafarnuwa ta fita a guje tana amai, inda suka bita hankali a tashe suna tambayar ta "me ya same ta?" Nan take ce masu tana da 2wks pregnant, aikuwa sun mata murna sosai nan suka ce ta zauna ta huta, su sa shiga su ƙarasa aikin.
After 8wks
Nihal ce an sha wanka, da wata exclusive atamfa kalar maroon da ratsin butter color, ɗinƙin riga da skirt, kayan sun amshe ta, tayi matuƙar kyau, nan shima yaya ashmir ya shirya suka fita, hanyar gidan sarauta suka shiga, bayan isar su ne suka fara zuwa fadar mai martaba da suka gaishe shi, yayi matuƙar farin ciki da ganin su, sannan suka ƙarasa part ɗin hajiya kilishi wato mahaifiyar yarima adnan, itama tayi matuƙar farin ciki da zuwan su, tunda yanzu ta gane ta daina kishi da mum, har part ɗin ta take zuwa, itama mum tana zuwa nata part ɗin, bayan sun ɗan zauna kaɗan sai suka tashi suka tafi part ɗin mummy, nan barori suka dinga kawo masu gaisuwa, suna kawo abubuwa, su kawo wannan su kawo wancan, mum tayi matuƙar farin ciki da ganin su a tare, gashi yar ta, ta ƙara wani kyau, skin ɗin ta, ya dada haske da kyau, a gaskiya ta yaba da kiwon ɗan ta