Follow us on social media

Showing 27001 words to 29865 words out of 29865 words

Chapter 10 - SO MAKAHO NE Rikicin Zukata by Qwinn minerhly

ashmir, sai shi masu albarka take, nan yaya ashmir ya miƙe yana masu sallama, sannan yace wa nihal ta zauna ta yini zai dawo sannan su tafi, aikuwa nihal sun sha hira da mum, dan har part ɗin hajiya kilishi ta koma, itama ta haɗa wa nihal kayan gyara iri daban daban, sai bayan magriba yaya ashmir ya dawo suka tafi gida, a hanyar su ta komawa ma sai da yaya ashmir ya kai su shopping mall.

Bayan sun isa gida ne, kowanne su ya shiga wanka, suka yi sallan ishai sannan suka ci abincin da suka siyo sannan suka fara shirin kwanciya.


After 9months
Yaya ashmir ne da nihal a cikin garden ɗin gidan su, babban garden ne mai tattare da komai na more rayuwa, yaya ashmirr ne zaune a kan wani ɗan ƙaramin godo dake cikin gurin, ita kuma nihal tana kwance, kanta akan cinyar sa, mix fruit ne a cikin wani jug mai kyau, ga kuma milkshake a kusa da su, hira suke mai ban sha'awa a tsakanin su, nihal ce ta ga yaya ashmir yana zubar da hawaye, tace da shi "yaya na, me ya faru, wani abu ne yake damun ka?"
A'a baby luv, babu abinda yake damuna sai son ki, wlh na rainu da soyayyar ki, wlh kece mace ta farko dana fara so a rayuwata, hakikanin gaskiya SO MAKAHO NE domin ya maƙantar dani da soyayyar ki, ya zame min abinci na da ruwan sha na, ke nake gani a mafarki na, ke nake yawan tunani, wlh nihal tun ranar da na fara ganin ki naji na fara son ki, amma nauyin baƙi ya hanani faɗa, sai ranar da na ji abokina fayal yana zancen ki, har ta kai ya nuna min hoton ki to a ranar ne na ƙasa boye abinda yake raina, na shiga cikin damuwa har sai da ta kai ta kwantar dani, wlh ina sonki my baby, I luv u, I need u, I can't do without you my luv," ya ƙarasa maganar yana yi mata wani hot kiss a baƙin ta.

Hmmm yaya na, ashe duk abu ɗaya muka ji, ashe a rana ɗaya muka fara son junan mu, wlh nima tun ranar da muka fara haɗuwa naji na fara son ka, lallai SO MAKAHO NE domin nima shi ya maƙantar dani, bana ganin kowane ɗa namiji sai kai, na kasa miƙa soyayya ta ga kowa sabida ruhina yana tattare da naka, i luv u more my love, I can't stay without u, I love u more, ta fada tana rungumo shi haɗe da rikunkume shi kamar za'a sace Mata shi, suna cikin haka sai ga wayar ta yana ringing, nan ta ɗaga da sauri sabida taga sunan noor ce mai ƙiran, bayan sun gaisa ne take ce mata wai minal ta haihu, baby boy ɗazu, nan nihal ta shiga murna sosai tana cewa lallai kice mun yi ɗa, bayan tayi hang-up, take gayawa yaya ashmir zancen haihuwar minal, shima yayi matuƙar murna sosai, sannan shima ya shafo cikin ta yana cewa "nima na ƙosa naga ɗana, kai insha Allahu ma yan biyu ne a cikin nan," kasancewar sun je sunyi gwaji sun tabbatar tana da ciki.
ita dai nihal murmushi kawai take dokawa sabida zumuɗin shi akan wannan cikin yayi yawa, sannan tace "nifa wlh yaya ashmir tausayin noor nake, kaga ita kaɗai ce har yanzu bata samu ba, sannan ga shi duk tare muka yi aure." Hannu ya maza ya sa mata a baƙi alamar tayi shiru kar ta ƙarasa, sannan ya ɗaura da "kul karna ƙara ji kin yi wannan zancen baby luv, shi haihuwa ai na Allah ne, muma daya bamu ba dabarar mu bane, kuma ita ma ɗin ai Allah bai manta da ita ba, kuma ma duk gaba ɗaya yaushe aka yi auren ɓalle ki damu, don haka kar na ƙara ji kinyi wannan zancen kinji my baby?" Girgiza mashi kanta tayi tana hawaye, sannan yace "baby luv meyasa kike kuka, ko dan nayi miki nasiha ne?" A'a wlh yaya ashmir ko ɗaya, kawai dai nasihar ka ce ta ratsa ni, kuma na gode da tunatar war ka, ita kuma Allah ya bata mai Albarka, suka amsa da "Amin"


Washe gari da safe
Suna kwance a kan gado a cikin ɗakin yaya ashmir, nihal tana kwance a kusa da shi tana wasa da gashin kansa, wai ita kitso zata mishi, sai jagwalgwala masa kan take, shi kuma dadin hakan yake ji shi yasa yayi lamo a kwance, can dai nihal ta tashi tace da shi "yaya na ina zuwa" miƙe wa tayi ta nufi kitchen ɗin sama ta fara masu aikin breakfast wai yau sai tayi mishi surprise, don kuwa abincin gargajiya take ta haɗa wa, tayi masu awara mai kwai, ta soya masu wainar fulawa, tayi masu ɗan wake, ta soya masu kosai, da alala, sannan ta dama masu kunun gyaɗa, sannan ta haɗa masu soɓo, ta kuma haɗa da ruwan tea.
Kan dinning table ɗin sama ta nufa, ta shirya masu komai anan, kasancewar komai da yake asama a kwai a ƙasa, wanka taje tayi sannan ta shirya tsaf cikin wata shadda ɗinkin stone work, doguwar riga, kalar blue, ta kashe ɗaurin ɗankwali, sannan ta nufi ɗaki taje ta tashe shi, ya shiga yayi wanka shima ya shirya sannan suka nufi dinning, nihal ce take ce mashi "yaya ashmir guest what?" Nan ya ɗan juya idon sa, sannan yace "hmm I can't guest anything but u." Nidai don Allah a bani naci, tun da na fito nake jin kanshi ya baɗa ko'ina, pls a taimaka wa wannan bawan Allah, wlh ana shiga hakkin sa sosai." Murmushi nihal tayi sannan tace "hmm to gaskiya kayi failing ace ka kasa gane me nayi hmm amma dai bari kawai dai mu ci." Ta faɗa tana kashe masa ido ɗaya, sannan ta fara ɗiban kowanne tana zuba wa a cikin plate, ta zuba masu kunun gyada da zoɓo, a cups sannan tace da shi "Bismillah" to yanzu banda abin ki a'ina zan gane duk waɗannan abincin, abu ba ɗaya ba, ba biyu ba, amma fa gaskiya sunyi kyau, sannan dan Allah wai dama duk kin iya irin waɗannan abincin ne dama, a gaskiya sai dai Allah ya biya su mum, amma wlh ni na ɗauka ma ko ba ki iya girki ba sai dai a miki, wai ashe kina shiga kitchen a gida, to ai dama wannnan shine gatan ya mace, amma ace kaga yarinya kawai sabida tana cikin daula amma sai ta ƙi shiga kitchen sai anyi aure a yi ta fama da miji, yanzu gashi mun huta da ɗaukan kuku, tunda kince zaki iya mana abinci da kan ki, masu share share da wanke wanke, da goge gogen gida kawai kika ce a kawo, sai mai gadi, kinga ai kin samu tarbiyya, amma ban da haka kina yar gidan sarauta ga kuɗi ga mulki amma kina wa mijin ki hidima, baby Allah ya biya ki da gidan Aljanna, Allah ya sakawa iyayen mu da gidan aljanna, a tare suka ce "Amin" bayan sun kammala cin abincin ne yaya ashmir sai santi yake zubawa yana cewa dan Allah ta ringa yi mishi ire iren kalar abincin nan, dan shi wlh dama ya gaji da cin na zamani, nan tace da shi "insha Allahu zata dinga yi" yau ma da rana dambun shinkafa zata yi, da source ɗin ƙoda, da lemun kankana, aikuwa yayi matuƙar farin ciki da jin haka.


Bayan anyi sunan ɗan su minal yaro yaci sunan mahaifin su yaya nasir, ana ƙiran shi da, "abid" suna yayi dad'i domin kuwa an yi lafiya an tashi lafiya.


After 9months
Nihal ce kwance a ɗakin labour sai kuka take yi, yaya ashmir kuwa yana riƙe da hannun ta, yana bata baƙi, sai cewa take "na shiga uku yaya ashmir wlh mutuwa zan yi, ni kaɗai na san abinda nake ji, yaya ashmir kataimake ni kada na mutu wayyo Allah na" yaya ashmir kuwa duk ta ruɗa sa ya rasa mai zai mata, kawai sai hawaye yake yana cewa "ba zaki mutu ba baby insha Allahu, zaki haihu lafiya, kinji baby na, ki yawaita cewa innalillahi wainna ilaihi rajiun. Nan kuwa nihal ta ɗin ga faɗan haka, can sai ta fara wani nishi, tana ƙiran sunan ashmir, kawai sai faya ta fashe, sai ga ɗa ya faɗo, aikuwa ashmir ya taro ɗan sa, yana kwalawa doctor's mata kira, dama can shi ya ƙore su, yace su zo su gyara masa matar sa da babyn sa, aikuwa sai ga su sun shigo da sauri suna yes sir, nan da nan suka fara gyara su, kawai sai su ka ga nihal tana wani yunkurin ashe yaya biyu ne acikin, na da nan suka karbi ɗayan haihuwar, da gudun su suka fito suna yiwa dr ashmir albishir, aikuwa sun sha tukuici don kuwa kyautar mota yayi wa kowaccen su, ƙirar kia K5 babbar mota ce aikuwa sunyi farin ciki sosai, kan kace me asibiti ya cika fal da yan uwa.

Bayan kwana biyu da haihuwar nihal, bayan an sallame ta daga asibiti, mum tace gidan ta za'a kawo nihal, wato government house, nan suka kwashi nihal da twins ɗin ta, duk mata ne, kuma sun ci sunan mummy's, sunan maman su ashmir, da maman su nihal, ana kiran su da suna "af'reen, da jasmin, nan kuwa aka cika gidan tab, rana bata ƙarya sai de uwar ɗiya taji kunya, domin kuwa yaune ranar suna, sunan daya tara dumbban mutane, rabo kuwa an sha rabo kala kala, har da su atamfofi chiganvi, da dai sauransu an sha shagali ba kaɗan ba, an ci an sha an watse lafiya. Sai da nihal tayi arba'in sannnan mum ta bari aka maida ita, amma fa sai da ta sha gyara, domin tun daga sudan mum tayi waya aka zo aka aka gyara ta na musamman sannan ta koma, a ranar da ta koma ashmir ji yayi kamar aranar aka ɗaura masu aure don farin ciki.

Bayan kwana biyu twins ne, a hannun baban su, sai wasa yake ma su, nihal ce ta miƙo masa wayar sa da yake ta ringing amma sabida ya shagala da wasa yaran shi bai ji ba, ya ɗaga cikin girmamawa, ya gaishe da daddy, bayan sun gama gaisawa ne, ya tambayi nihal da yara, sannan yace "dafatan kuna cikin koshin lafiya?" Ashmir ya amsa da "kowa lafiya daddy, sannan daddy ya fara yi mishi nasiha akan rashin zuwan sa aiki tun bayan da yayi aure, ya ɗaura da cewa "idan ma yanzu kana ganin ga yara, to ba mummyn ka ta samo maku me kula da su ba?" ashmir yace "eh daddy ta kawo wata dattijuwa" to ka gani pls son ka koma baƙin aikin ka, kasan cewa aikin ka na taimakon al'umma ne, yanzu nan da monday u should go back to ur duty right? Da sauri ashmir ya cewa daddy "yes dad, insha Allahu Rabbi I will do so, kuma nagode da tuna min abinda na manta, dama daɗin iyaye kenan, nagode Allah ya ƙara girma dad, daddy ya amsa da "Amin son, ka gaishe min da doughter ta, tare da yamma ta na," murmushi ashmir yayi sannan yace "zasu ji insha Allahu"
To bayan dad ya gama waya da ashmir ne sai mom take tambayar dad "wai da son kake ta waya ne?" Murmushi dad yayi sannan yace "eh wlh wannan lover boy ɗin ɗan naki ne wai dan anyi aure shikenan kuma sai a daina fita nema, ko dan yaga ya tara dukiya ne, to kuma duk yawan su, idan ba'a nema ai sai su ƙare ko?" Ya ƙarasa maganar yana kashe wa mum ido ɗaya, murmushi tayi sannan tace "hmm ina ruwan son, kasan shi bai iya son abu ba, tun yana yaro haka yake, amma kuma idan baya son abu an shiga uku, ko kallon arziki baya wa abun, to shi yasa ma nake masa uzuri." Dad ne yace "eh ai nasani dama kece ke ɗaure masa gindi ko?" murmushi mum tayi kawai bata ce komai ba, kamo ta dad yayi yana cewa zo nan wa na kama? Naga kwana biyun nan sai wani share ni kike ko? Ko dan kinga mun fara jikoki, to aikuwa kina azabtar dani dan ba haka kika sabar min ba, kuma yau sai nayi maganin ki, ya faɗa yana rungumo ta, ita dai mum kawai dariya take, to anan dai na jawo masu kofa, dan naga abun harda tsofaffi, lol.

Bayan shekara ɗaya da haihuwar nihal, afreen da jasmin sun yi matukar wayau, ga girma kamar ya'yan turawa, ga kyau, ɗaya tana kama da nihal, ɗaya tana kama da ashmir, kunga kuwa an haɗa kyau kam masha Allah, rayuwa suke yi mai cike da ban sha'awa da birgewa, ba'a taɓa jin kan su ba, suna kula da hakkin junan su, basa son bacin ran juna, shi yasa suke burge kowa a family, kowa sha'awar su yake, ana alfahari da wannan auren, ga arziki kam masha Allah sai abin da ya karu a gidan ashmir, domin itama nihal yanzu tana da kanfaninnuka, ta zama wata shahararriya mai kuɗi gata babbar lauyer mai zaman kanta, don yanzu ma bata zuwa office sai dai idan taga dama zata je tayi hanging wani case, shima talakawa take wa sabida taimakon su, ita da ashmir sun zama tamkar wasu taurari, abin sha'awa, daddyn su ashmir ya sauka a kujerar gwamna, yanzu na shugaban ƙasa yake nema, don haka shima doctor ashmir ya faɗa harkan siyasa, yanzu haka kujerar gwamna yake nema, kuma alhamdulillah anyi zaɓe an gama kowa ya samu abinda yake so, ashimir an zama his excellence doctor ashmir abdulkareem nasir gaya, fannin su noor da minal abun sai dai ace masha Allah, dan yanzu haka itama noor tana ɗauke da ƙaramin ciki, kuma yanzu haka mai martaba ya kusan mubaya'a, sabida karfi ya fara ja, ana shirye shiryen naɗa yarima adnan sarauta, gimbiya noor za'a koma sarauniya noor, shi kuwa doctor nasir, ya zama babban Kwamishina of healthcare na ƙasa baki ɗaya, hajiya minal an zama babban hajiya.
Amira da fayal ɗin ta suna zaman lafiya abin su, suna da ɗa ɗaya, itama islam suna zaune lafiya da Alh adam ɗin ta, ya haɗa su guri ɗaya, da matar sa, amma suna zaman lafiya abin su, sai dai ita Islam har yanzu bata samu rabo ba.


Ashmir ne ya riƙo hannun nihal da gudu yana cewa " shikenan sai a dinga wani share ni idan an yi baƙi, kina ganin baƙi ne dani, suna can office suna jira na, amma nace sai na gama da iyalina, dan haka ki saurare ni da kyau kinji ni ko," abi wlh ba wani gu zani ba, abin sha nake so na kawo maka," a'a na yafe zo nan, nan suka shige cikin bargo suna nishaɗantar da junan su, sai a nan nihal take ce mashi tana da wani ƙaramin cikin, aikuwa yayi matukar murna da samun wannan ƙaruwar, bayan sun kammala ne, nihal tayi firgigit zata mike kawai sai taga ya kuma riƙo ta, sannan yace "ina zaki ai bamu gama ba, second round zamu yi ko sai gurin ya warke, dariya suka kwashe da shi da tuna first night ɗin su, sannan ya kuma janyo ta suka lulluba da blanket, ashmir har an fara romancing kawai suka jiyo ihun su jasmin, nan kuwa suka sakko a ɗari, suka fito da gudu, suna fitowa suka gan su a parlon su na yara sunyi kaca kaca da parlon, tambayar su, suka shiga yi suna cewa "Meya faru kuka zabga uban ihu haka, "cewar nihal" aikuwa banza suka yi mata kamar basu ji ta ba, nan nihal ta fusa ta tana cewa "bada ku nake ba, kunyi mana shiru, shi ko ashmir tagumi yayi yana kallon su cike da so, sabida yasan yaran sun biyo su a miskilanci, musamman ma shi yaji labari, nan nihal ta fara shirin dukan su, ai da gudu suka buɗe baƙi suna cewa "daddy wai wannan ne teddyn ta, nata ba red bane cewar afreen" itama jasmin cewa tayi "ni wlh yanzu bana son red ɗin daddy, nafi son black ɗin, dariya ashmir yayi sannan yace wa nihal "kul kar na ƙara gani, wai zaki dake waɗannan yan tayin, To wlh kul." Sannan ya kallo su yana cewa "my kids kuje mummy ta daɗa shirya min ku na kai ku shopping mall ku ƙara kayan wasa, ko mummy ya fada yana kallon nihal" murmushi tayi mai sauti sannan tace "hmm baban kids a rage son yara fa, wata rana sai sun hana ka shiga lambun maman su, ko ka manta me ya faru ɗazu? Ta faɗa tana rungume afreen sannan shima ya haɗa su har jasmin ya rungumo haɗe da saka wani sabon dariya dukan su ma dariyar suke, yace "My beautiful families, Allah ya bar mu tare"



ALHMDULILLAHI BI NI'IMAT

Allah shine abun godiya daya bani ikon sauke wannan book ɗin lafiya, Allah yasa mu amfana da abun daya ƙunsa, kuskeren da nayi aciki, Allah ka yafe mana baki ɗaya, Allah ya bani ikon faɗakar da ku masoya na.



Ina godiya ga daukakin lovers ɗin wannan book ɗin, Allah ya bar kauna.



Kasancewar wannan book din na SOYAYYA ne, na sadaukar da shi ga mijina abin alfahari na.



Sai kun jini acikin sabon book ɗina mai suna RAYUWAR SALEEMA.




mr yusuf
❤️❤️❤️

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login